Showing 9001 words to 12000 words out of 72189 words

Chapter 4 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt

17 Mar 2026

30

gaskiya, yayi kyau sosai wallahi, nagode.

-To idan kika tashi kwanceshi, zan sake maki wanda yafi wannan.

-A'a gaskiya ba zan iya kara irin wannan zaman ba, ai sai duwawuna su fashe..

Dube dube Sarah take tana neman abinda zata jefi Jinah dashi, fahimtar abinda zata yi yasa Jinah tayi waje da gudu.

-Shakiyiya!
Sarah ta fada tana dariya.

Bayan wasu yan mintuna suna zaune cikin daki, suka ji Bukari yana ta kwada sallama. Sarah ce ta amsa sannan tace masa ya shigo.

-Wai kai Bukari, ba nasha fada maka idan kayi sallama biyu ta isa, sai ka jira a amsa ba?
Cewar Jinah.

-Babu banbanci idan biyu nayi ma tayi, idan kuma shida nayi ma tayi ko Tanti Sarah?
Bukari ya fada cikin muryarshi ta yarinta.

-Da gaskiyarka Bukari..
Sarah ta fada tana dariya, ita dai tana son Bukari, tana jinsa kamar danta. Bata samu sa'ar samun haihuwa ba gashi kuma ita mai son 'ya'ya ce. Sai dai ta dalilin Jinah da Bukari tana jinta tamkar Uwa kuma hakan yana mata dadi.

-Jinah! kitsonki yayi kyau!
Bukari ya fada yana kallon kitson Jinah.

-Hmm nagode, Sarah ce tayi min.
-Tanti Sarah kin iya kitso, fada mani kudinshi koda dubu dubu ne yanzu na biya..

Cewar Bukari, shi a dole dagaske yake, kallon juna matan suka yi. Barkoncin Bukari yasa yake da saurin shiga rai. Yaron yanada hankali da wayo, yana da cikin yaran kauyen masu zuwa school.

Kwada masa kira yaji ana yi, ya amsa.
-La'ilah, na manta! Tanti Sarah, Jinah mama tace na kirawoku kuci abinci.
Sannan ya juya ya fita da gudu.

-Duk wannan surutun da yake yi, ashe aikoshi aka yi kinji sai yanzu ya tuna.
Cewar Jinah tana mikewa.

Bayan sun ci abinci, kowa ya shige dakinsa, Jinah ta tarar da Lasaini dan uwan Sarah zaune tsakiyar gida. Yau tsawon kwanaki kenan tana son yi masa magana, sai dai bata samu dama ba dan bai cika zama gida ba.

-Ina wuni?
Ta fada, dago kai yayi ya kalleta, suka hada ido kafin ya amsa gaisuwarta.

-Zamu iya magana?

-Ina saurarenki.

Zaunawa tayi bisa benci dake kusa dashi.

-Magana ce nake son muyi akan Sarah.

Yamutsa fuska yayi kafin yace
-Kinga yarinya, ina mai baki shawara da kar ki shiga abinda ba ruwanki, dan baki san komai ba.

-Ta bani labarin komai.

-Wannan ba abinda ya dameki ba ne, dan haka ki fita daga wannan maganar kuma ki je ki kwanta dare yayi.

-Ba'a gyara wata matsalar da kunno kan wata matsalar.

Dakatar da ita yaso yi, amma ta rokeshi da ya saurareta.

-Yanzu kamar kai, idan rana tsaka aka ce ka rabu da matarka, zaka iya?... ko kuma idan aka ce ita ta barka, ya zaka ji?

Sunne kai Lasaini yayi alamar yana tunani.

-Lasaini, Sarah tana son wannan mutumin sosai, ta yanda lokaci daya a nuna mata wani aibu nashi ba zata yarda ba. Wani lokacin soyayya tana hana mu ganin aibun masoyi. Ka dan yi tunanin ace kai ne ita na wani dan lokaci kaji. Tana cutuwa da irin rashin ko in kula da kake yi mata, wanda har ta kasa boye hakan, batada iyaye, batada 'ya'ya, kai ne komai nata a halin yanzu. Har zuwa wane lokaci zaka bar cutar da ita? Har zuwa wane lokaci zaka dawo yayanta na da? 'yar uwarka ce fah, kuma wajibinka ne ka kula da ita.

Shiru Jinah tayi sannan ta mike da niyyar tafiya, itama tana jin tayi gangancin fadama mutumin da ya girme mata irin wadannan maganganun amma kuma tasan gaskiya ta fada.

-Jinah!
Kiran sunanta yayi, ta juyo tana fuskantarsa.

- Wai nace shekarunki nawa?

Idanu ta fiddo, tana mamakin me ya kawo kuma wannan tambayar?

-Kawai naji kamar mahaifiyata ce a gabana...

Ba tare da ta bashi amsa ba ta juya tana murmushi, cikin ziciyarta tace "Ashe dai maganganuna sunyi tasiri cikin dan karamin kanshi!

Ai kuwa, safiyar ranar, Lasaini yaje har gun kanwarsa ya nemi gafagarta. Sarah kasa gasgata hakan tayi, dan ranar tasha kuka, tayi ta yiwa Jinah buhu buhun godiya, gashi ta sanadinta ta shirya rashin jituwar dake tsakanin yan uwa.
Fita Jinah tayi, ta barsu. Ta nufi bakin kogi. Rage kayan jikinta tayi ta fada cikin kogin. Cen taji ance
-Kyanki ya kara fitowa, da kika yi kitso.

Sauri tayi ta fito, ta saka kayanta sanin ta gane mai muryar.

-Sarkin naci!
Ta fada kasa da murya.
-Sunana dai Dauda ba sarkin naci ba.
Ya fada yana mai nuna mata alamar ya ji abinda ta fada. Kunya ce ta kamata.

-A'a ai da kin cigaba da wankanki, kiyi kamar bana wajen.
Ya fada ganin ta juya zata tafi.

-A'a dama na kare.

-Toh, dan Allah kar ki tafi, daman yau tsawon kwanaki kenan nake ta son na ganki.

-Ni kuma?

-Eh

-Saboda me?

-Ai na fada maki, kin riga kin fada komata.

-Ni kuma ai na fada maka, bansan me kake nufi da hakan ba!

-Zo ki zauna dan Allah, sai na fada maki ma'anar hakan.

Haka dai ta hakura ganin magiyar da yake ta yi mata. Zaunawa suka yi bisa wan dutse.

-Toh ina sauraronka?

Cikin wata marainiyar murya ya fara fadin
-Jinaaaaah, tuuuuun lokaaacin...
Dakatar dashi tayi, tace
-Dauda bafa waka nace ka yimin ba.

-Jinah, bana ganin komai a duk lokacin da na ganki, bana tunanin komai a duk lokacin da nake tunaninki!

-Ni fah ban gane komai ba a cikin wannan waken naka, ka yimin gwari gwari.

-A takaice kin fada komata ne!

-Oh Allah, wai Dauda wannan kalamin naka ba fahimtarshi nake ba.

-Yi hakuri, to "ay gaba ni Jinah"

-Da Hausa!

-Ina sonki Jinah, ina matukar kaunarki, kuma ina son ki kasance matata.

Tuni ta dade da harbo jirginshi, kawai dai tana so taji daga bakinshi ne. Sai dai bata so yaji ba dadi, dan tasan amsar da zata bashi ba zata yi masa dadi ba. Itama tana son Dauda, gashi hadadde, sai dai ta bashi zuciyarta wannan ba mai yiyuwa bane.
Shuru dukansu suka yi, kafin ita ta mike da niyyar tafiya gida. jiri ne ya debeta ta koma ta zauna.

-Bana jin dadi Dauda!
Ta fada tana dafe kai.

-Sannu, me yake damunki? tashi muje na rakaki gida.

Mikewa tayi yana mata sannu, suka kama hanyar gida, sai dai ba wanda ke yiwa wani magana har suka karaso kofar gida.

-Yauwa ya isa nan, Dauda zaka iya tafiya nagode.
Ta fada tana rike da kanta.
-Kin tabbata?
Ya tambayeta da alamar damuwa a fuskarshi.
-Eh kar ka damu! nagode
Ta juya da niyyar shiga gida, ya kira sunanta
-Jinah!
Waiwayowa tayi, yace
-Ina jiran amsarki.
Bai jira jin me zata ce ba, ya juya ya tafi.

Jinah tarar da Sarah tayi ita kadai cikin daki, Sarah ta damu ganin halin da Jinah take ciki. Kwantar da ita Sarah tayi, ta kura mata ido kafin tace
-Jinah, amma kwanan nan kina jin tashin zuciya ko?

-Eh ina jin haka dan wani lokacin sai naji kamar nayi amai.

-Tinda kika zo gidan nan, ko kin taba ganin al'adarki?

-A'ah ban taba ba.

-Innalillahi, Jinah kar dai ciki ne da ke?


---------------------------------------
Bon, zan dakata nan a yau. Sai kuma zuwa gobe idan Allah ya kaimu.

Fatan dai wannan chapter ta burge ku? To ku fada min abinda kuke tunani, i want to know hahaha. 😂

Muje zuwa a wata sabuwar chapter, kuma kar ku manta da yin comment domin shi nafi bukata. 🤗

Watty : @El_Ashtar

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story

CHAPTER 4

Asubar fari na yi, Sarah da Jinah suka fito da shirin zuwa asibitin dake kauyen. Suna fitowa, suka ga Safiya ce matar Lasaini kadai ta tashi, sauran har yanzu bacci suke. Bakin murhu take tana kokarin kunna wutar dumama tuwan karin kumallo.

-"Mat arango Safiya?" Ina kwana Safiya?
Sarah da Jinah ne suka gaisheta da yaren zabarmanci, ko kuma dai nace Sarah, dan Jinah tana cikin tashin hankalin da magana ma wahala take mata.

-"Samaï day no. Mat ni kani bani?" Lafiya lau, an tashi lafiya?
Safiya ta amsa masu gaisuwar.

-"Samaï day no wallah." Lafiya lau wallahi.
Sarah ta fada kafin tace
-"Jinah sigama inga gahamo kani, aygo ga dum loktoru koira." Jinah bata jin dadi, shine zan raka asibiti.

-"Ayyah! Irkoy madi ase, ma konda aran bani." Ayyah! Allah ya koro sauki, sai kun dawo.

-"Aminna, kala tonton." Amin sai mun dawo.

Hanyar asibiti suka dauka. Jinah har yanzu shiru babu alamar magana, duk tsoro da fargaba sun mamayeta. Bayan yar doguwar tafiyar da suka yi suka karaso asibitin, ba wata babbar asibiti bace kasancewar kauyuka irin Mambila sun fi ganewa yin maganin gargajiya akan na bature. Bayan sun je sun ciri tikitin ganin doctor. Kusa da Jinah Sarah ta zauna, ita kuma sai ta dora kanta bisa kafafun Sarah, Hankalin Jinah a matukar tashe yake tun jiya da Sarah ta tambayeta ko ciki ne da ita. Lallai idan dai ya tabbata ciki ne da ita, ta shiga uku dan bata san waye uban yaron ba, shin ta yaya ta samu cikin kuma wanne lokaci ne hakan ta faru. Addu'a ta cigaba da yi Allah yasa ba ciki bane, duk da tasan yanayinta yana nuna mai alamar mai ciki ne. Juyar da kanta tayi jin hawaye na son zubo mata. Hankalinta ne ya kai kan maganganun wata mata da bata zata wuce shekaru 50 ba da wata matashiyar budurwa da ba zata wuce 17 ba duke tana rizgar kuka.

-Me kike so na fada ma ubanki? Kin bani kunya Nana!

-Wallahi Mama ki yarda da ni, ba abinda nayi!

-"Ah to Nudu gunde par magie?" Ah kina nufin a ruwa kika shashi ko me? Kin bani kunya Nana, yanzu da wane ido zan kalli mutanen kauyen nan? Shikenan kin ja mutanen kauye su zageni suce na sakeki kin je kin yi ciki. To sai ki sani inda dare yayi maki dan yau kam ba dai a gidana ba, ni kinga tafiyata!

Juyawa matar tayi ta tafi cike da damuwa, ta bar yarinyar durkushe tana kuka. Mutane sai kallonta suke amma ita ko a jikinta.

-Bari naje na samo mana abin kari.
Cewar Sarah tana mikewa, gyada mata kai kawai Jinah tayi. Bayan tafiyar Sarah, Jinah matsawa tayi kusan yarinyar dake kuka.

-Yi shiru ki daina kuka, kar ki sawa kanki wani ciwon.
Jinah ta fada cikin sigar lallashi, ba tare da ta dago kai taga mai lallashinta ba, ta fara ba Jinah labarin abinda ya faru. Haka na kasancewa ga kowa, idan muna cikin damuwa mu kan so mu bayyanawa wani ita ko da ba zai iya yi mana maganinta ba kawai dai hakan nasa muji damuwar ta ragu.

-Na rantse da Allah ban yi komai ba, ni ban ma taba sanin yaya gaban namiji yake ba indai ba na yaro karami ba, ni ko saurayi banidashi, ba abinda na sani in ba karatu ba, ba anan kauyen nake ba, ina karatu ne a Niamey (babban birnin kasar Nijar). Nazo nan hutu ne, gashi yanzu wai nice da ciki, to wa yayi min shi?

Yanda take bada labarin da yanayinta zai tabbatar maka ita iya gaskiyarta take fada, hakan ya zama ruwan dare a kauyuka ba dama yarinya tazo daga birni, abin kamar maita. Haka saurayi zai je ma yarinya da sigar yana sonta, daga nan zai yaudareta, yayi mata ciki, in ma da saninta, ko kuma yayi mata asiri, ko kuma ya zuba mata wani abu a abin sha ta sha, daga nan ya gudu ya barta da taraddadi. Shikenan fa rayuwar yarinya ta lalace, haka zaka ga wasu sun zama karuwai, wasu su kashe kansu, wasu kuma ana samun maza masu tawakkali da dogon ilimi su auresu. Allah ya kyauta!

Hankalin Jinah kara tashi yayi jin labarin yarinyar gashi yana kamanceceniya da nata, sai dai ita tana ganin Sarah bata koreta bane, ganin ba a tabbatar da nata cikin ba.

Lokacin da layi yazo kanta, lokacin yarinya mai kuka ta tafi, Sarah ta dawo har sun karya. Wani bugawa zuciyar Jinah ke yi da sauri sauri dan da tafiyar hawainiya ta shiga ofishin doctor. Yana zaune yana duba wasu takardu, ba tare da ya dago kai ba yayi masu izini da zasu zauna, tareda cewa
-Ku dan jira yanzu abokin aikina yazo ya duba marar lafiyar.

Ganin har lokaci ya dan ja, abokin aikin nasa bai zo ba, ya dago kai yace
-Tinda har yanzu bai zo ba, bari ni na dubaku. Yanzu fada min me yake damunki?
Ya fada yana kallon agogo.

Sarah tace
-Kwanan nan ne take fama da zazzabi da tashin zuciya, shine muke son sanin ko...

-Ko me?

-Ina son sanin inada ciki ko a'a!
Jinah ta fada dan ita ta matsu taji wanne hali take ciki.

Bayan yan gwaje-gwaje da doctor yayi, ya tabbatar masu da Jinah tana da ciki. Doctor ya basu shawarar suna iya sake zuwa wani wajen ayi masu gwajin dan kara tabbatarwa sai dai ita Jinah batada wannan ra'ayin. Fita tayi daga asibitin da dan gudunta Sarah ta bita a baya. Sai dai Sarah bata yi nasarar cimmata ba sai da suka kai gida.

-Kalleni nan Jinah.
Sarah ta fada, cusa kanta tayi cikin katifa tana kuka. Ba wai tana kuka bane dan tanada ciki, a'a tunawa ne tayi matar nan ta dazu a asibiti dake hantarar yarta dan tayi ciki. Gani take itama haka Sarah zata yi mata, tasan itama haka mutanen garin zasu rinka nunenta suna zaginta.

-Ki daina kuka Jinah, nasan ke ba irin wannan yaran bane masu kai kansu ga maza.

-Kinada tabbacin haka Sarah? Idan fa saboda hakan ne aka koreni daga gida?
Jinah ta fada tana fito da kanta daga cikin katifa.

-Me kike cewa haka? kika sani ko kinada aure ne?

-Ki duba fa samari nawa suka zo neman aurena, ai ba wanda aka taba fadawa inada aure. To yanzu kina tunanin akwai wanda zai yarda idan aka ce na taba aure ko inada aure? Yanzu wane kallo kike tunanin zasu yi maki keda kika bani mafaka? Ina ga zan yi tafiyata kafin mutanen kauyen nan su gane har na ja maki abin kunya...

Kuka ne yaci karfinta.

-Eh na sani dole zasu yi ta fada, dan kina karkashin kulawata ne, kuma hakan ba zai yimin dadi ba. Amma hakan kasheni zai yi? ko kwantar dani zai yi rashin lafiya? A'a ba fah abinda zai sameni. dan haka ki daina wannan kukan ki natsu muyi tunanin samun mafita.

Mikewa Jinah tayi tana goge fuskarta tace zata je bakin kogi.

Sarah bata hanata ba don tana ganin wata kila hakan zai ragewa Jinar damuwa. Da zuwanta bakin kogi ta zauna ta hade kai da gwiwa. Zuwa cen taji kamar kana kallonta, juyawa tayi taga Dauda ne, karasowa yayi ya zauna gefenta.

-Yaya kike?

-Lafiya lau.
Ta bashi amsa a takaice.
-Anya dai?
Ya fada yana kare mata kallo, dan ya hangi damuwa a tattare da ita.

-Na fada maka lafiya nake.
Ta fada a dan tsawace.

Duk da hakan bai hakura ba ya kara tambayarta.
-Fada mun me yake damunki dan Allah?

-Kaga ko na fada maka ba abinda zaka iya yi a kai, kuma wai wane sani ne nayi maka da har zan fada maka damuwata? Dan haka ka rabu dani.

Duk wannan maganganun da ta fada mashi, basu hanashi yin dariya ba.

-Abin dariya ma ya baka kenan? Dan Allah ka rabu dani.

-Fushi baya maki kyau, kanki sai ya koma wani kala abin dariya.
Ya fada yana dariya. Ganin so yake ya kara bata mata rai yasa ta mike da niyyar tafiya.

Da sauri yace
-Yi hakuri dawo ki zauna dan Allah, duk da bansan me yake damunki ba, amma na damu ganinki cikin wannan hali.

Dawowa tayi ta zauna, sannan ta bashi hakuri akan daga masa murya da tayi dazun. Ya nuna mata ba komai.

Cewa yayi ta fada masa abinda ke damunta, amma taki. Rokonta yayi ta yi akan sai ta fada mashi, ganin nacin da yake mata, kuma ita kanta taji tana son ta bashi labarinta. Dan yan kwanakin da suka yi a tare ta fahimci Dauda mutum ne mai tausayi da kuma barkwanci. Sai dai tana tsoron idan yaji tanada ciki ya kasa fahimtarta. Daga karshe dai yanke sharawar ta fada masa tayi, bayan ta gama bashi labarin yace
-Yanzu kina nufin babu wani abu da kike iya tunawa na rayuwarki ta baya?

-Eh, abinda kawai nake tunawa ranar da na bude ido na ganni a wannan kauyen sai sunana. Kuma babban tashin hankalin shine....

-Ina jinki meye?

-Inada ciki!

Da sauri Dauda ya mike, cikin tashin hankali yace
-Ciki?

Sunne kai Jinah tayi tana hawaye sannan tace
-Wallahi bansan ya aka yi hakan ta faru ba, inada aure ne ko kuwa, ban sani ba? Nasan mutane zasu ta min kallon yar iska, ita kuma Sarah suyi ta nunata. Na jawo mata abin kunya.

Hada kai da gwiwa tayi ta cigaba da rera kuka. Shi kuwa Dauda safa da marwa ya fara a wurin kafin yace
-Ni nasan yanda za'ayi!
Da sauri Jinah ta dago tace
-Ta yaya?

-Abu mai sauki, na aureki kinga mutane zasu yi tunanin dan nawa ne.

Duk da hawayen dake fuskar Jinah hakan bai hanata kyalkyata dariya ba tana yi tana cewa
-Daman na dade ina wannan tunanin, ba isashiyar lafiya gareka ba...

-Allah Jinah da gaske nake!

-Gaskiya bakada hankali, ni kaga tafiyata.

-Ki dakata Jinah, Allah da gaske nake, hakan ita kadai ce mafita.

-Kaga, bamu san juna ba kace kana sona, haka ka cigaba da bibiyata tin daga ranar da wannan abun ya faru, a duk lokacin da nazo cikin jeji ko bakin kogi sai na tarar da kai. Yanzu kuma nace maka inada ciki ba tareda nasan ta yaya na sameshi ba, kai kace zaka aureni. Fada mani wane mai hankali ne zai yin irin wannan?

-Kinada gaskiya Jinah, amma kin manta da cewa idan mutum ya kamu da soyayya, zaucewa yake yi. Saboda daga ranar ba kwalwa bace ke jagorantarsa, Zuciyarsa ce, zuciya Jinah!

-A dauka na amince, idan kuma aka je inada aure, kuma na tuna komai?

-Daga ranar babu aurenmu, na amince zan barki ki tafi.

-Ni fah bana sonka Dauda!

Duk da yaji maganar tata kamar saukar aradu, hakan bai hanashi cijewa yayi dariya ba.

-Kai abin dariya ma ya baka kenan?

-Ina dariya ne, dan zan aureki dan ina sonki duk da ke baki sona, amma zan zauna zaman jiran ranar da kema zaki bude baki kice kina sona.

-Gaskiya ba zan iya ba Dauda, kayi hakuri.
Ta juya ta tafi, ta barshi a tsaye kamar an dasashi, shi kanshi yayi mamakin kalamanta sai dai wannan itace mafitar da zai iya samun Jinah, don har cikin zuciyarshi yana sonta. Tun jiya da ya fada mata yana sonta, bai ga alamar amincewa a idonta ba, yasan taki fada masa ne dan kar yaji ba dadi.
Yanzu kuma yana cikin farin ciki ganin zai aureta, sai dai sam bai ji dadin jin tanada ciki ba. Amma yana tunanin komai zai zama daidai da ya aureta.

Jinah karasawa tayi gida da kuka, ita dai bata san me yasa rayuwa tazo mata a haka ba, duk da ta fara sabawa da cutar mantau din da yake damunta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login