Showing 30001 words to 33000 words out of 72189 words
Chapter 11 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt
yi nisa ba. Ke Jinah lallabi Ayu ni zan fita waje ko zan ganta.
Jinah tayi tayi amma Ayu yaki yin shuru, kokowa ma yake yana son uwar ta saukeshi. Abun fa kara ta'azzara yayi lokacin Dauda ya dawo ba tare da Aya ba. Zuciyar Jinah bugawa take da sauri ta yanda tayi tunanin ko fasa kirjinta zata yi ta fito.
(.....)
A waje kuwa, wani masifaffen fada ya turnuke. Fally ji yayi ya fara gajiya, ba zan bari ya tafi da 'yata ba, shine abinda yake ta maimatawa. A takaice dai, aljanun sun gano inda suke, shine daya daga cikin aljanun yake so ko ta yaya ya dauke Aya, kuma yayi nasarar dauketa har ma yayi nisa da gida da ita. Sedai Fally ya tareshi, sai gwabza fada suke tamkar wasu mayunwatan zakuna. Bayan wani dan lokaci, Fally yayi nasara akan aljanin da karfinsa ya kare da kyar ya iya guduwa yana fadar :
-Zan dawo, kuma bani daya ba, ka san da wannan!
A wata bishiya Fally ya zauna yana maida numfashi, Aya kusa dashi, tana masa wani irin kallo. Tabbas dole ya sake daura damarar kare ya'yansa daga waddanan miyagu. Da wannan tunanin ya dauki Aya ya kaita har kofar gida kuma daidai da fitowar Sarah da Abdul cike da mamaki suka ga Aya a waje ita daya. Sarah ta dauketa suka koma cikin gida. Suna shiga Jinah tazo da gudunta, bata tsaya amsa tambayar da Sarah da Abdul ke yi mata ba kan ya akayi Aya ta fita waje ba ta amshe yarta tareda kankameta. Kuma a take Ayu ya daina kukan da yake yi.
-Wai mun gode Allah, _Cewar Dauda tareda ajiyar zuciya._ Shikenan daina kukan tunda an ganta.
Da Nafisa yake da ke ta rizgar kuka tana tunanin laifinta ne. Yayanta ya matso kusa da ita tare da rungumeta yana lallashinta. Shi da Sarah basa bukatar wani dogon bayani akan me yakai Aya a waje, komai ya wuce tunda dai gashi an ganta.
Washe gari, ranar daurin aure, ba tare da wani shagali ba aka daura aure a masallaci kamar yanda Jinah ta bukata. Duk da ba wani jagali ba aka yi amma kowa gidan cikin farin ciki yake. A marecen ranar ma basu yi bacci ba. Suna ta hirar duniya. Abdul da Nafi har sun saba da zaman gidan, duk da har yanzu zaman jiran mahaifinsu suke domin su koma cen asalin gidansu...
-Sarah, wata alfarma nake son ki yimin.
Cewar Dauda cikin yanayin dagaske yake. Shuru kowa yayi yana sauraron me zai ce.
-Ina sauraronka Dauda.
-Kamar yadda kuka sani, yau Jinah ta zama matata, tawa, toh shine...
-Ahan muna sauraronka.
-Shine... Nake son ki dauki yaran, ni kuma sai na dauki matata.
Dariya Abdul yayi, su kuma matan rike baki suka yi suna mamakin Dauda...
-Bakada dama Dauda, toh shikenan, dare yayi yanzu ni zan je in kwanta. Sai da safenku.
-Toh yara kuma ku tashi dare yayi aje a kwanta.
Dauda ke fadawa Abdul da Nafi yana dariya. Seda suka dan taba raha kafin su je su kwanta. Ya rage sai amarya da Ango.
-Kinsan wani abu Jinah, har yanzu na kasa gasgata yau kece a matsayin matata, komai ina jinsa kamar a mafarki. Yanzu da nake a tare dake sai nake ji kamar babu wani abu na bakin ciki da ya faru dani a baya. Kin baiwa rayuwata ma'ana Jinah. Nayi maki alkawarin har indai ina raye, zaki kasance cikin farin ciki.
Murmushi Jinah, tayi sosai kalamansa suka tabata.
-Kayi min abinda ba zan taba mantawa ba Dauda, kayi abinda ba kowanne namiji zai iya yi ba. Ba zan boye maka ba, a duk lokacin da ka furta min kalmar "Ina sonki" na kanji ba zan iya baka amsa ba, amma kuma duk da haka bani nadamar aurenka, ina fatan wata rana na soka, son da yafi kalmar so.
Hannu Dauda ya kai kan fuskarta ya janye gashin kanta da ya zubo a fuskarta zuwa bayan kunnenta sannan ya kai mata lafiyayyen kiss a kumatu. Mikewa yayi tsaye sannan ya mika mata hannu ta kama ta tashi tsaye. A haka har suka je daki. Ba tare da bata lokaci ba, ya fara kwabe mata kaya, zafin da a duk lokacin da ya rabeta yake ji, yanzun ma shi yake ji, sedai wannan karon zafin yafi na ko yaushe, hakan bai dakatar dashi ba domin shima sha'awar da yake tattare da ita mai karfi ce. karfi biyu ya hadu a lokaci daya, sai duka suka bayar da masifaffen zafin da yafi wuta. Da taimakon dan hasken dakin da kuma na farin wata, Dauda ke karewa kyakyawar surar Jinah kallo, zafin jikinsa karuwa yayi, idanunsa suka kafe, ya fadi gefenta matacce ko sumamme...!
Da alama shi Dauda aljanin bai bari yaje ko'ina ba lol. π
------------------------------
Salam, fatan kuna nan lafiya? Kuma ina fata zaku ji dadin wannan chapter kuma ta fanshe fushin da kuke yi dani na rashin posting da wuri? π
Ina jiran jin ra'ayinku π€
Mu hadu a wata chapter bayan sallah idan Allah ya kaimu. π€
Β©El_Ashtar
π JINAH (Matar Aljani)π
by Malik al-Ashtar βοΈ
On wattpad π https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New β€οΈ Story
CHAPTER 13
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).π¦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the restπ¦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
-'Ya'ya nawa kike son kara samu?
Dauda ya tambayeta.
-Ban sani ba, ta fada tare da daga kafada. Ko nawa na samu. Hudu, biyar, shidda... Duk ina so.
-Amsa mai kyau. To kuwa yau zaki samu!
-Marar kunya!
Jinah ta fada tana boye fuskarta alamar kunya.
-Me? Toh ni me nace?
Ya fada da yanayin shi ba ruwansa.
-Zamu kasance cikin farin ciki a tare, zo ki rungume mijinki abar kaunata.
Ya fada yana bude mata hannuwansa. Bata jira komai, ta fada jikinsa kamar wata karamar yarinya.
-Ina tunanin fa na fara sonka.
Ta fada kamar daga sama.
-Jinah! Zaki iya maimatawa dan Allah?
-Ina sonka Dauda.
-Wow zuciyata cike da guguwar farin ciki, naji dadin jin haka.
Rufe ido Jinah tayi cike da jin dadin rungumar mijinta, sedai dan lokaci kadan komai ya tsaya, bude ido tayi ta ganta ita kadai.
-Dauda? Ina kake?
Tafiya take tana kiran sunan Dauda ba tare da tasan inda ta nufa ba. Jiri ta fara ji yana daukanta kafin ta fadi. Lokacin da ta bude ido, a wannan karon, cikin dakinta a bisa gadonta ta tsinci kanta. Dauda kwance a gefe. Tunawa tayi lokaci na karshe da take cikin dakin, mijinta ya fadi gefe, tayi tayi ta tasheshi amma bai tashi ba, ganin haka yasa ta juya gefe dayan gadon ta kwanta tareda rufe ido. Wanne al'amari ke shirin faruwa, daman maganar da tayi da Dauda, mafarki ne ko me? Kara rufe ido tayi, Dauda ta gani, amma wannan karon nesa da ita yake yana mata murmushi. Da gudunta ta nufeshi, amma ta kasa cimmasa, kara gudu take don ganin taje gunsa amma kuma kamar kara mata nisa yake, tsayawa tayi tana sauke ajiyar zuciya, suma ta kuma yi a karo na biyu tana farkawa ta ganta bisa gadonta, Dauda kwance a gefe.
Wannan karon saukowa tayi daga kan gadon daidai ladani ya fara kiran sallah. Fitowa tayi waje ta tarar da Sarah da Abdul da kuma Nafi suna alwala domin yin sallar asuba, itama alwalar tayi.
-Ina Dauda?
Sarah ta tambayeta.
-Yana zuwa.
Jinah ta bata amsa a takaice.
Shimfida babbar tabarma Sarah tayi, kowannensu yayi raka'a biyu nafila kafin Abdul yayi limanci suyi farillah. Suna idawa dukansu shiga tambayar Jinah dalilin da yasa mijinta bai fito yayi sallah a tare dasu ba. Wannan karon shuru tayi, bata amsa ba, shurun da ya dau hankalin su Sarah.
Lokacin da wani abu ya zamar mamu kamar almara, lokacin da wani abu ya girgiza mu sosai, lokacin da muke tunanin wani abu na cutar damu, cutarwa mai tsanani, mun fi son muyi kokarin manta abun, muyi kamar abun bai taba faruwa ba. Sedai hakan ba wai zai sa mu manta da abun baki daya ba, a kullum yana dunkule a cikin zuciyarmu.
Lokacin da Jinah taga Sarah ta fito daga dakinta baki toshe da hannu, nan ta kara gasgata mutuwar Dauda, hawaye ne suka fara ambaliya a fuskarta kafin ta fashe da kuka mai ban tausayi. Abdul da Nafisa tambayar Sarah abinda ke faruwa suke domin su har yanzu sun kasa fahimtar komai, ganin Sarah batada niyyar basu amsa suma suka kutsa kai cikin dakin Jinah, anan suka samu amsar tambayoyinsu.
Abdul kasa tsayuwa yayi, yayi dishen a kasa. Ita kuma Nafi da saurin kuka, ta fara kamar an aikota. Kwanakin da suka yi da Dauda ba masu yawa bane, amma dattakonsa da kuma barkwancinsa yasa yake da shiga rai, suke jin tamkar shekaru masu yawa suka yi da saninsa. Dukansu cikin tashin hankali suke, ganin bai fi awanni masu yawa ba da suke tare dashi anata wasa da dariya. Yaya hakan zata kasance ace Dauda ya mutu? Tambayar da suke ta yiwa kansu kenan.
Sedai wannan ba wani abun mamaki bane, domin mutuwa bata bukatar shiri, tana zuwa ne ba tare da sallama ba, lokacin da taso, inda taso a kuma yanda taso.
Sedai wannan mutuwar ta Dauda, ba ta ajali ba ce, a yanzu Jinah ta tabbatar akwai wani babban al'amari dake tattare da ita, ta tabbata Dauda ya mutu ne ta sanadinta. Bayan Idrisa, Isa yanzu kuma Dauda, yanzu kam ta gama tabbatar da laifinta a ciki. "Dauda yayi min halacci a rayuwa, ni kuma me nayi, na kasheshi." Ta fada a hankali tana cigaba da kuka. Nan fah ta rantse kan ba zata kara barin wani namiji ya rabeta ba, bare kuma ya kusanceta.
-Jinah!
Firgigit tayi ta dawo hayyacinta jin Sarah ta kira sunanta. Tsabar dogon tunanin da ta shiga, bata san lokacin da har Sarah ta shiga daki ta canja kaya ba.
-Zan je na sanar da yan uwansa, dan Allah ki daina kukan nan, ba yanda muka iya lokacinsa ne yayi.
Sarah tace mata cikin Sanyanyar murya da tausayawa.
-Ba zaki gane ba Sarah, nice..lai.. laifina ne.
Jinah ta fada tana sarkewa saboda kuka.
-Me kike cewa ne? Daina wannan shashancin, tashi kije ki duba ya'yanki, kila ma sun tashi daga bacci, ni na tafi.
Kallon Sarah da ta fara nisa take cike da tausayinta, tasan ba abu bane mai sauki kai irin wannan labarin ga dangin Dauda. Ji tayi an dafata, daga kai tayi taga Nafisa ce.
-Kiyi hakuri. Cewar Nafisa. Addu'a kawai zamu yi masa, Allah yasa aljanna ce makomarsa.
Rungumeta Jinah tayi, bayan wani dan lokaci suka saki juna, Jinah ta nufi daki. Tarar da yan tagwaye tayi, cike da mamaki zaune kan gado. Yanzu har sun saba idan suka tashi basu yin wata hayaniya. Kamar sunji halin da mahaifiyarsu take ciki, zaunawa tayi itama kan gadon, rarrafowa suka yi tareda rungumeta kamar zasu koma cikinta, suka yi kamar ba zasu saketa ba. Da mamaki, Jinah taji damuwarta na raguwa. Haka suka kasance kusan mintuna 30 kafin Abdul da Nafi su kwankwasa kofa a hankali, sai a lokacin tagwayen suka saketa.
-Ku shigo! Ta fada.
Shigowa suka yi, sedai babu wanda yayi magana. Fita Nafisa tayi da yaran sannan ta maidosu bayan tayi masu wanka tare da sanya masu kaya. Dan uwanta da Jinah suna zaune kan gado kowane yayi shuru, ya zurfafa cikin tunani. Sai zuwan Sarah sannan suka samu damar yin magana.
-Kinyi saurin dawowa, Jinah ta fara fada.
-Eh na samu dan acaba ne.
-Ya suka ji labarin mutuwar? Wayyo Allah nasan mahaifiyarsa zata shiga cikin tashin hankalin jin labarin mutuwar danta mafi soyuwa a gareta. Yana yawan bani labarin irin son da mahaifiyarsa take masa da kuma irin shirmen da yake yi mata, duk da ya girma bai bar kwana a dakinta ba har sai da muka yi aure, ya fada min shine abokin hirarta da kuma na rakiyarta idan zata je wani kauyen, mahaifiyarsa ita ce komai garesa...
Jinah ta fada murmushi da kuma ambaliyar hawaye a fuskarta.
-Eh, lokacin da taji labarin, halin da ta shiga ya tabani sosai, kasa jure kallonta nayi.
Hankalin Jinah kara tashi, ta fashe da kuka tareda tashi da gudu zuwa tsakar gida tana kuka, hanyar dakinta ta nufa da niyyar zuwa ta tashe da Dauda, sai kuma ta tsaya cak sakamakon tunawa da tayi cewa idan mutum ya mutu, ya tafi kenan baya dawowa. Zaunawa tayi kan wani benci ta cigaba da rera kukanta.
-Dan Allah Jinah ki dakata da kukan nan, kar ki jawa kanki wani ciwo, kukan da kike ba abinda zai anfanar. Cewar Abdul cikin sigar lallashi.
Tashi tayi ta nufi hanyar fita daga gidan, tana bude murfin kofar kuma sai ta tsaya.
-Ina zaki je?
Abdul ne ke tambayarta.
Bata bashi amsa ba ta juya da niyyar fita.
-Gata nan! gata nan! ita ce mayya mai cin kurwar maza.
Kafin ta fahimci meke faruwa, ta jita sheme a kasa, lafiyayyun mari biyu suka biyo baya, sannan aka rufeta da duka da itace. Cikin tashin hankalin ne ta fahimci wasu daga cikin yan uwan Dauda da kuma Auntynshi cikin masu dukanta. Bata tsaya tantance sauran matan ba, ta boye fuskarta kar suyi mata lahani. Da gudu Abdul, Sarah da kuma Nafisa suka zo domin kawo mata dauki. Sedai matan sunada yawa. Shi Abdul, nasarar kwace itacen hannun matan yayi, su kuwa basu hakura ba suka koma dukanta da hannuwa.
-Ku kyalesu, ku kyalesu su kasheni, ni ce, laifina ne, ni na kasheshi. Jinah take ta fada da shakakkiyar muryarta alhali kuwa azaba take ta ci. Jinah bata ga laifin matan ba, ita tana ganin ta cancanci wannan hukuncin, da son samu ne su kasheta, domin ita ce silar mutuwar Dauda.
Matan taji sun daina dukanta sakamakon suma da suka ji ana dukansu da itace, har da karin yakushi da cizo, alhali su basa ganin mai aikin.
-Wayyoh Allah, mayya ce da gaske! Gashi ta fara cin naman jikinmu alhali kwance take kasa.
-Wayyoh dan Allah kiyi mana rai!
-Bayan kin kashe yan uwanmu, garemu zaki dawo...
Ihu suke suna sambatu tsabar azabar da suke ji, ganin ba sarki sai Allah kowaccensu ta ranci na kare su kuwa su Sarah suka yo kan Jinah tareda taimaka mata zuwa dakinta. Sam matan basu ji tausayinta ba domin ta bugu sosai. Kuka kawai Sarah ke yi tun lokacin da matan suka fara dukan Jinah.
-Kamata yayi mu kaita asibiti, tsinannun mata! Idan da ba mata bane, na rantse sai sun gane kurensu. Wannan ai dabbanci ne!
Ran Abdul ya baci sosai ganin aika-aikar da matan suka yiwa Jinah.
-Gaskiya wannan ba mutane bane, wannan rashin imanin har ina???
Nafisa ta fada, cike da tausayawa Jinah.
-Zan je na nemo amalanke domin kaita asibiti.
Tagwaye sai kuka suke, farko dai suna kukan halin da mahaifiyarsu ke ciki sannan suna ganin hukuncin da suka yiwa matan bai isa ba. Eh sune wanda suka hukunta matan ta hanyar yakushi da cizo da kuma taimakon mahaifinsu da yayi ta dukan matan da itace. Fally yayi takaicin rashin zuwansa da wuri, gashi duk sun illata masa Jinah. lokacin da yaji mutuwar Dauda, ji yayi kamar yayi ta tikar rawa har sai ya gaji duk da hakan keta ce, soyayyarsa ga Jinah takai matsayin da babu ruwansa da komai zai faru. Sedai Farin cikinsa gushewa yayi lokacin da ya tarar da matan nan sunan dukan abar kaunarsa da kuma irin wahalar da take sha.
Hakane, idan muna yiwa mutum so na gaskiya, ba zamu iya kasancewa cikin farin ciki ba alhali shi yana cikin bakin ciki.
Kasa jurewa Fally yayi ganin Jinah har ta fara kukan azabar da matan ke gana mata, cikin jeji ya shiga ya karyo wani lafiyayyen reshen wata bishiya, ya dawo yayi ta dukan matan dake dukar masa mata.
Lokacin da Abdul ya tafi neman amalanke, Fally ya shigo dakin ba wanda ke ganinsa sai yan tagwaye, da karfin siddabarunsa ya warkar da duk ciwon dake jikin Jinah.
-Yauwa ku taimaka ku fiddota ga amalanken nan na samo.
Cewar Abdul da ya shigo a hargitse cikin dakin. Sarah, dake zaune a bakin gado, ta dora goshinta jikin gadon, hannunta cikin na Jinah, tana kuka a hankali, ta dago da sauri tare da mikewa. Nafisa dake zaune kan tabarma ta mike itama. Nufo Jinah suka yi da niyyar dagata, turjewa suka yi, suna kallon kallo. Sarah ce tayi karfin halin duduba jikin Jinah, hannu, kafafuwa, gadon bayanta amma babu ko alamar ciwo. Jinah bata ma san ana yi ba, wani nauyayyen bacci take abunta. Hannu Abdul ya kai kan hancin Jinah domin tabbatar ko dai mutuwa ce tayi shi yasa raunukan suka bace, sedai Jinah da ranta cikin koshin lafiya.
-Assalamu alaikum!
Suka ji ana kwada sallama a waje, fita Sarah tayi ta tarar da wasu maza, ta gane wasu daga ciki yan uwan Dauda ne, sun zo daukan gawar Dauda ne. Sarah ta nuna masu suka dauka suka tafi.
-Wannan ba mai yiyuwa ba!
Cewar Abdul.
-Ko dai mafarki muke?
Cewar Nafisa.
-Mu fita mu barta tayi bacci.
Cewar Sarah.
(....)
-A ina zamu samu bayanin abinda muka gani?
Nafisa ta tambayi dan uwanta lokacin da Sarah ta tafi kasuwa, daga su sai yan tagwaye.
-Ni kaina ban sani ba, domin komai ina ganinsa ne kamar almara.
-Kuma ka duba matan nan da aka yita duka alhali ba'a ganin mai dukan nasu. To ko dai da gaske Jinah...
-A'a wannan ma ba gaskiya bane, kawai dai akwai boyayyen al'amarin dake faruwa.
Haka suka zauna cikin wannan tunani har Sarah ta dawo daga kasuwa. shiga tayi kitchen ta gyara abincin da ta siyo kasuwa domin tashin hankalin da take ciki bata ji zata iya dora girki ba, Shi ma domin su Abdul ta siyo.
Haka suka zauna gidan shuru kowa cikin taraddadin abinda ya faru har zuwa lokacin da ihun Jinah ya dawo da su hayyacinsu.
-Ina suke? Sarah suna ina?
Jinah ta fada lokacin da Sarah ta kunno kai dakin, Abdul da yar uwarshi a bayanta kowanne rike da yaro a hannu.
-Me kike cewa ne Jinah?
-Raunukana, radadin da nake ji, me yasa bana jin komai yanzu? Bai dace hakan ya kasance ba.
-Kwantar da hankalinki Jinah!
-A'a a'a, na cancanci wannan ciwon, me yasa duka suka bace? Ina suka yi ne?
Duk ta hargitse, ta fara fita hayyacinta, ta zama abar tausayi. Kara takurewa tayi cen karshen gadon tareda hade kai da gwiwa sannan ta hana kowa ya kusanto inda take, hatta yaranta dake ta kuka taki kulasu. Sarah ta rasa me zata yi, fita tayi daga dakin ta nufi kitchen ta zauna kan kujera ta shiga rera kuka mai ciwo. Duk wadannan abubuwa dake faruwa sun zo sun cunkushe mata, ga kuma halin da Jinah take ciki, rashin sanin abinda zata yi ne ya