Showing 54001 words to 57000 words out of 72189 words

Chapter 19 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt

17 Mar 2026

51

da ya shiga.

Yanzu ba wai Aya bace kadai kwance da alamun babu rai, har da Ayu. Sai kuma Jinah da ta fara wani abu kamar zautatta. Nan fa, shi kanshi ya kasa fahimta.

--------------------------------------

G day readers, ina fata yanzu masu tambayar : "Ta yaya suka farfado ba tare da Aya ta samu cikon abu na uku ba?" da kuma "Wanne irin laifi ne Fally ya yiwa Jinah?" sun samu amsoshinsu?

Ganin comments dinku, ke sa na gane ko labarin yana shiga...😊

Β©Al_Ashtar


πŸ’ž JINAH (Matar Aljani)πŸ’ž
by Malik al-Ashtar βœ’οΈ

On wattpad πŸ‘‰ https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❀️ Story

CHAPTER 23

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).πŸ’¦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the restπŸ’¦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Fally ganin duka 'ya'yanshi kwance ba a hayyacinsu ba, ji yayi kasa ta kasa daukanshi, ya kasa yin numfashi da kyau, iskar shaka na neman ta gagareshi. Ya amince da wadda sam bai kamata ya yarda da ita ba. A cikin ransa yace ta yaya na yarda da wannan matar, matar da ita tayi sanadin mutuwar mahaifiyata. A yanzu ya gane irin kuskuren da ya tabka.

A daidai lokacin ne suka dunguma zuwa asibitin kauyen, Jinah bata daina kuka ba, duk tabi ta firgice, suna zuwa likitoci suka sanar dasu yaran suna numfashi.

Kallon Fally Jinah tayi anan ta tuna da hakurin da yake bata dazu.

-Fally me ka aikata ne?

Ta tambayeshi da alamun tuhuma.

-Ina son ki dawo gareni ne, mu sake raya soyayyar mu, ina son mu koma kamar da ne.

-Fally ka fada min, me ka aikata? Wannan karon muryar Jinah cike take da zafi da kuma rashin tsoro.

-Dole mu hakura da daya daga cikin su, Hindu....

-Innalillahi Fally! Me yasa ita? Ta yaya kayi hakan? Ka maido min da yarana Fally! Ba ruwana da koma me zaka yi, ni yarana kawai nake so!

Jinah ta fada kafin ta sake fashewa da wani sabon kukan. Kokarin rungumeta Fally yayi amma ta goce tareda furta :

-Ka tafi, kada ka kara sako kafar ka anan, ba tare da ka dawo min da yarana ba! Bana kaunar ganin ka kafin nan!

Bai yi wata-wata ba ya bace daga wurin, zuciyarshi na kuna ganin zai rasa daya daga cikin 'ya'yansa gashi kuma zai rasa wadda yake yaruwa domin ta, bayan duk wasu wahalhalu da yasha a baya da sadaukarwar da yayi. Yanke shawarar yaje yaga Hindu yayi, sai dai wata matsalar bai ma san ko ta yaya zai ganinta ba. Koma dai meye zai yi iya kokarinsa yaga ya nemota ta karya abinda tayi. To kuma idan yayi hakan su zasu rayu ne? Tambayar da yayi wa kanshi kenan. Koma dai meye zai je ya nemi Hindu ta san abinda zata yi.

Jinah ce zaune kan benci dake madakatar jiran likita kamar jaririn da yake jiran a haifeshi haka take. Taci kuka iya kuka ta yanda har idanun nata sun kafe babu ko digon hawaye. Duk dakikar da zata shude,sai taji wani abu ya soki zuciyarta.

-Zasu tashi.

Abinda Sarah da su Abdul ke ta maimaita mata kenan, domin likitoci sun tabbatar masu da yan biyu ba mutuwa suka yi ba, sun fita hayyacinsu ne, kuma likitocin na sa ran cetonsu. Ita kuwa Jinah tasan ba zasu iya yin komai ba domin ba kamar kowanne irin ciwo bane.

Kamar an tsikareta ta mike tare da fita daga asibitin. Da gudu Sarah tabi bayanta, ta tsayar da ita.

-Ina zaki je ne?

-Kar ki damu Sarah, yanzu na dawo, kawai ina son na samu natsuwa ne.

-Bari na rakaki.

-A'a dan Allah, ni kadai nake son tafiya.

-Amma...

-Dan Allah...

-Shikenan kar ki dade.

Sarah na nan tsaye har Jinah ta soma yin nisa, bata so ta barta ta tafi ba, amma kuma tana ganin hakan shi zai sa Jinah ta samu dan sukuni.

Jinah tafiya take yi ba tare da tasan inda zata je ba, har wani dishi-dishi take gani tsabar wahala. Ganin jiri na dibanta ta samu wani gindin bishiyar kuka ta zauna. Hada kai da gwiwa tayi. Ta kai tsawon wasu mintuna a haka, kafin ta dago kai taga wani a gabanta. Da ganinshi ta tabbatarwa kanta aljani ne. Kura masa ido tayi, shi kuma sai kallonta yake da mamaki dan ganin ko motsawa bata yi ba.

-Kina ganina ne?

Aljanin ya tambayeta, cike da mamakin ganin yanda Jinah ke kallonsa da alama tana ganinshi ne.

-Ta yaya kike iya ganina, alhali ke bil'adama ce?

Jinah bata ce masa kala ba.

-Gashi kuma kinada kyau irin na aljanu, zan so naji labarinki.

Har yanzu dai bata amsa mashi ba.

-Zan iya sanin sunanki?

Sai da tayi kamar ba zata amsa mashi ba, kafin tace :

-Jinah!

-Eh na san kin san ni aljani ne kuma da mamaki yanda baki ji tsorona ba, kuma nasan ke ba jinsin mu bace, sunanki nake tambaya.

-Sunana Jinah!

-Abin dariya, na taba sanin wata bil'adama mai irin wannan sunan, tana rayuwa ne cikin aljanu, Jinah a cikin "jinni"...

Shuru yayi yana kallonta kafin yace :
-Jinah! Jinah ta Fally kece?

Fiddo ido Jinah tayi, tana tunanin shi kuwa wannan ina ya santa. Kafin ta karasa tunaninta taji ya rungumeta.

-Jinah nine, INFA! Dan Narama da Gausu! Kin tuna ni?

-Infa! Kai ne?

Jinah ta fada da alamun ta ganeshi, murna ce fal cikin ranta da kuma hawayen jin dadin ganin wanda ta dade bata gani ba.

-Amma me kike yi anan? Ke kadai kuma ma ina Fally, da iyayenku? Yaya suke? Me ya faru duk tsayin wannan lokacin?

-Abubuwa da dama sun faru Infa.

Jinah ta fada yanayin fuskarta ya sauya zuwa damuwa.

-Ina jinki bani labari.

Ta fara da cewa :
-Iyayen mu sun mutu.

-Mene? yaushe? Ta yaya? Shi kuma Fally yana ina?

Tambayarshi ta karshe tasa fuskar Jinah tayi ja na tsana jin ya tuna mata da Fally.

-Shi, ban kaunar jin sunanshi, idan har bai dawo mun da 'ya'yana ba...

-'Ya'yanki? Yaya ne wannan labarin yake?...

Labarin komai Jinah ta bashi, abinda ya faru tun daga tafiyar Infa har zuwa yanzu da 'ya'yanta suke cikin wannan halin. Shi kuwa tun lokacin da yaji ta ambaci sunan Hindu, zuciyarsa ke tafarfasa na bakin ciki, tsana, da kuma son daukar fansa a gurin me wannan sunan. Shi ma Infa yana daga cikin wanda Hindu ta zalunta, lokacin da yake karami, shi ma yana rayuwa a cikin kauye daya da su Jinah, shine yaro daya bayan Fally mai son Jinah, yana shige mata fada idan wasu yaran aljanun suna son cutar da ita. Haka suke shakikan abokai, har ana masu lakabi da yan uku, duk da ya girmema Fally da Jinah na shekaru biyar. Komai yana tafiyar masa daidai har wata rana da ya dawo gida ya tarar iyayenshi da kanwarshi sun mutu, anan yaji ga makotansu cewar aikin Hindu ne, kuma idan shima bai gudu ba zata dawo ta hada dashi. Nan da taimakon mahaifiyar Fally ya gudu. Kuma har yanzu bai san dalilin da yasa Hindu ta kashe masa dangi ba.

Yanzu da ya girma, ya dawo da niyyar daukar fansa, duk da cikin ranshi yasan ba zai iya galaba a kanta ba, amma duk da haka zai yi iya kokarinsa.

-gaskiya nayi mamaki sosai, na kasa yarda, wai yan biyu kuma ruwa biyu. Kuma gaskiya Fally bai kyauta ba, amma kuma...

-A'a Infa, kar ma ka fara nemar masa wata afuwa!

-Ina tunanin a wannan karon, mu zamu yi nasara!

cewar Infa cike da jin dadi.

-Ban gane ba, akan me kake magana?

-Yaushe yan biyu suka shiga wannan halin?

-Yau da safe.

-Akwai sa ran ceto yaranki!

-Da gaske kake? Toh ta yaya?

-Kin tuna babana yana yawan son bamu labarin kakanin mu?

-Eh.

-Toh wani lokacin ko daga ni sai shi ne, yana bani labarin sirrukan duniyarmu da abubuwa da dama. Kuma har da labarin yan biyu ruwa biyu yana bani.

-Me yace?

-Abubuwa da yawa, amma ki sani, zamu iya ceto yaranki a yanzu, domin ita ma Hindu tana cikin irin halin da suke, domin haka aikin yake idan tana son ta janye duk wani karfi nasu.
Idan har aikin ya ida, yan biyu zasu mutu ita kuma karfinta zai karu. Sa'o'i sha biyu suka rage mana mu nemo Hindu mu kasheta domin a yanzu ne damarmu take ta yanda ba zata iya kare kanta ba.

Jinah taji dadi sosai da Infa yazo mata da hanyar ceton 'ya'yanta, sai dai matsalar a yanzu basu san inda zasu nemo Hindu ba, nemo aljani a cikin duniyar nan ba abu ne mai wahala, amma yafi ga irin su Hindu, domin sun san a halin yanzu sai da ta boye kanta kafin ta shiga wannan halin, dan gudun kar wani ya cutar da ita.

-Ya kamata mu nemo inda take.
Cewar Jinah.

-Nafi ki son mu nemota ko dan ta girbe abinda ta shuka na kashe min iyaye kuma ta fada min dalili.

-Bamu da lokacin bata lokaci!

-Mu fara daga wajenku inda taje cen wajen Fally.

-Toh, amma mu fara biyawa asibiti domin na sanar da dangina.

Shuru tayi kafin ta sake maimaitawa "dangina". Wannan ne karon farko da ta fadi hakan da nufin cewa Sarah da su Abdul.

Suna zuwa asibitin ta sanar da Sarah zata tafi wani waje, kuma ba zata dade ba zata dawo. Nan suka fita ita da Infa neman Hindu.

Sun bincika kasa da sama, suna yi suna tambayar duk wani aljani da suka hadu dashi, wasu ma basu amsa masu idan suka ji sun ambaci sunan Hindu. Kuma babu wani da yake da niyyar taimakonsu, amma duk da haka basu karaya ba.

Abin tashin hankalin garesu, yau ce rana ta karshe da aikin Hindu zai kammala. Sa'o'i kadan ne suka rage.

-Kiyi hakuri Jinah!
Cewar Infa.

-Koda dakiku ne suka rage mana, bazan fidda ran ceton yarana ba, bare kuma Sa'o'i ne suka rage mana. Mu dai mu cigaba da nema.

Infa yana mamakin karfin halin Jinah, kuma fa haka ne uwa a shirye take da yin komai domin 'ya'yanta. Jinah duk yinin yau babu abinda taci ko tasha, ko kuma samun damar bacci, amma duk da haka batada alamar gajiya.

Kamar daga sama Jinah ta fara kuka.

Da mamaki Infa ya kalleta yace :

-Me ya faru kuma Jinah?

-Me yasa banyi wannan tunanin ba tun dazu?

-Wane tunani kenan?

-Kamata yayi ka shiga jikin daya daga cikin yan biyun domin sanin inda karfinsu ke zuwa.

-Toh ai wannan mun sani cikin jikin Hindu yake zuwa.

-Baka gane ba, ina nufin inda zamu ga Hindu!

-Kuma fa haka ne, sai munyi sauri akwai sauran lokaci.

Ba bata lokaci sai gasu sun bayyana kusa da yan biyu, shi ma haka Fally yazo a daidai zuwansu, shima da tunanin yin abinda suke kokarin yi, yayi mamakin ganin wani tare da Jinah, amma daga shi har Infa basu wani bata lokaci ba, kowanne ya shiga jikin yan biyu. Bayan wasu yan dakiku sai gasu sun fito daga asibitin, kama hannun Jinah Infa yayi suka bace, basu dira ko'ina ba sai inda Hindu take.

Wuri ne dake cike da tsoro saboda duhunsa, gawarwaki da kwarangwal a ko'ina, ga kuma jini a jikin bango da kuma a kasa, sai kuma wasu maganganu da koke da basu san daga inda suke fitowa ba. A irin wannan wurin, kamata yayi ace Jinah ta tsorata, amma babu wannan alamar a gareta domin yanzu babu komai cikin kanta face ta ceci 'ya'yanta.

-Karki tsaya anan Jinah, nine ya kamata na gyara kuskure na. Ki tafi daga nan, ta yiyuwa akwai hatsari anan.

Cewar Fally da ya bayyana a gabansu. Ita kuwa yi tayi kamar bata jishi ba.

-Ba zan taba yafewa kaina ba, idan wani abu ya sameki. Na rokeki ki koma gida. Koma kai waye ina son ka mayar da ita inda ka ganta. Ya fada yana kallon Infa.

-Fally nine fa! baka gane ni ba? Infa! Yan uku!

Ya karashe maganarsa yana nunasu duka ukun. Rike baki Fally yayi yana mamaki, sai da ya dau wani dan lokaci cikin mamaki kafin su rungume juna.

-Dan Allah, ku aje wannan sanayyar a gefe, lokaci kure mana yake. Kai kuma Fally babu abinda zaka ce da zai sa na bar wannan wurin. Dan haka muyi sauri mu gano Hindu.

Ba tare da sunce kala ba suka rufa mata baya. Basu wani taku mai yawa ba, suka tsinkayeta a kwance. Ita kadai ce a wajen, hakan ya basu mamaki, amma kuma daga karshe suka yankewa kansu ko tana tsoron kar daya daga cikin bayinta yayi kokarin kasheta ganin bata iya kare kanta.
Wata zarceciyar takobi ce ta bayyana a hannun Infa lokacin da suka karaso kusa da Hindu. Rike takobin yayi da hannu biyu, yana mai setata daidai zuciyar Hindu, hawayen farin ciki na kwaranya a kumatunsa, shikenan yau zai dau fansar iyayenshi, da na sauran duk wasu wanda shedaniyar nan ta cuta. Ganin idan yayi mata na farat daya zata yi saurin mutuwa, yasa ya janye takobin zuwa kan ruwan cikinta da niyyar ya fara barka cikinta kafin ya fizgo zuciyarta....

Yana cikin wannan tunanin yaji Jinah ta kwala kara :

-Yi hankali Infa!!
Hindu ce ta farka tare da yin watsi da Infa gefe daya.
Sake kwala kara Jinah tayi tana cewa :

-A'a! A'a! 'Ya'yana!

Hindu ba alamar karfi a jikinta ta sake faduwa. Su kuwa kallon kallo suka shiga yi tsakaninsu da mamaki.

-Me hakan ke nufi? kenan 'ya'yana sun...

Fally taimakawa Infa yayi ya mike, sannan shima ya dauki takobin da niyyar sokawa Hindu a zuciya. Ganin haka Hindu tace :

-Aikin da nake yi a yanzu haka ya kusa karewa, kuma idan kuka kasheni a yanzu, zamu mutu mu uku, ni da kuma yan biyu.

Ta fadi hakan ne ba tare da ta motsa ba.

-Karya kike!

-Kasheni ni kadai zai yiwu, amma da a tsakiyar aikin ne, a yanzu kuma idan kuka yi haka bani kadai zan mutu ba.

-Bai dace mu barta a raye ba!
Cewar Infa.

-Amma kuma idan kuka kasheta ya'yana ma zasu mutu.

-Jinah wannan matar shedaniya ce, bare kuma yanzu da zata sake karfi ta hanyar mallakar karfin yan biyu. Zata iya yin duk abinda take so damu. Ka kasheta Fally!
Cewar Infa.

-A'a Fally! Kar ka manta kai ma 'ya'yanka ne! kana so ka kashesu ne? Dan Allah, na yafe maka abinda kayi min, amma kuma idan kayi sanadin mutuwarsu, zan tsakaneka har abada.

-Amma kuma idan muka barta a raye, dukan mu zamu mutu.
Cewar Infa.

-Nafi so na mutu kina kaunata, da na mutu kina tsanata.
Cewar Fally yana mai sakin takobin hannunsa.

-Ku biyun duka kun haukace! Ba zan kyaleku ku saka rayuwar duka mutane a hatsari ba saboda mutum biyu.

Takobin ya dauka ya nufi kan Hindu.

Su kuwa kwala kara suka yi :
-A'a!

-Inada wata hanyar bayan wannan.
Cewar Hindu.

Dakatawa Infa yayi sannan yace :
-Me? Fadi muna jinki!

-Hakan zai dawo da yarana ne?
Jinah ta tambaya.

-Zan iya amfani da karfina na baya, 'ya'yanki zasu rayu cikin koshin lafiya, kuma nima ba zan sake shiga rayuwarku ba, ba ma zan iyawa ba domin ba za'a iya kwatanta karfin yan biyu ba da nawa. Amma sai dai zaki manta komai Jinah, zaki koma daidai ranar da kika farka, kika tuna rayuwarki ta baya, amma wannan karon ba zaki tuna da rayuwarki ta baya ba, zaki koma kamar a baya ki kasa tuna komai, ki manta ko ke wacece, daga ina kika zo, ta yaya kika samu 'ya'yanki ko kuma waye ubansu.

-Me zan yi yanzu?
Jinah ta fada ba tare da ta tsaya yin wata shawara ba.

-A'a Jinah! Kar kiyi haka, ba zan iya sake rayuwa cikin wancen kuncin ba! Naga wani katon yana tabaki, ki kasa tuna soyayyar da nake miki. Na rasa abubuwa da dama saboda ke Jinah kar kiyi min haka.

-Toh ya kake so nayi kenan Fally?

-Zamu samu wata hanyar ki taimaka Jinah!

-So kake na bar 'ya'yana su mutu ko me?...

Infa ne ya katsesu da cewa :

-Na shirya ajiye fansata har wani lokacin, amma kuyi sauri ku yanke abunyi saboda lokaci kurewa yake.

Wata yar karamar kwalba ce ta bayyana a hannun Hindu, ta mikawa Jinah da cewa tasha abinda ke ciki. Matsowa Jinah tayi, ta karbi kwalbar tareda budewa. Baki ta kai da niyyar tasha, Fally bai yi wata-wata ba ya buge kwalbar, ta tarwatse kasa. Jinah bata yi kasa a gwiwa ba, ta durkusa ta fara lashe ruwan da suka yi saura a kasa, ba tare da ta damu da tattakar kwalbar dake cikin ruwan ba.

Dukansu kallonta suke da mamaki, ba kamar Fally, da yanzu ya tabbatarwa kanshi, Jinah bata sonshi, bayada wani muhimmanci a gareta, tana son tayi hakan ne domin ta fitar dashi daga rayuwarta.

-Kin cika maci amana Jinah! Sai kinyi da nasanin abinda kika yi!
Ganin yanda Fally ke maganar zaka gane ranshi yayi mugun baci, kuma zaka ga tsantsar tsanar Jinah a idanunshi. Ya gama yanke sai ya hukunta Jinah, babu ruwanshi da alakar dake tsakanin su, in taso ma zata iya wargajewa.

-Me kake fada ne Fally, kasan...

Bata kai ga karasa maganarta ba, ta sulale kasa. Tana farkawa ta ganta bisa gadonta, yan biyu kusa da ita.

Da alamar komai ya dawo daidai, sai dai bala'in dake jiran Jinah yafi wanda ta gani a baya.

Kamar yanda ake cewa tsakanin soyayya da kiyayya bai wuce taku daya ba.

--------------------------------------------------

Bon Vendredi a vous tous readers ! πŸ’•

Bye πŸ‘‹ Γ  la prochaine πŸ’“ sur vous.


πŸ’ž JINAH (Matar Aljani)πŸ’ž
by Malik al-Ashtar βœ’οΈ

On wattpad πŸ‘‰ https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❀️ Story

CHAPTER 24

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).πŸ’¦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the restπŸ’¦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

Ana yawan fadar cewa duk ana haihuwar mu ne a matsayin mutanen kirki, idan kuma daga baya muka zama miyagu, dalilin irin tarbiyar da muka samu ne, da irin jarabawowin da muka gani da kuma dalilin mutanen da ke kewaye damu... Wata kila haka ne, domin muna zuwa duniyar nan ne bamu san komai ba, bamu iya komai ba, komai muna koyonshi ne anan. Ta dalilin wasu da muke ganin suna aikata abun.

Nasan kun taba ganin yaro na kwarai da zuciya mai kyau amma kuma gidan da ya fito, tasu zuciyar ba mai kyau ba ce? Akwai kuma wani yaron wanda bakar zuciya gareshi, amma gidan su mutanen kirki ne.

Haka akwai wani wanda cikin rayuwarshi, ya taso a na kwarai, rana daya zai juye zuwa mugu dalilin wani abu da aka yi masa, ko kuma wata rayuwa da yake fuskanta...

Toh Fally yana cikin irin wannan rukunin na masu sauya halinsu, kamar an tsoma zuciyarshi cikin ruwan kwalta ta tashi daga launin ja zuwa bakakirin har taso tafi kwaltar baki. Kiyayya ta rufe masa ido, shi da ba zai iya cutar da wani ba ma, amma yau gashi yana cutar da abar kaunarshi wadda a shirye yake ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login