Showing 6001 words to 9000 words out of 72189 words
Chapter 3 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt
ban sani ba...
Sarah ce tayi dariya, kafin su hada ido da Lasaini ta gimtse dariyarta.
-Zaka kwana anan kafin safiya, tinda yanzu dare ya riga yayi.
Cewar Lasaini kafin ya mike tareda cewa su Sarah su ma su je su kwanta.
Sarah ce ta juyo tareda kiran dan uwan nata
-Lasaini!
A fusace ya juyo yace
-Ya aka yi ne!
Sunne kai Sarah tayi cikin i'ina tace
-ah daman... daman.. so nake.. ba komai ma sai da safe.
Tsaki yaja bai kara bi ta kanta ba, yayi gaba. Kwalla ne suka zubo mata, ta rasa sai yaushe tsakaninta da dan uwanta zai daidaita. Tana fata watara ya yafe mata, su koma kamar yanda suke da.
Kama hannunta Jinah tayi ba tare da tace mata wani abu ba, suka wuce daki.
Suna shiga dakin kowace ta nufi makwancinta, Sai dai bacci ya kasa daukansu.
Jinah ce ta sauko daga nata gadon tana fuskantar Sarah tace
-Sarah, kin san dalilin da yasa yayi kamar ya mutu? Alhali bai san abinda ya faru dashi ba, kawai fasa ihu ne fa yayi ya fadi. Daman ana irin wannan ciwon ko kuwa?
Sarah ta kalleta tace
-Ba wani ciwo a yanda yace ya ganki, yayi tunanin aljana ce ba dole ya tsorata ya suma ba. Ai yayi kokari ma da bai hade zuciya ba tsabar tsoro.
Dariya dukansu suka yi, kafin Jinah tace
-Tinda baki jin bacci, ki bani labarin ki, da abinda ke tsakanin ki da dan uwanki, naga baku cika magana ba, kuma na lura duk lokacin da zai yi maki magana fuskarsa a daure take. Dazun ma naga haka, kece babba ko shi ne?
Ajiyar zuciya Sarah tayi kafin tace
-Yayana ne, shekara daya ce a tsakanin mu.
Tabe baki Jinah tayi, tace
-Shekara daya ya baki, shi ne ya rainaki har haka?
-Haba, ai kuwa sai na fada masa.
Zaro ido Jinah tayi tace
-Lah rufa min asiri da wasa nake, ai mutumin kirki ne.
Ganin yanda Jinah take zaro ido ya baiwa Sarah dariya.
Shuru na dan lokaci ya biyo baya, kafin Jinah tace
-To meye musabbabin abinda ya hada ku?
Shuru Sarah tayi kafin ta fara ba Jinah labarin
-Hakan ya fara faruwa ne lokacin da na fara soyayya. Ni da dan uwana mun kasance tamkar jini da hanta, kullum muna tare bama rabuwa, duk inda za'a ga keyata to ki tabbata za'a ga tashi...
Murmushi Sarah tayi tare da kwalla na tuno alakarta da dan uwanta a baya. Ta cigaba
-Na fada soyayya...
Kara matsowa Jinah tayi, cikin zumudin jin labarin soyayyar Sarah.
-Na fada soyayya ne da babban makiyin yayana mai suna Kimba. Kimba kyakyawa ne ajin farko ga kuma kudi, bai cika zama a kauyen nan ba saboda mutum ne mai yawan tafiye-tafiye. Yayana ya tsani Kimba kamar rai da ajali, lokacin da ya gane muna soyayya, sai da ya share kusan sati bai min magana kuma haka shi ne ya fara zama silar wargajewar alakarmu. Yayi kokarin ganin ya datse alakata da Kimba, amma fir na kiya, na nuna masa nifa ina son Kimba. Yana yawan fada mani, Kimba ba mutumin kirki bane, yaudarata kawai zai yi. Amma ina ni soyayya ta rufe min ido. Kimba ya turo yan uwanshi neman aurena, iyayen mu suka bashi, kowa na dangi na murna da auren mu amma banda yayana. Ana gobe daurin auren mu, da yawan samarin kauyen suka yi wata tafiya zuwa wani kauye dan nesa da mu mai suna Kumana. Hankalina bai kwanta ba dan tafiyar har da Kimba da yayana a ciki. Ina tsoron kar yayana yaje yayi wa Kimba wani abu. Saidai cikin ikon Allah suka dawo kowa lafiya lau. Sai dai Yayana yazo min da wani labari wanda shi yayi sanadin datse alakar dake tsakanin mu. Ya bani labarin cewa lokacin da suka isa kauyen Kumana, Kimba yayi shaye shaye ya bugu, ya shiga cikin jeji lokacin da ya dawo sai yaji yana ba abokinshi labari wai ya samu wata yarinya a jeji ya kore kishirwarshi, wato yayi lalata da yarinyar. Bansan lokacin da na wanke yayana da mari ba, ba zan taba manta abinda yayi ta nanata min ba "Yanzu Sarah ni zaki mara akan wannan dan iskan? To ki sani daga yau babu ke babu ni, kuma ba zan kara shiga tsakanin ki da wannan dan iskan ba!" Wadannan kalaman har yanzu suna min yawo a cikin kwakwalwa, amma ko kala ban ce masa ba dan nima a lokacin haushin sa nake ji, dan kazafin da yayi wa Kimba.
Da safe aka daura auren mu, shiru ban ga alamar yayana ba har aka daukeni zuwa gidan Kimba, tun daga ranar ban kara ganin yayana ba. A farkon auren mu, na kasance cikin farin ciki, na irin soyayyar da Kimba yake nuna min, duk abinda nake so Kimba yana yimin. Bayan wasu watanni Kimba ya nemi da na bishi garin da yake kasuwanci, hakan na damu sosai dan bana son nayi nisa da yan uwana, bare ma yayana, ina son na rinka ganinshi kullum koda kuwa baya min magana. Ba yanda zan yi dole na bishi, saboda mijina ne dole nayi masa biyayya.
Tafiya mai nisa muka yi kafin mu kai kauyen tsakiyar dare lokacin kowa yayi bacci banda wata mata wadda da alama zata fini shekaru kadan. Bayan mun aje kayan mu, matar tazo tace min naje ga ruwa cen ban daki nayi wanka. Bayan na gama, na kwanta baccin gajiya.
Hawaye ne suka zubo daga idon Sarah, shuru tayi dan ba zata iya cigaba da ba Jinah labarin ba, domin tana jin kamar yanzu ne abun yake faruwa. Rokonta Jinah tayi ta yi akan dan Allah ta cigaba. Share hawayen da suka zubo mata tayi kafin ta cigaba.
-Da safe, motsin yara ne dake wasa da kuma matan gidan da ke daka ya tayar dani, dubawa nayi gefena amma ban ga Kimba ba. Fitowata daga dakin naci karo da matar jiya da dare, bayan mun gaisa nake tambayarta ko taga mijina Kimba. Budar bakinta sai tace min wai "Ya tafi wajen daya daga cikin matansa, ni sunana Mariya nice matarsa ta biyu ke kuma kece matarsa ta biyar." Jiri naji ya fara dibana, a take maganar yayana ta fado min. Sai dai ba zan yi saurin yarda da maganar wannan matar ba. Nuna mata nayi da ban fahimci me take nufi ba. Anan take bani labarin cewa ai Kimba yanada mata da yawa da 'ya'ya a wurare daban daban, wannan ma shine karon farko da ya hade matan sa biyu waje daya. Bayan ta gama bani labari komawa nayi daki nasha kukana, shine abu mafi muni da nake ganin ya faru a Rayuwata. Ban taba tunanin Kimba zai min haka ba, dan yasha fada min "Kece matata ta farko kuma kece ta karshe." Bai taba fada min cewa yanada wasu matan ba. Kuma wani bangaren na zuciyata kasa gasgata maganar matar yayi, dole Kimba ne zai fada min gaskiyar abinda ke faruwa, haka na bar abin a zuciyata na zauna jiran dawowar Kimba. Kwanaki da yawa sun shude, babu labarin Kimba, nan na fara gasgata maganar yayana tabbas Kimba mayaudari ne. Bai tashi dawowa ba sai bayan wata daya, da zuwanshi na haushi da masifa da kuka akan ni sai ya sakeni na koma gidan mu, babu tausayi ya lakada min dan banzan duka, naci kuka da neman taimako amma babu wanda yazo ya kwaceni, saka Mariya yayi ta tattara 'ya'yanta suka tafi, bansan ina ya turata ba. Kashedi yayi min akan idan har ina son zaman lafiya to dole inyi masa biyayya. Haka dan zaman da Kimba yayi na kwana biyu ya mayar dani tamkar jaka, dukan safe daban na rana daban. Gashi ya hanani zuwa ko ganin gida, idan ya tashi zuwa wajen sauran matanshi, haka zai barni ni kadai a gida gashi babu damar naje gida, dan mu a al'adar mu idan aka yi aure ko yaji ba'a yi bare saki, da kin ga aure ya mutu to ki tabbata daya ne ya mutu ya bar daya. Haka gidan Kimba ya zame mani tamkar gidan yari...
Kuka ne yaci karfin ta, lallashinta Jinah kawai take yi, dan sosai ita ma ta tausaya mata.
Share hawaye tayi ta cigaba
-Na dauki shekaru masu yawa gidan Kimba babu wani sauyi, lokacin da ya aureni inada shekaru 18, yanzu kuma shekaruna 32. Bayan wani lokaci naji labarin matarshi ta farko a Nigeria take, kuma yafi dadewa a cen dan wani lokacin yana kwashe har shekaru 2 wajenta. Kuma yanzu cen ne zai je, ganin hakan yasa na rokeshi da ya barni naje ganin gida daga karshe ya amince amma da sharadin kafin ya dawo yana son ya tarar dani na dawo. A haka na amince akan zan zo naga dangina uwa uba yayana dan yau kimanin shekaru 5 da rasuwar Abban mu, ita kuma umman mu shekaru 3 kenan. Har lokacin yayana baya min magana, ranar da nazo, na durkusa har kasa nayi ta rokonshi akan ya yafe mani, amma ko kallon banza bai min ba. Nasan har yanzu yana sona, dan duk wata kulawa yana bani ne ta hanyar matarshi, ban rasa komai ba anan, ko ba komai ina jin dadin ganina kusa da yayana dan shi kadai ne ya rage min a dangi, gashi ban taba haihuwa ba.
A wannan karon har Jinah kuka take yi, dan Sarah ta bata tausayi ba kadan ba. Bayan sun ci kukan su sun gaji, Jinah tayi mata alkawari da zata daidaita tsakanin ta da yayan ta. Hakan yayi wa Sarah dadi kuma tana fatan haka. Ganin dare yayi nisa yasa kowace ta nemi makwancinta. Asuba ta gari!
Safiya na wayewa, Sarah ta tafi kasuwa yin cefane, ita kuma Jinah wanka ta shiga, bayan ta fito ta zauna taci abin karinta. Tana idawa ta kwanta da niyyar komawa bacci, wata murya taji na rera wasu baituka masu dadi a kunnenta. Baituka ne kamar na mutumin da yayi kewar masoyiyarsa.
Yanda Jinah ta kashe kunne, zai tabbatar maka da lallai tana jin dadin baitukan, tashi tayi ta leka ta window da niyyar ganin mai wannan dadaddiyar murya, sai dai kafin ta karasa lekawa taji sallama a bakin kofa. Amsawa tayi tareda tambayar waye.
Dauda ne ya amsa da
-Nine Dauda!
Fitowa tayi ta tarar dashi bakin kofa.
-Nazo nayi maki sai an jima, dan tafiya zan yi.
Ba tare da Jinah ta kalleshi ba tace
-To sai an jima..
Kallonta yayi yace
-Sai kuma yaushe zamu sake haduwa?
Zaro ido Jinah tayi tace
-A'ah ba da ni ba?
Dauda yace
-Saboda me?
Tace
-So kake ka mutu a hannuna? kaje kawai nagode.
Dariya Dauda yayi, abin dariya yake bashi ganin yadda Jinah ta kakkahe ita dagaske take.
-Ai ki kwantar hankalinki ni da nake fatan mu kasance na har abada..
Ya fada yana kashe mata ido.
Irin kallon sama da kasa Jinah tayi masa kafin tace
-Ban fa gane ba!
-Zaki gane nan gaba kadan, kyakyawar aljanata.
Ya fada yana murmushi tare da juyawa zai tafi, Jinah kuwa kamewa tayi kamar an shukata, tana ta juya maganar tashi dan ita sam bata fahimta ba. Tunawa tayi da dadaddiyar muryar nan da taji, da saurinta taje ta leka windon dakin amma bata ga kowa ba.
Tunani take a zuciyarta, waye wannan mai muryar, me yasa take jin wani abu a lokacin da yake rera baitukan kuma me yasa har yanzu muryarshi ke mata yawo a kwakwalwa?
Da wannan tarin tambayoyin da batada amsar su, ta nufi jeji da muryarta mai dadi tana rera daya daga cikin wakokin Umar M. Shareef.
Wa zani ba kaina? in ba ke ba a cikin yan mata
Wa zani ba raina? kece dai nake kira yar gata
Kaunar da nake miki ban yiwa kaina, kin riga kinyi rata
Kowa yazo tanka mini kan kaunarki yanzu ma fafata
In zaku yimin take, bani son wata sai ke
Ga masara ga wake, ni dai nace sai ke...
You can watch lyrics of this song by Umar M Shareef 👉 https://youtu.be/Q0tGz9DJ1Ck
---------------------------
To fah wannan shine Chapter din mu na yau. Bayyana ra'ayin ku akan labarin yana karan karfin gwiwar cigaba.
Zaku iya cigaba da bibiyar labarin a wattpad ta wannan link din 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story
CHAPTER 3
Kamar yanda yake a duniyar mutane haka yake a duniyar aljanu, idan har aljani ya taka daya daga cikin dokokin al'adarsu, ana yanke masa hukunci daidai da laifinsa. Abinda ya faru ga Fally kenan, ya rasa duk wani karfi nashi da iko irin na kowanne aljani. Idan kuwa haka ta kasance ga aljani, kwanaki kadan suke rage masa a maimakon dubannin shekarun da zai yi. Aljanun da sarki ya turo sun yi nasarar cafke Fally ne, lokacin da yake kokarin bin Mahaifiyarshi da Jinah. Sanadin abinda ya aikata aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
-Me kayi aka kawo ka wannan wajen?
Cewar wani aljani da suke daki daya da Fally a gidan yarin.
Ba tare da Fally ya bashi amsa ba ya cigaba da cewa
-An yanke mana hukuncin daurin rai da rai ne, kuma ko ba dade ko ba jima dole zamu mutu a bayan wannan kantar, dan haka kayi amfani da sauran lokacin da ya rage ma da wannan zaman tunanin da kake... tam duk da ka ki kayi magana, kuma nasan kana ji na, bari na baka labarina da dalilin zuwana wannan waje. Na kasance daya daga cikin aljanu masu tafiye tafiye daga wannan kasa zuwa wata kasa bisa umarnin sarki. Inada mata, na kan dade ban koma gida ba, hakan yasa matata take amfani da wannan damar tana kawo kwarata gida. Nasha kamata amma bansan wane mataki zan dauka ba, har dai wata rana da na kamasu zuciya ta debeni na cire masu kai ita da kwartan nata sannan na kona gawarsu. Wannan yasa aka yanke min hukuncin daurin rai da rai.
Ko a cikin aljanu ko cikin mutane, cin amana mummunan abu ne, yana iya kasancewa ga mace ko ga namiji, wannan ya zama kamar ruwan dare. Cin amanar wanda muke so yanada ciwo. Ba zaka taba sanin zafin cin amana ba sai lokacin da wanda ka yarda dashi yaci amanarka. Sai dai daukar hukunci kamar yanda wannan aljanin yayi ba abinda zai rage maka na daga radadin zuciya.
Har yanzu Fally bai da alamar yin magana, dan ba lalle bane ma yaji abinda aljanin yake fada. Hankalinsa yana cen a tunanin abar kaunarsa, yana cikin kewarta sosai kuma da fama ciwon rashinta a kusa dashi.
Wani aljani daya daga cikin masu gadin gidan yarin ne, yazo ya sanar dashi, mahaifiyarshi ta kawo masa ziyara. Bayan yazo daidai inda mai kawo ziyara ke haduwa da fursuna, mahaifiyarsa ya gani, take ya ji zuciyarsa ta rage zafi. Ita ma ta ji dadin ganin danta duk da akwai shamaki tsakaninta dashi.
-Yaya kake dana?
Tace tana mai tausaya masa
-Lafiya lau nake, ke fa yaya kike?
-Lafiya nake, sai dai nayi kewarka sosai.
-Nima haka, yaya baba?
-Lafiya lau yake, shi ma zuwa an jima zai zo ganinka.
Ta fada, yanayinta na nuna alamar damuwa. Fally ya fahimci bata zo da labari mai dadi ba.
- Ba zasu sake ni ba koh mama?
-A'a dana...
-Haba! Mama kinsan fah kwanakina kidayayyi ne anan.
-Na sani Fally, na sani, hakan shi ke kara tayar min da hankali, kusan zaucewa nake ganin na samu hanyar fitar da kai!
-Na sani Mama, kawai ina jin tsoron ranar da zan...
-Ranar da zaka mutu? Ka yarda da ni, mutuwa ba yanzu zaka yita ba, zan fitar da kai daga wannan guri koda kuwa zan rasa raina.
Haka ta cigaba da kwantar masa da hankali tare da yi masa alkawarin zata fitar dashi koda kuwa hakan zai zama ajalinta. Uwa kenan, ta kan so ta wahala akan danta ya wahala, Uwa zata iya sadaukar da komai dan ganin murmushin danta. Ga uwa farin cikin danta shine gaba da komai.
Bayan tafiyar mahaifiyarsa, damuwarsa ta rage, farin ciki fal a zuciyarsa, tabbas yasan mahaifiyarsa zata fitar dashi, abinda yafi sanyashi farin ciki shine idan ya fita zai ga sanyin idaniyarshi Jinah, wadda ta dalilin ta ya rasa duk wata kima tashi ta aljanu, wadda ba zai taba daina sonta ba har abada..
-Kana ganin Jinah ba zata manta da kai ba kuwa?
Wani bangare na zuciyarsa ne ke fadar haka.
-A'a ba yanda za'ayi ta manta da ni...
Nan fa rikici ya barke tsakanin bangarorin zuciyarshi.
-Kana da tabbaci ne? Tayi fa nisa da kai yanzu!
-Nisa ba abinda zai iya a soyayyar mu.
-Ka tuna, tana da masifaffen kyau, kuma ba wani namiji da zai ganta bai kyasa ba.
Murmushi yayi.
-Baka yarda ba kenan?
-A'a abokina, ni da Jinah mun riga mun yi aure, tare da alkawarin zama na har abada. Duk namijin da yayi kuskuren kusantarta, to fah jikinsa zai zama tamkar kifin da aka fiddo awa daya daga cikin ruwa. Mutuwa zata tabbata ga mutumin da yayi kuskuren yin hakan. Eh, Jinah tawa ce ni kadai har abada!
A bangaren su Jinah
Sarah ce ta shinfida tabarma, Jinah ta zauna. Dauko matajin kai da Man kwakwa Sarah tayi sannan ta zauna a bayan Jinah.
-Bari muga yanda za'a yima wannan gashin naki, ki rage yawo dashi haka buzuzu.
Sarah ta fada tana yamutsa gashin Jinah da mataji.
Sarah sai da ta fara da nasanin farawa Jinah kitso, dan gashinta ba dai yawa ba, ga kuma santsi. Lura tayi da wani tabon haihuwa a bayan wuyan Jinah, tsayawa tayi, dan ta tuna mijinta yanada irinshi komai da komai shima kuma daidai da inda na Jinah yake. Abin daureta mata kai yayi, amma sai ta barshi a zuciyarta kafin ta maida hankalin ga yi mata kitson.
Duk lokacin da ta kamo gashin da niyyar kitsawa sai Jinah tayi ta murkususu tana fadin "da zafi." tana turo baki. Sarah bata tanka mata ba, da abin Jinah ya isheta sai tayi mata rankwashi a tsakar ka ita kuma Jinah ta fasa kara. Haka suka cigaba da yi abin gwanin ban sha'awa.
-To an kare!
Sarah ta fada, mikewa jinah tayi tana ajiyar zuciya tace
-Haba kin ji yanda mazaunaina suka yi kamar zasu kama da wuta.
-Je ki duba madubi, zaki ga yanda na gyara maki shi, sai kin min godiya..
Dariya suka yi kafin Jinah taje ta duba a madubi, gashin yayi kamar an zatse kwarya, shi ba babba ba shi ba karami ba. Koda Jinah ta gani kasa motsawa tayi dan yayi bala'in kyau. Manyan zane ne Sarah tayi mata a tsakiyar kai tare da game jelar gashin ta dunkule waje daya ya sauka a gadon bayanta, kasancewar Jinah fara, haka fatar gashinta fara ce yasa zanen kitson ya fito da kyau.
-Sarah kinyi