Showing 15001 words to 18000 words out of 72189 words

Chapter 6 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt

17 Mar 2026

38

budurci bane.

Ajiyar zuciya Sarah tayi. Ta shiga ta tarar da Jinah, Rungumeta tayi ba tare da tace wani abu ba. Haka suka kasance rungume da juna na tsawon dan lokaci kafin Sarah ta rada mata a kunne.

-Nasan baku yi wani abu ba Jinah, amma ki shirya lokaci na zuwa. Dan Allah kiyi kwanciyarki daki, kar ki fita su fahimci wani abu. Kuma idan kina bukatar wani abu ki zo ki ganni zan baki, idan kin tuna da rayuwarki ta baya ki zo ki fadamin. Ki kula da kanki, zan kasance kullum domin ki kuma zan yi kewarki.

Gyada mata kai kawai Jinah tayi, tana hawaye, dan itama tasan zata yi kewar Sarar. A haka Dauda yazo ya tarar dasu, ya dade yana mamakin irin wannan shakuwa tasu, gashi basu hada komai ba, amma Sarah tana jin Jinah tamkar 'yar uwarta ko kuma 'yar da ta haifa.

Mikewa Sarah tayi, kafin ta tafi ta kara jaddadawa Dauda alkawarin da yayi mata na kulawa da Jinah.

Bayan ya raka Sarah, ya dawo daki wajen matarshi. Babban daki ne da makeken gado a tsakiya, a gefe kuma akwai dressing table da wardrobe, sannan bathroom madaidaici. Dakin ya kawatu sosai, har da gidan ma baki daya. Saboda idan ka shigo cikinsa zaka dauka a birni kake, duk da yanzu kauyuka da dama ana ta samun cigaba amma wannan ya banbata da sauran, dan a kauyen babu irinsa.

Bayan wani dan lokaci, Jinah ta fara jiwo wani sauti, wata murya, ba yau ba ne na farko da ta fara jiwo wannan sautin. Amma wannan karon taji kamar sautin kusa yake ba kamar da ba da take jiwoshi daga nesa. Shurun da tayi tana sauraran sautin ne yasa Dauda ya tambayeta.

-Me yake faruwa?

-Daga ina wannan sautin yake fitowa?

-Wane sauti kike magana?

-Saurara kaji.

Saurarawa Dauda yayi kafin ya fahimci me take nufi.

-Wannan kiran sallah ne!

-Kiran Sallah? me hakan ke nufi? A da ina jiwo sautin ne daga nesa amma yanzu kamar...

-Eh anan cikin gidan ne, muryar Buraima ce, yayana. Hakan yana nuna alamar lokacin sallah yayi.

Ya fada cikin yanayin damuwa, dan ya fahimci matarshi babu abinda ta sani game da musulunci, wata kila yana daga cikin matsalar mantau da ta samu ne. Ya fahimci hakan ne tun ranar da ya fada mata yana sonta. Duk da irin wannan ba wani abin mamaki bane a kauyuka. A kauye mutane na amsa sunan musulmai ne amma basa yin komai da ya danganci musuluncin, suna yawan fadar za suyi idan sun tsufa, su a tunaninsu addinin ana yinsa ne idan aka cimma kabari wato tsufa, akasarinsu matasa ne suka yi imani da wannan da'awar. Shi kanshi Dauda a baya yana fadar hakan har zuwa lokacin da yaje Maradi wajen wani kawunsa, anan yaga yaro dan shekara 7 bakwai yana sallah abin gwanin ban sha'awa. A ranar yaji kunya ba kadan ba, tun daga ranar ya shiga neman ilimin addini. Anan ya gano muhimmanci da kuma wajibi na gudanar da addini. Yana dawowa kauyensu yasa mahaifinsa ya gina masallaci a cikin gidansu kuma da taimakon wani malami a kauyen yayi nasarar jawo hankalin yan gidansu da ma makota suna zuwa sallah. Duk da har yanzu ba wani sani gareshi sosai a cikin addinin ba, amma yasan hakkoki da kuma gujewa duk wani sabon Allah. Duk da yan kwanakin nan yana fama da muguwar sha'awa, hakan yasa yake yawaita azumi da tsayuwar dare dan gudun fadawa tarkon shedan.

-Matso nan kusa dani!
Ya umarci Jinah, ba musu ta matso ta zauna dab dashi bisa gado.

-Kinsan addinin musulunci?
Ya tambayeta.

-A'a.

-Ok, bari yanzu idan na dawo daga masallaci, sai muje gurin liman.

Bata fahimci komai ba cikin maganar, shi kuma murmushi yayi ganin yanda take ta kyafce-kyafce.

Kamar yanda yayi alkawari, yana dawowa, ya kaita wurin Liman. Liman ya biya mata kalmar shahada. Cikin yan kwanaki kadan Jinah ta iya abubuwa sosai na musulunci, haka itama ta koyawa Sarah lokacin da taje gida.

Kamar walkiya lokaci yake wucewa, Jinah tana zaune lafiya da mijinta da sauran danginshi. Sai dai matsalarta daya rashin iya girki, amma cikin sa'a Dauda yayiwa mahaifiyarsa bayani. Ba tare da bata lokaci ba, a boye mahaifiyar tashi ta fara koyamata. Dan ita kanta abin kunya ne gareta sauran mutanen gidan su fahimci sirikarta bata iya girki ba. Jinah tayi sa'ar sirika, dan bayan girki har da abubuwa da dama take koya mata.

A farkon watan June cikin Jinah ya fara bayyana, dan yanzu zai kai wata hudu. Dauda yana nuna kulawarsa sosai akan cikin, amma ita sam bata son cikin dan ko maganarshi bata so ana yi, wani lokacin ma shigewa daki take ta yita kuka. Kullum Dauda cikin rarrashinta yake da nuna mata ko ta wanne hali ta samu cikin, jininta ne kuma dole ta kaunaceshi. Duk zaman nan da suke, ko kuskuren tabata Dauda yayi to fa ranar sai ya kwana da jinya. Ganin haka da kanshi yaba kanshi baki, kuma shima hakan ce ta fiye masa.

Wata ranar lahadi da yamma, Dauda ne zaune ya buga uban tagumi, ya fada duniyar tunani. Wanda hakan ba halinsa bane. Ganin haka, Sarah ta tambayeshi ko lafiya. Dan karamin tsaki yaja kafin yace
-Ba komai, kawai bana jin dadi ne.
Mikewa yayi ya nufi tsakar gida. Tarar da Kakarshi yayi ta tara yara tana yi masu tatsuniya.

Wata aljana ce mai kyau da dogon gashi. Da dare yayi sai ta boye fuskarta, ta sa fararen kaya, ta shiga cikin kauye tana cinye mutanen kauyen yara da manya...

Bai tsaya jin karshen labarin ba, ya juya cikin daki wajen matarshi.

-Inada wata dabara!
Ya fada tareda yin murmushin mugunta.

-Toh, wace irin dabara?
Jinah ta tambayeshi.

-Kinada farar riga doguwa?

-Eh... inada.. me zaka yi da ita?

-Ina so ki sakata, dan yau ina son kallon drama ne.

-Ban fahimta ba, me zamu yi da ita?

-Kaka ce ta tara yara tana masu tatsuniya.
Bata labarin abinda yaji kakar na fada yayi, sannan ta fahimta.

-Ka tabbatar tsorata su zaka yi? Kar fa a samu matsala?

-Ba wata matsala da za'a samu ke dai sako rigar, kawai dan ayi nishadi ne.
Ya fada yana murmushi.

Ba tare da tana son yin wannan wasa ba, dan kawai bin umarninsa zata yi.

Saka rigar tayi, doguwa har kasa sannan ta kunce gashinta ya barbazu a fuskarta. Fita suka yi tsakiyar gida, labewa Jinah tayi, shi kuma Dauda yaje cikin yaran yayi zaune.

-Kinga Kaka ki daina basu labarin aljanun nan, kinsan idan ana bada labarinsu bayyana suke...
Dauda ya fada yana mai gargadin kakar tashi. Karyatashi kakar tayi sannan ta cigaba da ba yaran labari.

-Shikenan ni dai na fada maku, amma baku ji ba.
Ya fada yana mikewa, Jinah ce ta fito daga inda ta buya ta dunfarosu. Kaka ce ta fara kara sannan ta gudu, yaran ma suka rufa mata baya suna fadin "Da gaske Dauda yake akwai aljana", Kyalkyacewa da dariya Jinah da Dauda suka yi, sannan suka gudu suka buya. Mutanen gidan ne suka fito dan ganin meke faruwa.

-Wallahi ku dai anyi yara, bansan yaushe zaku girma ba.

Mahaifiyar Dauda ce ke fadar haka da ta tarar dasu suna kyalkyatar dariya.

-Ai Mama ko ba komai, Kaka ta motsa jikinta.
Dauda ya fada yana dariya.

-Haba zaku gane kurenku idan ta gano kune, kuka yi mata wannan shakiyancin.
Mahaifiyar ta fada kafin ta koma daki.

-Gaskiya ka cika yarinta Dauda!
Jinah ta fada.

-hahaha, ai ni ba abinda nayi, kece kika tsorata su. Kinga yanda kika yi kuwa? Kin bazo gashi ga kuma katon cikin ki.
Dauda ya fada yana dariya.

Bata rai Jinah tayi jin yayi maganar cikin. Dan sam bata son maganar cikin.

-Ke lafiya, wannan fa danki ne, ya kamata ki daina wannan abun. Me yasa baki son ana maganarshi? Wallahi ni ina jinsa kamar dana ne, duk da ba nawa bane. Dan haka ki daina wannan abun. Kinga zo muje ki dan tattaka.

Suna yin taku kadan, wani ya tari gabansu. Idrisa ne, daya daga cikin yan uwan Dauda da suke uba guda. Murtuke fuska Dauda yayi, dan sam basu shiri tsakanin su, kuma Jinah ta lura da hakan tun zuwanta gidan, haka ma akwai wasu sauran yan uwan da duk basu shiri.

-Zaka iya matsawa, dan muna so mu wuce.
Dauda ya fada cikin yanayin bacin rai.

-Naji duk abinda kuke fada, kuma nasan wannan shegen cikin ba danka bane.
Idrisa ya fada yana nuna cikin Jinah tare da yin wani shu'umin murmushi. Zuciyar Jinah ce ta bada wani dum, shi kuma Dauda yi yayi kamar bai ji abinda Idrisa ya fada ba. Kama hannun matarsa yayi suka yi gaba suka bar Idrisa dashe a wurin.

Idrisa baida wani makiyi duniya da ya wuce Dauda, kuma yasha alwashin ko ta wane hali sai ya yiwa Dauda illa, gashi yanzu yaji wannan labari sai dai rashin tsoro da ya gani a idon Dauda yasa ya fara konkonto. Tunani ya fara, kafin daga bisani ya tuna koda ya fallasa wannan sirrin babu wanda zai yarda dashi dan kowa yasan ba kaunar Dauda yake ba, cewa za'a yi kawai sharri ne.

Rarrashin Jinah Dauda yayi ta yi, kan babu abinda dan uwansa zai ce. Sai dai ita tsoro duk ya mamayeta dan tana tsoron Idrisa ya fallasa wannan sirri.

Bayan kwana biyu, zuwa karfe uku na rana kusan kowa yana wurin aiki, ciki har da Dauda. Bugun kofarta Jinah taji ana yi, budewar da zata yi taga Idrisa.

-Ki biyoni dakina yanzu ko na fallasa wannan cikin naki, yanzu kowa ya sani.

Ganin yanayin da yayi maganar, yasa Jinah bata yi tunanin komai ba, ta bishi a baya ba tare da tayi tunanin me zata yi a dakin dan uwan mijinta ba. Suna shiga, yaja kofa ya garkame.

-Yau dan iskan mijin nan naki zai gane kurensa. Zan nuna masa shi karamin dan iska idan yazo ya tarar da abinda zan maki yanzu. Nine babba gareshi amma har yanzu banyi aure ba, shine shi har da zuwa ya auro zukekiyar mace!

Kokarin bude kofa Jinah tayi, shi kuma ya janyota tareda gamata da bango, kokarin kwatar kanta ta fara, ya kifa mata wani gigitaccen mari. Ganin ba sarki sai Allah Jinah ta fara hawaye.

-Dama na dade, ina fakonki!

Harshe yasa yana lasar kuncinta kafin ya gaura kanta da gini ta suma. Daukanta yayi ya jefa kan gado tare da cire kayan jikinta. Ba tareda wani tunani ba yayi kokarin shigarta.

Sandarewa yayi sakamakon wani addababben zafi da ya shiga jikinsa, haka yayi ta kokowa neman numfashi amma babu dama, bayan wani dan lokaci da ya dauka cikin wannan azabar Kamar buhun dankali haka ya fadi tim gefen Jinah matacce!


------------------------------------------------------------

Ko kuma nasan zaku ce, yanzu kuka san labarin Jinah matar aljani kuke karantawa. Tinda gashi Aljani har ya fara aikin kula da matarshi. lol.πŸ˜‚


Sai kuma idan mun hadu a sabuwar chapter. Amma fa kuyi hakuri ba lokaci, ku dai kawai sai in kun ga update.

@El_Ashtar

πŸ’ž JINAH (Matar Aljani)πŸ’ž
by Malik al-Ashtar βœ’οΈ

On wattpad πŸ‘‰ https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❀️ Story

CHAPTER 7

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).πŸ’¦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the restπŸ’¦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

A kullum dan adam yana da mafarkai wanda yake da burin wata rana su zama gaske, haka dan adam, akwai wasu abubuwa da suke faruwa a rayuwarsa wadanda zai yi burin a ce mafarki ne yake.

Wannan shine abinda Dauda yayi burin a ce mafarki yake, da ganin wannan rana dan uwansa a kan matarsa.

Sanadin ranar da ake yi mai zafi da sanya kishi, Dauda ya ajiye aikin da yake yi, ya nufi cikin rumfar hutu dake cikin masana'antar domin samun ruwan da zai jika makoshinsa. Yayi mamaki na rashin ganin Idrisa, bai kawo komai ba a ransa yaje yasha ruwa ya cigaba da aikinsa. Tunawa yayi da abinda ya faru tsakanin shi da Idrisa, da alwashin da Idrisa yasha na sai yayi masa abinda har ya mutu ba zai manta dashi ba. "Tabbas zai iya aikata abinda yayi niya." ya fada a zuciyarshi. Tunawa yayi da ya ganshi lokacin da yake fita daga masana'antar, alhali kuma lokacin tashi daga aiki bai yi ba. "Jinah!" yada cikin tashin hankali, bai tsaya wani dogon tunani ba yaje ya fadawa mahaifinsa zai je gida.

Lokacin da yazo gida ya nemi Jinah ko'ina bai ganta ba, haka shima Idrisa bai ganshi ba. Tunani kala-kala yayi tayi, ga kuma zuciyasa dake tsananta buguwa. Dakin Idrisa ya nufa, ya tarar da dakin a kulle. Juyawa yayi da niyyar dubawa makota, amma sai ya fasa da ya tuna babu inda Jinah take zuwa. Yana nan tsaye bakin kofar dakin Idrisan, sai ga Surayya 'yar yayarshi.

-Surayya baki ga Jinah ba?

-A'a ban ganta ba!

-Kawunki fah Idrisa?

-Dazu na ganshi ya shiga dakinsa.

-Yauwa to jeka abinka.

Ya fada kafin ya nufi dakin auntinshi wadda ke da duk wani sifayen yan makullayen dakunan gidan. Kusan sau biyar yana kwankwasa kofar kafin ta bude, fuskarta alamar bacci.

-Ya aka yi ne?
Ta fada cikin yanayin bacin rai da tunanin ko wasar da Dauda ya saba yi mata ne. Dan idan yayi niyyar yi mata shakiyanci, da ya bubbuga mata kofa ta bude, sai yace mata ai yayi makuwar daki ne. Murmushi yayi da ya fahimci abinda take nufi.

-Baba ne ya aikoni daukan kayan aiki da suke dakin Idrisa, sai dai na manta ban karbo makullin dakin ba, shine nake son ki bani na hannunki na bude.

Yayi mata karya, ita kuwa bata yi tunanin komai ba ta dauko masa makullin. Yaje ya bude kofar gabansa na dukan uku-uku. Jiri ne ya debeshi, Da sauri ya koma ya rufe kofar, kafafuwansa kasa daukanshi suka yi, ja da baya yayi ya jingina da bango.
Bai taba tunanin tsanar da Idrisa ke nuna masa zai kai ya iya aikatawa matarsa wannan danyen aiki ba. Karasawa yayi, kokarin ture Idrisa yayi daga bisa gadon, ya girgiza ganin Idrisa ya fado kasa kamar gawa. Dan tun farko bai lura Idrisa bai motsi ba. Wani mugun kunci ne ya turnukeshi ganin matarshi ba kaya, jikin da ya dade yana mafarkin gani amma bai taba tunanin a irin wannan yanayin ba. Idanun Jinah a rufe suke, alamar tana bacci, anan ya fahimci sumar da ita ne Idrisa yayi, kayanta ya saka mata sannan ya dauketa ya kaita har dakinsu ya shimfideta kan gado.

Komawa yayi dakin dan uwan nashi da har yanzu yake kwance a kasa. Nan fah hankalinshi ya tashi, kunnensa ya kara a kirjin Idrisa anan yaji zuciyarshi bata bugawa. A hankali ya sakama dan uwan nashi wando, sannan ya ya barshi anan kwance. Bai rufe dakin ba, yaje ya kaiwa auntynshi makullin.

Kada Ashanti (godiyarshi) yayi, nesa da gida. Yayi hakan ne ko zai manta tare da rage damuwar abinda ya faru. Abinda dan uwansa yayi ko yake kokarin yiwa matarshi, ko kuma mutuwar dan uwan nashi bai san wane ne yafi masa ciwo ba.

Bayan yayi tafiya mai nisa, ya juya ya koma gida. Tarar da gidan yayi makil da mutane, dan kusan kowa yana nan, sai dai abinda ya bashi mamaki babu alamun an yi mutuwa a gidan, sauke ajiyar zuciya dan yana tunanin wata kil Idrisa ba mutuwa yayi ba. Daki ya nufa dan ganin ko Jinah ta farka. Tarar da ita yayi ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gado, sam baya jin dadin ganin matarshi kuma abar kaunarshi cikin damuwa.

-Bansan me yayi min ba, ya..ya..umarceni da in bishi dakinsa, na bishi, naji tsoro, tsoron kar ya fada cikin dake a jikina ba naka bane..na..na..
Jinah ce ke fadin haka cikin kuka ba tare da ta jira ya tambayeta abinda ya faru ba.

-Ki daina kuka dan Allah Jinah!

-Na..naje dakinsa Dauda, hanani yin ihu yayi, ya tsoratani, san..sannan ya buga kaina a bango, sannan, sannan, sannan...Wayyoh Allah! bansan me yayi min ba. Me yayi min, ba zan iya tunawa ba...

Ganin tashin hankalin da matarshi ta shiga, Dauda ji yayi yana son ya rarrasheta, ya kwantar mata da hankali, ya gusar mata da wannan tunanin da take.

-Bai tabaki ba, nazo kan lokaci sannan na fitar dake daga wurin, bai yi maki komai ba.

Shiru Jinah tayi da alamar rashin yarda tace
-Ka tabbata?

Tsareta yayi da ido don shi kam baida tabbaci, ya fada mata haka ne dan ganin ta kwantar da hankalinta. Itama Jinah tsareshi tayi da nata idon dan jin ya tabbatar mata da maganarshi.

-Eh, na tabbata bai yi maki komai ba.

Cikin dan kankanin lokacin da baiyi tsammani ba yaji ta fado jikinsa, ta kankameshi tana kuka marar sauti. Ji yayi zuciyoyinsu na bugawa a tare, lallausar fatarta na gugan tashi, tunda suke hakan bai taba faruwa ba, bai taba jin dadi irin na yau ba, haka bai taba jin matsanancin zafi da radadin jiki irin na yau ba. Dan ji yayi kamar an kunna mashi wuta a jiki. Lallai abu ne marar misaltuwa a wurinshi dadi da ciwo a lokaci guda. Ganin idan suka cigaba da kasancewa manne da juna to fah zai iya kamawa da wutar gaske yasa ya janye jikinshi daga nata. Ba'a dau lokaci ba kuwa ya bar jin zafin jikin.

-Nagode kwarai da gaske!
Jinah ta fada cike da farin ciki, murmushi kan lebenta.

-Nauyina ne hakan, kuma ki kwantar da hankalinki ba zai taba fadawa kowa ba abinda yaji.

Ya bata amsa kafin ta mike ta nufi ban daki. Wanka tayi da ta fito bata ganshi ba, kaya ta sake, tayi sallah sannan ta kwanta kan gado. Bata fatan ta kara haduwa da Idrisa, inuwar ma mai kama da Idrisa bata fatan sake gani dan ya tsoratata sosai, dan haka dole tayi taka tsantsan dashi. Da irin wannan tunanin bacci marar nauyi ya fara saceta.

Cen cikin baccinta sama-sama taji kara daga wajen tsakar gida, zuciya na dukan uku-uku, Jinah ta fito daga daki dan ganin meke faruwa. Matan gidan ne ke ta kuka, Maza kuwa na kokarin rarrashinsu, wasu dora hannuwa biyu suka yi a kai, wasu na girgiza kai irin na anga abin alhini, Habi ta gani uwar gidan sirikinta kwance tana birgima a kasa, 'ya'yanta mata biyu suna riketa. Kasa fahimtar komai tayi, zuciyarta na bugawa kwarai. Neman Dauda ta fara yi kafin ta hangeshi kusan kofar dakin mamarshi, fuska a dame.

-Wayyoh dana! me yasa Allah bai daukeni ba a maimakonsa, wayyoh Idrisana.

Muryar Habi ke karade ko'ina da kukan rashin danta. Nan Jinah ta fahimci abinda ke faruwa, toshe bakinta tayi da hannuwanta ta zauna dirshen bisa wani benci dake kusa da ita.
Duk abinda yayi mata, ba zata yi mashi fatan mutuwa ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login