Showing 39001 words to 42000 words out of 72189 words
Chapter 14 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt
cewar Jinah, ko me yake damunsa?
-Ni zan je na kwanta domin na gaji sosai.
Da zuwanta daki, ta zauna kan gado, tunani ta fara yi kan abinda ya faru jiya. Hayyacinta ta dawo sakamakon bugun kofarta da taji ana yi.
-Shigo! Ta fada da tunanin ko daya daga cikin yan matan ne. Sai dai da mamakinta taga Abdul ne ya shigo.
-Me kake yi a dakina?
-Ina son muyi magana ne.
-Ina sauraronka.
-Ina sonki Sarah.
Fiddo ido tayi waje.
-Ba zai yiwu ba Abdul, ka fara hauka ina ga.
-Ba hauka ba nake Sarah, da gaske ina sonki, nasan hakan akwai rikitarwa domin ke matar babana ce.
-Kuma bayan haka, na girme maka...
-Sarah soyayya ba ruwanta da shekaru, kuma ni hakan bai dameni ba, ki barni na soki Sarah, ni kaina nayi yaki da hakan amma na kasa, dole na yada makamaina.
-Ka fita dan Allah Abdul.
A karo na biyu, yanzun ma kamar tsafi taga katon maciji kan gadonta. Tsalle tayi ta fada kan Abdul.
-Maci... Ta juya da niyyar nuna masa amma bata ga komai ba.
-Kwantar da hankalinki babu komai.
-Amma..ni..
-Shiit, idan kina jin tsoro ne, zan iya tsayawa.
-Ba zai yiwu ba!
-Sarah ba komai fa zan yi ba, illa gadinki.
Kwantawa tayi shi kuma ya zauna gefen gado.
-Me yasa kake min duk wannan abun?
-Na fada maki ina sonki har cikin raina.
-Babu namijin da ya taba bani irin wannan kulawa.
-Idan har namiji ya sameki kuma har ya kasa baki kulawa to shi ba namiji bane.
Shuru suka yi, kowa na saka da warwara cikin zuciyarshi. Ita kanta Sarah taji ta kamu da kaunarshi amma kuma tana jin tsoro na kasancewarshi dan mijinta. Kalamanshi suna tabata sosai, tana jin ina zata samu damar dandana jikin wannan matashin. Amma kuma ta kasa daina maimaita. Zan daure, zan cije, ba zan iya ba.
-Zan iya tabaki? Kamar daga sama taji tambayar tashi, zai tabani, kenan ba zai iya yin haka ba sai da izinina? Kuma yace tabani kawai zai yi, tabani din kawai zai yi kenan? Tunanin da tayi kenan.
-Eh! Ta fada cikin kasalalliyar murya.
Hannu Abdul ya dora kan kafarta.
-Fatarki akwai laushi, zan iya shafawa?
-Eh, ai shafawa kawai zaka yi ko?
-Sosai ma.
Wata irin shafa ya fara yi mata, wadda duk tabi ta daga mata hankali. Ganin ta fara fita hayyacinta, ya kai hannuwansa kan ruwan cikinta. A hankali hannuwansa suka kai kan kirjinta ya cigaba da shafata. Ganin kamar tana jin dadin abun, ya kunce mata zanin gaba daya. Sai gata babu komai a jikinta. Abun nasa gaba gaba ya fara yi. Tsawa ta daka masa.
-Abdul ya isa haka! Ba tare da yayi magana ba ya koma dakinsa, kwabe kayan jikinsa yayi duka, sannan ya kwanta kan gado idonsa na kallon rufin dakin kamar mai jiran zuwan wani. Rufe idonsa yayi, cen yaji kamar mutum kusa dashi, bude idonshi yayi yaga Sarah a tsaye. Wani makirin murmushi yayi, ita kuma bata yi wata-wata ba ta kwabe kayan jikinta baki daya sannan ta hau gadon. Zumana ya samu abinda yake so, ya samu burin cika farkon plan dinshi.
(....)
-Tunanin me kake? Aya ke tambayar dan uwanta da taga kamar yana cikin tunani.
-Ko kin taba lura da irin wannan abun da Aljanin nan ya sakawa baba?
-A'a, me yasa kace haka?
-Ni na taba ganinsa a inda muka yi fada da wannan aljanun.
Ayu tun lokacin da aljanin ke warkar da baban nasu ya lura da abinda yayi anfani. Komawa suka yi shi da kanwar tashi inda suka yi fada da aljanun, anan suka ga ire iren abun a kasa, wanda aljanu suke anfani dashi wajen sankarar da mutum wuri daya ta yanda ba zai iya motsi ba. Komowa suka yi wajen mahaifin nasu, suka cire abun na kan goshinsa da kuma na kirjinsa. Wani ihun wahala Fally ya saki tare da yin tari. Bayan kamar mintuna goma, Fally ya dawo hayyacinsa, mikewa yayi. Cike da murna yan tagwayen suka rungumeshi. Daidai lokacin Zumana ya karaso wurin, ya tsorata da ganin Fally ya tashi amma bai bari suka lura da canjin fuskarsa ba. Washe hakorin dole ya shiga yi kafin ya fada cikin rada:
-Muje a plan B!
©El_Ashtar
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story
CHAPTER 16
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
A wannan rayuwar akwai mutumin da na abincin da zai ci kawai yake so, akwai mutum mai na abincin kuma yana da burin mallakar gida, akwai mutum yana da gidan kuma mota yake da burin mallaka, akwai mai gida da mota kuma kari yake so sannan akwai mai shi da yawa duk da haka kari yake so. Duk adadin samun mutum a duniya kalmar "Bai isheni ba" ba zata taba gushewa ba daga bakinsa. A kullum idan mutum ya samu cikar burinsa to wani burin ne ke maye gurbin tsohon burin. Kuma ya kan manta da cewa duk wani abu da ya tara a duniyar nan, ba mallakinsa bane haka zai wuce ya bar abun....
Haka yake a gun Hindu, tsohuwar aljana da tafi sauran aljanun tsufa a duniyar da Jinah ta taso, duk adadin karfin tsafin dake gareta, burinta a yanzu bai wuce mallakar yan tagwaye ba domin kara habbaka karfin tsafinta ta yanda zata dawo gagarabadau a duniyarsu. Domin haka su ma sauran aljanun suka dau haramar samun hanyoyin da zasu mallaki wannan yara, saidai ita Hindu a dage take kallonsu domin ita tanada nata plan da ta shirya. A ganinta sauran aljanun kawai shirmen banza zasu yi da yan tagwayen domin basu son komai ba game da asalin karfinsu kamar yanda ta sani.
-Ranki shi dade Hindu!
Wani Aljani daya daga cikin amintattun masu yi mata hidima ne ya kira sunanta a yayin da yake shigowa hankali a tashe.
-Ya aka yi ne Manfa? Wane labari ka zo min dashi?
-Labarin marar dadi ne ranki shi dade.
-Haifoshi zan iya goyashi!
-Zumana da ga sarki Mombi na kabilar Fomba wayon tsiya ne dashi, a yanzu haka yana tare da yaran, yana taimaka masu su san karfinsu.
Shuru Hindu tayi kafin ta kyalkyace da wata mahaukaciyar dariya. Cike da mamaki Manfa ya tambayeta :
-Ya naga baki damu ba, ranki shi dade? Ya kamata mu san yanda zamu wargaza masa plan.
-A'a Manfa, fili kawai Zumana yake share mana.
-Kamar ya?
- A sannu zaka fahimta!
Manfa bai kara cewa kala ba, ko daya baya tantamar fadar uwar gijiyarshi, domin shi shaida ne a kan karfin da take dashi.
-Ina fata baka manta da babban aikin da zaka yimin ba?
-Wane ni da zan manta, da ni da ahalina ai duk mallakinki ne, kuma ba zan taba da nasanin abinda zan yi maki ranki shi dade.
-Naji dadin jin wannan! Mu tafi yanzu.
Cikin kankanin lokaci suka dira a inda suke son zuwa.
-Tona ramin! Hindu ta bashi umarni.
A take ya tone ramin, yana gamawa ya fada mata da ya gama. Wani umarnin ta sake bashi.
Shiga yayi cikin ramin, ya kwanta kan abinda suka tarar cikin ramin, wasu ruwa Hindu ta shiga zuba masa har sai da ya jike sharkaf, sannan ta shiga fadin wasu kalmomi da ita tasan anfaninsu. Da tafin hannunta take bin ko'ina na ramin tana cigaba da fadin maganganunta, a take wata wuta mai karfi ta fara ci a cikin ramin. Azabar da Manfa yaji tasa ya saki wani azabataccen ihu, ihun da kamar mala'ikan mutuwa na zare ran kafiri. Duk da Hindu bata dakata da sambatun da take ba, sai ma kara daga murya da tayi. Bayan ihun da Manfa yake yi, za'a iya jiyo ihun wasu amma ba daga wannan ramin ba ihun yake fitowa, yana fitowa ne kamar daga nesa. Wutar daina ci tayi kamar bata taba kamawa ba, kara rufe ramin Hindu tayi. Sannan ta daga hannunta sama tana maimaita : wili, wili sela! Ba bata lokaci sai ga hannuwa biyu sun fito daga cikin ramin, kamar zombie zai fito daga cikin kabarinsa. Mutum ne lafiyayye ya fito daga cikin ramin ya tashi tsaye gabanta. Wani makirin murmushi ta fara yi, kafin daga bisani ta kyalkyace da wata mahaukaciyar dariya, dariyar da ta karade ko'ina na dajin.
(..........)
-Ina son magana da kai, kai kadai idan zai yiwu.
Zumana ya fada da damuwar karya a fuskarsa.
-A'a, muma muna son jin abinda zaka fada, da kuma yanda zaka kare kanka domin kayi wasa da kwalwarmu.
Cewar Ayu.
-Eh, ba kamar ni da na dauki yardata na baka.
Cewar Aya tana wa Zumana kallon a barni na kasheka.
-Baba, ka kyalemu da shi muyi maganinsa.
Cewar Ayu cike da tsana kafin ya nuna yatsa zuwa wuyan Zumana. A take Zumana ya fara kakarin amai da kokowar kwatar numfashi. Ji yake tamkar an ratayeshi ne da igiya, fara karewa karfinsa yayi, ya durkushe kasa.
-Dakata Ayu, ya kamata mu fara jin me yasa yayi hakan.
Umarnin mahaifin nasa yabi, ya saki Zumana. Tarin wahala ya fara yana mayar da numfashi. Fally bai ce komai ba, dakatawa yayi na dan lokaci domin ganin ko Zumana zai yi kokarin guduwa, amma da mamakinsa sai yaga babu alamun haka. Amincewa yayi suyi maganar a gefe su biyu, yaji ya yarda dashi domin da yana son ya cutar da 'ya'yan ne da tuni ya cutar dasu.
-Me kake bukata?
Fally ya fada bayan sun koma gefe. A wahalce Zumana ya fara fadin:
-Ban zo ba da niyyar na cutar daku, na nemi nayi magana da kai ne domin nasan kai zaka fahimce ni.
-Kamar yaya?
-Ba ina son na kasheka bane, kawai nayi hakan ne domin ita, domin nasan ba zaka barni na rabeta ba idan lafiyarka kalau. Ina so ne na cika wani burina a kanta.
-Ni fa ban fahimci inda ka dosa ba.
-Na kamu da soyayyar bil'adama ce, kamar kai.
Ja fuskar Fally tayi tsabar bacin rai.
-Ba wai soyayyar Jinah ba, ta Sarah nake nufi.
Zumana yayi saurin fada domin ya lura kadan ya rage Fally ya fizgo zuciyarshi.
-Ba nazo bane domin yan tagwaye, domin ita nazo. Kuma shima na wani dan lokaci ne, nasan ba zai yiwu ba na har abada, dole zan fita daga jikin wannan saurayin. Amma... Ina son... Kasan me nake nufi... Yana fin karfina a duk lokacin da nake tare da ita. Ina rokonka gafara ka yafe mani cutar da kai da nayi.
Karyar da Zumana yake ta zubawa Fally kenan, tausayinsa ne ya kama Fally domin yana ganin kamar irin halin da yake ciki ne. Yana tsananin bukatar ace Jinah ta tuna dashi, ta kasance kowanne lokaci a tare dashi, yaji ta bude baki tace tana sonsa.
-Na fahimceka. Fally ya fada cike da alamun tausayi. Sai dai bai dace ka dauki jikin Abdul, Zaka haifar da babbar matsala ne tsakaninsa da matar babanshi bayan tafiyarka.
-Kana da gaskiya, ban yi wannan tunanin ba ni, na kasance sakarai mai biyewa son zuciyarsa ne...
-Yanzu ya tsakaninku yake?
-Ina tunanin tana sona sosai, ina nufin ta fara kamuwa da soyayyar Abdul ba ni ba.
Ya fada da yanayin damuwa. Shuru Fally yayi yana kare masa kallo, sai dai bai fahimci komai ba face tsantsar gaskiya a idon Zumana. Zumana yasan hakan na iya faruwa kuma da yake kwararre ne wajen iya controling yanayinsa da boye iya ainahin suffarsa ga mutane da kuma yan uwansa aljanu.
-Na fahimci wani abu, uwar 'ya'yanka bata iya ganinka, alhali kuwa ya kamata a ce tana ganinka domin 'ya'yan dake tsakanin ku saboda karfin jinin dake tsakaninku a yanzu.
-Eh hakane, ni kaina ban san ya zan yi ba, domin bata iya tuna komai na rayuwarmu a baya.
Fally ya fada cike da matsananciyar damuwa.
-Na fahimta, mahaifiyarka ko mahaifinka wani daga ciki yayi mata wankin kwalwa.
Ido Fally ya fiddo waje da alamun mamaki.
-Ta yaya ka... Wa ya koya maka duk wadannan abubuwan?
-Mahaifina.
-Ni nawa, ba mu samu lokacin da zai bayyana min komai da ya shafi duniyarmu ba. A hankali na fahimci babu komai da na sani a kan kaina.
-Zan iya taimaka maka.
-Taimako a kan me?
-Domin matarka ta tuna da kai.
-Da... Da gaske kake?
-Sosai ma.
-Kai, bana tunanin zai yiwu.
-Ka yarda da ni, akwai wani abokin mahaifina yanada karfi sosai kan duk wani sirri na duniyar nan tamu. Yana da mafitar kowacce irin matsala. Tsoho ne da ya shafe karnika da dama.
A take damuwa ta mamaye zuciyar Fally, tunawa da yayi da mahaifiyarsa lokacin da taje neman taimakon Hindu, kwatancen yayi kama da na Zumana. Wadda tayi ajalin mahaifiyarsa domin cetonsa.
-A'a, ba zan je ba! Ba zan iya sadaukar da kowa ba.
-Shi ba kamar Hindu yake ba.
Cewar Zumana kamar ya karanci tunanin Fally.
-Ka santa ne?
-Waye bai santa ba, shedan ne a suffar mace!
Bayan shuru da kuma zurfin tunani na dan lokaci da Fally yayi. Yace :
-Yaushe zamu je?
-Yanzu ma zamu iya idan kana so, wani abu kuma, za'a iya daukan lokaci baka dawo ba.
-Zai fi dai a ce anyi aikin da wuri, domin na gaji da wannan rayuwar, ina kusa da matata amma bata ganina.
-Na fahimceka. Cewar Zumana da tausayin Fally na karya a fuskarsa.
-Ina son kayi min wani taimako.
-Ina sauraronka.
-Ina son ka kula min da 'ya'yana kafin dawowata, hankalina ba zai kwanta ba idan na barsu su kadai, zan fi jin dadi a ce kana kusa dasu, kuma kaga kasan abubuwa da dama kan karfinsu.
Zumana ji yayi kamar ya kurma ihun dadi, ganin Fally ya kara saukaka masa plan dinshi. Kira yaran yayi, yayi masu bayani a takaice. Sai dai hankalinsu sam bai kwanta ba, domin basu yarda da wannan aljanin ba.
-Kada kaje baba. Cewar yar yarinya Aya.
-Dole na tafi 'yata, domin kasancewarmu cikin farin ciki ne ni da ku da kuma mahaifiyarku.
-To ka dawo da wuri. Cewar Ayu.
-Kar ku damu. Mu tafi! Ya karashe maganarsa ga Zumana.
Ba bata lokaci suka dauki hanya. Suna zuwa wani guri, Zumana yayi masa nuni da ya shiga wani dan karamin daki dake gabansu, da saka kafarsa cikin dakin yaji saukar mashi a gadon bayansa, wata azabatacciyar kara ya saki. kokarin sa hannunsa yayi domin ganin ya cire mashin amma ya kasa. Faduwa yayi kasa. Murmushin keta Zumana yake, wani aljani ne ya fito daga cikin dakin shi ma yana murmushi, babban abokinsa ne da ya fadawa duka sirrinsa. Su biyu suka kama Fally suka daure jikin bishiya da dioru. Igiyar da ake daure aljani ta yadda ba zai iya anfani da karfinsa ba.
-Da alama wannan gubar taka tanada karfi.
Cewar Zumana ga Aljanin da ya taimaka masa.
-Tantama ma kake a kan aikina?
Cewar abokin nasa.
-Ai daga yau na dena! Ni zan koma, ka tsareshi da kyau, kuma ina sonsa a raye na wani dan lokaci.
Bayan fadar haka, kamar walkiya ya dira wajen Sarah. Da yan tagwaye yaci karo.
-Yaushe babanmu zai dawo? Cewar Ayu.
-Ban sani ba, abinda kawai na sani idan ya dawo zaku kasance cikin farin ciki ku da Mahaifiyarku.
Ya fada da kudirin ko zai iya dawo da yardar da yan tagwayen suka yi masa a baya, shi yasa yayi masu magana cikin sanyi.
-Idan bai dawo ba da wuri, zaka kaimu wajensa mu mu dawo dashi.
Cewar Ayu cikin yanayi mai kama da gargadi.
Murmushi Zumana yayi, alhali cikin zuciyarsa tsoro ne fal, domin ya fara jin tsoron yaran. Bayan yaran sun juya sun tafi, tunawa yayi da wani babban bangare na plan dinshi, wani makirin murmushi. Kyabtawa da bismillah ya dira cikin dakin Sarah. Ihun tsoro Sarah ta saki da ta ganshi.
-Ta yaya ka shigo? Ka tsorata ni!
-Ina ta konkwasawa amma da yake kina nan kin zurfafa cikin tunanina sai baki ji ba.
Ya fada da murmushi a fuskarsa. Shuru Sarah tayi kafin tace:
-Gaskiya Abdul, nayi da na sanin abinda ya faru tsakaninmu, domin a yanzu haka na kasa hada ido da yar uwarka.
Ba tare da ya bata amsa ba, ya kama hannuwanta ya saka cikin nashi tare da sanya idonsa cikin nata. Wata azabatacciyar wutar sonsa taji na kara ruruwa a zuciyarta. Bata yi wata-wata ba ta hade bakunansu. Bayan wani dan lokaci ta janye bakinta tana kallonsa kafin tace : Manta da abinda nace, ba zan iya rayuwa ba babu kai, Ina sonka Abdul. Sosai Abdul yaji dadi. Ba tare da bata lokaci ba suka lula wata duniyar da sauran yan gidan basu san da ita ba. Haka suka cigaba da soyayyarsu, Sarah ta gama mutowa a kan Abdul, mutumin nan rijiya yake son jefata amma ita bata sani ba. Haka aljanin ya cigaba da anfani da wannan damar a plan dinsa. Ya Fara sawa Sarah a kai wai Jinah sonshi take, shi yasa take mata wasu abubuwan. Bata yarda da hakan ba sai ranar da ta jiyo Jinah na fadawa Nafisa : Ina son dan uwanki, yana da natsuwa sosai. Bata tsaya jin karshen maganar Jinah da take cewa : Ina jinsa kamar dan uwana, amma kwanan nan na kasa gane masa. Sai wata rana kuma da taga ita Jinah tana rungumar Abdul din. Hankalinta yayi matukar tashi, abinda bata sani ba duk cikin makircin Zumana ne. Daga ranar duk tsantsar soyayyar da take wa Jinah ta juye zuwa kiyayya. Yarinyar da ta dauka tamkar diyar cikinta, take matukar so, yau gashi ta zamar mata wata da take tunanin zata kwace namijin da tafi so a rayuwarta. Jinah lura tayi da wannan kiyayyar, take zuciyarta ta karye, ba zata iya jure ganin wadda ta dauka a matsayin mahaifiyarta na nuna mata irin wannan tsanar ba. Wata rana ta kudiri sai taji ko me ta yiwa Sarah domin ta nemi yafiyarta.
-Dan Allah Sarah ki fada min ko nayi maki wani laifi ne?
Nan fa Sarah ta shiga fada ba dali, inda ta shiga ba ta nan take fita ba. Daga karshe tace Jinah ta fitar mata daga gida. Kasa motsawa Jinah tayi tsabar firgicin mamakin jin wannan daga bakin Sarah.
-Ki fice min daga gida! Ki fita nace!
Abinda take ta maimaitawa kenan, tana tasa keyar Jinah kan taje ta kwashe kayanta.
-Kayi wani abu dan Allah, baka ganin korarta zata yi daga gidan?
Cewar Nafisa ga dan uwanta, bai ko bi ta kanta ba yayi shigewarsa daki. Takaici ne ya kama Nafisa domin ta lura kamar ma farin ciki yake da faruwar lamarin. Shi kuwa abinda yake so kenan Jinah ta bar gidan ita da 'ya'yanta shi kuma sai ya bisu da niyyar taimaka masu, inda zai kaisu a matsayin masauki dama cen ya zuba tarko sai su kama tagwayen suyi yanda suke so suyi dasu.
Nafisa bin Jinah tayi cikin daki tana bata hakuri kan dan Allah kar ta tafi.
-Ba zan iya tsayawa a nan ba, gidanta ne kuma ita