Showing 72001 words to 72189 words out of 72189 words
Chapter 25 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt
ya samu Jinah, sautin kukan Aya kawai ke tashi a falon.
Fally nufa yayi da Jinah gidan su da ba nisa da na su Sarah, yana shiga ya kaita ɗakin su, ya kwantar da ita bisa gado. Shi ma kwantawa yayi kusa da ita, a take shi ma rai yayi halin sa. Amma kafin ruhin sa ya karasa fita daga jikin sa baki daya, yace :
-Me kike tunani Jinah, dubunnan shekarun da suka rage min na rayu ba tare da ke ba, ba zai yiwu ba. Nima dole na mutu, yayin da nasan kema baki duniyar. Zuciya ta tana bugawa ne a tare da taki, babu abinda zan yi a wannan duniyar babu ke, ni da ke mun haɗu mun zama ɗaya, kuma ɗaya bata taɓa bada biyu ba. Sai mun haɗu a duniyar matattu, Habibty.
Jinah was, is, kuma forever will be matar aljani.
-----------------------------------------
ALHAMDULILLAHI, c'est fini lol. Bye bye matar Aljani.
Ina fata kun faɗakartu, nishanɗantu, kun kuma ilmantu da wannan dogon labarin nawa. Sannan ina mika sakon gaisuwa ta ga masoya wanda suka jima suna bibiyar wannan labari. Allah ya bar hannu da kaifin ido. Ameen ya Allah