Showing 66001 words to 69000 words out of 72189 words
Chapter 23 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt
tun kafin ta iya rarrafe, shi ya taimaka mata ta iya rarrafe, ya taimaka mata ta iya tafiya, ya kula da ita, ya saka kan sa a haɗari domin ta, ya sadaukar domin ta, ba sau ɗaya ba. Yanzu ya manta da ita, amma kuma zuciyar sa da ruhin sa sun san ita ko wacece. Akwai alaƙa mai girma tsakanin Jinah da Fally kuma babu abinda zai canja hakan.
-Ta yaya kike son na taimake ki?
-ƴaƴana, kafin ka shiga ɗaki na, nayi mafarkin suna cikin haɗari. Gashi yanzu ina tunani, kuma ina jin tsoron abi..abinda zai same su.
-ƴaƴan ki?
-ƴaƴan mu, ƴan biyu, Aya da Ayu!
-Su..suna tare da shugaba ta, Hindu.
-Mene? A'a! Ka cece su, nayi maka alƙawarin, zaka samu amsoshin tambayoyin ka. Hindu tana amfani da kai ne, kada ka yarda da wannan sheɗaniyar.
-Ke ma ba zan yarda da ke ba.
-Kalle ni cikin ido Fally, ka yarda da ni, dan Allah.
Dan jim Fally yayi kafin yace :
-Shikenan!
Da falar haka, ba'a dau wani lokaci ba, sai gasu sun bayyana a maɓoyar Hindu. Da isar su wurin, kasa ta fara girgiza, sama tayi jawur. Duk da wannan bai tayar da hankalin Jinah ba, dalilin tsinkayo ɗanta da tayi a kwance, jini na zuba, ga kuma wani mashi soke a daidai zuciyar shi. Numfashi ne ya fara gagarar Jinah, yin ƙarar ma ta kasa, lokaci guda ta koma tamkar marar baki. Ɗanta ya mutu, bata gasgata hakan ba, sai da taga ya koma normal yaro, da ba zai wuce shekaru uku ba. Idan jin zafi yana kashe mutum a take, toh da tuni Jinah ta jima da mutuwa domin zafin da take ji, ya wuce na misali.
Dauda yana nan a wurin, yana kallon ta, ba tare da ya iya matsowa kusa da ita ba, bare ya rungume ta, ya tayata bakin ciki, domin kafafuwan sa tamkar an saka siminti. Ba kuma zai iya faɗa mata : Kada kiyi kuka Jinah, kwantar da hankalin ki, kiyi juriya, Allah yana tare da ke, komai zai wuce, ke jaruma ce... saboda babu murya.
Shi kuwa Fally, ba tare da sanin dalili ba, wata shawara ta zo masa a kai, ya kashe wannan Hindun, abinda bai sani ba, shi ne : Karfin ta ya karu, ta yanda lokacin da yayi ƙoƙarin kai mata farmaki, naushi ɗaya tayi masa, sai gashi ya bugu da bango, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake kai mata wani farmakin. Wannan karon, a daidai ƙafafuwan Jinah ta jefo shi.
-Ki bar nan! Ni zan ji da ita! Ki gudu!
Cewar Fally, kafin ya sake miƙewa; Aya! Jinah ta shiga kiran sunan ƴarta, idanu ta shiga rarrabawa, cen ta hango ƴar tata a kwance. Wani karfi ne yazo mata, ta ɗauka a guje ta nufi wajen ƴarta, ɗaukan ta tayi ta rungume.
Gudu Jinah take iya karfin ta, ba tare da tasan inda take nufa ba, hawayen kuwa sun kasa daina zubo mata. Wata iriyar faɗuwa tayi, lokacin da Hindu ta dira gaban ta.
-Ita! Babu inda zata je!
A yanayin yanda Hindu tayi maganar, zai iya fasa kunnen mutum tsabar rashin dadi da tsoratarwa. Ita kan ta Jinah sai da taji zuciyar ta, ta canja bugu tamkar ana buga ganga. Fally ne ya bayyana a gurin tare da kaiwa Hindu wani mahaukacin naushi, a nan take su biyun suka bace, ita kuwa Jinah ta cigaba da gudun ta. Hakan ce tayi ta faruwa, kuma a ko da yaushe sai Jinah tayi tunanin tasu ta ƙare.
Fally ya gaji, kawai ya riƙe wuta ne, kuma kare kai kawai yake yi, domin ba zai iya hada ƙarfin sa da na Hindu ba, sake taso shi daga mutuwa, shi ya kara masa ƙarfi, sai dai ita Hindu nata ninkin ba ninkin nasa ne, domin cen dama ita mai ƙarfi ce, gashi kuma ta ƙara da na ɗaya daga cikin ƴan biyu, duk da ba duka ƙarfin Ayu ba ta kwashe, domin sai an ɗau lokaci kafin ta same shi baki ɗaya. Fally kam yayi ƙoƙari tunda har ya iya kai wannan lokaci yana gwabzawa da ita.
Amma yanzu, Karfin sa ya ƙare, ganin tsayuwa na shirin gagarar sa, ya shammaci Hindu, ya ɓace da Jinah, ya kaita gida. Sannan ya haɗa wata katangar tsafi a bakin kofar da ta hana Hindu shigowa.
-Gata nan zuwa! Gata nan tafe! Sheɗaniya!
Yo kan Jinah su Sarah suka yi, cike da ruɗu da farin cikin ganin ta, tuni suka dawo hayyacin su, sai dai yanzu kuma wani sabon tsoron ne ya shige su, jin abinda Jinah ta faɗa.
-Ku mu gudu daga nan, za.. Sauran kalaman nata suka tsaya a baki, ganin Fally ya faɗo daga sama a kan idon su. Kafin suyi wani yunƙuri tuni Surayya ta dira gaban su, cikin wata mummunar shiga. Jinah kara ƙanƙame ƴarta tayi cikin ƙirjin ta, Nafisa ta ɓoye bayan Sarah da Abdul.
Ita kuwa dan ta ƙara tsorata su, sai ta ɓacewa ganin su. Jinah ji tayi ana ƙoƙarin ƙwace mata ƴa ba tare da tana ganin ko waye ba, faɗa ta shiga yi iya ƙarfin ta domin ganin ƴarta tata bata bar jikin ta ba. Sake bayyana Hindu tayi rai a ɓace.
-Ya..ya aka yi na kasa raba ku?!
Hindu ta faɗa cike da ƙaraji da jin haushi.
-Ki bani ita, ni kuma zan rabu da ku!
Hindu ta sake faɗa, ita kuwa Jinah taƙi sakin ɗiyar. Hindu kallon Sarah kawai tayi, ita kuwa ta shiga kokowar ƙwatar numfashi kamar an shaƙe ta.
-Ki rabuta da ita, dan Allah!
Jinah ta shiga roƙon Hindu. Abdul ne ya taƙarƙare, ƙawadawa Hindu wani benci dake kusa da shi. Hakan da yayi kuwa, yayi nasar dawo da numfashin Sarah. Sai dai kuma hakan ya ƙara fusata Hindu, nuna hannu kawai tayi sai ga Abdul yayi sama, kanshi ya gauru da bango, ya faƙi sumamme.
-Abdul! Dukan su, suka kira sunan sa a tare. Da gudu yar uwar shi tayi kan sa tana jijjiga shi, tana kuka.
-Kin raba ni da ɗana, ki ƙyale min ƴata, ki bar min ita! Ki bar min ita!
-Ta kashe min dan uwa, mama!
Aya ta faɗa da wata ƙaramar murya, ta faɗi hakan ne ba tare da bakin ta ya buɗe ba. Da alama gubar ta fara raguwa.
-Ayu ya mutu mama, na sani, kuma naji a jiki na. Aya ta sake faɗa, har wa yau tana kwance jikin maman ta.
Hakan yasa Jinah ƙara shiga cikin ƙunci, kalamn ƴarta sun taɓa ta.
-Bani da lokaci! Ki bani ita yanzu kafin ta wartsake daga gubar, ko kuma na kashe su duka.
Hindu ta fada a fusace tana nuna su Sarah, Jinah kuka take iya ƙarfin ta, zaɓi tsakanin ƴarta ko Sarah, wadda ta zame mata kamar uwa, ƴar uwa, babbar aminiya... a taiƙace ita komai ce gareta. Sai kuma Abdul da Nafisa, mutanen nan biyu da take matuƙar so, waɗanda take jin kamar akwai wata alaƙa mai ƙarfi tsakanin su... Ta yaya zata iya wannan zaɓi.
-Ni ki ɗauke ni, ki rabu da su. Cewar Sarah. Wata mahaukaciyar dariya Hindu tayi.
-Babu wani amfani da zaki min!
-Mama, ki barta ta ɗauke ni. Cewar Aya, wadda maman ta ce kadai taji hakan, jin maman tata na shakku tace :
-Ki yarda da ni mama, komai zai tafi daidai.
-Ki ɗauke ta, amma kafin nan ki barsu su tafi, ki barsu su kai Abdul asibiti.
Cewar Jinah cike da dauriyar zuciya,tana mai miƙawa Hindu Aya. Ita kuwa Hindu tsabar murna, kamar ƙyaftawar ido, ta kai su Abdul asibiti, sannan ta dawo ba ɓata lokaci, ta ɗauki ƴar yarinya Aya, sai dai farin cikin nata bai wani ɗauki lokaci ba, domin Aya tuni ta ɓacewa ganin ta, daga kan hannayen ta.
-A'A! AHHHH!!! Hindu rai a ɓace, tayi wata kururuwa, ƙasa ta shiga girgiza, tuni guba aikin ta ya ƙare a jikin Aya, Hindu bata yi tsamanin abun ba zai mata sauki ba kamar yanda tayi fata. Ƙoƙarin kama Jinah take domin tayi garkuwa da ita, kafin Aya tayi wani yunƙuri, bata kai ga kudirin ta ba, taji wani abu na mata tafiya cikin jiki, kafin tayi ƙoƙarin kakkaɓe wannan abun, tuni har ya kai ga zuciyar ta. Wani masifaffen zafi ne taji da yabi kowanne sassa na jikin ta, razananniyar kara ta saki, kara mai bala'in karfi, karar da tafi wacce bokanya Karaba tayi, lokacin da Kiriku ya saka hakorin sa domin cire ƙayar dake a gadon bayan ta, wadda ta mayar da ita matsafiya.
Hindu durkushewa tayi kasa tana cigaba da ihun azaba, lokaci kaɗan Jinah ta hangi ƴarta, haƙoran ta datse kan ƙirjin Hindu, da take ta ihun neman taimako.
-Ki dakata Aya, cewar Jinah, sai dai bata da alamun dakatawa, kamar wani shedani ya shiga jikin ta. Da hakoran ta, ta yage duka fatar jikin Hindu, sannan ta saka hannun ta, ta fizgo zuciyar Hindu da tuni ta jima da mutuwa. Kuma Aya ta sani amma duk da haka bata dakata ba, kuma bata daina maimaita :"Ita ta kashe min dan uwa!" ba, hawaye na zubo mata. Ganin haka, Jinah ta taso ta janye ta, tare da rungume ta, tana lallashin ta.
-Jinah.
Dauda ne da ya karaso wajen ya kira sunan ta. Hannayen sa dauke da gawar Ayu.
-A'a, a'a, ba zan iya jure kallon sa, ba zan iya ba!
Jinah ta faɗa tana kuka, ganin gawar ɗanta. Ɗaki Dauda ya wuce, ya kwantar da shi. Sannan ya dawo da niyyar lallashin Jinah. Kukan Jinah ƙaruwa yayi da ta tsinkayi Fally a kwance dan nesa da ita, rarrafawa tayi wajen sa, ta shiga kokarin tashe shi.
-Ka tashi Fally, kar ka barni, ba yanzu ba, ɗan mu ya mutu, kar ka tafi ka barni!
-Bai mutu ba, cewar Aya.
-Toh me yasa yaki tashi?
-Gangar jikin sa ce ta mutu, amma shi yana raye.
"Toh meye banbanci ya mutun kenan." Jinah ta fada cikin ranta, tana mai shashantar da maganar yar tata, kafin ta cewa Dauda ya tafi da Aya, su ɗan barta ita kaɗai na wani dan lokaci.
Dora kanta tayi kan ƙirjin Fally, ta shiga magana magana ita kaɗai :
-Ku biyu a rana ɗaya, ta fada tare da jan dogan numfashi. Ka kula min da Ayu na idan kuka haɗu, na san shi da taurin kai, amma kar ka dukan min shi, yaron kirki ne, ka faɗa masa ina son shi, da dukan zuciya ta, ba zan taɓa manta shi ba, ba zan taɓa mantawa da ku ba.
-Har yanzu ina nan!
Kamar daga sama taji anyi maganar.
-Fally?
Ta shiga waige waige.
-Ruhina har yanzu yana nan Jinah!
Ya sake maimaitawa, gangar jikin da ke gaban ta, babu alamun rai a tare da ita, bata numfashi, bata magana, amma gashi tana jin muryar sa.
-Toh ka tsaya a nan dan Allah, kada ka tafi, jin alamun ka ya ishe ni, ka tsaya a tare da ni.
-Ba zan iya ba, ko ba jima ko ba daɗe dole zan ɓace na har abada.
-Kada kace haka, b..ba..bana son..
-Ina tune da komai Jinah, ta yaya zaki so kara kasancewa da ni bayan abubuwa nai miki? Kamata yayi ki tsane ni.
-Ban sani ba, kuma bana ma son na sani, idan ba soyayya ba, babu abinda nake ji game da kai...
-Jinah! Bata karasa abinda take son faɗa ba, sakamakon jin Dauda da ya ƙaraso wajen shi da Aya, ya kira sunan ta.
Lokacin da Jinah ta ɗaga idanu ta kalle shi, ya riƙe ƴar wuƙa a hannun sa, ya saita ta daidai zuciyar sa. Yanayin fuskar sa ya canja, kafin tayi wani yunkuri tuni ya cakawa zuciyar tashi wuƙar.
-Dauda!!!!
Jinah ta ƙwalla ƙara, alhali kuwa ƴarta, murmushi ne akan laɓɓanta, tana wani mo-motsa hannuwa, bakin ta na faɗar wasu kalamai, ba tare da Jinah ta fahimci wani abu ba. "Kar dai ita ma ta koma sheɗaniya bayan abinda ta yiwa Hindu". Tunanin da Jinah ke yi kenan.
-Fally! Fally! Shi ma shuru ba amsa, ta rasa su baki ɗaya.
------------------------
A très long chapter, ina fata zaku ji dadin ta!!!
Mu hadu chapter ƙarshe idan Allah ya kai mu.
Merci de toujours être là 💪💪
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story
END
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Jinah dafe kan ta tayi sosai da hannayen ta, kamar tana tsoron ya tarwatse, zaune take a kasa, kafin kuma tayi kwance tare da rufe idanunta. Ta gaji sosai, babu wani sauran ƙarfi a jikin ta. Sosai take fatan ace duk wannan abun, mafarki ne ba zahiri ba.
-Na gaji, na gaji da wannan rayuwar, zuciya ta na ƙuna, jiki na ya gaji. Shin yaushe duk wannan zai ƙare, wata ƙila sai ranar da na mutu. Me yasa Allah ba zaka ɗauke ni ba? Ina roƙon ka ka ɗauke ni..!
Jinah ke faɗar haka, idanun ta a rufe, cikin murya mai ban tausayi. Tana magana ne ita kaɗai, sai dai bata karasa kalaman ta ba, taji an ƙatse ta da cewa :
-Astagfirullah! Kada ki ƙara faɗar haka! Idan ba so kike na sake mutuwa ba.
-Fally! Jinah ta faɗa tare da miƙewa da sauri tana mamaki. Eh muryar Fally ce, sai dai lokacin da ta buɗe idanu, Dauda ta gani.
-Me..m..me..
Kalamai suka gagara fita daga bakin ta, ƴarta ta gani tana mata murmushi.
-Mama, su ne! Cewar ƴar tata. Baba da uncle Dauda!
-Zo nan , matso kusa da ni. Cewar shi. Jinah kasa motsawa tayi. Matsowa yayi ya kama hannun ta, take Jinah taji wani abu. Janyo ta yayi jikin sa, sannan ya dora bakin sa kan nata, nan taji wani lantarki ya ratsa ko'ina na jikin ta. Fally ne kaɗai ya iya saka ta a irin wannan yanayin, kuka ta fara sosai, kukan farin ciki sannan ta rungume shi sosai kamar zata tsaga shi ta shiga. Zuwa cen ta sake shi, sannan ta rungume ƴarta tana kukan farin ciki.
Bata san ta yaya hakan ta yiwu ba, bata san ina gangar jikin Fally dake wurin take ba, ko kuma ta yaya Dauda da ya cakawa kan sa wuƙa ɗazun, yake a gaban ta yanzun, bata san ta yaya duk hakan ta faru ba, kuma bata damu da ta sani ba. Gashi sun dawo mata su duka biyun, a cikin gangar jiki daya : Kyakyawar fuskar Dauda, murmushin sa mai sanyaya rai, murɗaɗɗen jikin sa, namijin gaske, namijin da ya cece ta lokacin da take tsaka da neman taimako, namijin da ya juyawa duka dangin sa baya domin ta, namijin da ya dawo mata da murmushi a lokacin da take cikin ƙunci, namijin da ya sota duk da yasan tana son wani, namijin da bata fatan ta rasa shi.
Da kuma daɗin ƙarin ruhin Fally, namijin da idan zata tsaya ta ɓata lokacin bada labarin abubuwan da yayi domin ta tun yarintar su da kuma girma, to ba zata gama ba, namijin da bugun zuciyar sa yafi tsananin gudun jirgin kasa domin sonta, namijin da ta dinga jin kewar sa, alhalin bata ma iya tuna ko shi waye ba.
Samun wannan mazajen, ba karamin farin ciki bane a gare ta, duk da zata yi kewar fuskar Fally, yana nan, tana jin sa a kusa da ita, hakan ma ya wadace ta. Ƴarta, rabin ranta, tana nan bata sauya ba, bata koma sheɗaniya ba. Wannan farin ciki ne marar adadi gare ta!
-Ina son ki, mama! Cewar Aya, kamar tasan tunanin ta mahaifiyar tata take. Murmushi Jinah tayi mata, sannan ta bata amsa :
-Nima haka gimbiyata, nima haka... ƙarasa kalaman nata tayi tare da fashewa da kuka, kafin ta nufi dakin ta inda ta tarar dashi a kwance, Ayu. Shine ya faɗo mata a rai, ƙarasawa tayi kusan shi tare da rungume shi, ƙara fashewa da wani sabon kukan tayi lokacin da ta haɗa jikin ta da nashi.
-Kiyi shuru, ki daina kuka Jinah. Cewar Dauda ko kuma muce Fally, da ya shigo ɗakin yana ɗauke da Aya, da ita ma take cikin damuwa, na rashin wani ɓare nata, kuma abokin ta. Langwaɓar da kanta tayi jikin baban nata, tare da rufe ido, domin bata son kallon gawar ɗan uwan nata.
Daƙyar Fally ya shawo kan Jinah, ta aje gawar ɗan nata, tare da komawa wani ɗakin daban. Sauka Aya tayi daga jikin mahaifin nata, ta kwanta kan gado kusa da mahaifiyar ta, tare da sauya kamanni zuwa na ɗan uwan ta. Murmushi Jinah tayi tana hawaye tare da shafa fuskar ɗan nata.
Sunan sa ta kira, duk da tasan ba shi bane. Ƙara janyo shi tayi tare da ƙanƙame shi jikin ta.
-Duk lokacin da kika yi tunanin sa, ki faɗa min, ni kuma zan zama shi, mama. Hakan zai sa ba zaki yi kewar sa ba.
Cewar Aya, cikin kamannin ɗan uwan ta.
Murmushi Jinah tayi tare da gyaɗa mata kai. Ƙoƙarin barin ɗakin take, tunawa da tayi da su Sarah. Amma Fally/Dauda ya tabbatar mata da zai kula da su, ta koma tayi kwanciyar ta. Ba a jima ba, Jinah bacci ya ɗauke ta, tana rungume da ƴarta, ita ma Aya bata jima ba tayi baccin. Fally ya dan jima a ɗakin yana kallon su, cike da jin zafin ganin halin da suke ciki ba tare da iya yin wani abu ba. Yana jin zafi domin yasan haƙƙin da ya gagara saukewa na daga cikin wahalar da Jinah take ciki.
Fita yayi daga ɗakin, shi kaɗai, ya shiga rera kuka. A gaban Jinah ya iya riƙe hawayen sa, a gaban ta, bai son ya nuna mata gazawar shi. Amma mutuwar ɗansa ta taɓa shi. Durkushewa yayi a ƙasa, ya jingina da bangon ɗakin, ya haɗa kai da gwiwa, yana zubar da hawaye.
Abubuwa da dama sun saka shi kuka, bugu da ƙari mutuwar Ayu. Yanzu ya gane iyayen shi sunyi gaskiya. Da bai auri bil'adama ba da duk wannan bai faru ba.
Fally yayi nadamar abubuwa da dama, abubuwa da dama yaso ina basu faru ba; kamar kowannen mu. Sau tari muna aikata kuskure, wanda daga baya mu zo muna da nasanin aikata shi. Sai dai da na sani, baya wani canja babban abu, idan har bayan mun yi nadama, bamu daina aikata kuskuren ba. Gyara kuskure, shi ne mantawa da shi da sakawa a rai ba zamu sake aikata shi ba.
Fally ya ɗaukar wa kansa wannan alƙawarin, Jinah ba zata sake cutuwa ba, ta dalilin sa, har abada, ba zai sake maimaita kuskuren da yayi a baya ba, tare da yin alƙawarin zata zama macen da tafi kowacce farin ciki a