Showing 33001 words to 36000 words out of 72189 words

Chapter 12 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt

17 Mar 2026

40

sata kuka. Ba ita ta haifeta ba, amma tana jinta tamkar mahaifiyarta, kuma cilas ne idan Da ya shiga mawuyacin hali itama uwar ta tsinci kanta.

Hakama Abdul da Nafi suna cikin firgici sosai. A cen tsakiyar kwakwalansu neman duk wani abu da zai warware masu kullin dake cikin wannan al'amari suke. Abinda basu sani ba shine basu ga komai ba a kan tashin hankalin da ke gaba.

=============================

Salam, fatan kowa yayi sallah lafiya? Allah ya nuna mana ta wata shekarar da ran da lafiya.

Ameen


Allez à bientôt pour la suite. 😍


©El_Ashtar


Oooh na manta, ku dinga hakuri da kuskuren typing, ni kaina ina ganinsu duk lokacin da nake sake karantawa....

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story

CHAPTER 14

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp



Kwanaki da yawa sun shude da mutuwar Dauda, sai dai babu wani sauyi da ya samu, komai yana nan kamar a baya. Ba mai yiyuwa bane, me yasa har yanzu ta kasa ganina? Me yasa ta kasa tuna ni? Idan saboda ta fada soyayya da Dauda ne yasa ta manta ni, ai yanzu kuma baya duniyar, ya kamata ta tuna ni tunda yanzu baya nan. Maganar da kullum Fally yake maimaitawa kenan. Alhali, a cen tsakiyar kwalwarsa yasan amsar duk wannan tambayoyin, kawai dai ya kasa yarda ne. Yanzu ya tabbatar Jinah ba wai ta mantashi bane domin tana soyayya da Dauda, mahaifiyarsa ce, tayi sanadin da abar kaunarsa ta manta da duk wata rayuwa da tayi dasu. Yana jin takaicin abun sosai, domin shi bai ga wata hujja da zata saka mahaifiyarsa yin hakan ba, sanin yadda duka biyun suke son junansu, ga kuma duk sadaukarwar da yayi domin kawai kasancewa da Jinah. Wani barin na zuciyarshi yana ganin kawai Jinah amanarsa taci, ba sonshi dama take ba.

-Kai ne Babanmu ko? kananun muryaoyin suka dawo da Fally daga dogon tunanin da yake. Murmushi yayi har kunne ganin yan tagwaye ne da tuni suka fara magana.

-Eh! Na jima ina jiran wannan ranar da zaku fara magana, ko ba komai kadaicina zai ragu.

-Idan kai babanmu ne, me yasa mama bata ganinka? Kuma bata taba maganarka ba? Aya ce tayi masa wannan tambayar, walwalar dake fuskar baban nasu ta gushe.

-Labari ne mai tsawo! Fally ya fada.
Matsowa Ayu yayi wajensa tare da dora hannunsa akan goshinsa.

-A'a kar kayi haka! Aya ta fada tare da janye hannun dan uwan nata da sauri.

-Me? Meye yake son yi? Fally ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.

-Duba rayuwarka ta baya, sanin duk wani labari na rayuwarka da kace mana mai tsawo ne.

-Da gaske, zaku iya yin hakan?

-Muna iya yin fiye da haka ma. Ayu ya bashi amsa.

-Tabbas, ansha bamu labarin abubuwan da irinku wanda rabinsu aljanu rabinsu mutane ke yi, amma ban taba samun nasarar ganinsu ba. Sai gashi yau gaku kuma a matsayin 'ya'yana. Dole aljanu su shiga farautarku, amma karku damu zan kasance a kullum domin kareku.

-Mune zamu ce maka kar ka damu, ba zasu iya yi mana komai ba.

Cewar Ayu. Murmushi Fally yayi, tunawa da yayi da kuruciyarsa, kamannin Ayu da komai kamar shine yayi kaki ya zubar.

-A'a Dana, yawan fariya, yana kashe yarda. Zan so ku gwada min duk wani karfin da kuke da.

-A gaskiya, bamu san iya adadin karfin dake garemu ba, abubuwan suna zuwa ne lokaci lokaci.

-Oh na gane, Aya fada min me yasa kika hana dan uwanki yasan labarina?

-Saboda ina so ne kai ka bamu labarin da kanka! Babu ladabi idan muka bincika labarinka ba tare da izininka ba.

-Dakyau 'yata haka ake so, Ayu ya kamata ka dinga koyi da yar uwarka.

-Eh, ai ita a komai sai ta zake.

Dariya sosai Fally yayi kafin yace:
-Shikenan bari na baku labarina, Ni da mamanku tare muka taso tun muna kanana, tun lokacin na fahimci ba daya muke ba, ta banbanta da duk wanda da ke yankin mu. Da farko na fara magana, ita kuma a'a. Na fara tafiya, amma ita a'a, ina iya yin abubuwa da dama, da aljanu ke yi, amma ita a'a. Idan muka ga wani abu na cutarwa, ni zan iya bacewa amma banda mamanku, anan na fahimci nine ya kamata na kula da ita, na kareta daga duk wani da zai yi kokarin cutar da ita. A koda yaushe muna tare, zan iya fada da kowa saboda ita. Haka lokuta na shudewa, ina cigaba da zama mai bata kariya da kuma jin ina zama ita, ita ma tana zama ni. Wata rana, ba zan wuce shekara 13 ba, muka je wajen wani wasan dambe da ake shiryawa a yankin mu, akwai wani matashin aljani da ya dan fimu shekaru, ba a yankinmu ba yake, dalili kuwa ban taba ganinsa ba ko jin labarinsa ganin yanda yake ta dambe yana zubar da maza a kasa, domin da a yankin mu yake to da tuni labarinsa ya tsayawa kowa a baki. Ana cikin wasa na hangeshi ya nufi inda Jinah take zaune, zaunawa yayi kusa da ita suka fara fira. Babu mai iya yin haka a yankin mu. Duka sun san Jinah mutum ce, shi yasa babu mai rabenta idan ba cutar da ita ba zai yi. Dariya Jinah ta fashe da ita da alamu firar da suke tana mata dadi, tuni wani haushi ya turnukeni na nufi inda suke, finciko Jinah nayi muka nufi hanyar gida. Zai fi mun a ce shekara dari za'a yi ana dukana ba tare da tsayawa ba, da ganin Jinah tare da wani kuma har alakarsu ta wuce abota. Anan na fara fahimtar ina sonta sosai, ta yanda komai zan iya yi saboda ita. Haka komai ya cigaba da tafiyar mana cikin jin dadi, domin itama tana sona da dukkan zuciyarta, ina da yakini akan cewa mamanku ta gari ce, batada keta ga kowa, zuciyar zinare ce da ita, ita tilon fure ce a tsakiyar sahara, ita...

-Mun gane baba, ka cigaba.
Cewar Ayu yana murmushin yanda baban nasu ya fara mayar da labarin tamkar waka.

-Iyayen mu basa gajiya da nuna mana kuskuren da muke son tabkawa, abu ne da ba zai yiwu ba kuma anyi hani da hakan. Sai dai mu bamu taba baiwa maganarsu muhimmanci ba. Komai yana tafiyar mana daidai ni da mamanku har ranar da muka shirya zuwa mu daurawa kanmu aure, wanda shine sanadin wargajewar duk wani farin ciki nawa, shine yayi sanadin abar kaunata ta manta dani, kallon soyayya ya kare tsakaninmu. Ta daina ganina indai ba ni na nuna mata kaina ba, kuma idan nayi haka, tsorata take. Sam ta kasa tunani.

-Amma me yasa, ina nufin me ya faru ta kasa tunawa da kai?

Aya ta tambaya.

-Ni kaina ban sani ba, bani da tabbacin... yauwa ya isa haka yanzu ku je kuyi wasa, wata rana ma cigaba.

Ganin baban nasu babu abinda zai kara fada masu suka juya zuwa gurin wasansu. Murmushi Fally yayi domin yana tunanin wannan ita ce hanyar da zai iya dawo da memorin Jinah.

(.....)

Tun ranar da raunukan Jinah suka bace, bata kara samun kwanciyar hankali ba, duk ta wani hargitse kamar mahaukaciya, kullum tana rakube cikin daki, idan ka ganta waje to ban daki zata shiga. Abinda yafi daga mata hankali ma, yan tagwayenta da suka fara magana, magana da kalmomi daki daki kamar manyan mutane... Cewa take ko dai ta fara cin kai ne. Yaran da basu kai ga cike shekara daya da haihuwa ba, bai dace ace suna magana daidai ba, ta kara tabbatar da ta haukace, sai ranar da taga yaran sun bace a kan idonta kuma sun bayyana, sai tace kawai duk cikin haukan da take ne kwalwarta ke shirya mata irin wannan abun.

-Ina son magana da ke Jinah.
Cewar Sarah tare da zaunawa kan gadon kusa da Jinah.

-Ki yimin magana dan Allah Jinah.
Ta maimaita ganin Jinah bata da niyyar bata amsa.

-Ni ya zan yi? Ya zan yi... Na haukace Sarah!

Cewar Jinah tana mai saka kanta tsakan kafafuwanta.

-Me yasa kike wannan tunanin? ko saboda abinda ya faru, to ai mu ma muna a wajen, koko dan yan tagwaye suna ta saurin girma ne, suna magana kamar manyan mutane... Eh ba ke kadai bace kike ganin wannan abun ba, kinga kenan idan mahaukaciya ce ke, to mu ma mahaukata ne. Abun da tsoro na sani, amma me yasa ba zaki yarda da cewa wannan ikon Allah ba ne, ba a koda yaushe ba ne muke fahimtar abubuwan dake faruwa damu, wasu abubuwan basa fassaruwa. Mutuwar Dauda ba abu bane mai dadi garemu baki daya, fada mun wa yake iya yaki da kaddara? Zamu iya goge rubutun da bamu ma san yana rubuce ba? Wata rana kila zaki fahimta, amma kafin wannan ranar, kiyi rayuwarki kamar yanda tazo maki a yanzu.

A lokacin ne Jinah ta fara yarda da wasu abubuwan. Rungume Sarah tayi na dan wani lokaci kafin taji an dafata a kafada. Nafisa ce.

-Nagode. ta fada kafin ta mike ta nufi tsakar gida, tarar da yaran nata da Abdul tayi suna wasa.

-Nima nazo ayi wasar da ni!
Ta fada tana kallonsu tare da murmushi.

Murmushin jin dadin ganinta Abdul yayi, su kuwa tagwayen a guje suka nufi uwar tasu.

Abdul yace
-Naji dadin ganinki. Har cikin ransa yake fadar haka, domin baya jin dadin ganin halin da take ciki, yana ganin tunda yanzu ba Dauda shine wanda ya kamata ya zama mai tallafa mata.

Bayan ta gama da Abdul ta dawo kan yaranta. Rungumesu tayi kwarai kamar zata maidasu ciki tana maimaita ku yafe mani, hawaye na zubo mata kamar fanfo. Tana dana sani sosai na watsi da tayi da su kwana biyu.

-Kar kiyi kuka mama, mun fahimta.

Cewar Aya. Idan da yarinyar nan ta fadi haka awannin da suka wuce, to fa Jinah zata iya zundumawa da gudu, tace ta haukace, abinda taji ba gaskiya ba ne.

-Ina sonku sosai, rabin raina.

Nafi da Sarah suka nufi kitchen domin sarrafa abinda zasu ci, suka bar Jinah da Abdul da kuma tagwaye da kamar walkiya suka bace daga wurin ba tare da mahaifiyar tasu ta lura ba.

-Har yanzu babu wani labari game da mahaifinku?

-A'a, wannan ma ba wani abun damuwa bane, domin ya saba irin wannan ba tare da mun samu labarinsa ba. Abinda yafi daure mun kai yanayin da ya shiga da kuma maganganun da ya fada kafin ya tafi.

-Nima haka ban fahimci komai ba.

-Mu bar dai maganar a yanzu, me zai hana ki tashi mu zagaya gari?

-Toh bari na dauko mayafina.

-Eh gaskiya kam, ko dan kar mutane suyi ta rantan na kare ba.

Dariya dukansu suka yi kafin taje ta dauko mayafinta.

A hanya labarin dariya Abdul yake ta bata, tana ta kyalkyata dariya.

Cikin dariya tace
-Dan Allah ka dena, ba zan iya ba, cikina ya fara ciwo. Kamar Dauda kake sai ku nemi kashe mutum da dariya.

Shuru tayi tana hawaye tunawa da tayi da Dauda.

Kwantar da kanta Abdul yayi a kirjinsa, yana lallashinta, shi kansa yana kewar Dauda sosai.

-Hum yaran yanzu ba kunya, suyi ta manne mannen juna kamar chewing-gum a kan hanya. Tirr, shi yasa a wannan zamanin 'ya'yan shegu suka yi yawa.

Cewar wani tsoho da yaje wucewa ta kusan Abdul da Jinah. Dukansu Kyalkyacewa da dariya suka yi.

-Kai mutane akwai kananan kwakwale, ta yuwu mu yan uwa ne, amma su basa wannan tunanin, sun saba da ganin aibu a kullum, idan basu da tabbaci akan abu, to fa abinda zasu yi ta yadawa zai zamo na kuskure ne.

Abdul ya fada, sakinsa Jinah tayi tana dariyar wannan tsoho. Abdul ne ya katse zancen da cewa:

-Fada min da gaske kina son Dauda... Ina son na sani ne, saboda wata rana yace min zai yi komai ganin kin soshi, ni kuma na fada masa kina sonsa ganin yanda kuke a kullum amma yace min a'a.

Dogon numfashi Jinah ta sauke kafin tace:
-Eh ina son Dauda, amma ba kamar yanda yake so ba. Ina jin wani abu ne a cikin zuciyata kamar ina son wani wanda na yiwa alkwarin bashi zuciyata ba tare da na hada sonshi da na wani ba.

-Ikon Allah!

-Hmm na sani.

Haka suka cigaba da tafiya shuru ba wanda ke magana, bayan sun dan zagaya suka dauki hanyar komawa gida. Suna kawowa gida, Jinah taja burki ta tsaya, waiwaye take kamar wadda ta bata.

-Me ya faru?
Abdul ya tambayeta.

-Ina jin alamun wasu ne anan.

-Me?

-Ba yau na fara jin haka ba.

Kallonta Abdul yake na irin kodai ta fara cin kai ne. Sedai da gaske ne, koda Jinah bata ganinsu, tana jin alamunsu idan suna kusa da ita, wato aljanu. Har ta saba da hakan din sakamakon kasancewar Fally kullum a kusa da ita. Sai dai wannan karon ba Fally bane, tana jin alamun kamar suna da yawa. Dakarun aljanu ne da dama suka zo, sun zo ne domin yan tagwaye. Tuni yan tagwayen da mahaifinsu sun ga aljanun, ganin yawansu Fally ya karaya, yasan ba zai iya masu ba amma yayi alkwarin ba zasu taba daukan yaran ba sai bayan ranshi.

-Kamar yanda nayi alkwari, gani na dawo, kuma bani kadai ba, bakada wata dama ta kubuta a nan. Ka barmu mu tafi dasu, mu kuma zamu kyaleka.

Cewar wannan aljanin da yayi fada da Fally a baya.

-Ku fara bi ta kan gawata tukunna!

-Toh ka sani koda mu bamu yi nasarar tafiya dasu ba, to wasu zasu zo, dan haka ba zaku taba samun sukuni ba...

Kafin ma ya karasa maganarsa sai ga Aya da Ayu sun bayyana a gurin.

-Ban fada maku, ku buya ba?

Fally ya dakawa yaran tsawa.

-Mu suke son dauka baba, su gwada kamamu idan zasu iya.

Gama fadin haka keda wuya, tagwayen suka arce da wani masifaffen gudu. Makwamusan da kuma mahaifin nasu suka bi bayansu. Dukansu mamaki suke na irin masifaffen gudun yaran. Tsayawa suka yi, domin basa ganin yaran. Tagwayen sun bace.

-Kay gamu nan, me kuke jira ku zo ku kamamu!

Cewar Ayu yana dariyar keta.

-Wannan wane tashin hankali ne, double bacewa!

Cewar daya daga cikin aljanun, suma sauran al'ajabin abun suka shiga yi fahimtar abinda ke faruwa. Bayan karfin dake garesu na iya bacewa idon bil'adama, tagwayen zasu iya bacewa suma aljanu. Da taimakon mahaifinsu suka yi ta shammatar aljanun. Dukansu suke ta ko'ina, aljanun duk sun jigata. Anan suka tabbatar da dalilin da yasa shugabansu ke son su kwato masa tagwayen. Da yawa daga cikinsu suna jin labarin yara rabi mutum rabi aljanu, amma basu taba haduwa ba dasu ko jin labarin irin karfin dake garesu.

Bayan wani dan lokaci, wasu aljanu hudu suka yiwa Fally kawanya, kokarin kubutar da kanshi yake amma ya kasa, dirarwa biyu daga ciki yayi, su kuwa biyun suka yi kansa suna duka, daya daga cikinsu yayi nasarar shaudawa Fally bulalar nan mai fasa jikin mutum ta sakar masa kwari masu cin nama, bulalar ta sauka a kirjinsa. Wani azabataccen ihu Fally ya saki, wanda yayi nasarar jawo hankalin yan tagwayen dake cen suna fafatawa da sauran aljanun, basu lura da mahaifinsu yana bukatar taimako ba. Da sauri suka nufi mahaifin nasu, ganin wannan kwarin na cin nama jikinsa, basu san me zasu yi ba, basu san cewa kwarin zasu bar jikin mahaifin nasu ba ne idan suka dauki wani aljanin suka dora kan mahaifinsu, sannan kwarin zasu bar jikin mahaifinsu. Kuka Aya ta fara, tayi ta kokarin cire kwarin da hannunta, amma kamar tana kara masu yawa. Tashin hankalin da suka shiga yasa suka kasa sarrafa karfinsu, har suka dawo aljanun na ganinsu, Ayu kokari yake na hana aljanun kaiwa garesu, amma hakan ya faskara har lokacin da daya daga cikin aljanun yayi masa wani mugun naushi. Kara ya saki ya fadi kasa.

Aya ganin dan uwanta kwance a kasa, wani ja fuskarta tayi, ranta ya baci, aljanun cigaba da karasowa kanta suka yi, ita kuma barin ran da ta shiga, ta rufe idonta tareda dunkule hannuwanta, ba tare da sanin me zata yi ba ta watsa hannuwanta daidai aljanun kamar tayi jifa, wani haske da kuma guguwa suka fito daga hannunta.

Wannan guguwar tayi ta daukan aljanun tana jefarwa, wasu suka yi ta fadawa kan bishiyu, wasu kuwa a kasa. Wanda suka fada kan bishiyu, duk suka ji manyan raunuka sakamakon reshinan bishiyun. Tsoro ne ya kama Aya, ta boye hannuwanta, tareda jin tsoron ba zata sake aikata irin wannan ba. Ita ba abinda taso yi ba kenan, bata san cewa kananan hannuwan nan nata zasu iya yin wannan aikin ba. Juyawa tayi kan dan uwanta taga har yanzu bai farka ba, gashi kuma wannan kwarin sai cin naman babanta suke. Dole ne ta nemo hanyar da zata cecesu, gashi bata san ta ina zata fara ba.
Tambayar kanta take wa zai iya taimakonta, tunawa tayi da mamanta. A take ta bace da dan uwanta da kuma babanta, bata bayyana ko'ina sai cikin gidansu, kwantar dasu tayi, ta nufi cikin gidan da gudu domin nemo mahaifiyarta, sai dai itama tarar da ita tayi kwance bata motsi, Sarah da Abdul na ta kokarin tasheta. Amma ina, babu alamar rai a tare da ita.


--------------------------------

Hello 👋 Fatan kuna nan lafiya? Ya hakurin zaman jira? A cigaba dashi dan Allah, laifin school ne.

Ga wannan kuyi maneji dashi 🤗

Insha Allahu zan yi kokari duk ranar da nake free naga na kawo maku chapter 😍

©El_Ashtar

💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️

On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5

You'd like this New ❤️ Story

CHAPTER 15

~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦

Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp

-Banzaye marassa anfani !

Cewar Shugaban nasu cikin bacin rai.

-Amma, shugaba yaran ne karfin tsiya ne dasu.

-Babu abinda ya shafeni da komai ke garesu, zaku koma kuma idan har kuka dawo ba tare dasu ba, to ku tabbata zaku mutu !

-Shugaba, ba zamu iya...

Mai maganar bai samu karasawa ba sakamakon nunashi da sanda da shugaban yayi, a take ya daskare a gurin kamar dutse. Tsorata duka sauran aljanun suka yi ganin irin mutuwar da dan uwansu yayi, babu wanda ya kara samun kuzarin bude baki. Umarni shugaban ya baiwa wasu da basu je da farko ba, da su raka sauran su tafi neman yan tagwaye.

Dakatawa suka yi lokacin da wata murya tayi masu umarnin su dakata, ba kowa bane face dan shugaban nasu.

-Me kake aikatawa haka Zumana ? Me yasa...

-Saurara kaji baba, idan har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login