Showing 69001 words to 72000 words out of 72189 words

Chapter 24 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt

17 Mar 2026

48

duniya.

Goge fuskar sa yayi, sannan ya ɓace daga wurin zuwa asibiti, Sarah ya tarar a zaune, Nafisa na kwance bisa ƙafafun ta. Ƙarasawa yayi kusa da su.

-Sarah ya kira sunan ta a hankali. Lokaci guda Nafisa ta ɗago.

-Yaya Jinah da ƴan biyu?
Suka tambaya a tare.

-Suna nan lafiya, kar ku damu.

Dauda ya basu amsa a taƙaice, ba tare da ya faɗa masu halin da Ayu yake ciki ba.

-Ita..i..ita kuma mayyar, tana ina?

-ku kwantar da hankalin ku, har abada ba zaku sake ganin ta ba.

-Alhamdulillahi! Cewar Sarah.

-Ban..ban.. ban taɓa jin tsoro da ganin irin wannan halittar ba.

-Nima haka, amma me ya kawo ta, daga ina take?

-Zaku ji komi idan muka koma gida. Ina Abdul yake?

Da jin wannan tambayar, Nafisa ta fara zubar da hawaye kamar fanfo. Dauda ne ya shiga lallashin ta.

-Ina tsoron kar na rasa ɗan uwa na Dauda. Ta faɗa cike da fidda rai daga samun lafiyar ɗan uwanta.

-Zai warke, cewar Dauda. Nayi miki alƙawari!

Miƙewa yayi, Sarah tace :

-A wancen ɗakin suka kai shi. Ta faɗa tana nuna masa ɗakin da yatsa.

-Ina zuwa. Cewar Dauda kafin ya bar wurin. Ɓacewa yayi, sannan ya bayyana cikin ɗakin da aka kwantar da Abdul, ba tare da likitocin na ganin sa ba. Iya ƙoƙarin su suke ganin sun ceto ran Abdul.

-Ina ga sai an wuce da shi birni.

Cewar ɗaya daga cikin likitocin.

-Kana da gaskiya, idan ba haka ba, zamu rasa shi.

Cewar wani likitan.

Matsowa Dauda/Fally yayi kusa da Abdul, tare da ɗora hannun sa bisa goshin Abdul. Ya shiga karanto wasu kalamai, idanun sa a rufe. Bayan wasu yan mintuna, ɗaya daga cikin likitocin yace :

-Allah mai iko! Bugun zuciyar sa ya dawo normal.

Kallon kallo likitocin suka shiga yi, na mamakin ganin Abdul ya dawo hayyacin sa ba tare da sun yi masa wani taimako ba.

Dauda fita yayi ya koma wajen su Sarah, ya bar likitocin cikin ruɗu.

-Har yanzu likitocin basu fito ba?

Ya tambaye su.

-A'a...

Basu ƙarasa ba faɗa ba, sai ga wani likita ya fito. Miƙewa suka yi, suka tarbe shi.

-Ya ake ciki likita? Cewar Sarah.

-Yaya ɗan uwana yake doctor? Cewar Nafisa.

-Zan iya ce maku, yau mun ga ikon Allah, ɗan uwan ku yana nan lafiya, zamu riƙe shi zuwa gobe idan babu sauaran wani abu sai mu sake shi.

Tsalle Nafisa tayi, ta rungume Sarah cike da farin ciki.

-Ko zamu iya ganin sa?

-A'a, ku ɗan ƙara jira, har mu canja masa ɗaki.

Bayan wani lokaci, suka ga Abdul, a hayyacin sa, yayi farin ciki sosai da ganin su cikin ƙoshin lafiya. Tambayar ina Jinah da ƴan biyu yayi, suka tabbatar masa da suna nan lafiya. Sannan hankalin sa ya kwanta.

Komawa Dauda yayi gida, ya tarar da Jinah kwance, amma ba bacci take ba, matsawa yayi tare da zaunawa kusa da ita.

-Yaya Abdul ɗin yake?
Jinah ta tambaye shi.

-Lafiya ƙalau, sun ce zuwa gobe zasu iya sallamar shi.

Ya bata amsa yana mata murmushi, ita ma murmushin tayi cike da farin ciki.

Washe gari, aka sallami Abdul. Da shigar su gidan, Sarah da Dauda da ya koma asibitin da safe, suka nufi ɗakin da Jinah take ita ƴarta.

Sarah ita ce ta riga shiga ɗakin domin ita ce a gaba kuma tafi su sauri, da zumuɗin son ganin Jinah. Da shigar ta ɗakin, ta rungume Jinah sosai.

Sauran su ma haka suka yi, Nafisa da ɗan uwanta, bayan sun gama da Jinah suka koma kan Aya.

Bayan wasu mintuna na farin cikin ganin juna. A tare duka ukun suka tambayi :

-Wai ina Ayu?

-Ta kashe shi. Jinah ta basu amsa a taƙaice.

Abdul dake bakin gadon zaune yayi da jin abinda Jinah ta faɗa, ita kuwa Nafisa ta ƙwalla kara tare da fashewa da kuka, Sarah kuwa hannu tasa ta dafe bakin ta, hawaye na zubo mata, tana maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Kowannen su ya shiga ruɗu, babu wani dake da niyyar lallashin wani.

Washe gari aka kai Ayu makwancin sa. Jinah da Fally suka fayyacewa yan gidan asalin ko su waye ƴan biyu, abinda Hindu take so, yanda Dauda yake a zahiri, a taiƙace dai komai suka basu labari. Sun girgiza, amma kuma basu sha wani wahalan gasgatawa ba, bayan ganin abinda idanun su suka gane musu a cikin gidan. A yanzu sun bar abinda ya faru a matsayin sirrin gidan nasu.

Kwanaki na shuɗewa, kewar Ayu na daɗa damun su. Akwai zafi rasa makusanci, domin kuwa ya tafi kenan, zamu cigaba da rayuwar mu ba tare da shi ba, zamu goge shi daga duk wani program na gobe da muka shirya da shi, zai zamana mun yawaita ambaton sa yayin da muka tuna baya. Akai akai muna ɗorawa kan mu irin tambayoyin nan : idan da wane yana nan, da abu kaza da kaza ga yadda zai kasance, da wane na nan, da zai ce kaza ko kuma yayi kaza. Mu kan yawaita jin rashin sa a kasan zuciyoyin mu. Ga duk wadanda suka rasa makusantan su, Allah ya ƙara maku hakuri da juriyar rashi.

Sarah ce a cikin kitchen tana haɗa karin kumallo, lokacin da Abdul ya shigo.

Gaishe ta yayi, ta amsa a takure. Tun bayan faruwar abinda ya faru tsakanin su, take jin wata matsananciyar kunya, ba kamar kunyar Abdul din, shi yasa take gujewa duk wani wuri da zasu haɗu daga ita sai shi.

-Nazo ne, ina son muyi wata magana.

Benci dake kusa da su suka zauna. Abdul ya fara da cewa :

-Nazo ne na baki hakuri kan duk wani abu da ya faru, na rantse miki ba zan iya tuna komai ba na wata alaƙa da ta shiga tsakanin mu. Amma ina ji a jikina na aikata, ban san yaya zan fahimtar dake, ki gane gaskiya nake faɗa miki. Ba zan iya cigaba da kasancewa da wannan nauyin ba, shi yasa na yanke shawarar komawa Nigeria. Ina son duka mu koma a tare, ni kuma daga cen zan wuce Canada karatu. Ina son ki cigaba da kular min da ƴar uwa kamar yanda kike yi a yanzu. Dan Allah kar kice min a'a, ki sayar da wannan gidan, hankali na zai fi kwanciya idan duka kuna cen. Ina tsoron abinda ya faru da mu, ya sake faruwa.

Sarah ta yarda da maganar sa, kuma bata wani bata lokaci ba ta amince domin gidan nan yana tuna mata da abubuwa marasa kyau. Sai dai ta fara jin ta bakin sauran kafin ta yanke hukunci. Godiya Abdul yayi mata cikin farin ciki.

-Amma ta yaya zaka iya biyan kudin karatun ka a ƙasar wajen?
Sarah ta tambaye shi.

-Akwai gadon da muka gada ni da Nafi na mama mu. Kuma zan nemi scholarship, kar ki damu dama ina da wannan wannan program tun da daɗewa.

-Shikenan. Cewar Sarah.

Mikewa yayi, ya barta. Tarar da Dauda yayi zaune ya tsunduma cikin tunani.

-Kai kuwa, tunanin me kake? Oh ba sai ka faɗa ba ma, na sani na Jinah!

Dariya dukan su suka yi.

-Lallai, ka canka!

-Cikin sauki ma, domin shi kaɗai ka iya.

Dariya suka yi.

-Da gaske, ina son ka faɗa min, naga kwana biyu kana wani nesa nesa da Jinah.

-Na cutar da ita sosai, kuma ina tunanin ba lallai bane ta yafe min. Shi yasa nake ɗan nesa da ita, domin ina tsoron tace bata sona. Ni kuwa ba zan iya jurar hakan ba.

-Ko ma me zai faru, ka fara yi mata magana, ba zaka iya gane me take ji game da kai ba.

-Baka yi karya ba.

-Never man!

Dariya suka yi, kafin ya tashi ya tarar da Jinah cikin daki.

Jinah murmushi tayi da ganin shi, tace a ranta yau ya gaji da gudun. Zaunawa yayi bisa gadon, kusa da ita. Sannan yace:

-Zaki iya yafe min wata rana? Zan iya sa ran haka? Shin zaki iya kallo na wata rana ba tare da kin tuna mutuwar ɗanki ba? Na rantse miki, nayi nadama Jinah, ki yafe min, na tsani kaina ni Fally, irin cutar da Jinah da nayi. Ni...

Sauran kalaman sa, suka tsaya masa a maƙoshi, sadda kai yayi ƙasa, hawaye suka zubo masa.

-Fally, cewar Jinah cikin sanyayar murya, tana mai dago kan shi. Yi tunani ace zafin da nake naji yakai girman tekun maliya, lokacin da naga ka dawo gare ni, baka tafi ba, ina jin kasancewar ka a kusa da ni, na kwanta na tashi kana gefe na, wannan girman tekun maliyan, yana ragewa a duk lokacin da kake kusa da ni. Saboda kai da Aya, yasa bana jin zafin mutuwar Ayu sosai.

Ban manta Wata rana lokacin da muna yara, ka fita kai da baba, ni kuwa ina gida tare da mama lokacin tana bacci, na fita da niyyar na ga gari kuma kasan irin son da sauran aljanu ke min, ta faɗa tana murmushi, domin tasan akasin so suke mata.

Naga irin hantara a ranar, da kuka na koma gida. Raina a bace, naji na tsane su, ta yanda ba zan taba yafe musu ba abinda suka min. Bayan mama ta lallashe ni, nayi shuru, tace min : Jinah, yafiya ita ce babban magani ga zuciyar da aka cutar, yafiya tana haskaka zuciya da ruhi, yafiya tana ƴantar da bawa, yafiya tana gusar da mummunan tunani, yafiya tana saka farin ciki. Kada ki kasance marar yafiya Jinah, idan an cutar dake, ki kalli abu mai kyau cikin cutarwar, idan baki ganshi ba, ki nemeshi zaki ganshi, idan kika yi hakan zaki samu salama da kwanciyar hankali a zuciyar ki. Da jin haka, nace : Kin yi gaskiya mama, da ba'a yimin haka ba yau da ban samu wannan kyakyawar hudubar ba daga gare ki. Dariya tayi sannan ta rungume ni, a wannan lokacin ne, na fitar da duk wani mummunan tunanin da na saka a zuciya ta.

Shuru tayi domin tuna mahaifiyar tata (uwar riƙon ta) da tayi.

-Bana ƙin ka Fally, ta cigaba. A baya da na faɗa maka munanan kalamai, kawai dan ina cikin fushi ne, ina farin ciki na ganin ka kusa da ni, na yanda baka tunani. Ka daina damun kanka Fally, na daɗe da yafe maka.

Da gama faɗin haka, ta rungume shi, Fally kuwa ya riƙe ta sosai kamar zai sanya ta cikin jikin sa.

-Ina sonki Jinah, ina sonki sosai, sosai...


-Nima ina son ka Fally, nayi kewar ka sosai,...


-Za.. zaki iya maimaitawa dan Allah?


-Ina sonka.

Dariya suka yi.

-Fally.

-Hum.

-Zaka iya saki na yanzu, domin bana numfashi da kyau.

-Haha, yi hakuri habibty.

Daga wannan rana, suka fara sabuwar rayuwar soyayya, Jinah da Fally.

Sun fara da barin wannan kauyen, wannan kasar, Niger zuwa wata kasar Nigeria. Dukan su baki daya.

Fally yana kula da Jinah tamkar wata jinjira, baya barin wani abu ya same ta na cutarwa, duk wani abu da zai zo masa a kai, kuma yasan zai daɗaɗa ran Jinah, shi yake yi. Yana rayuwa ne kawai domin ta, farin cikin ta, shi ne nashi. Sanin Jinah tana son zaga duniya, yasa yake nuna mata hotunan wurare masu kyau na cikin duniya, kawai da ta nuna wuri, a take zai ɗauke ta ya kai ta. Cikin kwanaki kaɗan, ya kaita wurare da dama, irin su : Bahamas, pyramids of Giza a kasar Egypte, Hawaii, Paris, Dubai, The Colosseum, Ha Long Bay, Grand Canyon... da sauran su.

Yau ma a wannan lokacin, suna a Pamukkale, ɗaya daga cikin kayataccin wurare a ƙasar Turkey. Jinah kamar ƙaramar yarinya, Fally sai dariya yake mata. Bayan sun gaji da yawo, suka dawo bakin kogi suka yi zaune, ta dora kanta bisa kafadar shi.

-Ina cikin farin ciki sosai Fally.

Bata jira jin me zai ce ba, ta ƙara laɓewa cikin jikin sa.

-Yanzu dai mu koma gida, nayi kewar princess ɗita.

Da fadin haka, sai gasu a Nigeria, da gudu Aya ta ƙanƙame maman ta, lokacin da ta ganta.

-Ina kuka tafi yau? bani labari mama.

-Toh ƴata yanzu kuwa.

Murmushi tayi, mamar ta ta shiga bata labarin duk abubuwan da ta gani a Pamukkale, shi kuwa Fally yana gefe ya zuba masu na mujiya.

Bayan wasu yan mintuna, Nafisa ta shigo, ta basu labarin sun fita ita da Aya, mutane na ta kallon ta kamar sun ga aljana, har yau ma wasu sun nemi da ta zamo ambassador ta wani brand na yara.

-Dan Allah Jinah ki amince, my little princess ta zamo tauraruwa. Tuni har nayi suna cikin anguwar nan dalilin ta, toh ya kike gani idan aka fara ganin ta a social media, wow!

-Ashe dai princess din tawa haka take da kyau!
Cewar Jinah tana murmushi.

-Kamar ke mama!
Cewar Aya. Kuma da gaske tana da kyau sosai ita ma, ko ma taso tafi Jinah, duk da gashin ta bai kai tsayin na mahaifiyar ta ba, amma yana da tsawo shi ma. Idanun ta irin na baban ta ne, a taikace dai ita ma zubin aljanun gareta.

A yanzu, ta iya controlling karfin ta sosai, kuma ta daidaita shekarun ta ba kamar da ba, yanzu da ka ganta yarinya ce yar shekara bakwai kuma tana cigaba da girma kamar kowanne lafiyayyen yaro.

-Kai ya kake gani?
Jinah ta tambayi Fally.

-Idan kin amince, toh nima na amince.
Ya bata amsa murmushi kan laɓɓan sa.

-Ke kuma Aya?
Ta tambayi ƴar tata, Nafisa na mata irin kallon dan Allah ki amince.

-Nima ina so mama!

-Toh shikenan

-Cooool! Nafisa ta daka tsalle. Ina da number daya daga cikin su. Brand din su yafi zama popular, bari na kira shi yanzu.

Akwai wani abu kuma. Cewar ita Nafi, da murmushin mugunta a fuska.

-Menene?

-Na.. na nuna mishi pic din ki, kema yace yana son...

-Ba zai yiwu ba!
Bata kai ga ƙarasawa ba, Fally ya katse ta.

-Kin ji amsar ki.
Cewar Jinah, tana ƙyalƙyata dariya.

-Wai irin namijin kishin nan!
Cewar Nafisa tana masa hararan wasa. Dariya suka yi su duka.

Kafin ta kira mutumin, sai da taji ta bakin Sarah tukun, kuma ta amince. Cikin kwanaki kaɗan ƴar yarinya Aya ta zama Star.

Wata rana da yamma, suna a falo suna fira, wani ya ƙonƙwasa ƙofa. Nafisa ta tafi ta bude, sannan ta dawo tare da wani mutum, da ba zai wuce shekaru 40 ba, irin mai ƙasaitar nan, da kyakyawar fuskar shi daidai gwargwado. Da alama ta san shi.

-Aunty Sarah, uncle Ahmad ke son ganin ki.

Sarah abin yayi matuƙar bata mamaki, bata ƙarasa mamakin ta ba sai gashi ya shigo falon, sauran tashi suka yi suka basu wuri.

-Kin san shi? Fally ke tambayar Nafisa.

-Eh, maƙocin mu ne, gida mai kallon namu.

-Kin san ko me ya kawo shi?

-A'a, ban sani ba.

-Ina da wata dabara!
Cewar Jinah.

-Nima haka cewar Aya.

-Aya! Ban faɗa miki ki daina karanta cikin kawunan mutane ba. Ki daina bana son haka.

-Amma mama, bamu san shi ba, kinga dole muyi takatsantsan.

-Kada ki sake, babu kyau.

Da alama Aya bata so maman tata, ta taka mata birki ba. komawa tayi wajen baban ta tana zumɓuro baki.

-Ba maman ki hakuri. Baban ta ya raɗa mata a kunne.

-Kiyi haƙuri mama. Ta faɗa.

Gyaɗa mata kai Jinah tayi da alamar ta haƙura, sannan ta buɗe hannayen ta, yarinyar bata yi musu ba, tazo ta rungume ta.

Cigaba da hirar duniya suka yi, har lokacin da Sarah ta dawo.

-Me ya kawo shi?
Cewar Dauda cikin nuna kulawa.

-Matar aure yake nema!
Sarah ta faɗa ba tare da ta kalle su.

Washe baki Jinah ta shiga yi.

-Matar aure? Kamar yaya? ke kuma ya faɗawa haka? Ohhhhh ko dai keh..., na gane. Aunty Sarah ki ce kin amince, Uncle Ahmad, mutumin kirki ne, matar shi ta rasu da daɗewa, kuma kinga kyakyawa ne, kuma ga kudi, ina tunanin ƴaƴa biyu kawai gare shi.

Nafisa ce ke ta zuba wannan surutun.

-Toh me kika ce masa?
Cewar Jinah.

-Nace masa sai nayi tunani.

-Da alamun mutumin kirki ne, amma ki ɗauki lokacin nazartar shi kafin nan.
Cewar Fally.

-Ni tuni ma yayi min!
Cewar Jinah.

-Nima haka!
Nafisa da Aya suka haɗa baki. Dariya dukan su suka yi.

Bayan wasu makonni, Sarah ta amince zata auri Ahmad, ta kuwa ɗauki lokaci tana nazartar shi, ta gano mutumin kirki ne, kuma sosai ƴaƴan shi suka shaƙu da ita. Suna jin daɗin kasancewa tare da ita, ba kamar idan Aya na gida suyi ta wasa.

Wata rana, Fally da Jinah su kaɗai a zaune suna fira, Jinah ta kawo zancen da Fally ya tsani jin sa.

-Zan mutu kafin kai. Ni kaga mutum ce, kiyasin shekarun da zan yi ba zasu wuce saba'in ba, wata kila tamanin, nayi masu yawa nayi ɗari. Kai kuma dubunnai ne a gaban ka. Wace kalar mace zaka sake a madadi na?

Jinah tayi masa wannan tambayar domin ayi dariya, sai dai tuni taga yanayin Fally ya canja.

-Ah habiby da wasa fa nake.

-Toh bana son irin wannan wasa, ina shiga damuwa idan na tuna haka Jinah.

-Toh yi hakuri na daina daga yau. Ta faɗa tare da shigewa jikin sa.

Fally ya tsani ayi masa irin wannan zancen, domin yasan dole wata rana haka zata faru, shi yasa yake shiga damuwa sosai.

Duk inda ke da rayuwa, akwai mutuwa, kaddara ce da babu mai iya guje mata. Sau tari, mu matasa, bamu cika tunawa da ita ba, mun fi tunanin tafi daukan tsofaffi. Abin dariyar ma, muna ganin yanda take ɗaukan matasa, yara kanana, hatta da jarirai, amma mu kullum tunanin mu mutuwa ta tsofaffi ce, har mamaki muke idan aka ce ta ɗauki matashi wane. Ya kamata mu daina yaudaran kan mu, mutuwa ba ruwanta da matashi, tsoho, talaka, mai kudi, mai kyau ko mai muni ne. Tana ɗaukan mu ne a lokacin da ta so ko a yanda ta so. Abinda da Sarah da wannan ahali nata suka fahimta kenan.

A wata yammar litinin, dukan su suna gidan Ahmad, gidan da a yanzu Sarah take ciki tun bayan auren ta da Ahmad. Fally, Jinah, ƴarsu, Nafisa da kuma ɗan uwanta da ya daɗe da dawowa bayan wasu shekaru. Sun haɗu domin taya Jinah murnar cika shekaru 27. Suna cikin fira, cikin nishadi, lokaci guda suka bar jin muryar ta, bayan mintuna da yawa, alhali da ita ake ta surutu. Fally ne ya kai hankalin sa gare ta, mamaki yayi da ya ganta da alamun tana bacci, wani irin bugu zuciyar sa tayi. Aya dake waje tare da ƴaƴan Ahmad, ta shigo falon a gigice, da shigowar ta ta durkushe kasa, ta riga da taji a jikinta tun kafin ta shigo falon. Sauran mamaki ne a fuskokin su ganin halin da Aya take, har zuwa lokacin da suka ga Dauda na kokarin tashe da Jinah ya kasa. Falon yayi tsit, suna tunanin ta yaya hakan zai yiwu. Eh tabbas, Jinah rai yayi halin sa, Fally mikewa yayi tare da ɗaukan ta. Sauran basu fahimci komai ba, sai dai jikin su yayi sanyi duk da sun kasa gasgata abinda suke tunanin shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login