Showing 60001 words to 63000 words out of 72189 words
Chapter 21 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt
Ka nemo mana ita dan Allah. Nayi kewar ta sosai.
Dan janye ta yayi daga jikin sa, yasa hannun sa ya goge mata hawaye, sannan ya sake rungume ta, tare da yi mata alkawarin nemo mahaifiyar ta.
Karawa yayi da cewa :
-To ki daina kuka kin ji, kin san bana son ganin yar karamar gimbiya ta na kuka, kin sani ko?
Goge hawaye ta shiga yi tana gyada kai, dan uwan ta ne ya karaso wajen, Infa a bayan shi.
Ayu shi ma yaji dadin ganin Dauda, kuma shi ma kamar Aya, yayi masa alkawarin zai nemo mahaifiyar su. Hakan ya sakawa Ayu, digon kwarin gwiwa, domin yana tantamar wai Dauda zai yi abinda su suka gagara yi. Amma da yake suna son ganin mahaifiyar su, sai basu raina ta Dauda ba.
Dauda juyawa yayi ga bakon gidan, gaisawa suka yi, sannan Dauda ya tambaye shi daga ina yake kuma ya aka yi ya samu kan shi a cikin wannan gidan. Nan Infa ya fada masa, yana kan hanya ne, shi ne ya sauka anan domin ya dan huta kafin ya wuce. Hankalin Dauda bai kwanta da Infa ba. Tantamar tashi bata karu ba, har sai da suka yi musabaha, hannuwan su suka hadu. Nan kowane yaji wani abu game da dan uwan nasa.
-Nasan akwai gajiya gareka Dauda, je ka huta.
-A'a Sarah, ba zan iya ba, zan je na aje kayana sannan na fita neman Jinah.
-Amma ai dare yayi yanzu Dauda...
Cewar Sarah.
-Ba zan iya runtsawa ba da sanin cewa bansan inda Jinah take ko halin da take ciki ba.
Da fadar haka, ya nufi dakin su shi da Jinah, amma kafin nan sai da ya wuce gurin su Nafi ya tabbatar masu da zai nemo Jinah.
Dauda bai jima cikin dakin ba, Infa ya shigo.
-Waye kai?
Infa ya tambayi Dauda.
-Kai ma, kai waye?
Ya bashi amsa da irin tambayar shi.
-Kai ba mutum bane, kuma kai ba aljani ba ne.
Cewar Infa.
-Kuma kai ma, ba mutum bane.
-Kana da gaskiya.
Cewar Ayu da ya fado cikin dakin yar uwar shi a bayan sa.
Aya ta kara da cewa :
-Wani tsohon abokin baban mu ne.
-Amma kai Dauda, ya aka yi kasan haka? Ya aka yi kasan shi ba mutum bane?
-Tambaya mai kyau, wannan mutumin ko ma waye a gare ku, yana boye muku wani abu, bani da tabbaci amma ina jin akwai aljani a jikin sa. Dan haka ka fada mana kai waye?
Duka hankalin su ya koma kan Dauda jin me zai ce.
-Ni aljani ne a cikin gangar jikin mutum. Wani lokacin aljanin ne ke nan, wani lokacin kuma ni. Shi yasa gangar jiki na da kuma ruhin aljanin kullum cikin kokowar wanda zai dauki control suke. Kuma sau tari aljanin ke cin nasara, amma wani abu da na gano da zan tsaya a ni, shine mahaifiyar ku, tunanin ta yana sa nayi nisa sosai da aljanin, a lokacin da na fahimci haka, sai naki tunanin komai idan ba nata ba.
-Amma ta yaya haka zata yiwu? Kuma ta yaya ka iya dawowa hayyacin ka?
-Hindu! Ita ce sanadin komai.
-Shedaniya! Cewar Infa cikin bacin rai. Kuma shine ta iya barin ka ka taho a haka?
-Eh.
Infa cike da zargin Dauda yake, domin yasan ba yanda za'a yi Hindu ta barshi ya zo ba tare da wani dalili ba, haka kawai cikin sauki.
-Dare yana kara yi, ya kamata kowa yaje ya kwanta, in yaso gobe mun fita neman Jinah.
Cewar Infa.
Dakunan baccin su kowanne ya nufa, banda yan biyu da suka wuce dakin Sarah, inda suke bacci tun ranar da mama su ta bata.
(.....)
-Me kake yi anan? Bana tunanin kayi nasara kan plan din mu a wannan dan lokacin.
Ta fada da mamakin ganin shi.
-A'a, nazo ne domin wani abun daban.
Ya bata amsa.
-Ina sauraron ka!
-Daya daga cikin su kike so ko ba haka ba, idan fa kika samu duka biyun?
-Zan zamo shedaniyar duka shedanu.
-Ki taimake ni, ke kuma ki samu duka biyun.
-Me kake so?
-Kema kin sani, ita nake so.
-.......
-......
........
**************
Washe gari da sassafe, dukan su, suna a tsakar gida, za'a iya cewa tun batan Jinah basu sake samun bacci mai kyau ba. Bacci ma ba mai yiyuwa bane, ga yan gidan da suka san daya daga cikin su, basu san a ina yake kuma a wane hali yake ciki ba.
Sarah ita, tana cen tana hada karin kumallo, domin duk abinda zai faru, kowanne hali zata tsinci kanta, ba zata gushe tana kulawa da sauran yan gidan ba.... Kowanne dare, wata kila sauran ba bacci suke ba, suna kwance ne kan gado, tunanin halin da Jinah take ciki suke yi, ita kuwa tana zaune ne, bisa tabarmar sallar ta, tana rokon Allah ya dawo mata da Jinah. A wajen ta, Jinah tamkar 'yarta ce ta bata, kuyi tunani halin da mahaifiya zata shiga idan ta wayi gari bata san halin da 'yarta take ciki ba.
-Ki goge min hawayen nan.
Cewar Dauda ga Sarah, da ya tarar da ita cikin cuisine (kitchen) ita kadai tana kuka.
-Su kadai suka rage min a halin yanzu Dauda.
-Zaki yi murmushi, idan nace maki nan da kafin faduwar rana zaki ga Jinah?
Zuciyar ta ce tayi wani irin bugawa.
-Da...da..gaske kake? Kasan inda Jinah'ta take?
Gyada mata kai kawai Dauda yayi, yana murmushi har kunne, hawaye na kwaranyo masa, shi ma yana cikin farin ciki kamar ita.
-Amma bana son ki fadawa kowa, ina son na basu mamaki.
Sarah bata bashi amsa ba, illa rungume shi da tayi, tana kukan farin ciki. Bayan wannan, Dauda ya dauki hanyar neman Jinah.
****
Kwanaki na ta shudewa, wahalar yau daban ta gobe daban Jinah ke sha a gurin Fally. Har ta kai ga babu digon hawaye a idanun ta. Jira kawai take idan ya gama abinda zai yi da ita ya kashe ta. Wani abun ma da Fally yake mata, kusan kokarin maida ta mahaukaciyar karfi da yaji yake yi. Sai ta dinga jin wasu muryoyi, motsi da abubuwa na ban tsoro wanda ba ganin mai aikatasu take yi ba. Bugu da kari, kullum sai ya tara da ita, duk da ba ganin shi take ba amma tasan wani yana amfani da jikin ta, abun akwai ban tsoro, ba kamar rashin iya kare kanta da bata yi.
Sai dai wani abun gun Fally, kwanaki na shudewa, azabar da yake ji tafi ta Jinah, adadin cutar da ita da yake yi, ninkin zafin da take ji, yake ji. Idan tana kuka, shi ma haka zai yi ta kuka. Idan tana jin zafi, sai yafi ta jin zafin. Amma duk da haka baida niyyar daina azabtar da ita, idan kuma wani bangare na zuciyar sa yana bashi shawarar ya daina, sai wani bangaren yace masa ai ita ta jawa kanta, dan haka ta cancanci hukunci.
-Me yasa kake min haka?
Jinah ta fada cikin wata shakakkiyar murya. Gaban Fally ya fadi. Dawowa yayi yana fuskantar ta, kamar suna kallon kallo.
Bude baki yayi yana son yayi magana, amma ya kasa. Ya kasa ganewa. Shin tana ganin sa ne? Shin tasan ko shi waye? Alhali shi bai bayyana mata kanshi ba a yanzu.
-Fada min, ka fidda ni a duhu, nayi wani abu ne da na cancanci duk wannan?
Jinah ta fada, ba tare da ta jira jin amsar ta, ta baya ba. Hankalin Fally ya tashi, domin bai shiryawa irin wannan ranar ba, ko kuma bai yi tsamanin ta ba tun yanzu.
-Nasan yanzu dangina da 'ya'yana sun fidda rai da gani na, na dade da mutuwa a tunanin su, ba zan iya cigaba da jure wannan azabar ba.
Fally bai taba jin ya tsani wani a duniyar nan, kamar yanda yake jin tsanar kan shi a yanzu ba. Sai a yanzu yake jin bai kyautawa Jinah ba, yaji a jikin sa yayi halin karanta.
-Dan Allah ka daina, ina rokon ka, ka taimaka ka kashe ni. Akwai zafk abinda kake min. Kai na da ko'ina na jiki na zafi yake min. Akwai zafi!
-Akwai zafi! Fally ya maimaita, ba wai zafin da Jinah take ji ba, a'a shi ma irin abinda yake ji kenan a jikin sa.
-A... a ina kake?
Jinah ta fada, tana dudubawa ko zata ga wanda yayi maganar. Anan ya fahimci ba ganin sa take ba, durkusowa yayi kusa da ita ta yanda har yana iya jin numfashin ta, sannan yace :
-Jinah...
Ita kuma, sai ta ce :
-Dauda? Ta sake maimaitawa Dauda!
-Ji...Jinah! Jinah ta!
Juyawa Fally yayi, da mamakin sa wa zai gani in ba Dauda ba. Mamaki yake ta yaya simple mutum zai iya kawo kan sa nan. Kafin ya dawo hayyacin sa, har Jinah ta fada jikin Dauda. Wani irin jan takaici kan Fally yayi, kafin yayi wani yunkuri, sai ga yan biyu da Infa sun bayyana a gurin, Ayu ne yayi surkullen da baban nashi ya kasa ko motsi.
-Mama! Cewar Aya. Jinah ji tayi kamar an tsomata cikin tekun farin ciki.
-'Ya'yana! Allah na gode maka! Dauda sakin Jinah yayi, ta rungume yaran ta. Jinah da yan biyu kuka suke, ita Jinah na kukan farin cikin ganin ya'yanta, su kuma suna kukan ganin halin da mama su take ciki. Kasa sakin junan su suka yi, kamar zasu rama duk lokutan da suka shude basu tare, ta hanyar runguma.
Ba su suka saki juna ba, har sai da Infa ya fara magana.
-Ta yaya ka iya aikata haka? Me ya shiga kwalwar ka, anh Fally?
-Na tsaneka baba!
Yan biyu suka fada lokaci guda. Jinah da Dauda basu fahimci meke faruwa ba, amma suna tunanin akwai wani anan kuma shine silar duk wannan abun.
-Daga yau, kai ba baban mu bane! Babu wata alaka da ta hada mu da kai yanzu. Na tsane ka, kuma zan cigaba da tsanar ka har abada, ba zan yafe maka zaluntar mama da kayi ba.
Cewar Aya cike da tsanar mahaifin nata.
Dan uwan ta, ya kara da cewa :
-Har abada!
Wadannan kalaman a kunnuwa basu wuce iya kalamai ba, amma abinda basu sani ba, kalaman nan suna wargaza wani abu, wata alaka... Faduwa Jinah tayi sumamma, ko kuma mu ce ta fada cikin wani abu mai kama da mafarki.
{{{
-Fally tsoro nake ji.
-Kar ki ji tsoro Jinah, ina tare da ke! Macecin ki, mai gadin ki!
Murmushi tayi har kunne.
-Mai gadi na! Ta maimaita.
-Eh mai gadin ki!
-Haha, daga yau, zan dinga kiran ka da wannan sunan!
-In dai zai saka ki farin ciki Jinah.
****
-Mama, me ya samu Jinah?
A rikice Fally yake tambayar Maman sa.
-Kasan nan ba son ta suke ba, ta fita yin wasa, sai...
Mama shi ta fada tana share kwalla.
-Mama, nayi nadamar yin nesa da ita, daman ban so zuwa wannan kauyen ba, ba tare da ita ba. Ki yafe min Jinah'ta, daga yau ba zan sake tafiya na barki ke kadai ba. Mama, ki duba yanda suka ji mata ciwo, sai sun biya abinda suka yi mata. Nayi miki alkawari Jinah.
-Lafiya ta kalau Fally, kar ka damu.
-Ba lafiya ba kike Jinah, dubi abinda suka yi miki.
-Na roke ka, kayi hakuri, ba zan sake fita ba, kai kadai zan dinga wasa da shi daga yanzu.
Murmushi ne ya bayyana a fuskar Fally.
****
-Fally, na gaji da tafiyar kasa, me yasa ba zamu iya bacewa ba muyi saurin zuwa gida, kamar yanda muke yi kullum?
-A'a, cikin wannan dajin, ba zan iya anfani da karfi na ba, amma me yasa tun dazu baki fada min kin gaji ba? Hawo baya na, na goya ki.
-A'a, bana son kai ma ka gaji!
-Jinah, hawo ko na dora ki ta karfi, kin san ba da wasa nake ba.
-Amma Fally...!
Bata karasa abinda take son fada ba, ya sunkuce ta kamar wata gimbiya, sannan suka cigaba da tafiya.
****
-Wash, wash!
-Jinah, Jinah, me ya same ki?
-Na yanke ne da wuka, wash kuma akwai zafi.
-Ha..har yanzu, ban san ya ake warkar da ciwo ba, gashi kuma mama da baba basu nan.
-Kar ka damu, zan daina jin zafin.
-A'a, ba zan iya barin ki a haka ba, tsaya ki gani...
-Kar ka yi haka Fally!
Shi ma wukar ya sanya ya yanka hannun sa.
-Kin ga yanzu sai muji zafin a tare.
****
-Ko kin san meye "taken soyayyar Fally"?
-Ikon Allah, meye kuma haka nan, kai kullum baka rabo da kayan shirme?
-Kina so, ki sani ko kuwa?
-hmm to ina jin ka, majnun!
-To, bari na fahimtar da ke : Taken soyayyar Fally, wannan soyayyar ce da batada karshe, tsabar girman ta, ba za'a iya kwatantata ba da komai saboda ita kadai ce, tana rayuwa ne domin farin cikin Jinah, soyayya ce da ko jirgin kasa mai tsananin gudu ba zai iya kamo ta ba. Soyayyar da hasken ta, ba zaya taba gushewa ba domin babu wanda yasan adadin sa. Soyayyar dake rayuwa cikin zuciya ta. Soyayyar dake sa ina rayuwa, tana kara min karfi, dake sa zuciya ta, a maimaikon ta dinga bum bum, sai ta dinga bumbumbumbumbum....
Fadawa jikin sa, Jinah tayi tana hawaye.
}}}
-Mama ki tashi!
Cewar Yan biyu, suna girgiza mahaifiyar tasu.
-Jinah, Jinah!
Dauda da Infa ke ta maimaita haka.
Bude ido Jinah tayi, sannan ta mike ta nufi inda Fally yake tare da durkushewa gaban sa.
-Fally. Ta kira sunan sa cikin disashiyar murya.
Anan dukan su, suka fahimci Jinah ta tuna komai.
-Fally. Ta sake fada, amma hawayen dake zubo mata sun kasa bari tayi magana. Kana tune da ranar da na kwanta rashin lafiya? Kowa na ta murna, amma kai kana a kusa da ni. Ka tuna abinda kace min?
-E..eh Jinah.
-Koda kowa zai tsane ni, koda kowa zai so ya cutar da ni... Amma kai kace min, ba zaka taba yin hakan ba, mutuwa zata fiye maka ganin ranar da zan ji ciwo kuma ya zama kai ne silar shi. Kuma zaka mayar da duk wata damuwa tawa zuwa farin ciki. Ka yi min wannan alkwarin, ka yi min wannan rantsuwar Fally! ...to..toh me yasa? Me yasa baka cika alkawarin ka ba, me yasa ka cutar da ni Fally?
-Nayi nadama Jinah, na roke ki, kiyi hakuri ki yafe min!
Cewar Fally yana kuka.
-Har abada! Ta fada cikin daga murya, hawaye na ambaliya a fuskar ta.
-Jinah!
-Muje mama!
Cewar Ayu.
-Yanzu na gane irin cutar dake da nayi, kuma nasan lokaci ya kure min, na bari shedan yayi galaba a kai na, kuma nayi nadama, na makance ba tare da na san abinda nake aikatawa ba. A cen cikin rai na, ina son ki dawo gare ni, amma nasan hakan ba mai yiyuwa bane. Duk lokacin da muka bar kiyayya tayi nasara a kan mu, mu kan bude kofar kwakwalan mu ta yanda duk wani mugun tunani zai shiga, ni kuma hakan ce ta kasance da ni. Duk da wannan Jinah, abu daya nake da tabbacin sa a cikin kai na, soyayya ta gare ki, ita ce kuma zata cigaba da zama "taken soyayyar Fally". Ina son ku, ke da yaran mu, kuma na gwammace na mutu, da rayuwa da sanin cewa kun tsane ni kuma na cancanci haka. Na barku lafiya!
Duk wannan doguwar maganar da yake fada, Jinah ta juya masa baya ne, ta nufi kofar fita. Amma kalaman Fally na karshe sun sa ta tsaya cak, wannan yasa ta juyo tana fuskantar sa. Sai dai kuma tuni ta makara, domin Fally ya cakawa zuciyar sa wukar da ita kadai take iya kawo karshen aljani. Kafafuwan Jinah kasa daukar ta suka yi, ta zube kasa kamar wacce aka datsewa kafafun.
-A..a'a...! Take fada tana kokarin rarrafawa inda yake.
***************************
©Al_Ashtar
💞 JINAH (Matar Aljani)💞
by Malik al-Ashtar ✒️
On wattpad 👉 https://my.w.tt/g6epSX3tJ5
You'd like this New ❤️ Story
CHAPTER 26
~*Wilaya Writers association of Nigeria*~
(Home of peace & hospitality).💦we are here to educate and entertain the heart of readers,we are the best among the rest💦
Visit to like our page:https://www.facebook.com/Al-wilaya-writers-association-of-Nigeria-113198586763490/?referrer=whatsappwhatsapp
Lokacin da Jinah ke kallon Fally a kwance, jini na malala, gangar jikin sa na bankwana da ruhin sa. Wani zafi taji da yafi duk wata azaba zafi na kwanakin da suka shuɗe.
-A..a'a Fally, ba zaka mutu ba, nayi nadamar abinda na faɗa maka, na yafe maka, amma kar ka tafi dan Allah.
-Ki daina mama, ya riga da ya mutu.
-Ku tashe shi! Kuyi duk abinda zaku yi, ina son ya tashi!
-Su tashe shi? Ai wannan ba mai yiyuwa ba ne!
Cewar Infa cike da mamakin abinda Jinah ke kokarin sanya ƴan biyu.
-Saboda me? Nasan zamu iya yin hakan da karfin mu!
Cewar Aya.
-Koda muna iyawa, ba zamu yi ba, domin abinda yayi wa mama! Ba...
Cewar Ayu, wanda da alama mutuwar mahaifin nasa bata taba shi ba. Kallon da mama tashi ta watsa masa ne yasa yayi shuru.
-Ko ma me ya aikata, shi ne kuma zai cigaba da kasancewa mahaifin ka. Kada ka bari kiyayya ta rinjaye ka. Ka..kada ka maimaita kuskuren mahaifin ka. Shuru tayi kafin ta cigaba. I..idan da kun san wani lokaci a baya, lokacin muna yara. Ni nasan shi a wancen lokacin, babu wani mai zuciya mai kyau irin mahaifin ku.
Ta faɗa da alamun ta tuna abubuwa da dama.
-Sai dai kuma yau, babu mugu irin shi, kalli fa irin azabtar dake da yayi mama!
Cewar Ayu cike da wani yanayi mai kama da tsana. Sai dai akasin haka ne, bangaren yar uwar shi, mutuwar mahaifin ta ta taɓata sosai, ita ma tana son ya dawo, domin ba zata so rashin mahaifi ba, a irin wannan yanayin, duk da mintuna kadan baya da yana raye, babu abinda take fata face mutuwar sa.
-Ni ina son ya tashi!
Cewar Jinah.
-Jinah, cewar Infa. Ina tunanin baki san wannan ba, tayar da aljanin da ya mutu abu ne da ba'a taba yin sa ba. Domin ba zai koma kamar yanda yake a baya ba, kuma a yanda zai tashi, hakan ba zai yiwa kowa daɗi ba. Domin zai iya tashi a sheɗani.
Kamar bata ji ko kalma daya daga abinda ya faɗa ba, Jinah ta umarci ƴaƴanta da su tashe da baban su. Kokarin tashe shi suka shiga yi, ba irin karfin da basu yi aiki dashi ba, ganin sun tayar da shi amma sun kasa. Bayan ɓata lokaci mai yawa da suka yi, daga karshe suka ce mata ba zasu iya ba. Cigaba da rizgar kukan ta tayi. Daƙyar suka iya bamɓare ta, suka bar wurin.
Jikin Dauda yayi sanyi, tun lokacin da yaga Fally ya mutu. Da farko saboda bai fahimci abinda ke faruwa ba, na biyu kuma ganin halin da Jinah take ciki. Sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa bai taɓa samun soyayyar da yake fata ba daga gare ta, ashe wani take so, kuma ba kowa ba face Fally. Kuma yaga irin girman soyayyar da take nunawa Fally : ta yafe mishi duk da irin cutarwar da yayi mata.
Murna marar misaltuwa sai gida gun Sarah. Kuka take yi ba