Showing 36001 words to 39000 words out of 72189 words

Chapter 13 - Jinah Complete Hausa Novel By Malik Ashtar.txt

17 Mar 2026

39

suka je, zasu dawo ne kamar yanda na farkon suka dawo ko ma nasu yafi na farkon.

-Toh yanzu ya kake son ayi, so kake mu rungume hannuwa har sai daya daga cikin makiyan mu yayi nasarar mallakarsu, ka sani wannan itace damarmu, domin mune kadai wanda muka san inda suke kuma ina jin tsoro idan muka kara yin sanyar zuwa, wasu su rigamu ba kamar ma Hindu, ita duk nafi tsoro, domin wannan matar...

-Na sani Baba, inada wata dabara ce da zan iya kawo su cikin sauki.

-Wacce dabara?

-Ka barni na tafi na wani lokaci, idan zan dawo ba zan dawo ni daya ba.

-Amma Dana, akwai ha...

-Ka yarda da ni baba. Wannan itace hanyar da zan nuna maka, na cancanci na gajeka. Kuma ai koda mun kamasu ba yana nuna zamu iya yin abinda muke son yi dasu ba. Idan muna son duka abinda muke so, to dole su yarda da mu sosai. Idan kuwa ana son haka to dole maganar aikin ilimi ne da wayo.

A haka dai mahaifin ya yarda, abinda bai sani ba tuni dan nasa ya shirya wani plan nashi, yasan duk mutanen dake tare da yan tagwayen. Yasan abubuwa da dama game dasu. Har ma cikinsu ya samu wata da ta fada tarkonsa, domin Zumana akwai rauni game da mata. Duk inda yaje sai ya samu wadda yayi soyayya da ita in ma aljana ce ko mutum. Bayan ya shirya ya dauki hanyar zuwa gidansu yan tagwaye, ba tare da wani ya rakashi ba.

(....)

Tashin hankali, tsoro da kuma rudewa ne suka bi suka addabi yar yarinya Aya, batagwayenta dan uwanta, mamata da kuma mahaifinta duka a kwance ba a hayyacinsu ba gashi ta rasa me zata yi.

-Ayu...Ayu dan Allah ka tashi.

Abinda take ta maimaitawa kenan, amma babu alamar zai motsa. A gajiye, sharce zufar dake fuskarta tayi sannan ta dauki hannun dan uwan nata ta dora a daidai saitin zuciyarta sannan ta runtse ido. A hankali, taji ya motsa, bude idonta tayi sannan ta rungumeshi.

-Ka tsoratani dan uwana!
Ta fada cike da murna.

-Baba fah?
Ayu ya tambayeta.

-Wannan kwarin har yanzu basu bar jikinsa ba gashi ban san me zan yi ba.
Yar uwarshi ta bashi amsa cikin yanayin damuwa.

-Mama ma haka.
Aya ta kara fada a sanyaye.

-Me, me ya samu mahaifiyarmu?

-Ban sani ba lokacin da naje ganinta, na tarar da ita ne a kwance bata motsi.

Da gudunsa ya nufi inda mamar tasu take, yar uwarshi a bayansa. Sai dai da mamakinsu, zaune suka tarar da Jinah tana shan ruwa, rugawa suka yi suka fada jikinta. A tunaninsu Mamarsu kawai ta dan ji ba dadi ne. Abinda basu sani ba ta fita hayyacinta ne domin danta shi ma baya cikin hayyacinsa, basu san cewa akwai wata alaka mai karfi ba tsakanin su da uwarsu, alakar da zata iya jin duk wani zafin ciwon da daya daga cikinsu zai ji.

-komai ya wuce, Allah ya kara kiyaye gaba.

Abdul ya fada. Sarah da Nafisa suka amsa da ameen. Juyawa yayi da niyyar barin gurin.

-Ina zaka je?
Nafisa ta tambayeshi.

-bandaki zan je! Ko kina da sako ne?

-A'a, Allah ya kiyaye hanya. Babban aiki za'a yo koh?

Yar uwar tashi ta fada cikin sigar zolaya. Kada mata hannu yayi irin haba zan kamaki kafin ya cigaba da tafiya.

Yana kan hanyar zuwa ban dakin yaji kamar ana binsa a baya ko kuma ana kallonsa... Bai dai gama tantance yanayin ba. Wani mugun tsoro mai iya sa mutum ya hadiye zuciya a take ne ya kamashi lokacin da yaga mutum zaune a gefen kusurwar bandakin, zuciyarsa ce ta buga. Kamar walkiya kuma yaga mutumin ya bace, sai dai kuma yaji kamar da mutum a bayansa. Kasa samun kuzarin juyawa yayi, hakan ma baida anfani domin yanzu mutumin ya dawo gabansa suna kallon juna. Wannan mutumin kuwa ba kowa bane face Aljani Zumana da yazo domin yan tagwaye. Kasa motsi Abdul yayi tsabar tsoro. Murmushi kawai Zumana yake bin Abdul dashi, shi kuwa Abdul tunanin guduwa ne yazo masa amma sai yaji kafafuwansa kamar an sa masu siminti, tunanin yayi ihu yayi, sai dai babu wani sauti da ya iya fita daga bakinsa. Tawa ta kare! Wani bangare na kwalwarsa ya ayyana masa haka. Cikin wannan yanayin na shuru da babu abinda ake ji sai bugun zuciyar Abdul, aljanin ya karaso kusa da dashi, a hankali yake karasowa kafin daga karshe ya shiga jikinsa.

-Haha, daman na sani, babban aiki kaje yi, idan ba haka ba, ba zaka dau lokaci har haka ba.

Cewar Nafisa tana yiwa wanda take tunanin dan uwanta ne dariya. Ba tare da ya kulata ba ya cigaba da tafiya. Hakan ya baiwa kowa mamaki.

-Ba Abdul bane!
Cewar Aya. Babu wanda yaji lokacin da tayi maganar sai dan uwanta da kuma Abdul din wato aljanin dake cikin jikin Abdul.

-Kai yan yarori ku zo ku taimaka min nan!

Cewar Abdul yana kokarin shiga dakinsa. Yan tagwayen binsa suka yi a baya.

-Waye kai? Ayu ya tambayeshi fuska a murtuke.

-Nazo ne domin na taimakeku. Naga abinda ya faru da babanku!

-Me yasa kake cikin jikin Abdul?

-Nasan yanda zan taimaki mahaifinku, amma yin hakan, dole sai na ari jikin wani dan adam. Kuma idan har na dauki na wani daban to mamanku da sauran yan gidan ba zasu amince da ni ba.

Shuru yan tagwayen suka yi suna juya maganarsa.

-Domin na tabbatar maku, ku kawo min mahaifin naku.
Ya fada dan ya kaudar masu da kokonton da suke.

-Amma ku sani aikin zai dau dan dogon lokaci.
Ya kara da fadin haka.

-Mu dai muna son ya warke.

Cewar Aya, amma dan uwanta bai ce komai ba, domin bai yarda da wannan mutumin ba. Amma tunaninsa ya canja lokacin da suka ga aljanin yanata fadin wasu dalasuman tsafi a tunaninsu na warkar da mahaifinsu ne, tsugunawa Abdul yayi sannan ya fiddo wani yan kananan abubuwa jajaye guda biyu. Dorashi yayi kan goshin Fally, sannan ya dauki dayan ya dannashi da karfi kan kirjin na Fally. Bude ido Fally yayi, dadi sosai yan tagwayen suka ji sunata washe baki har kunne ganin mahaifinsu ya tashi. Magana suka yi masa amma shuru ba amsa sai dai binsu da ido da yake yi kuma bai iya motsawa. Kallon Zumana suka yi cike da zargi.

-Dama na fada maku aikin zai dau lokaci, amma kar ku damu zan warkar dashi. Wancan ranar a bayan bishiyu naga irin yanda kuke kaunar babanku sai dai ba zan iya kawo maku wani taimako ba, yanzu ma ya kamata mu kaishi wani guri nesa da mutane, domin nan gaba zai iya komawa mutane sun dinga ganinsa.

Kamar yanda ya fada masu haka suka yi, suka dauke mahaifinsu zuwa wani wurin.

-Naga mamanku mutum ce, kenan ku ruwa biyu ne?

Ya tambayesu.

-Eh haka ne! Ayu ya bashi amsa. Kai ma so kake ka daukemu?

-Nesa dani da wannan kudirin. Amma zan iya taimaka maku ta yanda zaku yi ku iya sarrafa karfinku dakyau, mahaifina ya koyar dani sosai ilimin sanin irinku.

-Da gaske?
Cewar Aya.

-Eh da gaske. Ya bata amsa.

-Yaushe zamu fara? Wannan karon Ayu ne yayi tambayar.

-Lokacin da kuke so.

Murmushin jin dadi suka yi, barin dakin Abdul din suka yi lokacin da mahaifiyarsu ta kirasu. Wani shu'umin murmushin mugunta Zumana yayi, ganin komai na tafiyar masa daidai. Yana iya warkar da Mahaifinsu kyabtawa da bismillah amma da gangan sai ya kara saka masa wani abun da ba zai so ya tashi da wuri ba, domin yasan in har Fally ya tashi to zai iya wargaza masa plan.

Fita yayi daga dakin ya nufi gun sauran mutanen gidan, ya zauna ba tare da yayiwa wani magana ba.

-Me yake damunka? Ko wani kudan ne ya cijeka a bandaki?

Jinah ta fada cikin sigar zolaya.

-Rabu dashi, yan matsutsan nasa ne suka motsa.

Cewar Nafi, a tunaninta yayanta ne. Sai dai abun mamaki bai tankasu ba.

-Ku shafa masa lafiya, idan yana magana kuce ya cika magana kamar aku, yanzu kuma da yayi shuru kuke son saka shi dole sai yayi magana.

-Yauwa nagode Sarah! Sai yanzu yayi magana yana washe baki. Wani kallo yake bin Sarah dashi, wanda yasa ta tsargu. Tunani tayi ko sau daya Abdul bai taba mata irin wannan kallon ba. Sai dai abinda bata sani ba, babu ruwan Abdul da wannan aikin.

Zumana tun lokacin da ya fara zuwa leken asirin sanin inda su Jinah suke, anan hankalinsa yakai kan Sarah, wannan ma yasa ya shiga jikin mutum dan ya cimma kudirinsa. Domin yana iya yin abinda ya kawoshi ba tare da ya shiga jikin mutum ba, tunda yan tagwayen zasu iya ganinsa. Amma yaki yin haka dalilin fadawa soyayyar Sarah da yayi. Bayan sun gama cin abincin dare kowa ya nufi makwancinsa amma banda shi.

Washe gari da sassafe ya kira yan tagwaye dakin Abdul domin fara yi masu darasi. Fara masu yayi da yanda zasu iya karanta tunanin wani.

-Ku rufe idonku, ku ja dogon numfashi, kuyi tunanin gaku nan a wani gu, sai ku fada min abinda kuka gani. Idan kuka yi haka to kuna cikin kan wani ne, sannan ku zabi mutumin da zaku yiwa haka. To yanzu ku saki asalin tunaninku. Sannan...

-Wow nawa yayi!... Kayi... Amma kuma komai ya yamutse. Cewar Ayu yana bata fuska.

-Saboda baka aje hankali bane sosai.

Zumana ya rada masa. Bayan dan lokaci Aya ta bude idonta cike da murna.

-Ni dai bai yi ba. Cewar dan uwanta. Murmushi Abdul yayi.

-Halan nawa tunanin kake son karantawa?

-Eh ko ba zai yuwu bane?

Sai da yayi wata munafukar dariya kafin ya bashi amsa.

-Zai yuwu, amma yana bukatar lokaci kafin ku koyi karanta tunanin aljanu.

Yayi masu karya, domin babu wani banbanci tsakanin karanta tunanin mutane da na aljanu, kawai dai shi ne baya son su harbo plan dinshi, shi yasa da yaga yaron na kokarin shiga kanshi yayi sauri ya birkice komai. Haka ya cigaba da koyar dasu abubuwa da dama, amma sai yace masu basa yi sai ga mutane.

Kwanaki na ta shudewa, Zumana yana cigaba da koyar dasu, har yaran sun yarda dashi sosai, haka bangaren Sarah kullum cikin takurata yake da mayen kallo, har dai abun ya kai ya ishi Sarah wata rana tayi masa magana.

-Wai kai me yake damunka kwanan nan?

Ta tambayeshi.

-Kamar ya ban gane ba?
Yayi kamar bai fahimci akan me take magana ba.

Shuru Sarah tayi, jikinta yayi sanyi, domin tana tsoron kar aje itace ke tunanin abinda ba shi yake nufi ba.

-Shin ba kamar uwa ka daukeni ba?

Shuru yayi, murmushi kan lebensa ba tare da ya dauke ganinsa daga kanta ba.

-Kinada kyau sosai...

Katseshi tayi da sauri ta hanyar kiran sunansa.
-Abdul!

-Allah da gaske nake.

Mikewa tayi da niyyar tafiya, amma kuma kamar tsafi ta dawo ta zauna. Wani shu'umin murmushi Abdul yayi.

-Me yasa kike son kashe kuruciyarki anan? Ya tambayeta.

-Kamar ya? Ba auren mahaifinka nake ba.

-Oh wannan? To me yasa baya nan? Baki dace da irin wannan ba. Ba mutumin da zai bar mace kamarki yayi tafiyarshi. Mahaifina ne eh, amma sam baku dace ba.

-Duk da haka dai mijina ne, kuma indai har yana nan ba zan kalli wani namijin daban ba.

-Ku din nan, me kuke tattaunawa haka, kwanan nan fa na lura kuna daukan lokaci ku biyu kuyita maganganun da na kasa fahimta.

Cewar Jinah dake karasowa wajensu.

-Kece dai kika fara sa'ido shi yasa kike ganin haka.
Cewar Abdul.

Dama Sarah ta samu na zuwan Jinah ta mike da niyyar tafiya tana cewa
-Ni dai bari naje aikin gabana...

-A'a karki tafi dan Allah. Cewar Abdul yana wani kashe murya. Mamaki abun yaba Jinah, binsa take da kallo.


-Ya aka yi ne? Ya tambayeta.

-Abdul ka canja!

-Ni ba wani canjawa da nayi. Ya fada yana juya mata baya da niyyar tafiya. Kokarin tashi tayi da tabi bayansa, sai taji kafafuwanta kamar an saka mata danko, ta kasa motsawa. Ba aikin kowa bane face Zumana.

Sati daya bayan wannan ranar, Kuka da ihun Sarah dake durkushe tsakar gida ta dora hannu a kai ne ya karade ga baki daya gidan, gangar jikin wani ne kwance babu alamar rai a kusa da ita.

Abdul da Nafisa suka karaso wurin da sauri.

-Ba..ba.baba ne!
Nafisa ta fada tare da fadawa kan gangar jikin tana kuka.

-Dan Allah baba ka tashi, karka tafi ka barmu, ka tashi dan Allah, kada ka mayar dani marainiya, dan Allah baba.

Kokarin kamata Jinah tayi amma ta fizge, tashi tayi da gudu ta nufi dakinta, binta Jinah tayi, suma yan tagwaye suka rufa masu baya.

-Ba kyau, ki daina kuka Nafi.

Aya ta fada da sigar lallashi. Sai dai Nafisa ko sauraronta bata yi ta cigaba da rera kukanta. Zaunawa kusa da ita Jinah tayi, tare da rungumota, wannan karon bata yi turjiya ba, ta cigaba da kukanta. Ita kanta Jinah mutuwar ta tabata, ta kasa fahimta amma tana jin zafin mutuwar har cikin ranta. Yanda mutuwar bare bata taba mutum har haka. Hakan ne yasa ake cewa mutum ba zai ji zafin mutuwa ba har sai nashi ya mutu.

A waje kuwa, wanda suke tunanin Abdul ne, murna ce fal a ransa. Matsawa yayi kusa da Sarah ya rungumota. Yana shafa bayanta da sigar lallaba, alhali shi irin wannan ya dade yana fakon samu ace Sarah a cikin hannuwansa har yana taba jikinta. Ita kuwa Sarah cigaba da kuka take, domin ita bata kawo komai ba, hankalinta yana kan jimamin mutuwar masoyinta, duk da Kimba ya cutar da ita sosai, ba zata yi masa fatan mutuwa ba, tana tunanin wata rana zai iya gyaruwa suyi zama na amana dashi. Ba masoyinka ba ma ko makiyinka baka masa fatan mutuwa.

Wani sabon kukan ta shiga rerawa tunawa da tayi da sauran matansa da kuma diyansa wanda wata kila ba zasu ji mutuwarsa ba har abada, tunda babu wanda yasan a ina suke. Bata san ta yaya zata sanar dasu ba, ko a ina zata gansu, kuma ta kasa fahimtar yanda aka yi Kimba yazo gidan da kuma ta yaya ya mutu. Wadannan sune tambayoyin da suka tsaya mata a kwalwa kuma batada amsarsu.

-Karka damu, nayi alkawarin zan kula daku.
Sarah ke fadawa Abdul.

-A'a, ni kadai ne namiji yanzu a gidan nan, dan haka nine ya kamata na kula daku.

Murnushi tayi.

-Har yanzu kai yaro ne.

-Amma kuma kwalwata babba ce. Ya bata amsa yana murmushi.

Da taimakon wasu makota a kauyen, aka yi jana'izar Kimba zuwa makwancinsa na gaskiya. Taso taje cen kauyensu domin ta sanar da dan uwanta mutuwar, amma kuma tana tsoron yayan nata yayi ko a jikinsa domin rashin jituwar dake tsakaninsu, kuma bata son tafiya ta bar diyan mijin nata da kuma Jinah da yan tagwaye. Haka kwanaki suka cigaba da shudewa, Sarah tana cigaba da kulawa da diyan mijinta da kokarin kauda masu duk wata damuwar maraici tasu. Sai dai duk lokacin da take tare da Abdul sai ya zama kamar shi ke kula da ita...

Wata rana da dare, lokacin sauran sunyi bacci. Sarah ya gani ta wuce ta kofar dakinsa, da gangan ya jefar da kofin kwalba tare da sakin wata razananniyar kara. Da gudu Sarah ta fado dakin, a tsorace, bata ma tsaya tunanin konkwasa kofa ba. Da shigarta dakin, taja burki ta tsaya, sakamakon ganin Abdul zigidir babu komai a jikinsa, a idonta ba wai suffar matashin yaro take gani ba, A'a suffar babban mutum baligi wato suffar Zumana ce take gani. Kasa daidaita natsuwarta tayi kuma ta kasa dauke ido daga kallonshi. Aljanin ya fahimci halin da ta shiga, sai ya shiga dube-duben munafunci wai neman abunda zai rufe jikinsa dashi, hakan da yayi kuma dan ya kara bata damar karewa duk sauran jikin nasa kallo.

-Am..ina..ka...

I'ina ta fara, duk ta daburce ta kasa hada kalmomin da zata yi magana, juyawa tayi ta fita da saurinta domin ita kadai ce mafitar da ta iya samu. Wani tsallen farin ciki Abdul yayi tare da fadawa kan gadonsa.

Da zuwanta daki, safa da marwa ta shiga yi, tana mai jin haushin kanta na kasa fita da tayi daga dakin lokacin da ta shiga. Ta kasa goge hoton suffarsa da ta gani a cikin kwalwarta, tunani kala-kala yanata zuwar mata a kwalwa. A matsayin dana yake tunda dan mijina ne, kuma na girme mashi nesa ba kusa ba. Abinda take ta maimaitawa kenan. Idan da farko tana cikin tashin hankali, to yanzu fa cikin tashin tashinar hankali take. Kwabe kayan jikinta tayi, tayi daure gaba da zaninta, ta nufi gado da niyyar kwantawa taji ana konkwasa mata kofa. Zuwa tayi ta bude, Abdul ta gani daga shi sai singileti da karamin wando.

-Nazo ne na baki hakuri kan abinda ya faru dazu, ban yi tunanin wani zai shigo ba.

-A'a ni ya dace na baka hakuri domin ban konkwasa kofar ba kafin na shiga.

-Ah ba komai, sai da safe.

Yana juyawa da niyyar tafiya kamar tsafi, dan karamin kadangare ya fado kan kirjin Sarah. Kwalalo ido tayi a tsorace.

-Shiit, kar ki motsa. Ya rada mata.

A hankali ya cire kadangaren daga jikinta, ikon Allah ne ko kuma da gangan yayi, yankewa yayi a tafin hannunsa, jini ya falsu sai ga tsakiyar kirjin Sarah. Sai dai ita ba wannan bane damuwarta, damuwarta danta yaji ciwo.

-Innalillahi, kana zubar da jini! Shigo daga ciki na daure maka ciwon.

Cike da jin dadin plan dinshi na tafiya ya shiga dakin, wanke masa ciwon tayi sannan ta yagi wani tsohon zani nata ta daure masa. Daukan sauran zanin yayi, gadan-gadan ya nufeta.

-Me kake yi haka?
Ta tambayeshi tana fiddo idanuwan tsoro.

-So nake na goge maki jinin da ya zubar maki. Ya fada yana kai tissus din kan kirjinta.

-Abdul! Ta fada tana kallonsa.

-Gogewa kawai zan yi. Kamar wata sakarya ta barshi yana goge jinin, duk da tasan ba wai gogewar kadai yake son yi ba. A hankali yake yin kasa da hannunsa zuwa cikin zaninta.

-Abdul! Ta daka masa tsawa marar sauti.

-Gogewa ne fa nake yi.

-Ka goge, kuma gogewa kawai mana... Ta fada cikin wata kasalalliyar murya.

Da dayan hannun yake kokarin sauke zanin nata, ita kuwa Sarah tuni ta fita a hayyacinta bata san wainar da ake toyawa ba. Daidai yana kwance mata zanin ta dawo cikin hayyacinta, hannu biyu tasa iya karfinta ta ingijeshi. Ta sake daura zanin.

-Abdul fitar min daga daki!

-Kiyi hakuri. Ya fada kamar da gaske kafin ya fita.

Fashewa da kuka tayi. Me nake shirin aikatawa? Ta fada. A wannan daren kasa bacci tayi. Washe gari, kokari tayi na ganin bata hadu da Abdul ba.

-Lafiyarki kuwa Sarah?

-Eh me kika gani?

-Naga kamar da damuwa a fuskarki.

-Ba komai, kar ki damu.

-Humm to shikenan.

-Wai baku lura ba, dan uwana duk ya wani sauya?

Cewar Nafisa.

-Wallahi kuwa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login