Showing 144001 words to 147000 words out of 148158 words

Chapter 49 - SAKON SO BOOOK COMPLETE ROMANTIC.txt

M.Shakur   

24 Jul 2024

46696

gudu zaka dauka zaiyi flying motan ne.




Kusan tafiyan 45min sukayi sukakai wajajen dajin parking Abee yayi yafito dasauri yana daga kujeran dayake kai yaciro wata yar karaman bindiga Musty yakalleshi baice dai komiba ya karyi wata babban icce shima Abdul ya karyi icce dan duk basa tare da bindigarsu sannan suka fara tafiya suna shiga cikin dajin dasauri dasauri.






Ahankali Lujain kebude idanunta dasuke jujjuya mata tabi dakin da kallo ganin bataga Mandawari ba yasa ahankali taja jikinta ta tashi zaune cikinta namata wani kalan bala’in ciwo, jin karan ruwa yasa tagane kaman yana bayi, kokarin tashi tayi amman takasa hakan yasa tacigaba dajan jikinta tana har zuwa wajen kofa, dan mikewa tsaye kadan tayi tabude kofan jin a kulle yasa tajuyo tanabin dakin da kallo jikinta na rawa, aduke takarasa tanajin yanda jini kebin kafafunta takarasa gaban table din tadauki key datagani tazo wajen kofan tabude ahankali gani tayi acikin daji suke da kyar ta iya fita tafra tafiya aduke tarike cikinta gam takai hannunta daya baki tana kokarin cire tape din bakinta takasa dan kaman da super glue yakama bakin, da dan sauri sauri take tafiyan aduke tana layi kaman zata fadi dudda bawai wani sauri bane takeyi ba. “Where did you think you are going!” Kaman daga sama Lujain tayi muryan Mandawari, sosai take kuka ko tsayawa batayiba sai kara sauri datayi tana layi sosai, dariya yayi yana binta abaya yace “you think u can run away from me, Oya cigaba da tafiya lemme see how far u can go” wani kalan dingishi Lujain keyi tana kara sauri tana layi, kaman daga sama taji muryan Abee. “Lujaiiinnnn!”EPISODE 1️⃣0️⃣5️⃣








Dawani kalan sauri Lujain tashiga juya kanta tana neman Abee dataji muryanshi yana kwalamata kira takai hannunta saman bakinta tana kokarin yage seletef din dake kai daidai Mandawari yawani fizgo bayan riganta da gudu yajata zaiyi inda yay parking motanshi da ita jin muryan su Abee da wasu maza ana kwalamata kira.




Turjewa Lujain tayi da karfinta taki tafiya tana wani kalan kuka tana kalle kalle so kawai take taga Abee ya bullo yazo ya ceceta, awani kalan zuciye Mandawari yakai hannunshi bayan wandonshi yaciro wata yar karaman bindiga ya pointing nashi a abayan kan Lujain cikin ihu yace “walk or I shoot you!” Daidai su Abee sun bullo daga dajin, dawani kalan sauri Mandawari yaja Lujain jikinshi yay pointing gun din abayan kanta yana kallon su Abee yace “duk wanda yazo wajen nan wlh saina harbeta ta mutu” dasauri Abee yadaga hannayenshi sama yanuna kanshi da sauri yana kallon Lujain din dake kuka sosai tana kallonshi yace “shoot me instead Mandawari, dani kakeda matsala let her go, you are hurting my wife” cikin wani kalan ihu na kaman wanda yazare Mandawari yace “wlh wlh kasake kiranta matarka saina harbeta ta mutu nima na harbe kaina, Lujain is not your wife, wayau kamata ka aureta you stupid old wise man” lumshe idanu Abee yayi at this point he don’t care kozai mutu yabude idanunshi ahankali yasake daurasu akan Lujain, cikin wani kalan kuka Lujain ta mikamai hannunta alamun yazo ya ceceta Abee jiyayi komi nashi ya tsaya chak at this point he don’t care about his life, awani kalan zuciye yafara tahowa dasauri Mandawari yazare bindigar daga keyan Lujain yariketa da hannu daya yay pointing Abee da gun don yace “one more step I will shoot you Imrana na rantse” batare da Abee ya tsaya ba yace “shoot me I don’t care” yacigaba da tahowa, wani kalan ture Lujain kasa Mandawari yayi yarike bindigan da hannu biyu da kyau yana kokarin pulling trigger zai harbi Abee daga Musty Harun da Lujain dukansu gabansu faduwa yake ganin zai harbi Abee kana ganin yanda yarike bindigar ma kadan baitaba rikewa ba, daidai zai shooting Abee Lujain dake kwance akasa ta dago da kyar tasa duka karfinta ta ture kafafunshi yay tangal tangal zai fadi hakan yasa bindigan yabada tusss! Dasauri Lujain tajuyo takalli Abee daidai Abee ya iso gaban Mandawari dake shirin daukan bindigan daya fadi daga hannunshi kasa, wani kalan dagoshi Abee yayi baiyi wata wata ba ya watsama Mandawari wani irin mari tau! Wani kalan juyi Mandawari yafara yana layi zai fadi Abee yakaramai wani marin sai jini ta hancinshi, cikin tsantsan rashin Imani Abee yakama hannayenshi duka biyun yace “you dare lay your hands on my wife” karrr!!! Abee yakaryemai hannu duka biyun, saida Lujain tayi ihu jin karan bones na breaking, cikin tsantsan hauka Abee yace “now I will kill you ni” yawani kalan chapko wuyan Mandawarin yashakeshi zai kasheshi dasauri daga Harun har Musty suka banbare Abee daga jikinshi, cikin ihu Abee yace “my wife is bleeding Mustafa I want to kill this guy” ture Abee Musty yayi da karfi zuwa inda Lujain take Abee zai tashi dasauri Lujain yakama hannunshi kasa juyowa yakalleta Abee yayi, ahankali tadago kanta da kyar tadaura abayanshi dawani kalan sauri Abee yajuyo kawai ya rungumeta kam kam ajikinshi.EPISODE 1️⃣0️⃣6️⃣








Gently yadago fuskanta daga kirjinshi ahankali yay cupping fuskanta yana kallonta idanunshi sunyi jajir his heart is so weak da yanda yaga ta wahala, hannunshi yakai ahankali ya daye saletef din kan bakinta, fashewa da kuka Lujain tayi sosai sabida azaba, ahankali Abee yadaura goshinshi saman nata yana kallon kwayan idanunta gently wani kalan hawaye mai dumi yasauko daga kan idanunshi dan he’s feeling her pains, girgizamai kai tayi alamun karyay kuka, ahankali Abee yadaura lips nashi kan nata kafin gently yahau kissing dinta he don’t care about inda suke, Suwaye ke wajen, or what’s happening, he just wants to kiss matanshi that’s just abinda yakeso yayi, jiniyan motocin yan sanda dayaji yasa yasaki bakinta ahankali lumshe idanunta tayi ta kankameshi asume, mikewa tsaye Abee yayi yadauketa chak dasauri batare daya kalli su Musty da Mandawari ba dan idan idanunshi suka sauka akan Mandawari he might do abinda zai iya regretting later, dawani irin gudu Baba daya biyo su Abdul police yazo yana kallon Lujain da Abee yarike yace “yaya take Imrana” gyadamai kai Abee kawai yayi yama kasa magana, karasawa yayi wajen dasukai parking motansu ya kwantar da ita abaya, gaba Baba yashiga batare daya jira Imran dinba dan bazai iya tuki ba kana ganinshi yace “zauna da ita abaya Imrana bari na tukaku” jan motan Baba yayi Abee bai damu da Baba na wajen ba kankame Lujain yayi ajikinshi tsamtsam hawaye na fitowa daga idanunshi sosai, Baba sai kallonsu yake ta madubin gaba yana sauraron yanda zuciyanta ke bugawa ahankali very very weak, bini bini yana manna mata peck a goshi.
***






Bayan 1 week
Ahankali take bude idanunta AC dake aiki ta kalla kafin gently tasauke idanunta kasa Gwaggo tagani akan kujera tai tagumi tana kallon tv dake aiki a dakin hannunta rikeda charbi tanaja, kana ganinta kasan tana cikin tsantsan damuwa, lumshe idanunta tayi tasake budewa kafin ahankali muryanta da baya fita sosai tace “Gwag……go” dawani kalan sauri Gwaggo tajuyo da kanta takalli Lujain sai kawai tafashe da kuka takama hannayen Lujain tace “Lulu zaki tashi dama, wayyo Allah na Lulu na dauka baraki kara tashi ba hankalina ya matukar tashi, Lulu Allah zai saka miki kinji, wannan yaron daya azabtar dake dudda uwarshi tazo nan tana kuka wiwi tana bamu hakuri wlh bazan yafe mishi ba da yardan Allah saiya rube agidan Yarin dayake, wanan cikin naki dayasa yafita in sha Allahu hakkin nan bazai barshi zaman gidan duniya lafiya ba” “ru…..w…..” dasauri Gwaggo tace “ruwa zaki sha”? Gyadamata kai Lujain tayi kadan, dasauri Gwaggo ta tashi tadauki goran ruwa takawo dago gadon Gwaggo tayi yatsine fuska Lujain tayi zata fashe da kuka Gwaggo tace “sannu hakarkarinki daya ya karye inji likitoci ashe yaron nan ya bugamiki kujera aciki da kanshi yafadi dayaji azaba, yanzu haka an daure miki hakarkarin da belt ance zaki warke nan da sati, gashi sha ruwan” kadan ta kurbi ruwan sanan ta gyadama Gwaggo kai, ijiye ruwan Gwaggo tayi tace “bari naje nakira likita ni na mance me akace na danna adakin nan idan akwai wani abu, bari dai kiga nafita” tashi Gwaggo tayi zata fita saiga Hajiya da su Binta harda Kausar, ganin Lujain idanunta biyu yasa kowa yashigo dakin dasauri Hajiya tace “yaushe ta farka Gwaggo”? Cikeda fara’a sosai Gwaggo tana matse kwalla tace “yanzun nan fa likita ma zanje nakira” dasauri Kausar dake murna tace “bari nakira Dr” tajuya da gudu tafita ko kadan bata lurada mutu karo taci dawani Dr baya tayi zata fadi dasauri yarike mata hannu hakan yasa suka hada ido!.EPISODE 1️⃣0️⃣7️⃣






Wani kalan faduwa gabanta yayi dasauri ta fizge hannunta tace “sorry zan kira Dr ne dama ta farka” dan kallon Kausar yayi saikuma yakalli dakin da Lujain keciki yace “the patient with rib fracture”? Dasauri Kausar ta kalleshi hada ido sukayi dasauri tasauke kanta tace “eh” gabanta nafaduwa tarasa maisa, ahankali yace “my Dad is her Dr, just go inside zan kirashi” gyadamai kai Kausar tajuya saikuma hakanan tajuyo hada idanu sukayi dasauri tasauke kanta tace “thanks” sannan tabude kofan dakin da Lujain keciki tashiga tace “yana zuwa wai”.


Zama bakin gadon Hajiya tayi hannun Lujain takama tama peck ahankali tace “mekikeso kici tell me anything dakikeso” ahankali dan muryanta baya fitowa sosai tace “kunun gyada” dasauri Hajiya tace “Binta please je gida tunda kinfi kusa da asibitin” Gyadamata kai Binta tayi dasauri tana murmushi tajuya tafita, Hajiya sai peck take mata a hannu tanaji kaman ta cinye Lujain din, ahankali tace “bari nakira mijinki na sanar dashi zakiyi magana dashi?” Babu kunya dasauri ta gyadama Hajiya kai, saida Gwaggo tace “ohhh ke bakida kunya”? Duka yan dakin murmushi akayi harda Kausar, dialing number Abee Hajiya tayi da kanta ta sauka daga kan gadon takai wayan kunnen Lujain da sallama Abee yadauki wayan da muryan nan nashi nutsassiya. “Assalamu Alaykum Hajiya” shiru Lujain tayi batasan mesaba wani abu ne taji ya tsayamata awuya kawai ahankali tasaki kuka tareda kai duka hannayenta tarufe fuskanta sabida kuka daga kannen Abee Zainab, Sajida da Maman Aneesa da ita kanta Kausar atare suka hade baki sukace. “Awwwwwwwwnnnn”.


Komi na Abee tsayawa yayi chak jin kukan Lujain, awani irin hankali kaman yanama jariri magana yace “stop crying, do you want to see me”? Gyadamai kai tayi ahankali batare da tai magana, kaman yasan metace, murya chan ciki yace “I am coming now” katse wayan yayi, ahankali tajuye kunnenta batare data bude fuskanta ba ita kanta Hajiya murmushi tayi daidai Dr yazo wani magidanci ne tareda dan nashi da yana shigowa suka hada ido da Kausar, anatse yace “kubamu wuri mu dubata” fita duk sukayi daga dakin.EPISODE 1️⃣0️⃣8️⃣








Fitowa Dr yayi da danshi daya kara hada idanu da Kausar, dauke kanta Kausar tayi dasauri shikuma Dr yakasa cire idanunshi akanta har saida Maman Aneesarh ta lura da kallon dayakema Kausar, Babban Dr yace “Alhamdulilah she’s perfectly fine yanzu, fracture din ne kawai yarage shikuma with the help of belt din dake jikinta she will be fine, yanzu dai tai brush agoge mata jiki ta chanza kaya abata abinci taci dakuma lots of fruits, let’s watch her for 24hrs and see idan babu any complication zansa Dr Khalil here my son yazo yasallameta, zanje wani board meeting ne gobe” atare dukansu sukace thank you, Dr yawuce tareda Dr Khalil daketa kallon Kausar, komawa dakin sukayi Gwaggo zataje bayi debo ruwan zafi dasauri Sajida tace “Gwaggo ki zauna ki huta mu zamu debo” murmushi Gwaggo tayi tace “Allah shimiki Albarka” ruwan zafi tadebo sannan tafito tabude akwatin dake dakin taciro wani soft towel da brush, dan dago gadon kadan akayi da kyar ta iya jurewa tazauna kaman zatai kuka brush Sajida ta mata da taimakon Kausar tana zubawa awani kwano tawuce taje ta zubar abayi sannan Sajida tashiga goge mata jiki, bakaramin dadi Lujain tayi ba dudda tanajin kunya, wani half gown black na spongy Gwaggo takawo tace “ga wannan rigan zaku tayata sawa” Hajiya dauke kai tayi ganin yanda Lujain kejin kunya da bargon gadon ta kare kirjinta dazata cire nata rigan aka samata wani sannan ta ture bargon Gwaggo takawo turare aka feffesa mata da hula aka dan rufe gashin tai wani kalan simple kyau saiga Mama dasu Samira kaman sunsan ta tashi hardan murmushi saida Lujain tayi dataga yan uwanta saikuma ga Anty Binta da kunu.






Abee na zaune a office tareda Musty kiran nan yashigo, yana katse wayan yawani kalan daukan key dagakan table dasauri Musty yace “sai ina” batare da Abee ya kalleshi ba yace “Lujain is awake” cikeda farin ciki Musty yace “ohhh Alhamdulillah” biyo bayan Abee yayi atare suka shiga mota, gudu Abee yake agaban wani flower shop ya tsaya katse motan yayi yabude kofa Musty yabishi da kallo yana murmushi wato idan Allah yay shirin kamaka yana kamaka ne well look at Imran who would’ve thought Imrana zai taba so wata aduniya, just look at the small girl da jikinshi ke rawa akai, yana zaune nan cikin motan Abee yafito daga flower shop din rikeda wani red and white roses da aka hadasu tare sukai bala’in kyau ga dan tag akansu na get well soon wife, baki Musty yakama yana kallon Abee daya shigo cikin motan hararanshi Abee yayi baice komiba, Musty yace “wai haka ka iya soyayya dama Imrana banda labari wlh, iyye” tada motan Abee yayi yaja motan batare daya kula Musty ba, agaban wani super market ya tsaya yasake shiga, wani pink babban teddy yasaya mata da wasu lafiyayyen chocholate mai kyau sosai, dasu pringles, da biscuit, yabiya kudi yafito bude bayan mota yayi ya ijiye sannan yadawo gaba yashiga yazauna rufo kofan yayi yay shiru batare daya tada motan ba yana tunani Musty yace “what?” Ijiyan zuciya Abee ya fuzar ahankali yace “I can’t believe I lost my child” dafashi ahankali Musty yayi yace “Allah daya baka zai kara baka wani, kaida kake sharp shooter ma” hararan Musty yayi yatada motan yaja zuwa asibitin.EPISODE 1️⃣0️⃣9️⃣






Duk suna zazzaune adakin Gwaggo ita tama koma carpet ganin Allah yariga yabama Lujain masu kulada ita sama da ita ma aduniyan nan tana kallon kowa suna magana da Mama dakuma Gwaggo dan su ukun ne ke kan carpet, su Kausar dasu Samira duk suna kan gado, Kausar nabata kunun abaki da spoon tanasha ahankali, Anty Binta kuma na kansu supervising yanda Lujain keshan kunun, Lujain tarame idanunta sun fada ciki sosai amman kaman kyanta yakaru ne, duk suna zaune ahaka aka bude kofan dakin da sallama chan kasa ciki ciki dasauri kowa yajuyo harda Lujain, Abee ne tsaye gaban dakin yana sanye dawani black suit dayamai kyau sosai hannunshi rike da flowers din yahaderai kaman baitaba murmushi ba ganin yanda yara suka cika dakin, gefenshi kuma Musty ne yana rikeda teddy, da sauri su Kausar dasu Samira duk suka sauka daga kan gadon ganin Abee, Su Sajida sukace. “Sannu da zuwa Ya Imran” Kausar tace “Abee sannu da zuwa” su Samira sukace “ina yini Abee” dan sunji haka ake cemai, gyadamusu kai Abee yayi batare daya amsaba sannan yashigo dakin anatse batare daya kalli kan gadon ba yadan kalli Hajiya da Gwaggo da Mama yace “ina yininku” atare dukansu sukace “lafiya lau Imran” Gwaggo tace “barka barka ta tashi Imrana je kaji kaga matarka” dan juyoda kanshi Abee yayi ya sauke kwayar idanunshi kan Lujain dake kwance kan gado tana wani irin kallonshi kaman yaune rana na farko data fara ganinshi zuciyanta na bugawa abnormally, tana jin tafiyan wasu butterflies acikin cikinta sokawai take yazo wajenta, lumshe mata idanu yayi yabude batare data karasa gaban gadon ba, wani kalan hawaye ne suka bulbulo suka cika kwayan idanunta tana kallonshi ahankali tadaga hannunta tamikamai alamun yazo yariketa kowa na dakin hatta Musty yabisu da kallo is just like kowa nason love story nasu, kowa kuma nason yanda Lujain kemai kaman har karaman baby shi kaman wata his last born, Abee duk yanda yaso yadaure sabida mutanen dakin kasawa yayi yakarasa gaban gadon yana wani kalan kallon cikin kwayan idanunta gently yasa hannunshi yarike hannunta batare dayace uppan ba but the whole thing is like zuciyoyinsu na magana, fashewa dawani kalan kuka Lujain tayi kaman ba Lujain din da dazun nan take murmushi take shan kunu ba, wani kalan sangartaccen kuka takema Abee daya rikemata hannu yana kallonta, kasa daurewa Gwaggo tayi tace “ammandai Lula akwai tabara jama’a, Hajiya ba nan nan muke ganin yarinyar nan taga yan uwanta dasu Kausar sai murmushi take musu suna hira Kausar na bata kunu ba shine yanzu taga mijinta tana kuka uwa tsungulinta muketayi tun dazu, yau naga iya shege, yaushe Lulu takoyo wannan tabaran” dasauri Musty dake rike dariyanshi yace “Gwaggo zomuje waje muyi magana” tashi Hajiya tayi itama takalli sauran yaran tace “kumuje” dukansu fitowa sukayi daga dakin saida Abee yaga sun fita am maida kofa an rufe yaduko da kanshi ahankali lumshe idanunshi yayi kafin ahankali ya manna mata kiss agoshi.EPISODE 1️⃣1️⃣0️⃣








Yadade ahaka sannan yacire lips nashi daga forehead dinta kafin ahankali yasake dago kanshi yana kallon kwayar idanunta, murya chan kasa yace “stop crying I am here now” gyadamai kai tayi yakai yatsanshi ahankali ya sharce hawayen dake bulbulo mata daga gefen idanunta yana kallon kwayan idanunta stilll kafin gently yadaura lips nashi kan nata, ijiyan zuciya suka sauke dukansu atare sannan gently Abee yashiga kissing nata, irin kissing din dake holding so many messages yana gayamata how much yake sonta and how much he misses her, ahankali itama take maidamai da kiss din sun dade ahaka kafin ahankali yazare bakinshi dagakan nata batare daya raba fuskokinsu ba murya chan kasa yace “I love you Baby” hannayenta tadaga ta rungumeshi so tight tace “I love you nima sosai” dasauri yakalli fuskanta yace “kina sona Lujain?” Gyadamai kai tayi dasauri tace “ina sonka sosai” kissing dinta yasakeyi sanan yasaketa, dan dago gadon kadan yayi sannan yawuce yadauke teddy bear a inda Musty ya ijiye Abee yadawo gaban gadon yana kallon yanda take kallonshi, Teddy yafara bata, amsa tayi ahankali tana murmushi kafin yabata flowers din shima karba tayi takalli abinda tag din yafadi kafin takai fliwers din fuskanta kamshi sosai suke sannan ahankali yabata ledan budewa tayi chocholate tafara cirowa da sauri tabashi ashagwabe tace “ka budemin” hancinta yadanja yace “sweet tooth kawai” bude mata yayi yabata karba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login