Showing 18001 words to 21000 words out of 148158 words
da hannayen ta data dunkule kowa yabita da kallo adakin banda Abee da kanshi ke kasa, duk wani mai imani da zuciya yakalli Lujain saiyaji jikinshi yay sanyi, Gwaggo na rike da gyalen ta taka zuwa gaban table din da Abee ke zaune cikin ihu tace “kawani sauke kai kasa kaman sabon ango kalli jikana nace, dago kanta ta kalleta” ahankali Abee yadaga kanshi yadan kalli Gwaggo sannan gently yakalli direction din datake nunamai gabanshi na faduwa sauke idanunshi dasukai jaa yayi kan Lujain dake kuka sosai idanunta akasa yay shiru danji yayi zuciyanshi tai wani iri, komawa Gwaggo tayi wajen Baba ganin yana kallon Lujain din datace ta fizge paper da aka bama Lujain amakaranta tadawo ta ijiye gaban Abee tace “kaga yanda akama jikata wanka da lemu tundaga ka har kafa banda haka makarantan suka bamu takarda waisun koreta sabida fasika ce mugun iri zata bata musu sauran dalibai” fashewa Gwaggo tayi da kuka sosai daidai nan ta durkushe awajen ahankali Abee yasauke kanshi ganin yanda tsohuwar da akalla zata girmi Hajiyanshi da yan shekaru na kuka sosai agabanshi, Baba da Abdulhadi ne sukazo wajen da saurinsu zasu dagata tace “wlh kuka tabani zan daga muku nono awajen nan ku kayaleni kawai” tai maganan tana tashi takalli Abee da kanshi ke kasa sannan takalli Musty tace “kaga yarinyar nan dakake gani haka marainiya ce uwarta na nakuda kanta haifeta ta mutu agurguje akai operation aka cirota sabida wai tasha ruwan cikin wanda yamutu yarinyan nan dakuke gani saida tai kusan shekaru biyu acikin kwalban asibiti ni ke biyan komi ubanta wannan din nan dakuka gani” tanuna Baba dashima yasauke kanshi kasa tace “shi baida kudin biyan kudin kwalba duba sha biyar duk ranan duniya acirota daga kwalban wai mutafi gida, likita kuma yace ana cirota baifi tai awa ashirin da hudu ba zata mutu, mijina babansu mai kudin kauye ne daya mutu inada gado kap na saida gidaje na manya manya a binni guda hudu da shanaye na kauye haka na biya dubu sha biyar biyar na shekara biyu cur kafin acirota, nine komi na diyar nan tundaga zama a asibiti, abincinta, kayan sawanta da rainonta da komi ma, koda aka bani ita haka muka dawo gida yau lafiya gobe ciwo ko shigowa bayayi yadubata dan yanada wasu yaran lafiyayyu marasa ciwo, nikuma na nunamai zan iyama jikata mai ciwo gata tamafisu jin dadin duniya, saida yarinyar nan takai shekaru bakwai aduniya tafara makaranta” Gwaggo tashare idanu dan hawayen sinki tsayawa tace “bakuga yanzu tana shatara a SS2 ba bayan su Samira suna shekaru sha shidda sun zana jarabawan kare sakadire, amman ita har yanzu bata gamaba sabida ciwo, ni nasan wahalan danayi akan jikata nasan gumi rashin bacci rashin sukuni danasha akanta, har yau har gobe tunda tazo duniya bantaba baccin dare bantashi ba saita tadani, yau awayi gari sunanta yabaci kuce nai shiru koda akace zata mutu ban hakura akanta ba yanzu ne da lafiyanta kalau zan hakura nai shiru akanta wlh wlh Billahillazi La’ilaha Illahuwa bazata yuba ko laifinta ne ko laifinshi ne nidai nasan bakuyi fasikanci ba dan bangani alamu a jikinta ranan ina tareda ita data dawo daga makarantan ai kaima bakai kama da Babba mai lalata yaraba dan haka idan kunason zaman lpy abu dayan zan gayamaka shine ka auri jikata! Ka auri dan baran iya da raina da lafiya na inaji ina gani sunan jikata yabaci ba, tun yanzu a makarantan su kadai an mata wanka haka da koro uwa wacce aka kamata dumu dumu tana zina, ahanamini yarinya fita titi gudun kar adinga nunata wlh baran yarda ba, hanya dayace shine ka auri jikata!”
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAIJama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
EPISODE 1️⃣2️⃣
Kowa na dakin hatta Lujain din dake kuka sosai dashi kanshi Abee saida yadago kanshi yakalli Gwaggo jin abinda tafadi, cikin tsantsan nuna seriousness Gwaggo tace “eh haka nafadi, nace saika auri jikata! Duk abinda babba ya hango karami bazai hango ba, wannan video dakuka nunamin kokun watsashi aduniya mutane ba yarda zasuyi ba bazai wankemin jikata ba, hanya daya zai wanke jikata tastas shine ace kaidin mijinta ne da aure tsakaninku, daga masu gulma dashi usulin algugumi dan wutan jahannama daya yada video dana tabbata baku ganshi ba haryau saisuji kunya kaga ko banza yay aikin banza, shi bazai sami miliyan darin ba shibai samu kampanin ba” hannunta Baba yakama zaiyi magana Gwaggo ta fizge hannunta idanunta sunyi jajir tace “wlh wlh duk wanda yace saija dani cikinku saina tsine mishi albarka ubanme zaka gayamin lokacin dazata mutu ma baka tsaya mata ba yaune da aka kirata da fasika zaka tsaya mata? Nine komin Lujain, nine uwarta, nine ubanta, nine kakanta, kamin shiru kawai, wlh wlh saiya aureta akan wani dalili zaija sunan diyata ya baci kuma bazaiyi komi ya wanketa ba, wlh saiya aureta inba hakaba wlh wlh sai hukuma tarabamu, marainiyan yarinya na eh ku jibeta fa abin tausayi ubanta bai damu da ita ba sabida yaga batada mahaifiya, inda yau mahaifiyarta na raye Kunsan kalan tashin hankalin dazata shiga kuwa? Bayan kunsan rayuwa yakoma yanzu iskanci ado ne wajen namiji mace ce rayuwanta zai baci har abada, yanzu awannan video banda bayanshi anga fuskanshi eh? Yar yarinyar nan dai akaga fuskanta har akaga tana gyara riga, idanba aurenta yayi ba koya wanketa wazai auri Lujain iyye? Kufadamin wani namiji ne zai aureta? Wasu iyayene zasu bar dansu ya auri yarinyan da video fasikancinta ke yawo a yanar gizo? Shi yanzu bashi kwana biyu anmanta dashi itako fa? Namiji mutane barasu iya taranka ma itako Yar yarinya mace halama saidai tadaina fita danta fita tareta za’ayi amata duka a titi, yakukeso tayi? Matar ubanta kuma dama ba sonta takeba kaga gwara ka aureta naga kanada hankali kanada yara dasunma girmeta zaka rikemin ita amana koyau na mutu banda nadama dama kullum tunanina wazan aura mata da hankalina zai natsu dashi ashe kai Allah zai kawo mata amman ta wannan kaddaran” Gwaggo tafashe da kuka muryanta kawai akeji a duka office din ganin yanda take kuka kuma su Baba sun kasa mata magana gudun karta tsine musu yasa ahankali Mustafa yaje inda take tsugunnawa yayi yakamota kaman yakamo mahaifiyarshi hannu yasamata a fuska yana goge hawayen datake yace “dan Allah Gwaggo kiyakuri kidena kukan nan dan Allah sabida ni” ahankali tahadiye kukan tana kallonshi cikeda lallashi yace “Gwaggo kinga nan office neko wannan matsalan kuma matsala ce daya kamata atattauna agida kibamu address din gidanku anjima da daddare namiki alkawari dukanmu shima harda iyayenshi zamuzo sai ayi magana da kyau Gwaggo kinji Gwaggo amman yanzu kutafi, itama ku kaita gida tacire kayan nan kar wani abun yasameta maganganun nan da ake agabanta bai dace ba, kuma babu kyau yanda kike kuka agabanta, kece karfinta, kobaki hakura kitafi dan kowaba kiyi dan ita naga yanda kike sonta” juyawa Gwaggo tayi takalli Lujain dake kuka sosai har lokacin taji barata iya musuba tace “gidan mu na nan kwanan tipa a Gwarimpa idan kun shigo gida na biyar mai gate mai ruwan goro” anatse Musty yace “zamuzo anjima da daddare” tashi tayi tadauki gyalenta dake kasa taje wajen Lujain ta lullubeta dashi ta kama hannunta tadagata tace “muje Allah natare dake, nima ina tareda ke” su Baffa duk suka tashi, Musty yace “kaisu ta back door bata gaba ba sabida reporters” binsu su Ibro da Hamza sukayi dan kaisu sannan ahankali Musty yazauna tareda sauke wani ajiyan zuciya yana kallon Abee, Harun yace “wlh wlh idan aka kamo yaron nan I will make sure yay rotting at the worse Nigeria prison” Abdul yace “the guy is evil” daidai nan wayan Musty yashiga ringing ganin Hajiya ne yasa yakalli Abee da kanshi ke kasa yace “tashi muje gida Hajiya is calling” batare daya kalleshi ba yana kokarin fara typing yace “ban tashi daga aiki ba sai 4, and this is just 12:54” shiru Musty yayi yana kallonshi Allah kadai yasan yanda yake hurting right now amman bazai taba nunawa ba, ganin bakinciki Abee zai cusamai yasa yajuya yakalli su Harun yace “kumuje” saikuma yajuya afusace yadauki wayan Abee dake kan table yace “shima ka kwace idan ka isa” yawuce yafita fuuu daidai Hajiya na kara kira dauka yayi kafinma tayi magana yace “Hajiya gani nan zuwa komi yazo dasauki kada kidamu kanki hawan jininki yatashi” katse wayan yayi suna fita suka shiga mota sai gidansu Abdallah da Kausar sun dawo daga makaranta dudda sunada lectures ganin videos dake trending na babansu, Zainab data tafi daga ita har mijinta sun dawo, kofar gidansu yacika kaman anyi mutuwa dayan anguwa babu wanda baya sonshi a anguwan dukansu sun karyata guards na estate dinsu sun hana ko reporter daya ya shiga saida su Musty suka fara gaisawa da mutanen waje sukace shairi akamai sannan suka shiga ciki bayan babban Liman na anguwan wanda yake matsayin ubansu yabisu zuwa cikin gida duk suka zazzauna a falo idanun kausar yay jajir taci kuka harta gaji na Abdallah ma haka amman shi baiyi kuka ba.
Hajiya kafin suyi magana tace “ina yake”? Musty yace “ai kinsan Imran da taurin kai yace aiki yake sai 4 yake tashi daga aiki munbarshi achan danko jawoshi zamuyi da karfi bazai tahoba amman Ibro da Hamza na chan tareda shi karki damu” tagumi Hajiya tayi Anty Binta ta bubbuga mata baya yace “dan Allah Hajiya kada kidamu kanki” anatse Hajiya tace “Meya faru Musty”? Ahankali yabasu labarin daga farko har karshe tsaf da yanda iyayen yarinyar sukazo da abinda sukayi kowa yay tsit adakin na kusan minti biyar sannan Hajiya tai breaking shiru takalli Liman tace “Liman kaine kake matsayin mahaifin yaron nan yakake ganin za’ayi”? Ahankali Liman yace “shi aure rufin asiri ne kuma sutura ne ga mumini, gabaki dayan mu nan munsan Imran bazai taba iya aikata wannan abuba abinda nakeso kuduba anan shine ayar dake tattare da abin nan inhar Allah ya shiryamai wannan kaddaran to da dalili, saikuma abu nabiyu shine inhar akabar zancen nan haka shikenan yabata ma ita yarinyar dashi Imran suna nan da gobe zakuji wasu sabbin labarai da kazafi da sauransu natashi indai mutane ne, saikuma sana’arshi da kampaninshi zai jijjiga that is idan hukuma bata shigo bama ta rufe company gabadaya ba, amman yanzu duk idan kuka ijiye sauran hujjojin nan kuka dauki hujjan farko dana kawo kaddaran suce Allah yaga dama yakuma tsara musu ita ahakan dan haka ayarda da auren amusu auren amusu auren asanara duniya su daman ma’aurata ne dan killace mutuncinsu hakan kadaine za’ayi ya wankesu shikuma yaron kubashi dududu satin nan dakanshi zai kawo kafanshi yanemi gafara zan nunamai ayar Allah ba wasa bane sannan Allah sarki ne tsarkakke Al Azza Wajal! Dan haka mu amince da abinda sukace mu kalli maraicin yarinyar”, dan hawaye Hajja ta share tace “nasan bazai taba yarda yay aure nan ba, babu abinda Abee ya tsana kaman aure, amman yau zan nunamai nine mahaifiyarshi, zan iya komi dan kare mutuncinshi aduniyan nan” sallama Liman yamusu yatafi sukuma kowa yay zugum falo saida aka kira la’asar ne ma su Musty suka tuna ko azahar basuyibasuka wuce.
Biyar daidai on the dot Hamza da Ibro suka shigo office din yana zaune akan kujeran su kallo daya yamusu yadauke kai anatse Ibro yace “Yaya Imran is 5 mutafi gida” dago idanunshi yayi yakalleshi ahankali Ibro yasauke kanshi kasa dan gabaki dayansu babu mai iya jure idanun Ya Imran akansu kwarjininshi is way to much, kaman daga sama yace “yaushe nida ku muka fara barin office tare?” Da sauri dukansu suka dagakai suka kalleshi karamin Mac book dinshi da yan kananun abubuwanshi yashiga hadawa batare daya kallesu ba babu alamun wasa akan voice nashi yace “ku kama gabanku” daidai yatashi daga kan chair din tareda daukan Car key nashi laptop dinshi a hannunshi yafito wuce su yayi duk suna tsaye suna kallonshi yabude kofa yafice dasauri suka fito Ibro ya tsaya yana kulle office din ganin yayi hanyar dazai kaishi main entrance suda sukeso yabi ta kofan baya dan reporters har yanzu na main entrance yasa aguje suka bishi yana jinsu amman ko juyowa baiyiba yakallesu anatse yake tafiya one after another kaman mai sarauta har zuwa gate din suma security nashi daga gaban entrance din ganin Oga yasa sukaji kaman sucemai yajuya yakoma ta dayan exit din amman shakka da tsoro yahanasu, budemai kofa sukayi yafice reporters na ganinshi suka taso aguje ana binshi kowa da kalan tambayan dayake watsamai koransu security nashi suka dingayi suka rike hannu suka taresu shikuma yay wajen motanshi yabude laptop dinshi ya ijiye a dayan sit na gaban sannan yashiga yarufe kofa yatada motan yafice, su Hamza ma suka shiga motocin su suka mar mishi baya.
Agaban estate nasu wasu reporter yagani but anhanasu shiga dayake motarshi tinted ne basusan shibane aka budemai gate yashige abinshi yan jama’a yagani akofar gidansu ciki harda Arif dolenshi ya tsaya akofar gidansu yasauke glass batare daya sakko daga motan ba, chaaa jama’an anguwa sukamai akai suna Allah kyauta Alhaji duk mai nufinka da shairi Allah ya maida musu Liman yamana bayanin komi Allah natare dakai kuma zamu nunama mutumin ayar Allah ba abin wasa bane wlh saiyazo harnan anguwan dakanshi yabada hakuri dan murmushi yamusu yace “nagode” hakan yasa suka watse saura Arif kadai da idanunshi sukai jaa yataho wajen motan ahankali zubamai idanu Abee yayi kaman babu wani abu yace “what are you doing here kabar Amarya”? Kasa magana Arif yayi but kana ganin hankalinshi kasan atashe yake, dan murmushi Abee yamai kadan yace “wuce ka koma gidanka” gyadamai kai Arif yayi ahankali babu musu yakoma yashiga motarshi shikuma Abee yatada motanshi aka budemai gate yashiga cikin gidansu.
You can read EPISODE 13 a IG💃💃EPISODE 1️⃣3️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Parking yayi awajen parking nacikin gidan, yakai kusan 5min zaune acikin motan ya jinginar da kanshi tareda lumshe idanu sannan yatashi yabude kofan motan yafito ahankali da Maigadin yafaracin karo da shima idanunshi yay ja sai kallon Abee yake kaman yauya fara ganinshi, dauke kanshi Abee yayi, laptop dinshi ya dauka yamaida kofan motan yarufe sannan yay cikin gidan da sallama chan kasa yabude kofan Babban falonsu yashiga kowa na zaune falon harda Zainab dayasan takoma gidanta kaman gidan da akai mutuwa duk suna kallonshi ga Hajiya ita tabuga tagumi itama kallonshi take, ahankali yace “ina wuni Hajiya” batare daya jira amsanta ba yawuce stairs dasaurinshi dan baimason wani magana yana zuwa yabude dakinshi yashiga ciki, zama yayi ahankali bakin kujeranshi yacire takalminshi da safan kafanshi kafin yatashi yamike tsaye ahankali yake tafiya zuwa bakin gado gently ya kwanta akan gadon tareda fuzar da ajiyan zuciya ya lumshe ido ahankali yanajin kaman zazzabi na neman kamashi, knocking kofarshi da akayi yasa ya runtse idanunshi da karfi yabudesu ahankali batare dayay magana ba, muryan Kausar yaji ahankali tace “Abee” tashi zaune yayi da sauri yakalli kofan anatse yace “come in” bude kofan dakin akayi Kausar yagani tareda Abdallah idanunsu sunyi jaa suna tsaye gaban dakin duk suna kallonshi dawasu kalan disturbing eyes, wani abu yaji ya tsayamai azuciya amman yadaure batare da wani abu yanuna akan fuskanshi yace “kushigo” Kausar tafara shigowa da gudu tana zuwa batai wata wata ba kneeling tayi akasan gaban gadon gabanshi kawai tafada jikinshi tasa kanta akirjin ta rungumeshi ta kulle hannayenta ta bayanshi ta kankameshi sosai tawani kalan fashe da kuka duk duniyan nan batada abinda takeso kaman babanta, ahankali Abdallah da Abee ke kallo yanajin yanda Kausar ke kuka ajikinshi yakaraso wajen shima zama yayi akusa da mahaifin nashi agefen gado gently yadaura kanshi kan kafadan Babanshi batare dayace komiba, saukan dumin hawayenshi Abee yaji kan kafadarshi tunda abin nan yafaru sai yanzu ne Abee yaji kawai he’s completely heartbroken sabida yanda yaranshi suke kuka ajikinshi, Kausar ita wannan daman ta iya kuka but Abdallah rabon dayaga kukan Abdallah tunda mahaifiyarshi da yayyinshi suka rasu, shiru yayi jikinshi yayi wani kalan sanyi baimasan wane zai lallasa cikinsu ba, baisan mezai gayamusu ba, all he knows is yau shine reason behind his children tears, kusan 10min kuka suke ajikinshi hakan yasa yasauke ijiyan zuciya Abdallah yafara dago kanshi da hannunshi yace “mehaka kakeyi Abdallah Men don’t cry” dago fuskan Kausar yayi daga jikinshi dake kuka sosai hannunshi yakai yasharemata hawaye yadanyi murmushi tareda jan mata hanci yace “kinsan bansan kuka ko” girgizamai kai tayi cikin wani kalan sheshekan kuka tace “mekamusu akeson abata maka suna Abee, me Babana yamusu? Why you Abee”? Kifa kanta tayi akan kafanshi tahau kuka sosai gwanin ban tausayi, dagota Abee yayi idanunshi sunyi ja yakalleta dan murmushi yakakalo yakalli Abdallah dake kallonshi yama rasa abinda zaice musu kawai rungumesu duka yayi akirjinshi duk suka kankameshi kaman yanda he was holding them so tight, bayansu ya bubbuga anatse calmly trying to soothe them yace “everything is going to be fine I promise” yay shiru jin haryanzu hawayen su na zuba ajikinsu yace “if you two wants to break me kucigaba da kukan nan” kaman yabasu pills din tsayarda kukan sukayi hakan yasa yadago kansu murmushi yamusu yahada hannayensu biyu yakai bakinshi yamusu peck ahankali yace “you two are Abee’s strength if you break I break, so I want you to be my strength not my