Showing 1 words to 3000 words out of 57616 words
Chapter 1 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
FAHIMAH
Book 1 Complete
Writing by
Takori kabara
arewanovels.com.ng
SHIMFIDA
Misalin karfe ukku na yammacin ranar, wadda ta kasance Talata, cikin wata Unguwa a jihar Kano da ake kira ''Yankaba, Hajiya SAFIYYAH-BASUDANIYYAH (kamar yadda kowa da ya santa yake kuma alaqa da ita ke kiranta), na zaune bisa Kilishin tsakiyar falon ta, carbi ne dan madina a hannun ta tana ja, lokaci zuwa lokaci tana mai daga kanta zuwa ga tankareren agogon bango dake manne a fuskar gabas maso kudu na falon nata. Ga dukkan alamu akwai abinda take dakon jira, shiyasa tun da ta yi sallahr azuhur bata tashi a gurin ba take yawan kai idanun ta ga agogon bangon.
Kayataccen falo ne ne da ya ji kayan alatu na zamani wanda kallo daya zaka yi masa ka tabbatar masu gidan suna cikin wadatar rayuwa, daular duniya ta gama zaunawa dai-dai misali da burin kowanne dan adam. Komai dake falon kalarsa ruwan madara ne da ratsin ruwan goro (orange) wanda hakan ya maida falon kalar unique don kala ce da ba'a faya amfani da ita ba wajen tsara falukan zamani.
Tun Haj. Safeeyah bata damuwa, amma da ta ga yadda lokaci ya ja sai damuwa ta fara nunawa akan kyakkyawar Basudaniyar fuskar ta. Me ya tsayar da FAHIMAH a makaranta har yanzu da ake neman karfe uku na rana???
Sallamar mai aikin ta Talatu ya katse mata tunani, ta shigo dauke da butar Shayi irin ta larabawan SUDAN da 'yan kananan kofunan tangaran na shan shayin Sudanai, kai tsaye ta nufo inda uwargijiyar ta ke zaune ta russuna daga gefe ta ajiye, ga dukkan alamu abu ne da ya zamewa Hajiyar al'ada wato shan shayin akai-akai. Talatu tace, tana duban Hajiyar.
"Hajiya mutuniyata ko lafiya? Tun dazu nake duban hanyar ta har yanzu shiru, ko ta ce miki zata biya wani waje ne yau?"
Hajiya Safeeyah ta kai karshe a carbin da ta ke ja, tayi addua suka shafa tare da Talatu, sannan ta ce.
"Tunanin da nake ta yi tun dazu kenan, karfe daya da rabi yau tace min zata dawo, bari in kira wayar ta mu ji ko lafiya, don Fahimah bata zuwa wani waje ba tare da ta gaya min na mata izni ba".
Ta dauki wayar dake gefenta ta lalubo lambar Fahimah ta kira ta kara a kunnen ta, amma har tayi ta katse mai wayar bata amsa ba. Which was very unusual of her (kin daga waya). Wanda hakan ya kara dugunzuma zukatan Hajiya da Talatu.
Daidai lokacin da ya shigo falon yana balle 'links' din hannun farar rigar shi, gabadaya falon ya dauki kamshin sassanyan turarensa "Maison Francis (Kurkdjian, Paris)". Farar shaddah ce kal a jikin shi mai santsi da ake kira (London King) da farar hular Zanna mahadin shaddar jikin shi. Dogo ne, mai fadin kirji (physique chest) amma hakan bai hana ka kira shi siriri, don tsayi har ya rankwafa, kallo daya zaka yi mishi ka tabbatar ba cikakken bahaushe bane; ko dai ruwa-biyu (half-caste) ko kuma cikakken Ba-sudane. Sudanan ma irin fararen Sudanai ba bakaken cikin su ba, hancinsa don tsayi har lankwasawa yayi kadan, hular kansa ta nitse tsaf a cikin tarin sumar kansa wadda ta kara fallasa jinsin da ya fito daga cikin sa.
Ga dukkan alamu cikin sauri ya ke, sauri mai yawa, ya dubi mahaifiyar sa dake zaune nannade cikin laffaya shudiya da carbi a hannun ta, bai taba ganin ta da wata suttura ba ta Sudanese ba, Talatu na duke gabanta tana firfita mata shayi, yayi dan russunawa daga tsaye cikin tarin ladabi ga mahaifiyar sa...
"Ammi zan fita, zan koma office, don bamu tashi ba na dawo, amma bazan wuce karfe biyar na yamma ba yau zan dawo, insha Allah. Na baro wasu ayyuka da ban karasa ba nake so inje in karasa, don gobe da safe managern Gyadi-gyadi Branch zai karbe su daga ofis dina".
Bai kuma jira cewar mahaifiyar tasa ba ya doshi kofa, ko abincin ranar da aka shirya masa bisa makeken tebir din falon bai kalla ba.
"Uwais!"
Muryar mahaifiyar tasa ta dakatar da shi. Ba tare da ya juyo ba ya dakata a kagare.
Ta ce, Fahima ba ta dawo ba tun fitarta makaranta.
Annurin da ke fuskarsa nan da nan ya gushe. Gabadaya ya juyo fuskarsa a gintse, For Allah sake. Ammi ni ina ruwana? Is she a kid? Ko kuwa ba ta san hanya ba?
Hajiya Safiyya ta girgiza kai tana iya karantar tsanar maganar yarinyar da ta yi masa baro-baro a kan kykkyawar fuskarsa. To amma dole ta gaya masa sabida yadda kasar tamu ta koma daukan dan mutum ya zama kamar na kiyashi. Babu kuma wani namiji a gidan bayan shi, shi ne ubansu har ita da ta ke mahaifiyarsa.
Duk uzurin da ka ke da shi ka ajiye ka bi bayanta, ko in tashi ni da kaina in bi ta.
A matukar fusace ya sa kai ya fita daga falon ba tare da ya ce komai ba.
Daga yadda yake tukin motar kadai za ka fahimci ransa a bace yake, don dai fuskar sa ta kasance mai boye bacin rai ne, ko kadan ba abin da ya tsana a duniya irin Ammi ta hada sha'anin sa da na Fahimah. Ta ki yarda ta gane har yau shi zuciyarsa ba ta son Faheemah, kuma har abada ba za ta so ta ba! Ba don komai ba sai don ASALINTA.... Da wasu specific dalilan da suka dade da samun muhalli a ransa tun suna yara shi da Fahimar, muhimmi shi ne son da Ammin sa ke mata, wanda yake ittikafin da kyar in bai zarce wanda take masa shi da ta haifa ba.
Shi kuma tun asali mutum ne mai kishi akan abinda yake so, musamman Amminsa, wanda kishin nasa akan ta ne ya hanata sake aure har yau.
A daidai lokacin ya karya kan motarsa ya shiga makarantar YAN DUTSE COLLEGE, bayan maigadi ya bude masa kofar makarantar, abin haushi yana shigowa ita ya fara hangowa tun daga nesa suna tafe ita da kawarta Majida suna hira, sai dariya ta ke ba abinda ya dameta. Ta baro masa uwa cikin taraddadi don bata san zafinta ba. Her elegant black skin sai sheki ta ke cikin hasken ranar, babu wani abu mai haske a jikinta kamar fararen idanunta da jerarrun hakoranta. She's dark-skinned yet beautiful. Wasu irin idanuwa masu sparkling cikin idanun duk mai dubanta. Cikakken gashin girar da ya kusa hadewa da dan uwansa yana daga cikin abin da ya bambanta ta da sauran mata yan uwanta.
Uwais dauke kai ya yi yana sakin tsaki, tare da danna musu gigitaccen horn mai karfi don kamar ba su lura da tsayuwar shi ba. A ransa cewa ya ke, ko uban me suka zauna yi a makarantar har yanzu oho! Kwata-kwata su da suka rage cikin makarantar ba su fi a kirga da yatsun hannu ba.
Ta dago kai da sauri ta dubi inda horn din motar ya fito. Mutum na karshe da ba ta taba tsammanin gani a makarantarsu ba, da sunan dai ya zo daukanta. A gurguje ta yi sallama da kawar tata ta nufo inda yake kafafunta har hardewa suke don sauri da fargaba.
Ba yau ta fara ganin wannan moody expression din a kan kyakkyawar fuskarsa ba in dai a kanta ne, don haka inda sabo Fahimah ta saba. Ta bude kofar gefensa ta shiga, ya tada motar a guje ya bar makarantar ba tare da ya dube ta ba.
Maimakon ya dau hanyar gidansu kamar yadda ta yi tsammani, sai gani ta yi sun dau hanyar Bank Road, ita dai ba ta ce komai ba, amma ganin sun yi parking a wani branch bankin GT ta fahimci inda suka zo din, wajen aikinsa ne.
Ya bude kofarsa tare da daukar jakar loptop dinsa da wayoyinsa ya yi shigewarsa. Duk inda ya gifta sai maaikata yan uwansa sun kula shi sun gaishe shi, amma hannu kawai Uwais yake daga musu ya wuce, kowa ya saba da rashin walwalarsa shi ya sa shan kamshinsa ba ya damun kowa don farin jini gare shi ba na wasa ba, wanda kyawun surarsa ke sayo masa.
Yana kokarin zama a kujerar ofishinsa wanda ke zagaye cikin raw gilashi, kowa da ke wajen yana iya hango shi daga waje, wayar Ammi ta shigo, yana jan kujerarshi zai zauna ya amsa mata.
Muna tare.
Kawai ya ce tare da ajiye wayar bisa makeken tebirinsa baki wuluk mai sheki. Ammi hankalinta ya kwanta tunda ya ce yana tare da Fahimar.
Kai ba za ka ce ya ajiye mutum cikin mota ba, ya kunna kwamfutar kan tebirinsa ya durfafi ayyukan da ke gabansa cikin kwarewa da sanin makamar aikin sa, wadanda da ma su ya dawo don yayi. Ya manta da wata da wata mutum dan adam da ya ajiye a cikin mota, ba tare da ko ya sauke mata gilashi don ta sha iska ba.
A can kuma Faheema tun tana duba siririn agogon da ke daure a hannunta har ta kwantar da kanta a kan dash board din motar, ta sauke gilassan da ya rufe iska ta soma ratsa ta, wata irin yunwa na sakadarta. Rabonta da abinci tun karin kumallon safe da Ammi ta takura mata ta yi, ta san halin Uwais sarai, duk yadda aka yi Ammi ce ta takura masa ya bi sawunta shi ya sa ya zo ya shanya ta a harabar ofishinsu.
Ba kowa ya ja mata ba sai Mr. Edward malaminsu na Biology, shi ne ya zaunar da su yin practical na darasin da yake daukarsu bayan normal school hours kasancewar nan da watanni uku za su zana jarrabawar barin makarantar sakandire gabadaya. Ammi ta san Uwais ba ya son hada hanya da ita don me za ta sa shi ya biyo bayanta?!
Allah sarki Fahimah! Tun tana sauraron kidan da akuyar cikinta ke yi, har ta koma ta kwantar da kanta jikin kujerar motar, wani wahalallen barci ya yi awon gaba da ita.
Sai karfe biyar na yamma ya kammala duk abin da yake yi a bankin, ya tattaro wayoyinsa da kwamfutarsa ya fito. Sai da ya tunkaro motar sannan ya tuna da ita, ya bude gidan baya ya zuba shirginsa sannan ya shiga mazauninsa ya zauna. Kunna motar da ya yi, da reverse hadi da cin taya ya bar harabar bankin shi ya tada Faheemah daga wahalallen barcinta. Barcin yunwa da gajiya. Ta dube shi ta gefen ido, ya nutsu yana tukinsa cikin gwanancewa.
"Fuskar ta salihai, kyakkyawa a ido, amma kamar ta Firauna a zuciya. Fahima ta fada a zuciyarta.A shekaru goma shaf takwas na rayuwarta da ta yi tare da shi gida daya, bai taba kyautata mata ko sau daya ba, sannan ba za ta taba iya fadar wani alkhairi guda daya da ya yi mata ba a matsayinsa na Yayanta a kan dalilin da ba ta sani ba. Duk da kasancewar su biyu ne kacal a wajen mahaifiyarsu Hajiya Safiyya, ta sa a ranta Uwais makiyinta ne na babu gaira babu dalili, don bata san laifin da take masa ba, Ammi ma bata sani ba, don har a cikin kwayar idanunsa tana iya hango tsantsar kiyayyar da yake mata, a gaban kowa kuma ba ya iya boyewa including mahaifiyarsu Ammi Safiyyah.
Ita kuma nan duniya babu mai burge ta irin UWAIS ABDULKARIM SHAGARI!!!
Wani kwayan mutum guda daya da ya yi mata babakere a zuciya.Daga baya ta fahimci shi Ammi ta haifa ba ita ba daga lokacin da ta soma hankali, amma in za a yanka ta ba ta san alakar da ke tsakaninta da su ba.
Ita dai ta taso ta ganta a gaban Hajiya Safiyyah Basudaniyyah, cikin wata irin kulawa irin ta UWA da duk wata kyautatawa da uwa ke wa danta. Ammi Safiyya is more than a mother a gare ta, she is an ANGEL wadda Allah ya halicce ta a hannunta domin ta zame mata kafadar da za ta kwanta a kai ta yi kuka, ko dariya.
Yawan kyautatawar Ammi, jin kai da kulawarta gare ta ke hana ta yi mata titsiyen da Ammin ba ta so na ita wace ce uwarta, wane ne ubanta??? In tana son ganin bacin ran Ammi, to ta yi mata wadannan tambayoyin. Don haka ta dade da daina yi mata tun kafin ta kawo munzalin adolscence. Ta yarda da abin da Ammin ke gaya mata kullum, ITA CE UWARTA, ITA CE UBANTA amma ta sani watarana na zuwa da dole Ammin za ta yi mata confessing daga inda ta samar da ita tunda ko makaho ya shafa a halitta ya san Ammi balarabiyar usuli haka ba ita ta tsugunna ta haife ta ba.
Kodayake ba'a judging haihuwa da kamanni ko kalar fata, amma ita kam ko daga kalar fata, gashin kai da yanayin kirar jiki za ka san Ammi balarabiya ce, yayin da ita kallo daya za ka yi mata ka tabbatar cikakkiyar bahaushiya ce, jikar Barbushe da Tsimbirbira.
To amma me ta ke nema a iyaye wanda Ammi ba ta yi mata ba? Ta yi mata komai a rayuwa wanda a kullum yake mantar da ita cewa, ba ita ta haife ta ba, sai dai kulafuci irin na dan adam. Musamman akan son tabbatar da legitimacy din ta.
A duk lokacin da wani tunani makamancin haka ya sarke ta, fuskar Ammi da murmushinta na UWA a gare ta take daukowa ta dora a kan idanunta, sai kowanne tunani, da kowacce damuwa da kowanne bacin rai su bace su kama gabansu. A duk lokacin da Uwais ya yi mata kallon nan nasa na tsana da kyama, murmushin Ammi kadai ke gusar da shi komai girmansa.
A yayin da ka ke da uwa irin Ammi a gefe, babu wani bacin rai a rayuwa da ya isa ka yi masa kuka. Fahimah ta kan yawaita fadar hakan a zuciyarta.
Tana wannan tunanin cikinta kuma na ci gaba da kartawa ta ji Uwais ya kashe motar a parking lot na gidan su, sai a lokacin ta ankara sun zo gida. Ya fice ya barta a motar ba tare da ya ce da ita ko uffan ba.
Tana fitowa jiri ya kwashe ta, sai da dafa bango sannan ta iya karasawa zuwa cikin gida. Shi tuni ya jima da shigewa part dinsa. Wanda dole sai ka ratsa ta main parlour zaka isa part din nasa. Ammi bata yarda ta ware shi daga can waje ba, sabida tsantseni na tarbiyyah irin nata.
Ammi da Talatu har suna hada baki wajen tambayarta lokacin da ta shigo wujiga-wujiga da ita.
Fahimah, me ya zaunar da ke a makaranta haka?
A gurguje ta yi musu bayani Mr. Edward ya tsare su kan shirye-shiryen su na fara SSCE, da sassanyar muryar ta wadda ta kara sirancewa sabida yunwa da gajiya, sannan ta durfafi dining-table tana zuba abincin jikinta har rawa yake, kuma da ma tana da ulcer.
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: A bakin get ya tadda Jabir yana jiransa, a motar Uwais za su tafi, in sun dawo ya ajiye shi a gidansa ya juya. Tunda suka hau kan titin da zai kai su Bompai wuta ta dauke wa Uwais saboda fargabar irin tarbar da kuma amsar da zai samu daga Alhaji Umar Dikko. Jabir shi kadai yake zuba hirarsa ga dukkan alamu shi kam bai da sauran matsala a rayuwa, da ya fahimci halin da Uwais ke ciki, sai ya yi dariya ya dafa kafadarsa.
âDaddy is very friendly, kawai za ka sha tambayoyi, in ya ga dama kuma ya ce ka jira auta for 6 years ta gama MBBS dinta. This is for sure na tabbata zai fadi hakan.
Ashe da na tattaro kayana na koma gidansa a Abuja idan yana ganina kullum zai gane ba zan iya jiran ba".
Dariya Jabir ya sake yi, ya ce, Kada ka tsorata da dukkan tambayoyinsa, be brave, be yourself, sannan kada ka boye masa komai ya tambaye ka.
Alhaji Umar Dikko na zaune a luntsumemiyar kujerar sitting room dinsa, da ganinsa ka ga bafillacen usli, furfura ta cika a gashin kansa amma fatar jikinsa sumul ta ke, babu tsufan, sabida samun hutu. Jabir ya yi musu iso suka shiga already ya san da zuwan nasu.
Dukkansu a kasa suka zube suka kwashi gaisuwa, irin ta neman iri, fuska sake yake amsawa har yana tsokanar Uwais ya aka yi ya bari abokinsa ya shiga daga ciki shi yana daga waje har yanzu? This is kafin ya ji gundarin abin da ke tafe da su.
Daddy, kamar yadda ka sani Uwais abokina ne, tun a A.B.U, Daddy abin da ya kawo mu shi ne, ya zo neman amincewarka ya fara neman auren Amrah.
Cikin mamaki Alhaji Umar Dikko ya ce, Amrah? Amrah wacce?
Jabir ya ce, Autar Mama dai Daddy.
Ya tsura wa Uwais ido na 'yan dakikai inda ya hango cikar kamalarsa ko ta ina bai ga makusa ba kamar yadda komai da ke jikinshi ya nuna ba karamin mutum ba ne, ilmi da hatimin nasara sun wadace shi. Sannan ga wani irin sassanyan kyau da ya rasa gane daga kabilar da ya dauko shi. Above all Allah ya yi ma Uwais wani irin kwarjini, ilhama da cikar zati da ya wuce ya nemi alfarma wurin mutum a kasa yi mass.
Amsar da ya so bayarwa sai ta canza kanta ba tare da ya ankara ba, domin da farko so ya yi ya ce su