Showing 6001 words to 9000 words out of 57616 words

Chapter 3 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt

ke tare da ita tun Uwais na karami.
Shaawarta ga son diya mace bai canza ba bayan rasuwar mijinta, sai ma karuwa da ya yi a dalilin rashin miji mai tattali, soyayya, kulawa da nuna kauna wato Grand Khadi Shagari.
A wani dare da kadaici ya yi mata yawa, kuma ta yanke shawarar ci gaba da rayuwa a Nigeria madadin ta koma Sudan saboda aikinta, wani tunani ya fado mata.....
Ita dai ba za ta iya kara yin aure ba, don Uwais baya so, ya fada ya kara, muddin ta kara aure tayiwa Babansa kishiya a bayan ran sa shi Sudan zai koma wajen Kawunsa Shuraim wato Yayanta, wanda ke da da sa'ansa mai suna Mahdi, kuma ko ta yi aure ta san ba haihuwa za ta kara yi ba, don haka ta yanke shawarar dauko ya daga GIDAN MARAYU (Orphanage). Ta hada da Uwais ta rike sun isheta rayuwar duniya, tayi musu raino da tarbiyyah irin wanda take so sannan a karshe ta yi wa kowannen su aure da wuri, su haifa mata jikokin da zasu gina mata extended family mai albarka a kasar mijin ta, Nigeria.


******
"Tsintarta aka yi, a kofar makarantar firamare ta gidan Galadima, tana jaririya sabuwar haihuwa ko wanka ba a yi mata ba, a cikin kwalin taliyar indomie, ko suttura babu a jikinta, babu wata shaida da muka samu a kanta bayan wannan".
Shugabar gidan marayu na Kano wanda ke unguwar Nasarawa ta gaya wa Haj. Safiyya. Ta kara rike yar bakar yarinyar mai kyawun fuska sosai a jikinta, wadda ba ta fi shekaru uku ba. Ta cike duk wasu formalities na daukar Da a gidan marayu ta karbe ta cike da so da kauna.


Tunda suka taho a cikin motar ta babban dan yatsan yarinyar nan yana cikin bakinta tana tsotso, alamu ne na cewa, yarinya ce mai tsananin hakuri. A nan kantinan da ke kallon asibitin Nassarawa ta tsaya ta saya mata sutturun yara masu yawa, sannan suka karaso gida.


Ammi!


Uwais da ke wajen kwallon kwando a kofar gida tare da abokansa ya fada cikin mamaki a lokacin da ya ga ta fito daga mota dauke da yarinya.


Wace ce wannan? Ina kika samo ta
Ya sake tambaya.
Murmushi ta yi masa tare da kamo hannunsa, amma sai ya janye daga gare ta cikin tsoro.
Ammi ina ki ka samo ya?
Ta mika hannu za ta sake kamo hannunsa, ya kara ja da baya.
Haba Uwais! Kanwa ce na samo maka, were living a lonely life, ka ga ka samu abokiyar hira da wasa idan bana nan.
Kai ya shiga girgizawa da sauri da karfi.
Bana so Ammi, bana son ki da wani Da ba ni ba!.
Haushi ya sa ta shige cikin gida ta barshi a wajen.
Talatu ta fito daga kitchen tana wa Ammi barka da zuwa, tare da karbar yarinyar da ke hannunta. Ina muka samo ya? Tubarkallah haka?
Ammi ta ajiye handbag dinta a kan kujera, Kanwa ce na samo wa dan gidanki Talatu, ita ma ya ta ce daga yau.


Bayan wannan har inda yau ke motsi, Talatu ba ta san ina Hajiya Safiyyah ta samo yar ta Fahimah ba. Ta san dai ba sato ta ta yi ba, amma tunda ba ta taba bude baki ta gaya mata ba sai ba ta takura mata da tambaya ba.
Farat daya yarinyar ta shiga ranta, in Ammi na wajen aiki to Fahimah tana hannunta. Suka zage wajen kula da ita su biyu. Suna karba-karba in Ammi ta tafi aiki.
Albashin Ammi da shi suke rayuwa cikin rufin asiri, rayuwarsu very simple, ta wadanda ilmi ya wadata. A wancan lokacin cikin gidajen malamai na sabuwar jami'ar Bayero suke zaune gidan dajami'ar Bayero ta baiwa Ammi. Sabida ya fi wa Ammi saukin zirga-zirga. Acan ta sanya Fahimah a (staff school). Lokacin Uwais ya gama ya shiga sakandire a Musa Iliyasu wadda itama nan kusa dasu take. Grand Khadi Shagari ya bar musu gadon tankareren gidan da suke ciki a halin yanzu wanda suka dawo cikin sa bayan Fahimah ta fara karatun sakandire a 'Yan Dutse College, ya bar musu gidan wanda ke unguwar 'Yankaba da tsabar kudi a banki, wanda Ammi ta sayi hanun jari da su a bankuna duk wata suna karbar kamasho. A haka ta dauki nauyin karatun yayanta guda biyu, Uwais da Fahimah!


Cin zalin na duniya da mugunta iri-iri babu irin wanda Uwais bai yi wa Fahimah ba, wadda har gobe bai san a ina Ammi ta samo ta ba. Sai da ya shekara ashirin ne ya gane Ammi a gidan marayu ta dauko Fahimah, don lokaci zuwa lokaci yana kai su gidan marayu ta gaida wata mata wadda ya fahimci shugabar gidan ce.
Ita kanta Fahimah ba ta san hadinta da Hajiya Asabe ba, da Ammi ke yawan kai ta ta gaishe ta in ta samu lokaci, kuma hankalinta da dan guntun tunanin ta na lokacin bai taba ba ta cewa gidan marayu gidansu ne ba. Ta fi daukar Hajiya Asabe a matsayin kawar Ammi, don in suka hadu suka tsinke da hira har ba sa son rabuwa. Daga baya Hajiya Asabe har gidansu tana zuwa, Ammi na yi mata alheri sosai. Musanman lokacin da ta zo aurar da diyarta ta fari Ammi ce ta dauki nauyin gado da kujeru.


Tun daga lokacin da Uwais ya gane daga inda Ammi ta dauko Fahimah tsanarshi da ita ya karu, ya nunku. Ya tsani ya bude ido ya ganta gabansa, sabida yawan tsawar da yake mata ko hanyar dakinsa ba ta bi. Haka in yana falo ta leko ta ganshi komawa dakinta ta ke ta rufe kofa har sai ya fita.
A haka suka taso, Fahimah na mamakin abin da ya sa ita nata Yayan ya tsane ta, bayan ba haka ta ga sauran yayyen kawayenta na makaranta suna treating dinsu ba.
Duk ranar da uzuri ya sa Ammi ba ta dauko ta a makaranta ba, ta tura shi ya dauko ta sai ta dawo da kumburarriyar fuska, ya mammake ta a motar ko ya rarrankwashe ta. Dalili hakan ya sa Ammi daukar mata direba nata ita kadai lokacin da ta shiga sakandire a Yan Dutse.
Ammi ta yi nasihar, ta yi lallashin a kan Uwais ya karbi Fahimah a matsayin yar uwarsa da Allah ya ba shi, har ta koma ta zuba ido, domin kuwa Uwais kaifi daya ne. Kuma mai gabadaya. Abin nufi; In zai so abu dukkan soyayya yake masa, haka in zai ki shi, muguwar kiyayyah yake masa bata wasa ba. Ya sha gaya wa Ammi shi ba zai taba son wannan tsintacciyar magen da ta kawo musu ba.


Tun yana yaro Allah ya zuba masa baiwar kyau na larabawan ifriqiyyah, wani irin kyau mai sanyaya idanun duk mai kallon sa, ya hore masa kwakwalwar karatu musamman darasin lissafi, don haka ne da ya zo shiga jamia ya zabi ya karanta aikin banki. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a jamiar Ahmadu Bello, inda ya karanci fannin accountancy. Bai dade da kammala karatu ba ya samu aiki da babban bankin Guaranteed Trust (GT Bank) matsayin akawu (Accountant) sabida kyawun takardunsa.
Haka rayuwa ta mika wa wannan family cike da ci gaba da nasarori. Zuwa wannan lokacin Ammi Safiyyah na amsa rank na (Associate Professor) a tsangayar Economics da ta ke koyarwa. Fahimah na ajin karshe a sakandire. Uwais kullum cikin promotion yake daga bankin GT sabida kwazonsa da persevearance. A halin yanzu shine babban manajan Branch din GT da yake kan titin (Bank Road) da ke cikin birnin Kano.
Ya karbi ragamar kula da komai na nauyin gidansu ban da shaanin FAHIMAH. A wurin sa kam Ammi ce kawai dangin ta. Bai taba cewa wani yana da kanwa ba. Koda dangin su na Sudan. Baya bari ma wadanda suka san shi su san da wanzuwar ta tare da mahaifiyar sa. Ya tsaya kamar shine Grand Khadi Shagari, baka taba gane babu mai gida a gidan sabida tsayuwar dakan Uwais akan komai na gidan.


*****
Hajiya Safiyyah ta nisa a hankali lokacin da tunaninta ya zo nan. Ba ta haifi Faheemah ba, amma yadda ta ke jinta a zuciyarta ba maraba da yadda ta ke jin tilon danta Uwais. Abubuwa da yawa suka yi sanadiyyar wannan kauna; halayen Faheemah da matsananciyar biyayyar da ta ke yi mata. Kafin a samu yarinya nitsattsiya cikin yammata dubu irin Fahimah sai an tona. Sai dai daga ita har Fahimar sun kwana da sanin cewa babu wanda Uwais ya tsana a duniya irinta.


A shekarun ta na kuruciya Fahimah ta san Hajiya Safiyyah ba ta haife ta ba, amma in za'a kashe ta, ba ta san ta ya ya aka yi ta zo hannunta ba. Ta budi ido ne kawai ta ganta a gabanta cikin wata irin kulawa wadda mahaifiya ce kadai za ta yi wa dan da ta haifa.


Safiya ce mai tsananin hazo wadda matsanancin sanyin watan Nuwamba ya haifar, ranar ta kasance Litinin, aka ce ko Bature yana tsoron ki, tafe yake cikin motarsa Kia Picanto fara sol sanye cikin bakaken suit na maaikatan bankin GT, a nutse yake tukinsa kamar yadda ya saba misalin karfe bakwai na safe. Daidai lokacin da danja ta tsaida su a shateletalen Beirut Road ya rage gudun motar ya tsaya a gefen wata mota Toyota Camry. Hankalinsa na kan danja cike da kaguwar ta ba su hannu domin hakika ya kusa makara, sai ji ya yi daga gefensa an kira sunansa cikin tu'ajjibi..
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: UWAIS SHAGARI?!


Ya juya a hankali cikin aji irin nasa ya dubi mai kiran nasa, JABEER DIKKO. Ya kira sunan mutumin da yanayi na mamaki. Daidai lokacin da danja ta ba su hannu duk suka gangara gefen titi don su samu damar gaisawa da juna.
A tare suka fito daga motocinsu suka cafke hannun juna, they have been good friends during their university years a jamiar Ahmadu Bello, bayan sun kammala ne Jabir ya samu tafiya kasar Kuwait yin masters dinshi, yayin da shi Uwais ya ci gaba a nan Ahmadu Bello ba su kara haduwa ba kuma sai yau. A gurguje suka yi musayen lambar waya da alkawarin Uwais zai zo gidansa in ya tashi ofis don shi Jabir ya yi aure ba dadewa, a yanzun yana aiki ne da FCMB.


Kamar yadda ya yi alkawari yana tashi daga ofis ya dawo gida ya yi wanka ya sake shiryawa cikin shadda wagambari mai hasken sararin samaniya, inda duk ya gifta sanyin Maison Francis dinsa ke tashi. A falo ya tadda Ammi, Fahimah na murza mata menthol a kafafunta kamar yadda ta ke mata duk dare, kallo daya ya yi mata ya dauke kai, a ransa fadi yake, yarinya kullum kamar ana shafa mata shuni don baki. Ammi ta dube shi affectionately (cike da kauna) ko ita da ta haife shi in ya dau wankan nan kwarjini yake mata. Ta ce,
Sai ina haka? Bayan ga abinci Talatu ta shirya maka?
Ya ce "I'm sorry Ammi, an gayyace ni cin abincin dare, abokina Jabir na Kuwait da na ke ba ki labari yau Allah ya sake hada mu.
Ammi ta ce, A dawo lafiya, a gaishe shi. Ya sa kai ya fita, Fahimah na satar kallonsa ta gefen idonta, kirjinta na wani irin duka.
A karshe ita da Ammi suka ci abincin da ya bari din, suna gamawa ta kwashe komai ta kai kicin ta gyara wajen ta yi wa Ammi sallama cewa tana da karatun da za ta yi, sai ta shige dakinta ta kulle kanta.


“Fahimah Shagari.


Kamar yadda ake kiranta a makaranta, budurwa ce yar kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa. A bana ne za ta kare karatun sakandire. A jerin kyawawan mata ba za ka sanya Faheemah ba domin ba ta da artificial beauty irin na yammatan yanzu, komai nata natural daga kalar fata har gashin kai. Baka ce sidik, fatarta mai sulbi da daukar idanu. Tana da manyan ido mai haske da madaidaicin hanci, gashin kanta kakkarfa na asalin Hausawa wanda ba ta taba yi wa relaxing ba sai dai ta yi steaming dinsa. Bakinta dan madaidaici, ba ta a layin dogaye kamar yadda ba ta a layin gajeru, ga ta nan dai yar dagwas da ita, wadda tsafta da wanka suka kama jikinta.


Fahimah ta dauko littafin Food and Nutrition daga jakarta ta makaranta da niyyar karantawa kamar yadda ta yi niyya, don tana da gwaji (test) a kansa a washegari talata. Shine kuma best subject din ta. Amma me? Ko da ta bude shafin farko ba ta ga komai a ciki ba. Shafin ya koma blank, sannan basudaniyar fuskarsa ta maye gurbinsa. Ta bude shafi na biyu don a zatonta a wancan shafin ne kadai Uwais ke yi mata shifcin gizo, sai dai duka sammakal.
Cikin kowanne shafi da ta bude ba ta ganin komai sai Uwais Shagari, fuskarsa, tsayuwarsa, cin maganinsa da maganarsa cikin seriousness. A duniya ba ta taba ganin abin da ke wahalar da ita da dagula mata lissafi ya hana ta jin dadin rayuwarta ko ta ya ya irin tunanin miskilin Yayan nata, wanda bai san tana yi ba, bai san Allah ya yi ruwan tsirarta cikin gidan su ba. Ita din ba komai ba ce face abar wulakantawa, kuma abar kyama a gare shi, to a kan me ta ke yawan ganinsa cikin idonta? Take jin amsa-kuwwar husky voice din sa? Ta ke kuma jinsa har cikin ruhi da tsokar jikinta???
Za ta so a ce tana da wanda za ta iya yi wa wannan tambayar, tsakaninta da kawayenta na makaranta sabgar karatu ce kadai. Ammi kullum na gargadinta a kan tara kawaye da fada musu sirrinta, ta gaya mata ita kadai za ta mayar babbar aminiyarta, komai ta ke son tattaunawa na rayuwarta da ita za ta tattauna shi, amma wannan karon ba ta jin za ta iya gaya mata cewa tana da wani irin feeling a kan Yaya Uwais da ke takura ruhinta wanda ita kanta ta ke neman sani a kansa, ko me za ta ce? Da dai a ce ba Ammin ce ta haife shi ba shi ne za ta iya tattauna wannan alamarin da ita.


A karshe karatun da ta yi niyyar yi bai yiwu ba, haka ta tattara littattafan ta maidasu jakarta.
Ta koma ta kwanta a gadonta ta mike kafafu ta yi filo da hannayenta, ba don babu filon ba sai don ta fi jin dadin kwanciyar ta a haka. Ta bai wa tunanin Uwais dama ya zo ya sha sharafinsa...... yadda ya ke so, ya ci gaba da lugwigwita zuciyarta....
Idanunta a rufe ruf! Amma ba barci ta ke ba, ba ta hango komai sai surar Uwais dazu-dazu da zai fita, yana wadannan harare-hararen nasa, da maganar sa sauri-sauri da husky muryarsa mai huda mata ruhi da zuciya....


******


Tun kafin ya gama parking Jabir da matarsa Murjanatu suka fito tarbarsa. Murjanatu ta sha lullubi a kan kwalliyarta kai daga ganinta ka ga irin mutunci, sannan kuma yar babban gida.
Gidan Jabir Dikko madaidaicin flat ne a unguwar Eastern Bypass. Sun tsara gidansu shi da Murjanatu daidai da rayuwarsu ta yan boko. Ita ma Murjanatu maaikaciyar banki ce, sai dai ita tana Polaris, sun hadu da Jabir tun a jamia duk da yana gabanta sosai, hannun Jabir cikin na Uwais suka shiga kayataccen falon nasu.
Murjanatu ba ta tsaya ba, ta yi ta shige da fice daga kicin zuwa falo don wadata su da dukkan abin da za su bukata wajen cin abincinsu.


Suna tsaka da cin abincin ta fito daga uwardakin Murjanatu tana mika..., ga dukkan alamu ba ta san da mutane a falon ba, sannan daga barci ta tashi. Farar doguwar shimi ce a jikinta mai santsi (armless) kanta ko kallabi babu, ta matse gashin kanta mai tsayi da santsi a tsakiyar kanta. Kai ka ce jarumar nan ta fina-finan Hindi ce wato Sushmita Sen. Ga tsayi ga zati.


Wuta ta daukewa Uwais na dan lokaci, ya nemi zuqar numfashi ya kasa, bai taba ganin kyakkyawan abu da ya keta zuciyar sa irin wannan halitta da ke tsaye gabansa ba. Sannan a lokaci guda idanuwansu suka sarke cikin na juna, chemistry din ya afku a lokaci guda.


Amrah go and cover yourself.


Ta ji muryar yayanta a tsakar kanta, a lokacin ne ta ankara da yanayin sutturar jikinta, da bakon fuskar da ke falon wanda ta zama lost a cikin kallonsa. Da sauri ta juya ta shige daki, Uwais ya bi ta da ragaitattun idanunsa.


Tunda yake a rayuwarsa bai taba jin yana son mace da dukkan zuciyarsa da ruhi irin yau ba. Yes, ya yi dating iri-iri a makaranta amma bai taba jin abin har zuciyarsa ba. Yawanci ma matan ke fara kawo kansu. Yau kuwa ji ya ke ba shi da sauran buri a rayuwa irin na mallakar kyakkyawan abin da ya gani yanzun nan.


Jabir na ta yi masa hira, sai ya lura Uwais absent - mindedly yake sauraronsa. Ya dan doki kafadarsa,


Kai tunanin me ka ke haka ina ta magana ba ka jina?
Suka ci gaba da cin abincin su, amma Uwais bai kara nutsuwa ba. Sannan dandanon abincin bai kara hawa kansa ba duk da kwarewar da Murjanatu ta nuna wajen sarrafa shi.
Sai da Jabir ya rako shi zai tafi ne ya tambaye shi game da yarinyar da ya gani dazu, Jabir ya ce,
Wai Amrah? Kanwata ce uwa daya uba daya, ta zo mana hutu ne, a Malaysia ta ke karatu.
Duk miskilancin Uwais yau ya kasa sarrafa kansa.
Ya ce, To Jabir, ko in shigo daga ciki ne?
Dariya Jabir ya yi sosai ya ce, Ta yi kankanta da aure a gidan mu. Yanzu ne ta ke shekarar farko a karatunta na medicine, Daddy ya fi so ta kammala MBBS ma kafin ya yi mata aure.
Uwais ya marairaice wa Jabir, Ni dai don Allah ka shige min gaba, ka gabatar da ni ga Daddy, sai da izininsa zan fara nemanta. Wallahi na yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login