Showing 54001 words to 57000 words out of 57616 words

Chapter 19 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt

of you... this luscious lipsâ€? I’m gonna miss themâ€?.
Fahimah ta janye fuskarta daga tafukansa cikin tsananin damuwa, sannan ta kwantar da kai a kafadunsa sai ga hawaye suna zuba tarara! Wata uku! Babu Uwais! Na nufin komai a gare ta....,
Uwais ya sanya dan yatsar sa ya lakato hawayen ya ce, “Better, bayan muna gari daya ma kin biye wa Ammi kun sanya ni a kwandon shara, shi ne yanzu ki ke wani kuka, how dare you want me to believe you cewa hawayen a kan tafiyata ne???â€?
Fahimah ta ce, “Yaya Uwais ba za ka gane ba. I love you so muchâ€?!â€? Ta sake kankame shi tana kuka.
Amrah ta sha gaya masa wannan kalmar, amma yau da Fahimah ta fada wani madaukakin farin ciki ne ya lullube shi, wani excitement ya bakunce shi, ya yi mata kyakkyawan muhalli a cikin physique kirjinsa yana shafa kwantaccen gashin kanta. Sun dauki lokaci mai tsawo a haka kafin Uwais ya dago fuskar Fahimah cikin tafukansa, ya soma magana cikin taushin murya.


“I’m sorry for all the past inconveniences, I’m sorry for the rest of our lives. Fahhimah I hurt you so much cikin ajizanci irin na dan Adam. Da Ubangiji ya tashi hukunta ni sai ya hukunta ni ta hanyar sanya min sonki da kaunarki lokaci daya. Ba tareda na shiryawa hakan ba.


Today .... i must confess......ban sani ba ko in na tafi bazan dawo ba, I want to use this medium to tell you aloud that I LOVE YOU very-very much�!!!�
Suman wucin gadi Fahimah ta yi a tsaye, Allah ya so ta jikin Uwais ya yi mata garkuwa, ba don haka ba sulalewa za ta yi a kasa ta narke domin farin cikin is over-estimated.


Cikin yanayin da Uwais da Fahimah suka kasance kenan na lokaci mai tsawo ba tare da sun ankara da tafiyar lokaci ba, sai kiran assalatu suka ji a tsakar kansu. Dole tare suka yi sallar asuba bayan sun yi wanka. Sannan ne Uwais ya yi haramar tafiya amma ko ya tafi idan ya je bakin kofa sai ya dawo, kamar ba za su rabu ba, ganin watanni uku suke tamkar shekaru uku.
Sai da alarm din gefen gadon Fahimah ya buga karfe bakwai na safe sannan Uwais ya iya tafiya.
A wannan yanayi Fahimah ba ta yi barci ba, ta karar da ranar wajen addu’a ga Uwais da nema masa sa’a a wannan tafiya tashi da nema masa albarka a cikin nemansa.
Ko da Uwais ya shiga jirgi kafin su tashi, sai da ya fara kiran Fahimah. Da ta dauka muryarta rawa ta ke da alama ta ci kuka ta koshi.


“Yaya Uwais kun tashi?â€?


Ya ce, “Are you crying Fahhimah? Me ya sa ki kuka?â€?
Ta share hawayen ta ja hanci, sannan ta ce, “Gani nake kamar in ka tafi ba za ka dawo ba as you saidâ€?.
Ya canza positon na rikon wayarsa, ya ce, “Fah-himah, in kin ga ban dawo gareki ba, to na mutu acan, wanda bana fatan hakan yanzu. I would like to cuddle your black beauty babies in my arms..…â€?.
Wani hawayen ya zo wa Fahimah, amma this time around na farin ciki ne.
“Yaya Uwais kana son ‘ya’yana? Idan suka yi baki kamar ni fa?â€?
Uwais ya ji duk ya muzanta, nadama ta kara lullube shi, shi ya sa ba a son gorin halitta don ba ka san me gobe za ta haifar ba.


Muryarshi ta yi rauni kwarai a sanda yake cewa,
“Dan Adam ya kasance ajizi mai yawan kuskure, kuma Uwais yana cikin su. I’m sorry Fahima for the past weird experiences which are all regretful.
Yau kin sa na yi nadama irin wadda ban taba yi ba. Fahimah ‘ya’yanki, jikokin Ammi ne, sabida ‘yar ta ce wadda haifa ne kawai ba ta yi ba ta haifo su, sannan sun fito daga jikin Uwaisâ€? with all these .... and much more....zan so su fiye da yadda nake son kaina!â€?.


Hawayen Fahimah suka ninka na baya, farin cikin ya ninka na baya ta ce, “Ya Uwais na yafe maka, na kara yafe maka, ni da ma kullum uzuri nake yi maka. Is not easy da ma a so ‘ya’ya kamana sai ga exceptional mutane irin su Ammi, wadanda su kuma tsiraru ne a cikin al’ummah.
Ban taba rike ka ba ko da sau daya a zuciyata sabida an ce so hana ganin laifi, and I blindly love you at the time, fatana kawai shi ne ni ma ka so ni ko da rabin-rabin yadda nake sonka�.
“And you got it Fah-himah, halayenki sun sayo miki soyayya fiye da wadda ki ke kintace. Also bazan gaji da cewa ba you are a darling (ke abar so ce) da duk namijin da Allah ya yi wa baiwar samunta, hakika ya ba shi rabin addininsa.
Ya yi masa boyayyen gata irin wanda kudinsa da zabensa ko mulkin sa bai isa ya ba shi ba.
Ba ni da abin da zan ce wa Ammi a yanzu, sai dai in dauwama ina roka mata aljanna ita da mahaifina�.
A lokacin aka soma shela cikin jirgi cewa a daura belt jirgi zai tashi hakanan. Haka Uwais ya yi sallama da Fahimah jiki a sanyaye don har zuwa lokacin Fahimah ba ta daina kuka ba.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ta turo baki gaba, ta ce, “Kawai zan yi kewar Ammi neâ€?.
Ya ce, “Uwais fah?â€?
Ta kyabe baki, “Ko kadan ba zan yi baâ€?..â€?
Dariya ya yi ya ce, “Ohk, Amrah, is waiting, I’m leaving now, amma ki sani kina gab da tarewa a gidan ki da zarar Ammi ta dawoâ€?.
Ya mike bayan ya bata kyakkyawar sumba a goshi.
“Kin ce ba za ki yi kewata ba, ni kuma I will undoubtedly miss EVERYTHING da ke faruwa ko ya faru tsakanin mu in these few days... in na ce komai ina nufin KOMAI.... especially our Dambe, our first night, our Lagos life, our Sudan life, and our past inconveniences. I will still NOT say I love you sai ranar da na samu kyakkyawar sumba daga gare ki, sai ranar da ki ka tare a dakin ki, ki ka karbi girkin ki. In hakan ta faru na fi kowa sa’ar zuwa duniya.
I remain loyal to my mother, thankful and prayerful to her da ta mallaka min ke Fahhimah…â€?


Fahimah ta runtse idonta, kalaman Uwais na ratsa ta, suna gasa kowacce gaba ta jikinta tamkar a cikin oven. Amma kunya ta sa ba ta ce masa komai ba. Ya sake sumbatar goshinta, sannan karan hancinta, ya ja tunga a lips dinta, ganin zai zarme ga wayar shi na ta tsuwwa alamun matar shi ta gaji da jira, sai ta janye kadan.
“Please goâ€?..â€?. Ta fada cikin karfin hali irin nata.
“Korata ki ke yi Fah-himah?â€?
“Ba girkina ba ne, babu kyauâ€?.
“Ai ba a raba girkin baâ€?.
“Ni dai don Allah ka tafi Ya Uwaisâ€?. Ta fada da iyakacin courage din ta. Cikin shagwabar da ta kara tunzuro Uwais ya kasa tafiyar, sai kallonta cikin tsananin bege.
Wayar shi ta kara daukar ringing da tune na musamman da ya sanya wa Amrah. Dole ya juya ya tafi a sanyaye, don Fahimah ta juya da sassarfa shige dakin ta.


Tana shiga dakin ta rufe kofarta, ta jingina da jikin kofar tana maida ajiyar zuciya mai nauyi. Ta san barci yau zai yi wuya a gare ta, amma ta sa a ranta gara ma ta saba, Amrah ma na da hakki a kansa, kishi ba nata ba ne ita matar shige, don ta samu Allah ya kankaro mata 'yar darajar da mafarkin ta bai taba bata ba, bai kamata ta yi butulci ba.


Amrah ta cika fam, ta yi fushin har ta gaji. Lokacin da Uwais ya iso gidan Murjanatu, suna gaisawa shi da Aunty Murja a falo. Aunty Murja ta ce ta dauko jakarta su tafi, sai kumburi ta ke haka ta dauko jakar ta bi bayansa.
A cikin motar ya yi mata side hug sannan ya ba ta hakurin rashin zuwansa da wuri. Ta ce ita ba ta hakura ba, sai ya gaya mata inda ya je.
Ya maida hankalinsa ga tukin motar, “Amrah ki yarda da ni ba inda na je, ina gidaâ€?.
Ta san ba zai mata karya ba, don haka ta bar zancen.
“Me za ki ci mu tsaya mu saya kafin mu karasa gida? Bana son sake fitowa in na shiga, don a gajiye nake".
Amrah ta yamutse kyakkyawar fuskarta ta ce, “Ai ni yanzu ba komai nake iya ci ba Habiby, sai abu mai dan yaji-yaji, mu biya Chicken Republic ina son spicy chicken din suâ€?.
Ya bi umarninta.


Suna zuwa gida ta zuro kafar ta daya waje tana kokarin fitowa daga motar, sai ta juyo ta ce da shi,
“To amma fa Habib Qalby, ba za mu hada daki ba, wallahi ko kadan yanzu bana son turaren kaâ€?.
Cikin mamaki yake dubanta baki a sake.
“Amrah lafiyarki kalau kuwa?â€?
“Sumul kalau nakeâ€?.
“To kam, ai sai dai in canza kayan, amma abin da ki ke fadi ke ma kin san ba mai yiyuwa ba neâ€?.
Amrah kamar ta saka kuka, ta ce, “Wallahi ko ka cire ba ka daina kamshin (Maison Francis)â€?.


Ya ce, “Ai kuwa sai dai a yi wacce za a yi, amma ban da wannan yarenâ€?.




Sun yi shirin kwanciya, zullumi da damuwa duk sun ishi Amrah, ba da wasa ta ke ba turarensa hawa kanta yake, a baya babu kamshin da ta ke so irin na Uwais amma banda yanzu.
Uwais na sanya tafukansa a bayan wuyanta ya hada goshinsu zai lallashe ta don ya ji actual abin da ke damunta ta ke ta wannan yamutse-yamutsen fuskar. Ai kuwa ta kelayo masa wani uban amai, mai karni. Ya yi maza ya ja baya ita kuma ta ci gaba da amayar da spicy chicken din da ta ci tas! Sai da ta amayar da ita.
A daren ya ce su tafi asibiti, ita kuma ta dage ba ta zuwa ko’ina. Ai ta gaya masa turarensa ne ba ta so ya ki jin magana. Ya ki ya bar mata dakin.


Washegari sai da ya yi mata jan ido sannan ta yarda suka tafi asibitin standard. Awo na fitsari a tashin farko ya nuna ciki na watanni uku.
Tunda suka dauko hanyar dawowa Amrah ke kuka, kuka kashirban. Kamar ba ita bace a baya ta ce ta yi surrender ba. Bata taba tsammatarwa kanta ciki a wannan lokacin ba. Ta rantse ba ta shirya wa haihuwa yanzu ba, karatunta zai salwanta. Uwais sabida tsananin bacin rai ga kalaman Amrah a kan kyautar da Allah ya yi masa cewa ya yi,


“Wallahi in ki ka zubda cikin nan da gangan, to a bakin aurenkiâ€?.


Amrah ta zaro ido tana kallon Uwais, kallon mamaki da tsoro, ina soyayyar da yake ikirarin yana yi mata? Yanzu har ya fi son dan da zai haifa a kanta? Da ma Daddy ya ce soyayya karya ce, ka yi aure kawai don bukatarka ta dan Adam da cika sunnar Annabi, amma ba don soyayya ba, sabida it never exist in nowadays men, even if it exists da zarar sun gano wata za ta yi fading. Shin Daddy da gaske yake? Ko dai Uwais ya gano watan ne shi ya sa komai nata ke fading a idanunsa??? Ba za ta yi mamakin kowacce barazana daga gare shi ba, don ya nuna yana son cikinsa. Amma barazana da igiyar aurenta abin ya ba ta mamaki da tsoro sosai, ya kuma kara sagar mata da gwiwa akan canje-canjen data ta gani daga gare shi.


Tunda suka dawo kuwa ta raba daki da shi, shi ma bai kara takura mata ba. Yanzu lallabawa zai yi ta haife masa dansa ko ‘yarsa lafiya ya daina neman komai a wurinta. All thanks to AMMI yana da precious gem dinsa a gefe, a virtous wife who her priçe is far above rubies wadda sai yadda ya ga damar sarrafa ta (naïve and innocent FAH-HIMAH SHAGARI). Yau da bai san ina zai sa kansa ba da wannan takunkumin na Amrah.
Wuni guda Amrah ba ta kulla komai a gidan ba, ga shi duk ya yi kura, kasancewar an kwana biyu ba'a ciki, tunda suka zo sai abincin sayarwa yake ta faman sayo musu. Har ya fara gajiya da daukan mota yana fita yana dawowa.


Ita da kanta dattin gidan ya ishe ta, ta fito ta same shi a falo yana kallon ball da kungiyar da yake so Arsenal, yana shan wankakken inabi da ke kan tebirin gabansa. Daga can nesa da shi ta tsaya tana toshe hanci.
“Habiby, ina wannan yarinyar ta gidanku?â€?
Ya kalle ta cikin takaicin yadda ta ke toshe masa hanci kamar wani mushe, ya ce,
"Wace yarinya? Mu gidanmu da yarinya ne?�
Ta ce, “Wannan budurwar nake nufi, baka, mai kyau haka, mai jan class din nanâ€?.


Gaban Uwais ne ya bada wani irin damm! Ya bude ido kawai yana kallon ta.
Ta ce, “Don Allah don Annabi ka je ka dauko min ita ta taimaka min in kintsa gidan nan, ta yi min miya ko ta sati daya ce in sa a firji don wallahi ba ni son warin albasaâ€?.
Uwais ji ya yi tamkar Amrah ta yi masa gafara, zaman nan da ya yi yana shan inab tunaninta yake yi, ba ya son Amrah ta samu wani clue ne kasancewar Fahimah matar sa a yanzu, musamman cikin halin nan da ta ke ciki komai zai iya faruwa.
Ya yi niyyar gaya mata gaskiya tun kafin ya baro gidan Ammi, amma sai ga bayyanar maganar cikin, don haka ya fasa sai cikinta ya yi kwari. Ta yadda ko me ye zai biyo baya ba zai shafi lafiyar babynsa ba. Amma anya Fahimah za ta yarda ta zo gidansa?
Kuma in ya yi hakan ya yi wa Ammi da ita kanta Fahimar daidai duk da Amrah taimako ta nema?
Amma Amrah ta kafa naci, ta kasa ta tsare ita lallai ya je ya zo mata da mai aikin Ammi. Da ya rasa yadda zai mata bayani, sai ya fiddo wayarsa ya binciko lambar Ammi ta kasar Sudan ya kira.
Wayar na shiga ya mika mata, “Ungo nemi iznin Ammi da kankiâ€?.
Tana karba ta yi sallama, “Salamu alaikum, Ammi ni ce Amrahâ€?.
Ammi ta ce, “Maraba da mutanen Malaysia, ya ya karatun?â€?
“Ammi na samu mid-term break na sati biyu shi ne kawai na taho Kano. Amma Ammi ba ni da lafiya, ba na iya aikin gida da girki, shi ne na roke shi ya dauko min aron yarinyar wajenki kafin ki dawo, lokacin ne nima zan koma makaranta, tunda ita ma cikin kadaici ta ke, sai mu zauna tare ta taimaka mun har ki dawo, sai ya ce wai sai dai in tambaye ki da kaina. Don Allah Ammi a yi min alfarmaâ€?.
Ammi ta yi jimmmm! Kafin ta ce, “Babu laifi, zan masa magana ya dauko ta ya kawo miki, amma ku bari in fara magana da ita tukunna in nemi amincewar ta. Don Fahimah ba wai ta saba da shiga mutane ba neâ€?.
Amrah ta ce, “Ki roka min ita Ammi, ki gaya mata I’m not boring, ba zan dinga damunta ba sam, hira in ba tana so ba ba za mu yi ba, ni ma ba dadi nake ji ba kullum ina daki, sabida warin komai sai in ji shi ba daidai ba…â€?.
Ammi ta yi murmushi, ta ce, “A hankali komai zai dawo daidai, zan lallashi Fahimah ta zauna da ku din har in dawoâ€?.


A zuciyarta kuma addu’a ta yi, Allah ya bai wa Fahimah nata rabon itama cikin gaggawa. Ta rasa dalilinsa na kin gaya wa Amrah gaskiya cewa Fahimah kishiyar ta ce, amma ta san Uwais sarai ta san halayensa, ko me yake yi yana sane, kuma sai ya tabbata yana da hujja.
Kafin ta kira Fahimah sai da ta fara kiran Uwais a lokacin da ta tabbatar yana office. Ta ce,
“Uwais me zai hana ka gaya mata gaskiya in ya so Fahimah ta tare gabadaya su yi zaman mai dalili? Ni bana son abu na rashin gaskiya ko kankani, kada nan gaba ta gane ta ce mun yaudare ta".
Uwais ya ce, “Ammi ki rabu da Amrah kawai, zan gaya mata amma ba yanzu ba, don ba son cikin jikinta ta ke ba. Idan na gaya mata yanzu komai zai iya faruwa.
Za ta iya yin komai don ta huce wanda zai kare ne a kan cikin nan, don hakan sai nan da watanni hudu a gaba zan gaya mata. Lokacin na gama yi wa Fahimah gininta. Ita kuma cikin ya kusa isa haihuwa. Don yanzu na aza harsashin ginin�.
Ammi ta fahimce shi, as she has no option, ta ce, “To Allah ya kade fitina ya hada hankulansu in ka tashi sai ka biya ka tafi mata da Fahimar zan kira ta yanzu in mata bayani".


Fahimah ta fito wanka kenan tana shafa a gaban mudubi kiran Ammi ya shigo mata. Ta mika hannu ta daga da sallama, Ammi ta ce, “Ya ya na ji muryarki so pale? Are you alright?â€?
Fahimah ta ce, “Lafiya nake Ammi, barci ne bai ishe ni baâ€?.
Ammi ta ce, “To ki kwanta zuwa lokacin tashin Uwais zai zo ku tafi gidansa. Amrah ta roke ni kan ba ta da lafiya ki je ku zauna tare kafin na dawo.
Ki sa a ranki Amrah ba kishiya ba ce a gare ki, kanwa ce. Ko babu aure tsakaninki da Uwais in tana cikin lalura hakkinmu ne mu taimaka mata tunda iyayenta ba a gari suke ba�.


Fahimah ta ji kanta ya yi wani irin gingiringim. Idan kuma Uwais ya bada wata kafa da Amrah za ta fahimci something in between a tsakaninsu fa? Tunda daga shi har Ammi ba su shirya bayyana matsayinta ga Amrah ba? A kan dalilinsu da ba za ta ce mene ne shi ba? Amma matsayin Ammi ya wuce ta yi umarni ta saba, ko da bai yi daidai da son ranta ba.
Ammi ba ta yi haka don ta kaskantata ba, sai don ta zamo uwa mai adalci ga kowa (zuciyarta ta tunasar).
Sai kawai ta mike ta hau shiri, tana addu’a a cikin ranta, Allah ya ba ta juriya a zama da Amrah da zata je ta yi, ya rage mata kishinta da ke damun ranta.
Sanda Uwais ya shigo gidan a falo ya tadda ita jingine jikin jakar kayanta da ta hada. Ya tafi gaba-gadi da sassarfa ya yi mata wata kyakkyawar runguma tamkar ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login