Showing 42001 words to 45000 words out of 57616 words
Chapter 15 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
macen da ke sonsa kamarta.
Ba ta tanka masa ba ta dauki kayan da ta ke son canjawa ta yi toilet, ta sanya sannan ta fito duk Uwais na kallon ta. Ya rasa abin da ke damunsa a wannan dan tsukin a kan Fahimah da har ya biyo ta dakin ta again duk da wulakancin da ta yi masa jiya, wanda babu 'ya macen da ta taba yi masa. Alal hakika ji ya yi kawai yana son ganin ta kafin ya kwanta, ya tsokane ta ko âyar kokawar ce ya lakato su yi, it will keep him company tonight.
âFah- himah, ina magana shi ne ki ka yi banza da ni ko?â?
Ya fada cikin rauni, da muryar da Fahimah ta yi tantamar anya ta Uwais ce? Zama ta yi a bakin gado tana kallonsa da idanun mamaki dafe da goshin ta, kafin ta yi wani kasalallen murmushi.
âYaya Uwais ban gane tambayar taka ba ne, protest kamar yaya?â?
âIrin ki dan nuna wa Ammi rashin amincewar ki da auren, tunda kin san ba son ki nake ba, kema kuma na fahimci ba sona kike ba da baki yimin abinda kika yi jiya ba, amma sai ki ka yi shiru, aka kwaci sadaki daga mijin wata ta karfi da yaji aka baki, kuma an ce ki yi aikin sadakin kin kiâ?...â?.
Ya fada yana kallonta kai tsaye cikin idanunta da narkakkun kwayan idanunsa. Wani kallo ne mai nuna tsananin bukatuwar miji zuwa ga matarsa.... wanda Fahimah ba ta san maâanar sa ba.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Daga lokacin da ya taso zuwa lokacin da ya iso gare ta, Fahimah ba ta farga ba. Ta dai tsinci kanta ne a tsaye nannade cikin hannayen Uwais. And he began to kiss her, first softly, sannan gently, kafin ya maida shi a urunce (abruptly), kafin kuma ya dakata yana kallonta kasa-kasa.
âKarya ki ke Fah-himah, kina sona, kina son Yayanki Uwais ba tun yau ba, bakin ki bai fada ba amma zuciya da gangar jikin sun gama confessing, na tabbata son ne kuma ya sa ki ka amince da aurena babu protest.
A bisa hakan ,nake rokon ki da ki yi hakuri da ni, mu yi amfani da son da ke dankare cikin zuciyar ki mu gina kyakkyawar muâamala ta aure. Ki manta da cewa wai bana miki so irin na soyayyah. Babu abin da lokaci ba ya canzawa Fah-himah. Ki bar ni in tabbatar da sunnar da ke tsakanin mu, na yi miki alkawarin ba za ki yi da na sanin ba ni rayuwar ki ba.
Ban yi miki alkawarin SO ba, amma na yi miki alkawarin ADALCIâ?.
Wani haushi ya zo ya tokare Fahimah a kahon zucci, duk da kasalar Uwais da maganganun sa ya saukar mata, amma bacin ran kalamansa na karshe ya sa ta angije shi. Ta juya masa baya tana hawaye.
âYaya Uwais ka fita min a daki, pls, tunda ni da bakina ban furta maka kalmar so ba, don Allah ka daina furtan kiyayya. Babu adalcin da nake bukata daga gare ka duk ka hada ka baiwa matar so. Ina bukatar sarari wallahi, kasa daki na ya min kadan, kana sa min ciwon zuciyaâ?.
Uwais ya zuba hannayen shi duka biyu cikin aljihu yana kallonta da murmushi a siririyar fatar bakinsa.
âThen why are you jeolous? Da matar so da wadda za a karo?â?
Da sauri ta juyo, ba ta san ya karaso bayanta ba don haka kanta ya bigi kirjinsa. Ta sake ja da baya ta ce, âKishi kamar ya ya fa? Ban gane ba? Na ce kar ka yi aure, ko na ce kar ka koma wajen matar ka?â?
âBut you called her MATAR SOâ? in ba kishi ki ke ba don me za ki kira ta da wannan sunan?â?
Fahimah ta gama lura tsab yau Ya Uwais neman magana ya ke ji, ya zo ne musamman don ya yi ta takalar ta, tayi ta hargagi yana murmushin jin dadi, ta fahimci in za su kwana suna yi ba zai gaji ba. Sai kawai ta yi tattaki da baya-da baya ta shige toilet da sauri ta murza key ta barshi a wurin. Uwais ya karaso kofar toilet din ya ce,
âNi ki ka kulle wa kofa Fah-himah? Ai ba sai kin kulle ba na gaya miki tun shigowa ta Iâm not here for what you are thinking. Na zo ne mu fahimci juna, kuma alhmdulillah na gama fahimtar duk abin da nake son fahimta a kan ki.
Ya rage naki ki baiwa zuciyar ki salama da abin da ta ke so, ko ki yi ta zaman jiran tsammanin warabbuka (sai ranar da aka so ki kamar matar so). Ci ba daya ba kuwa, ai koshi bai taba zama dayaâ?.
Fahimah ba ta tanka sa ba, ta san ta shaka masa. A yadda ta ganshin nan da bata tsere ba abinda zai biyo baya Allah kadai ya sani. Ta ganshi ya koma kamar ranar su ta farko a Lagos. Rabar da period ne kadai ya ceceta. Tsoronta daya ne kada ya fita neman matan kan titin kamar yadda yake ikirari, don haka ta yi ta leke ta tagar bandakin ta tabbatar motarsa tana nan bai fita ba. Ta yi ajiyar zuciya ta fito ta rufe dakin ta ciki, sannan ta yi alwallah ta kwanta.
Ta kasa barci, sai tunanin maganganun Uwais dalla-dalla. A zahiri ta gane cewa; their relationship is taking another direction. Ta tuno yadda Uwais yake kissing nata a Ikko da dazu babu kyama, a hakan ma don tana zamewa ta ki sakar masa jiki. It was all sudden changes a tare da shi wadanda bata taba tsammanin za su faru da shi ba cikin dan kankanin lokaci irin haka. Sai dai ta lura shi a karan kansa bai san da wadannan tarin sauyukan a tare da shi ba.
Da ma an ce mahakurci mawadaci, kuma mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romon sa. Idan tafiyar su ta ci gaba a haka, ba ta san iya ina za ta kai su ba, amma dai ko ina ne destination din zai zamanto mai maâana ne.
Me ya kamata ta yi maimakon kwanciya? Ai kawai ta tashi ta gode wa Sarki Allah. Jallah Wa Azza. Wanda cikin mulkinSa da buwayarSa ne yake ta karkato mata da zuciyar Uwais, batare da shi din ya san hakan ce ke faruwa da shi ba. All of a sudden, da ma dai Ammi ta fada, âUwais bai iya rayuwa ba tare da mace ba", kuma ga zahiri tana ta gani.
****
Uwais da Fahimah, washegari a cikin jirgin SUDAN AIRWAYS, wannan karon bai kai ta economy class ba, ya barta a first class seats kusa da shi duk da cewa ya ki sakar mata fuska sabida abinda ta kara yi masa daren jiya. Tun da suka taho yake kumburi, ga wani bakin dark spaces ya maka wa kwayar idonsa, wanda ya boye halin da kwayar idanunsa ke ciki.
Ko abincin da aka ba su a jirgi bai taba ba, duk a cikin fushi ne, fushi yake sadidan da Fahimah, ita kuwa ko a jikinta. Ta ci abincinta ta yi nak! Aka zo aka kwashe kayan, ta soma jin barci, sai ta jingina da kujerar sa barci ya dauke ta.
Ba ta san ya ya aka yi ba, ta farka ne ta ganta kan kafadun Uwais tana barci. Ko ita ta sulmiyo zuwa jikinsa, ko shi ya gyara mata kwanciyar ba ta sani ba. Da asubahi suka sauka a Khartoum babban birnin kasar Sudan kuma garin su Ammi, Mahdi babban dan Baffa Shuraim shi ya zo ya tafi da su zuwa can main house din su Ammi, inda a can ne ake zaman makoki.
Ammi baki ya ki rufo, da ganin yadda Fahimah ta yi mulmul cikin 'yan kwanaki kalilan. Wannan ya tabbatar mata suna cikin kwanciyar hankali fiye da tunaninta. Duk da an yi adduâar bakwai an watse dangin Ammi na nan ba su koma ba, nan ta yi ta gabatar da Fahimah matsayin âyar ta da ta rike tun tana karama kuma matar Uwais. Wasu sun yaba, masu racism din ciki ba su yaba ba, kin san balarabe da kabilanci. Matar Mahdi sai da ta yi gulmar Ammi a bayan idonta ta ce da mijinta Mahdi cikin harshen larabci,
âDuk matan Sudan Ammi Safeeyyah ta rasa wadda za ta aura wa Uwais sai mara asali mara hasken fata?â?
Mahdi ya harareta yace "to ina ruwan ki? Ita ta ga tayi dai-dai da danta, ko ke kika haifa mata shi?"
Da yawa kuma tarin nutsuwar Fahimah da rashin rawar kanta, uwa uba kwarjinin da Ubangiji ya yi mata shi ya burge su zuciyar su ta kaunace ta.
Da daddare Uwais ya shigo yi wa Ammi sallama zai tafi masaukin shi ya kwanta, Mahdi na jiransa a waje cikin motarsa zai sauke shi. Sannan ya wuce nasa gidan. Fahimah na gefen Ammi tana cin abincin dare sanda Uwais ya shigo. Kallo daya ta yi masa ta dauke kai, shi ma ya yi kamar bai ganta ba, amma gani ta yi har duhu ya dan yi sabida gajiyar da ke tare da shi.
âAmmi fi-amanallah zan je na kwantaâ?.
Ammi ta ce, âAllah ya huta gajiya, a ina ku ka sauke shi Mahdi?â?
Mahdi ya ce, âNan gidan saukar bakin Abbu na gyara masa daki, amma shi ya ce ya fi son Fundaq (hotel)â?.
Ammi ta dubi Fahimah da ta kasa ci gaba da cin abincin ta ce, âSai ki tashi ku tafi, ni ba zan kwana gado daya da ke ba, hauri ki ke yi da wadannan dogayen kafafun naki in kina barciâ?.
Fahimah ta zaro ido tana kallon Ammi. Uwais bai ce komai ba ya juya ya fita, yanzu sai ta tsallake kowa da ke cikin gidan nan ta bi Uwais zuwa masauki? Ta bude baki za ta yi magana, Ammi ta jefa mata mayafin ta ce,
âDo as I saidâ?.
Tana kunkuni hadi da turo baki gaba ta mike, âDuk mutanen gidan nan Ammi?â?
Ammi ta ce, âSu ba a dakin mazan su suke ba? Bari mu koma gida da ni ki ke zancen, wallahi tarewa za ki yi ko kuma ya dawo da matarsa, ba zan dauki rainin hankali ba, ku zo ku sa ni a tsakiya ina dalili ni ba tsohuwar banza ba?â?
Tuni Fahimah ta kai kofa, ga uban horn da Uwais ke antayo mata don ya tsani jira a rayuwarsa.
Suna kan hanya shi da Mahdi da ke tukin mota suna gaba, ita kadai tana gidan baya. Uwais ya yi kwafa sannan ya yi magana da hausar da ya san Mahdi bai ji.
âDa ma kin dage kin ki biyo ni, aâa ke komai sai ki yi shiru ke ga sarkin biyayya wa Ammi, in kin biyo ni amfanin me kike amfana min? To ni zama da ni DEAL ne kin sani, gara ma ki rufa wa kanki asiri ki bi Mahdi ku komaâ?.
Fahimah ba ta tanka shi ba. Daidai lokacin da Mahdi ya shigar da mota hotel din, shi ya je ya yi musu komai, sannan suka haura dakinsu ta elavator.
Suna shiga dakin wanka ta shiga ta fara yi sabida tunda suka iso ba ta yi ba, jikinta har danko-danko yake mata, sanda ta fito Uwais na kishingide cikin kujera ya yi rub-da-ciki yana waya. Daga yadda yake magana kasa-kasa da tausasa murya ta fahimci shi da matarsa ne. Sun gama fadan kuma sun shirya.
Maganganun da ta ji ana yi cikin wayar sun girmi kwakwalwarta, don haka ta ga gara ta fita ta ba su fili kafin ta samu heart attack. Uwais har da gayya yake fadin,
âZan iya hakuri mana Amrah? Amma na kwana arbaâin, daga nan duk âyar akwalar da na samu zan yi maneji da ita, da yardar ki ko babu, kada ki ga laifina in ki ka dawo ki ka same ni da sabon aureâ¦â?.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Murjanatu ta ce, "Ki yi wa mijinki kyakkyawan zato Amrah, Uwais mutumin kirki ne a fili da boye as far as i know, bana zarginsa da wannan. Amma lallai ne Amrah in kina son aurenki ya dore, kuma martabarki ta dore a idon Uwais to ki sake shawara a kan karatun ki. Tunda ya fito fili ya nuna miki ba zai iya hakuri ba, bana jiye miki matan waje don Uwais ba irin nasu bane. Amma ina jiye miki kishiya da kuruciyar kiâ¦â?.
Gaban Amrah ya yi balaâin yankewa ya fadi da kalaman Murjanatu na karshe, wani abu da ba za ta taba iya yarda da shi ba (tarayya da wata a kan Uwais), gara mata ranar mutuwar ta da ganin wannan ranar.
Amrah ta dubi Antin ta Murja cikin karaya, ta ce, âAunty Murja, ba ni ce abun ji ba, Daddy ne, kuma dai kin san yadda karatun likita yake a kasar nan sai ka yi shekaru goma ma ba su sallame ka ba, sannan gaskiyar magana Uwais yana da takura, mayata har da hayyata. Tafiyata na dan lokaci ba ki ji hutawar da na yi ba da sararawar da na yi. Sannan ni ba zan iya karatu a Kano ba, gaskiya na riga na saba da Malaysiaâ?.
Aunty Murja ta ce, âTo Bamaleshiya, haifaffar Malay, sai kuwa ki baiwa Uwais dama ya yi aure shi ne kadai mafita ga matsalolin kuâ?.
Amrah ta kankance ido tana duban Murjanatu, ta ce,
"Over my dead body!".
Murjanatu ta ce, "Ki daina fadin haka kada ki fada da bakin Mala'iku Amrah, kuma ki mutun, a zo a yi, gara ma a yi kina rayen, kowacce ta murza kambunta, in ya so wadda ta fi son mijin ta kwace, don ina tantamar soyayyar ki ga Uwais idan ba ta fi cikin cokali ba. Ki yarda kin fi muhimmanta karatu da aure Amrah. Sannan kina son kan ki da yawa, kuma irin ku masu gudun kishiya an fi yi muku wallahi".
Maganganun Murja sun ki yi mata dadi ko kankami, domin Murjanatu irin mutanen nan ne masu tsage gaskiya komai dacinta. Don haka Amrah ta tashi ta bar mata falon tana kunkuni, cikin kunkunin fadin ta ke,
"Aunty Murja ba ta sonta, tunda ta ke mata fatan kishiya".
Murjanatu ta bi ta da kallo cike da tausayinta, ta san upbringing na gidansu shi ne babban abinda yake wahalar da ita, ita ma haka ta sha wahala da Jabeer don shi cewa ya yi ko haihuwa ba za su fara ba sai sun yi shekara goma da aure. So many challenges ta fuskance su a kan Jabeer irin na Amrah a kan tsananin bokon su. Farkon aurensu ko sallar asubah sai ya gama shirin ofis yake yinta don kada ya makara ofis. Sai da ta dage wajen kyautatawa da lallashi cikin hikima ya koma yarda ta tada shi sallar asubah. Amma har yanzu in yana wasu abubuwan za ka fahimci sun fi bai wa boko muhimmanci a kan addini.
Tana tausaya wa Amrah, musamman da ta fahimci weakness din mijinta, kwace mata shi daga wajen sauran mata na ciki ko na waje ba zai zamo abu mai wahala ba. Wai Hausawa suka ce kwace goruba a hannun kuturu ba wahala......
****
KHARTOUM
Ammi ce ta kira wayar Uwais ganin shiru-shiru har azahar ba su ba alamar su a main house. Ga shi Mahdi ya ce mata Fahimah ce ba ta jin dadi, don haka hankalinta ya ki kwanciya sam. Uwais na dagawa, ta ce, "Ya ya jikin Fahimah? Ko dai a kawo ni mu je asibiti?"
Uwais ya shafo lallausar sumar kansa cikin jin nauyi, ya ce, "Ammi ta wartsake fah, wanka ma ta ke yi yanzun, muna nan tafe zuwa karfe hudu".
Ammi ta ce, "To alhamdu lillah, abinci fa?"
Uwais ya ce, "Kada ki damu Ammi na yi order a nan an kawo mana tun dazun".
Hawayen farin ciki suka cicciko a idon Ammi, don ta gama gane ciwon na Fahimah ta ce, "Allah ya yi muku albarka Uwais, Allah ya jikan mahaifinka, yadda ka yi min biyayya Allah ya ba ka masu yi maka, yadda ka faranta min kai ma Allah ya faranta maka".
Tunda yake da Ammi ba ta taba yi masa addu'ar da ya ji dadi, kuma mai tsayi kamar wannan ba. Ko don ya ci gaba da samun wannan tofin albarkar ya yi alkawarin rike auren Fahimah da amana da hannaye bibbiyu. A ransa fadi ya ke, "Ammi ai gata ki ka yi mun, you gave me a precious gem, wanda ba zan gushe ba ina nema miki rahmar Ubangiji da gafarar sa a kansa.
Fahimah ta fito daga toilet, ta yi wanka amma ta dauko kayan da ta tube ta maka, kasancewar ta manta bata shiga da wadanda za ta canza ba, kuma ba za ta iya fitowa daure da tawul a gaban Uwais ba. Ya daga lumsassun idanunsa yana kallonta, her radiant black skin sai wani sheki ta ke kamar ta matan kasar Ghana, ta wani fannin kuma Somalis. Ta fiddo doguwar riga ruwan makuba kirar Dammam daga cikin kayan ta za ta saka, ba ta san lokacin da Uwais ya taso ya iso gabanta ba.
Fuskarta da ruwa bai iya zama sosai sabida santsinta ya dan shafo, sannan ya hau kici-kicin cire mata rigar da ta mako.
"Ya Uwais lafiya?"
Ta fada cikin kidima, don yanzu Uwais ya zame mata dodo. Yesterday night will forever remain fresh in her memory kuma bazata gushe ba tana tuno komai da ya wakana cikin daren ba a duk lokacin da Uwais ya kusance ta.
Cikin kokarin kwantar mata da hankali da rage mata karfin tsoron da ya gani cikin idanun ta a kansa ya tausasa murya ya ce.
"Nothing as you expect, daga nan har dare kina da hutu, kawai kayan zan canza miki da kaina don ki sani yanzu ke da Uwais, babu sauran shamaki, ki daina wannan nukunukun na canza kaya a gaba na".
Fahimah ta runtse idanunta a lokacin da Uwais ya fidda rigar jikinta gabadaya ta saman kanta, ya tsura mata idanu yana tazbihi ga mahaliccinsa. Ya juyo ta round sannan