Showing 21001 words to 24000 words out of 57616 words
Chapter 8 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
kai ki makaranta ba, nikuma ba kullum nake shiga Campus ba, tafiyar mu zata saba in kika fara daukar lacca".
Fahimah ta ce "Ammi to waye zai koya mini?" "Ni dai kin san bani da lokaci, tunda an shiga sabon semester, amma zan wa Uwais magana ya dinga koya miki a karshen mako".
Ammi ta kirkiro zancen koyon mota ne don ta samar da kusanci ko yaya tsakanin Uwais da Fahimah don ta ga abin nasu ba mai alamar karewa bane. Kada kuma auren ya lalace a haka.
Lokacin da Ammi ta furta masa wannan umarnin, fuskar Uwais komawa ta yi kamar hadarin da ya nausa yayi gabas. "In koya mata mota fa kika ce Ammi?" "Eh, abinda nace kenan" bai san sanda ya ce "Ammi muharramata ce?" Don shi shaf! Ya mance da wata Fahimah balle auren ta dake kansa.
Ammi dunkule yatsunta tayi ta mika masa "ungo nan (dakuwa). A'ah ba muharramar ka bace, kanwar tsohon ka dake kabari ce".
"Yau sabida Fahimah har Baban shi an zaga". Tashi yayi fuuuu! Ya wuce dakin sa. Abincin ma ya fasa ci. Ammi tana kai shi bango da yawa akan Fahimah yana hakuri ne kawai don UWA ta fi gaban wasa ammma da tuni Fahimah ta dade da komawa orphanage.
Washegari Ammi ta samu waya daga babban dan Kawu Shuraim wato Mahdi, cikin kuka mai tsanani Mahdi yace.
"Allah ya yi wa Abbu rasuwa yau din nan".
"Innalilllahi wainna ilaihi rajioun".
Ammi Safeeyah ta fada tana karawa.
Ashe shiyasa ya dage ya zo ya yi wa Uwais aure? Ashe sallama ce ya yi musu, ashe rabuwar kenan, ashe daga wannan lokacin Uwais yayi rashin Kawun sa mai son sa da kaunar sa... Allahu akbar!
Muryar Ammi kadai ya ji ya tabbatar kuka take yi. Uwais a zaune yake akan kujerar sa amma bai san sanda ya mike tsaye ba makale da wayar a kunnuwan sa, kansa ya kama ya dafe da hannayensa biyu a lokacin da Ammi ta fada masa rasuwar Kawu Shuraim. Babu irin kokarin da bai yi ba don ya samu excuse daga Banki ya bi Ammi Sudan amma bai samu ba, domin already yana daga cikin manyan ma'aikatan GT da zasu halarci seminar ta organization din nasu gabadaya, wadda suke yi duk karshen shekara a babban reshen su da ke jihar Lagos, zasu tafi cikin satinnan kuma an riga an mika sunan sa.
Ammi ta so tafiya da Fahimah, amma ga nata karatun da bai gama nuna ba, kuma tana so ta jima a Khartoum wannan karon kasancewar ta dade bata je ba. Don haka dole ta bar ta a gida.
Da daddare bayan Uwais ya dawo take tambayar sa "yaya ka samu excuse din ne zamu tafi tare ko yaya?" Ya kalli Ammi da tausayin ganin yadda mutuwar dan uwan ta ta buge ta, ta fyadar da ita a wuni guda, Ammi har ramewa ta yi. Idanun ta sun yi jazur sabida kuka. Ya ce a hankali "ban samu ba Ammi, don an tura ni cikin masu tafi seminar a Lagos nan da kwana uku, zan yi kwanaki ukku, sai dai idan na dawo, zan yi matukar kokari na samu adduar bakwai". Ammi ta ce yaushene tafiya Lagos din? Yace jibi Juma'ah, zamu dawo Lahadi don mu samu ofis litinin, sai in yi kokari a bar ni in zo Sudan ko na kwana biyune kacal".
Ammi ta ce "to Yaya za'a yi da Fahimah? Don ni zan yi akalla sati biyu kuma tana zuwa makaranta, ga Talatu bata dawo ba har yau, don haka tunda Juma'ah, Asabar da Lahadi ne ka tafi tare da ita Lagos din, bazan barta ita kadai a gidannan ba.
In kuka dawo ka samu izni daga ofis din sai ku taho Sudan tare ku samu addu'ar bakwai ku dawo tare, tunda dukkan ku kuna da passport na kasar Sudan".
Wani gumi ne ya shiga barkowa Uwais daga kowacce kafa mai tsatstsafar da gumi ta jikin sa. Bai san san da ya kira sunan Ammi da hanzari ba.
"AMMI!"
Tune din muryar kamar na wanda zai fashe da kuka. "Muharrama ta ce da zan tafi da ita wani gari har kwanaki?" Ammi bata san sanda ta kai masa bugu da filon hannun ta ba, ta ce "idan ka sake yi min wannan tambayar ta rainin hankali wai ko Fahimah muharramarka ce sai na sassaba maka kamanni. A'a ba muharramarka bace, karuwa ce nace ka dauka ka tafi da ita.
Kuma ka kula da marainiyar Allah Uwais, cin ta, shan ta da walwalarta. In ka ci amanata kai da Allah".
Uwais ya mike yana rangaji ya bar falon, bakin ciki kamar ya hadiye zuciyar sa. Wai me ke damun Ammi ne? Idan da yana tunanin Dimentia ne yanzu kam ya tabbatar lafiya kalau take, tana matukar son hada rayuwar sa da yarinyar nan, yarinyar data riga tasan ita kadai take son abarta. Ya dauketa ya shiga da ita cikin abokan aikin sa ma ya ce matar sa ce ai ya sayowa kansa raini a wurin ta da wurin su. Wannan matar leburori ce da marassa gata ba irin tashi bace. Shi fa ba abunda bai so ma a duniya irin ganin black fuskarta, balle yasa ta a gefensa yana yawo da ita cikin Nigeria wai har ma da wajen ta (Sudan).
Idan Amrah ta samu labari fa cewa he is with another woman me zata dauke shi? Hakan bai zama yaudara da cin amanar soyayyah ba? Zuciyar sa ta tambaya. Sannan ba tare da bata lokaci ba daya zuciyar ta halarto da amsa...
Bai zama cin amana ba, tunda itama ka biya sadakin ta, matsalar tun farko bai kamata ka boyewa Amrah ba. In har tana son ka zata baka goyon ne baya kayi biyayya ga mahaifiyar ka. Yadda zuciyar sa zata iya jure hada muhalli da Fahimah a bakon wuri inda basu san kowa ba har na tsayin wasu kwanaki shine babbar damuwa a gare shi.
****
Ya cigaba da yiwa Ammi shirin tafiya Sudan a yinin ranar duk da cewa he's frustrated amma bazaka taba ganin hakan akan fuskarsa ba, yana da charisma na boye fushi, ya saya mata tikiti, a lokaci guda yana nashi shirin na tafiya Lagos. Yayi waya da duka 'ya'yan Kawu Shuraim yayi musu ta'aziyyah musamman Mahdi, ya gaya musu uzurin sa na rashin biyo Ammi. A yau da daddare Ammi zata tashi, tun jiya Fahimah ta hada mata kayan da zata bukata a babbar jakar matafiya, bata san me ke faruwa tsakanin Ammi da Uwais akan ta ba.
Karfe shidda na yamma Ammi ta shigo dakin ta, ta zauna dab da ita, sannan tace.
"Fahimah, ban miki bayani ba tun jiya, na bari sai yau da zan tafi, ki hada kayan ki kamar kala shidda, idan na tafi yau, ku kuma gobe da safe zaku tashi zuwa Ikko".
"Ni da wa Ammi.. wa muka sani a Lagos?"
"Ke da mijin ki zaku tafi, ko akwai damuwa ne a cikin hakan?"
Ta yi mata tambayar tana mai tsatstsareta da ido, don kada ta bata damar cewa komai. Fahimah ta ji miyan bakin ta ya kafe, ta fiddo idanuwa kawai zuruuu! Tana kallon Ammi. Wani abu ya shiga kan Ammi da alama. Ammi ta fahimci kallon da take mata sarai don haka tayi murmushi ta ce.
"Kalle ni da kyau ki kara, lafiya ta sumul-kalau, a kullum ina addu'ar Allah ya kawo sanadin da shakuwa ko yaya zata shiga tsakanin ki da Uwais. Wannan nesa-nesan da kuke da juna shi yake bada babbar gudunmuwa wajen nesanta zukatanku da juna.
Na baku lokaci, ban zaci abin naku zai kai haka ba, amma na fahimci in za'a shekara a haka zaku zauna har auren ya lalace. Ban ce lallai sai kun zauna gida daya ba, ni in dai zaku amsa sunan miji da mata ko a gidannan ne kiyi ta zama Fahimah, ki haifa min jikoki masu irin tarbiyyar ki, masu kama da ku, wadanda ni Allah bai bani da yawa ba.
Uwais in dai irin halittar marigayi mahaifin sa gare shi, wallahi bai iya tsallake wannan tarkon dana dana masa. Ina nufin (bai iya yin kwanaki masu yawa babu mace). Don haka wuyar ta ku fahimci juna shike nan ina tabbatar miki komai zai wuce kamar ba'a yi shi ba. Sai tattali da soyayya da zasu biyo baya.
Soyayya zata yi kanta a zukatanku duk da yanzun ma bani da tabbacin kiyayya ce kuke wa juna. In ma kiyayyar ce sai dai daga Uwais amma banda ke Fahimah. Na ga soyayya mai yawa cikin kwarar idanun ki....shiyasa ma na jajirce na hada wannan auren, don idan mace na son namiji, to kuwa tabbas zata yi hakuri da shi duk rintsi, ta rike shi matsayin uban 'ya'yan ta albarkacin wannan so da ta ke masa.
Don haka bisa umarni na Fahimah, tashi ki hada kayan ki ki bi mijin ki zuwa inda duk yasa kafa wajen neman abincin sa. Allah yayi muku albarka".
Fahimah bata ce komai ba, abinda bata son yi agaban Ammi shi ya zo (tears). Ammi da kanta ta shiga zabo mata kayan da ya kamata ta dauka daga cikin na lefen ta da aka dinko. Hatta kayan shafa dana kwalliya duk a acikin na lefen ta ta diba mata, ta hada mata su a matsakaiciyar trolley. Fahimah sai bin ta take da jikakkun ido har ta gama. Ta dube ta tana daga zaune a bakin gado duk jikin ta ya mutu. Ta yi kamar bata gane halin data ke ciki ba na zullumi da anxiousness. "In da abinda kike bukata na amfanin ki sai ki kara, na gaya miki kwana uku zaku yi, kuma in kun dawo da kwana biyu zaku biyo ni Sudan.
Bakin Fahimah sai motsi yake tana so ta tambayi Ammi. "Shin Yaya Uwais ya amince da wannan tsarin nata?" Amma ta kasa furtawa har Ammi ta bar dakin.
Ba abinda ta kara kan kayan da Ammi ta hada mata sai inner wears, sannan ta dauki pad, kasancewar tasan ta kusa yin period.
Ita da Uwais din ne suka raka Ammi airport, karfe takwas na dare, kasancewar boarding flight zata bi. Suna can har karfe goma Uwais na shige da fice da kayan da Ammi zata tafi dasu gun (screening) kafin lokacin tashin su yayi.
Gab da zasu tashi ya iso inda suke zaune itada Fahimah akan kujerun silver, yace.
"Everything is set Ammi, Allah ya kiyaye hanya, safe journey".
Ammi ta daga ido ta dube shi da murmushi, daidai lokacin da aka soma kiran pasinjan Sudan da su shiga jirgi. "Ina fatan kafin in dawo, komai zai zama tarihi Uwais. I mean tsakanin ka da Fahimah. Za ka rungumi auren ka da hannu bubbiyu, ka yarda Fahimah amanar Allah ce a hannun mu Uwais. Idan kana ganin takurawa ce na yi maka kayi hakuri ka bani dama, just give it a try, ni na haifeka Uwais don haka ka yarda bazan cutar da kai ba, komai na yi maka sai dai ya zamo taimako da soyayya.
Kai da kanka watarana zaka zo kana gaya mini WACECE FAHIMAH? Wadanne irin baiwarwaki Allah yayi mata nayi maka wannan alkawarin. Kyal-kyal banza ya daina diban ka. Halin mutum shine abinda yake sawa a so shi ba nasaba ko zubin halitta ba...
Above all this black da kake cewa is but expensive beauty, but only ta BRAVE MEN Uwais......". Ta karasa da murmushi, sannan ta mike tsaye don kowa ya shige ya barta,
"I'm hoping that my son to be among them".
Sannan ta kama hannun Fahimah wadda kanta ke sunkuye tana hawaye, ta sanya cikin tattausan hannun Uwais. Ta dunkule su ta cure wuri guda, sannan ta dauki hand bag dinta ta wuce zuwa terminal.
Ya dade yana kalon bayan Ammi, sannan ya sauke ido akan hannun Fahimah dake dunkule cikin nasa, wadda tunda ta sunkuyar da kai hawaye take zubarwa bata dago ba. Ji take kamar ta bi Ammi, kamar Ammi sallama take musu, kamar in ta tafi ta bar su su kenan bazata dawo ba! Ta barta da miskilallen dan ta a inda bata da kowa. Kalaman Ammi Safeeyah sun luguiguita zuciyarta; wai namiji akewa wannan rokon akan ya so ta ita wace irin mara sa'a ce a rayuwar ta? Ta shiga ittikafin adadin soyayyar da Ammi ke mata....wadda duk itace silar hakan.
Ko don wannan kauna da soyayya na Ammi Safeeyah, ta ci alwashin zama karkashin igiyoyin auren Uwais no matter what, sannan against all odds, ko da zai dinga zaftarar naman jikin ta ne kullum yana sawa a miya saboda kiyayya.
Mu karasa a littafi na 2.
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: A daidai wannan lokacin Amrah na can cikin Aunties dinta ana yi mata kwalliya. Kasa daga kiran ta yi da ta ga sunansa ke yawo a screen din, domin Amrah yarinya ce mai alkunya. Aunty Murjanatu ta ce, Amrah ba kiranki ake bane?"
Aunty Wasila ta ce,
"Maybe angon ne ake jin kunyarmu".
Ita dai ba ta tanka su ba har wayar ta katse. Yau ji ta ke ba wanda ta ke jin nauyi duk duniya irin Uwais. Aunty Wasila ta ce, "Amrah a haka za ki kama mijin? Yo yanzu wa yake kunyar amsa wayar mijinsa a ko ina? Zauna nan kina fulako, matan waje su kwace, wannan mijin naki wanke hannu ka taba".
Duk aka yi dariya har make up artist din dake yi mata kwalliya. Still Amrah ta kasa daga wayar Uwais duk da sai kira yake har sau uku. Daga karshe ya turo text. Shi ma sai da ta saci idon su Aunty Murja sannan ta karanta.
"Finally Mrs. Shagari.
May this moment mark the beginning of the series of our blessings... May Allah's rahma cover us forever. I promised you eternal love Amrah and all the happiness that love can bring... I love you Amrah!"
Uwais Shagari.
Amrah ta yi catching numfashinta a hankali tana satar kallon yayyanta ko da wanda ya gane yadda sakon Uwais ya tafiyar da numfashinta na wucin gadi? Dukkansu hankalinsu ba ya kanta yana kan hirar dinner da za a yi yau da daddare. Ta yi ajiyar zuciya tana tunanin da idanun da za ta iya kara duban Uwais a sabon matsayinsa na miji a gare ta.
Amrah na son Uwais, amma soyayyar Uwais ta fi ta Amrah yawa. Probably za ta iya ci gaba da rayuwarta normally ko babu Uwais ko da akwai shi. Yayin da Uwais zazzafar soyayya yake yi wa Amrah ta yadda rayuwarsa ba za ta taba cika babu Amrah ba.
A can gidan Ammi yau ne wuni, don haka duk abokan arzikin Ammi sun zo, ciki har da Hajiya Asabe shugabar gidan marayu. Hajiya Asabe ta kwance jakarta ta soma fiddo 'yan kulle-kullen da ta zo da su tana yi wa Ammi bayani, kasancewar 'yar Sokoto ce ita, ta ce ita ga gudunmawarta kenan kayan gyaran amarya. Ammi ta karba ne kawai ta yi godiya, amma ta saka a ranta ba za ta bai wa Fahima komai ta ci ba. Matar da hankalin mijin ba ya kanta sam-sam za'a bai wa maganin mata ya sa ta ciwon mara a banza.
Fahimah ba ta san ta zama matar Uwais ba, da halin da ta samu kanta a ciki yau, da jin cewa bikin Uwais ake yi da ba ta shige shi ba.
Daga ita sai ubangijinta suka san cewa tana gab da zarewa. Wani dan karamin zaucewa ne ya same ta a daki sai safa da marwa ta ke a cikin dakinta tana magana ita kadai.
"Yaya Uwais ya yi aure, zai tafi ya barmu... Matarsa mai sa'a ce... Ni ba ni da sa'a... Sai koshin wahala. In ya tafi gidansa shi ke nan na daina ganinsa... Ganinsa kawai is a blessing because it heals... Allah ka ba ni juriya, Allah ka ba ni dangana. Allah ka fahimtar da zuciyata ta daina son abin da ba za ta taba samu ba...".
Sai ji ta yi ana bubbuga mata kofa da karfi. Muryar Ammi ce ke kiran sunanta, "Fahimah! Fahimah! Fito ku yi sallama da su Kawu Shuraim za su tashi yanzu zuwa Sudan".
Ta soma kokarin regaining consciousness dinta don tabbas Ammi ta ganta a wannan halin ba abin da zai hana ta gano ta... Ta zama zararriya a kan dan ta Uwais, kishinsa na neman hallaka ta.
Toilet ta fada da gudu ta wanke fuskarta da sabulu ta sanya hijab sannan ta fito, ta bi bayan Ammi zuwa falo. Duka kawunnin Uwais suka bi ta da kallo har ta samu gefen Ammi ta zauna. Ta gaishe su, muryarta ba ta fita sosai sabida kukan da ta ci. Baffa Haruna ya hau yi mata nasihar da ba ta san dalilinta ba, yana fadin ta zauna lafiya da abokiyar zamanta su ba wa mijinsu hadin kan da zai iya adalci a tsakaninsu. Ta dauki kishiyarta 'yar uwa ba kishiya ba, ta rike girmanta da Allah ya ba ta.
Fahimah dai ba ta dago ba har zuwa lokacin da Kawu Shuraim ya ce, "Ki yi hakuri da dan uwanki Uwais, kin san ba da son ransa aka yi aurenku ba. Wannan burin na mahaifiyarsa ne, don haka tabbas sai kin yi hakuri Fahimah a zamanki tare da Uwais. Don Uwais wani baudadden mutum ne wanda idan aka yi gabas shi sai ya yi yamma, in aka yi kudu shi sai ya yi arewa. Hakurin shi ne kadai maslaha har zuwa sanda Allah zai daidaita ku, don haka ba za mu gaji da cewa ki yi hakuri ba kin ji ko Fahimah?"
A hankali Fahimah ta dago rinannun idanunta ta sauke a kan Ammi Safeeyyah. So ta ke ta tantance ma'anar kalaman da ke fita daga bakunan kawunnan Uwais, shin ko idanun Ammi za su ba ta assurance na abin da dattijan nan ke cewa? A zahiri cikinsu babu sa'anta, babu abokin wasanta balle ta yi zaton wasa ne irin na kaka da jika suke yi mata.
Ammi ta gyada mata kai a hankali tana murmushi da ba ta tabbaci daga fararen kwayan idanunta.
"Uwargidan Uwais!".
In ji Ammi tana mai sanya tattausan hannunta cikin na Fahimah.
"Allah ya ba ku zaman lafiya.