Showing 15001 words to 18000 words out of 57616 words
Chapter 6 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
hakan ga kowa ba balle mahaifiya a gare shi. Idan ta tursasa shi ya aure ta to ta kai shi ina? Mutum gashinan kamar malaikan daukar rai wane dadi mace za ta ji a aurensa? Macen ma wadda ya fi tsana fiye da kowa a duniya?
Don haka ta soma tunanin abin da za ta fada wa Ammi ba tare da ta sanya mata kokonto ba. Abubuwa da yawa na damunta, not only UWAIS SHAGARI. Tana son sanin asalinta, tana son sanin su waye suka yi sanadin zuwanta duniya. Ammi ba ta son tambayar nan ko kankani, amma yau dole da ita za ta bi ta kare kanta da mutuncinta a idanun Ammi Safiyyah.
Ammi, babu ciwo mafi muni ga dan Adam irin a ce ba ya da asali, bai san su waye suka haife shi ba, bai san shi dan sunnah ne ko shege ba. Ammi ko ba ki fada ba na dade da ganewa, orphanage da muke zuwa shi ne gidanmu, shi ne asali da tushe na, a can ki ka dauko ni.
Ta karasa cikin wani irin kuka da ya keta har cikin zuciyar Hajiya Safiyyah.
A yau ita kanta Ammi ta rasa da kalaman da za ta lallashi Fahimah, ta fahimci irin ciwon da ta ke ji a ranta, kuma ba ta isa ta warkar mata da shi ba. Kama ta ta yi ta rungume a jikinta ta ce, Fahima, in kin yarda ni ma UWA ce, sannan kokarina ya kai na kowacce UWA, to ki dubi Allah ki cire wannan damuwar daga ranki. Im your mother, father and Uwais is your brother. Ki sani babu wanda rayuwa ta ke cikakka a gare shi, babu kuma wanda Ubangiji ba ya jarraba in one way or the other.
Mumini an sanshi da karbar kaddarar Ubangiji da kasancewa cikin godiyarsa ala kulli halin. Wannan damuwar da ki ka sanya kanki babu abin da za ta janyo sai nakasu ga lafiyar zuciya da kwakwalwar ki.
Insha Allah wata mai kamawa za mu je Umrah mu yi ibada mu nemi kusanci da Ubangiji, za ki samu sukunin zuciyarki insha Allahu.
Haka Ammi ta yi ta lallashin Fahimah, da kalamai masu dadi da nuna kauna har sai da ta sanya murmushi a kan fatar bakinta.
******
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Kafin muryarsan nan mai tada tsigogin jikinta ta biyo baya. A yau har wani kauri ta kara mai nuna ya zama cikakken mutum. Wanda ya gama mallakar duk abinda da Da namiji ke bukata a rayuwar sa. Ta juya a hankali ta dube su da fararen idanunta suna shigowa, hannun su cikin na juna sun yi balain dacewa da juna, kyau na bugun kyau. Ko hasidin iza hassada ya kalle su sai ya yaba su a ransa. Wani abu wai perfect match. Da gaske KISHI gaskiya ne a tare da kowacce diya mace, kuma Fahimah ta ji shi a kirjinta har fiye da misali, yau ga ta ga matar Uwais! Wadda ta dade tana kimanta zuwan ranar haduwar su da juna, amma murmushin da Amrah ta yi mata da innocence looks dinta sun sanya Fahimah mayar mata da martanin murmushinta. Ta kuma amsa sallamarta. Sannan ta maida kai ga abinda take yi bata kara kallon su ba.
Uwais kamar ya fashe don bakin ciki don bai so Amrah ta ganta ba shiyasa ya kawo ta da safe, lokacin da ya tabbata tana barci. Bayan sun wuce falon zuwa falo na gaba Amrah ta juya tana kallonsa da sigar da ta ke kallonsa, wadda ta bambanta da yadda ta ke kallon kowa, ta ce,
Ina ku ka samo kyakkyawar budurwa haka? Ba ka taba gaya min kana da sister ba. Cikin harshen Turanci ta yi maganar.
Fahimah daga inda ta ke tsaye tana jiyo shi yana bai wa matarshi amsa da cewa, Mai aikin Ammi ce.
Suka wuce turakar Ammi, Amrah na waiwayonta tana ta mata murmushi, sai ta samu kanta da kasa maida mata martani sakamakon zuciyarta ta yi bakikkirin da jin amsar da Uwais ya bayar a kanta. Daga bisani ta yi murmushi mai ciwo, cikin ranta ta ce, ban da abun ki Fahimah, don Uwais ya ce ke yar aikin gidansu ce ai ya kara miki matsayi, tunda bai ce da matarsa tsinto ki suka yi a gidan marayu ba. Maganar a ce ita matarsa ce ma ba ta taso ba.
Ta ci gaba da daukar aure a tsakaninsu a matsayin shifcin gizo, zai fi mata sauki; wato irin almarar nan mai zuwa ta wuce wa dan adam yadda kowacce almara ke zuwa ta wuce, haka aurenta da Uwais zai zo ya wuce ba tare da ya zama actual reality ba.
A hankali ta zame jiki daga wurin zuwa dakinta tana cewa cikin ranta, ina ma ita ce Amrah? Watakila da ita ce ke da kyan da Amrah ke da shi da Uwais ya so ta. Ta yi maza ta kwabi zuciyarta a kan hakan.
Shes proud of her own beauty no matter what, watakila ko da ta fi duk matan duniya kyau asalinta ma kadai ya isa ya sa Uwais ya kyamace ta. Don haka Fahimah ta soma kallon aurenta da Uwais a matsayin dabaibayi rather than defensive kamar yadda Ammi Safeeyah ke kallonsa.
Anya kuwa tunani da tsinkayen Ammi a kansu daidai ne? Ta yi ta zama da igiyar auren Uwais a kanta kenan don kawai a kira ta matarsa? Anya auren bai zame mata dabaibayi ba ya hana ta yancinta na yammatanci? Ko da ta ke yar gidan marayu in da Ammi ta yi hakuri ba za ta rasa me sonta a duniya ba, ko ta auri orphan dan uwanta a gidan marayun, soyayyar da zuciyarta ke yi wa Uwais da ma mai zaman kanta ce. Da Ammi ta yi hakuri ba ta yi amfani da karfin ikonta na uwa ba wajen ganin Uwais ya aure ta ba, da sannu za ta iya overcoming dinta (rinjayarta).
Haka ta yi ta saka da warwara ita kadai a daki tanajuyejuye akan gado, idan ta ce ta yi watsi da alamarin Uwais, idan tsautsayi ya gifta suka hadu ko yaya ne, tofa dole sai zuciyarta ta motsa. Daga nan ta gane cewa soyayyar gaskiya abu ce da zuciya ba za ta iya kaucewa ba. Saidai ayi mata pretending. Amma daga yau da Uwais ya gaya wa matarsa ita yar aikin gidansu ce, daga yau za ta soma yaki da duk wata soyayyar UWAIS daga zuciyarta, ko da kuwa da karfin addu'ah ne.
******
Amrah ba ta samu wata special reception daga Ammi ba, daga gaisuwa shi ke nan, ta ce,
In ce ko ba matsala?
Amrah ta ce, Babu Ammi.
To Allah ya yi muku albarka.
Daga haka ta shiga wata hidimar a daki. Ta dai fahimci Amrah za a zauna lafiya da ita daga dukkan alamu, bata da kwaramniya kuma bata da girman kai ba kamar sauran yayan masu kudi irinta ba, shes very simple a cikin muamalarta da kowa.
Tunda suka dauko hanyar komawa gida, Amrah ke zubo wa Uwais tambayoyi duk kuma a kan Fahimah, shi kuwa komai ta tambaya cewa yake bai sani ba. Yadda ta ga yarinyar shi ma haka ya ganta a gidan.
Amma wallahi Habib-Qalby ba ta yi kama da yan aiki ba. Zubinta irin na matan kasar Sirreleone irin kalar fatarta nake burin ina ma in samu. I hate so much brightness. Ga dasashin cikin bakin ta irin wanda nake shaawa, da a ce ni mazauniya ce da na roki Ammi ta bar min ita, I just like the girl.
Uwais dai sai "umh" yake cewa, yana ci gaba da tukin motarsa cikin nutsuwa har suka isa gida.
Sun yi shirin kwanciya ya shigo dakin Amrah da zummar yin wani abu, sai ya ganta tana kora magani a bakinta. Da sauri ya idasa shigowa dakin zuwa gabanta.
Lafiya Amrah? Ba ki da lafiya ne?
Ta ce, No, lafiyata kalau. Contraceptive pills ne nake hadiya sabida su aka min recommending kan cewa sun fi rashin illah ga wanda bai taba haihuwa ba.
Tunda Uwais ya hadu da Amrah daga dating (soyayya) zuwa aurensu ba su taba samun sabani ba, bai taba jin haushinta a ransa ko miskala zarratin ba. Amma yau ya ce,
Amrah!
Cikin kakkausar murya.
Zan amince da komai, karatu a Malaysia, amma ban da a dinga zubar min da kwayayen haihuwata. Ban sani ba ko iya su Allah ya yi nufin ba ni a duniya.
Amrah ta dube shi tana kankance idanu, Habib-Qalby, me ka ke nufi ne? Ina MBBS student in haihu yanzu? Kwata-kwata nawa nake? Ko shekaru ashirin ban rufa ba, ni karatuna ya fi min komai muhimmanci, wallahi...
Uwais ya yi mata wani irin kallo, ya ce, Har da ni Amrah?
Ai da abuna ka gan ni ka aure ni, ban ga dalilin da zai kai ni haihuwa yanzu ba.
Uwais ya yi sake da baki yana kallonta. Rana ta farko da ya soma tunanin anya nan gaba zai iya tankwara Amrah? Yayi sake tun farko. Anya bai yi kuskure ba da ya nuna wa Amrah matsananciyar soyayya a fili? Juyawa ya yi ba tare da ya ce komai ba, zuciyarsa na tafarfasa. Ba abin da yake so a duniya irin haihuwa, kasancewar shi daya tal! Allah ya bai wa mahaifiyarsa. Yayan da yake burin haifa su yake fatan su zamo masa yan uwa. Ashe Amrah rariya ta ke kora su.
Don haka kwanaki biyu da suka biyo baya ya dauke wa Amrah wuta, amarci da soyayya sun tsaya, wanda hakan ya jefa Amrah a damuwa. Amma abinda yake so da ita ba mai yiwuwa ba ne. Ya za ta yi da Da alhalin tana karatu a wata uwa duniya?
Sai yanzu ya fahimci cewa, ashe dai duk son da yake wa Amrah har gobe yana nan a Uwaisunsa. Murmushinsa duk ya tsaya, haka yawan sakewar da yake wa Amrah.
Damuwar da Amrah ta shiga ba ta misaltuwa, musamman da yake Uwais ya koyar da ita wata irin soyayya mai wuyar bari, yanzu ya dawo ya koma tamkar ba shi ba, ita kuma ba za ta iya bin raayinsa ba.
Aunty Murjanatu ta kira domin neman shawara tana kuka, Uwais have changed completely, haihuwa yake so Aunty Murja, ni kuma ban shirya ba. Ya kasa fahimtata, akalla ina bukatar shekaru biyar nan gaba kafin na amince na fara haihuwa.
Murja ta ce, Amrah in kina son kwanciyar hankali a gidan aurenki ki bi abin da mijinki ke so, tun ba ki yi sanadin da dimbin soyayyar da yake miki za ta ragu ba. Komai na Allah ne, ke ba ki isa ki tsarawa kanki rayuwa ba sai abin da Ubangiji ya tsara miki, haihuwa ba ta hana komai sai ki dauki Nanny.
Da haka Murjanatu ta samu ta rarrashi Amrah ta kuma tabbatar mata a daren yau za ta je ta bai wa Uwais hakuri.
Shiri na musamman Amrah ta yi zuwa dakin Uwais cikin wasu tausasan nighties. Uwais na loosing tie din wuyansa bayan ya dawo aiki bai ji motsin shigowar Amrah ba, sai ji ya yi ta rungume shi ta baya, kamshin sassanyan turarenta Yves Saint Laurent da sulbin hannunta su suka gaya masa ita ce. Ya lumshe ido yana tuno wahalar da ya sha a kwanakin nan da ya hora kansa da rashin Amrah.
Zai iya cewa shi ne horo mafi muni da ya taba karba a rayuwar sa bayan horon auren Fahimah wanda sanadin auren Amrah ya ja masa, amma ya fiye masa a kan ya biye wa abin da Amrah ke so. Ko Ammi ta ji za ta kara tsanarta ne a kara lika masa wannan abun aman (Fahima). Shi kuwa da wani abu makamancin auratayya ya shiga tsakaninsa da Fahimah gara ya koma mace (ya yi losing manhood dinsa).
Im sorry Habeeb-Qalby, something like this will not happen again I surrender.
Murmushi ya yi, ya janyo ta ta dawo gabansa, wani irin kissing dinta ya shiga yi, passionately, ya ce, Amrah in ki ka ba ni Da, kin gama min komai a rayuwa, ni ko ba za ki shayar da shi ba ki haifa ki ba ni abina, zan bai wa Ammi na ta kula min da shi.
Amma in ki ka ce sai kin zama likita za ki haihu Amrah ai zuwa lokacin na soma furfura ina neman abokin tafiya masallaci ne. Zan taya ki raino ke har nakudar in ba ki so na yarda ki yi epidural. Ni dai burina in haihu da ke Amrah ko sau daya ne a rayuwa sabida son da nake miki.
Yatsunta ta kai ta toshe masa baki, Na amince Habib-Qalby, Im now ready to conceive, kuma tare za mu raini dan mu ko yarmu insha Allahu, zan raba lokacina biyu in ba ku rabi, ka taya ni addua Allah ya ba ni kafadar dauka...
Da sauri Uwais ya ce, Lah yukallifullahu nafsan illa wusaha. Maana, Allah ba ya dora wa wata rai face abin da za ta iya. Ke mace ce Amrah, kuma mace da aure da haihuwa a ka santa, don ita jaruma ce fiye da namiji, boko shi ne last priority hidimar aure tana kan gaba da komai. Amrah don ita ce hanyar shiga aljannah.
Daga haka Uwais ya canza akalar hirar zuwa mafi aala a gare shi. Sumbutarta yake kusfa-kusfa kamar zai hadiye ta.
Ya yi kewar Amrah a kwanaki uku kacal yadda biro ya yi kadan ya bayyana, haka ita ma sai da ta ji idanunta sun cika da hawaye don tausayin Uwais, domin ta lura ba karamin azabtar da shi ta yi ba. Addua ta ke, Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran da za ta ci gaba da kulawa da bukatar gangar jikin Uwais da lafiyar haifa masa yaya, ta yarda Uwais mai sonta ne, mai kuma matukar kaunarta wanda ya bambanta da sauran maza a halayya da dabi'a wajen nuna wa matansu soyayya a fili, abinda maza da yawa basa iyawa a wannan zamanin sabida girman kai.
Alhaji Umar Dikko ya raini yayansa ne da tarbiyya ta ilmin boko zallah don haka ya;yan gidansu duka sun fi fifita boko a kan komai. Abin da Uwais ya lura da shi ke nan da ya sa yake ta yi wa Amrah uzuri a bisa sababbn dabiun da yake ta gani a tare da ita, wadanda suka sabawa nashi upbringing din. Alal misali, Amrah ba ta canza daga irin shigarta ta baya ba, wadda ta ke yi kafin aure ta dan kankanin gyale, hira da abokan karatunta maza, ta waya duk sanda take so, girki ma kuma ba kullum ta ke yi ba yanzu, in kuma ta yin, to sau daya a rana, sannan kuma very simple wanda ta tabbatar ba zai wuce mata minti goma ba, haka Uwais yake hakuri da abubuwa da dama bayan wadannan wadanda yake ganin sun sha bamban da na gidan da ya fito.
Su ma yan boko ne, amma ba masu dabiun nasara ba. Uwarsa is an Associate Professor. Amrah ko a ina ta ke za ta iya bude lemo ta sha a tsaye haka yanayin dressing dinta ba ka iya bambance shi da na budurwa mara aure. Wani abun ko ya gyara mata in bai yi daidai da raayin gidansu ba, ba za ta yi ba.
A wurin Uwais duka wannan mai sauki ne tunda yana samun yadda yake so da Amrah a shimfida. A wannan fannin kam yana yaba mata, kuma yana samun contentment don haka duk wani flaws na Amrah kankani ne a idanun sa. Hausawa suka ce, so hana ganin aibi, shi Uwais bayan son da yake wa Amrah har da kauna yar usli mara algus.
Ya kama nan da kwana uku Amrah za ta koma Malaysia, bayan sun shafe watanni ukku tare suna barzar amarci, don haka Uwais yau duk a dame yake, ya zama upset ya kasa nutsuwa a ofis. Kusan duk bayan mintuna talatin sai ya kira Amrah a waya don ji yake kamar kafin ya kima gida zai je ya tarar ta koma Malaysia.
Sai yanzu da ya san dadin aure ya fahimci cewa yayi babban kuskure da ya yarda da yarjejeniyar karatun Amrah, lokacin idanun sa sun rufe da neman aure, bai yi tunani consequences ba, yanzu kam ya fahimci bai iya rayuwa shikadai na tsayin sati biyu ma ba watanni hudu ba babu mace, in hakan ta faru akwai babbbar matsala, wadda bai san yaya zai yi da ita ba..
Duk da kasancewar sa matashi mai jini a jika, mai tashen kuruciya da hatiman banki, Ubangiji Allah bai dora masa sha'awar zina ba, bai taba fatanta wa kansa ba don haka ya shiga tunanin mafita ga rayuwar sa. Don ba zai bar Halal ya sabawa Ubangiji don karatun Amrah ba.
Don haka yau da ya taso aiki shine sayi banza sayi hopi duk da yasan Amrah na so na makulashe da kayan amfani saida ya biya ya sayo mata. Ya san abinda ya tarkowa kansa ba karami bane amma an ce faduwar gaba asarar namiji, kuma a ganin sa a halin yanzu ai yafi Alhaji Umar Dikko iko da Amrah.
Amrah tun daga kofar falo ta tare shi, ta ci sassanyar kwalliyar ta mai taba ruhin Uwais, bakaken riga da wando ne a jikin ta samfurin CK, ta makalkale cikin jikin sa kamar zata yi kuka "Habib-Qalby, yau ka dade baka dawo ba, saura kadan in bi bayanka, ga duhu ya fara shigowa ka sanni da tsoro". Makale ta yayi a kafadun sa suka karasa bedroom din su yana fadin " i'm sorry Amrah, na je nemo miki pizza dinnan ne da kike so ta Dominos, na tarar basu bude ba sai da naje wani wajen mai nisa" ya fada yana bude ledojin da yayo mata sayayyar, sai smiling take yi gashi duk abubuwan da take so ne. Uwais ya gama sanin Amrah ciki da bai, ta manna masa kyakkyawar sumba a kunci sannan tace "nagode Habiby, amma tare zamu ci, i'll be chewing it for you (zan dinga tauna maka)".
Dariya Uwais yayi ya marairaice ido tamkar yaron dake gaban Mamarsa "a hakan kuma da dukkan zuciyar ki murna kike zaki tafi ki barni ni