Showing 24001 words to 27000 words out of 57616 words
Chapter 9 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
Da zuri'a mai albarka. Allah ya kade fitina da dukkan abun ki".
Fahima sai ta samu kanta cikin wani hali na 'fita hayyaci' na wucin gadi. Ta nemi jinta da ganinta na 'yan dakikai ta rasa. Don haka har su Baffa suka yi sallama da Ammi suka fita Fahimah ba ta koma cikin hayyacinta ba. Watakila dai mafarki ta ke yi... Irin mafarkin da dan Adam ke yi idan ya cika sanya tunanin abu a ransa. Mafarkin kasancewa matar Uwais ai ba yau ta fara ba. Don haka na yau din ma in ta yi hakuri za ta farka ne kada ta yaudari kanta.
Har sai da Ammi ta raka su Baffa ta dawo Fahimah na nan kafe a inda Ammi ta barta, rokon Allah ta ke yi a zuci ya yi gaggawar farkar da ita daga wannan rudadden mafarki. Ammi na shigowa ta kama hannunta ta cira ta tsaye suka nufi dakin barcinta.
A gefen gadonta ta zaunar da Fahima wadda zuwa yanzu ta fara ji a jikinta yau ba mafarki ta ke ba, wani babban alamari ke shirin faruwa da ita, wanda ba za ta ce alkhairi ba ne. Idan kalamansu gaskiya ne sun aura mata Uwais shin hakan zai haifar da Da mai ido a gare ta?
Wanda ba ya sonka fa bai sonka har abada, kuma ba zai taba sonka ba balle an hada auren da na matar da yake so, ai kawai in hakan ya tabbata ta amince kawai karshen Fahimah ya zo (the end of FAHIMAH).
Don dai ta san Uwais ba zai barta da rai da numfashi ba, ba zai barta ta shaki numfashi a matsayin matarsa ba, balle su hada inuwa daya, inuwar ma wadda ta fi kowacce alfarma wato inuwar aure.
Maimakon farin ciki duk da mayataccen son da zuciyar Fahimah ke yi wa Uwais, ji ta yi wani irin tsoro da firgici ya mamaye ta, kada Allah ya nuna mata ranar da za ta kara haduwa da Yaya Uwais ko da a hanya ne. Kamar yadda suka ce burin na Ammi ne, ta yadda Ammi za ta yi mata kauna fin haka. Ji ta yi hawaye sun jika fuskarta sharkaf ba tare da ta ankara ba, Ammi gorar ruwa ta dauko a firji mai sanyi ta zubo a tambulan ta mika wa Fahimah, ganin yadda ta ke yanka gumi daga zaune kamar wadda ke dakin nakuda duk da rabar iyakwandishan da ta lullube dakin Ammin.
Kusa da ita Ammi ta zauna, ta ce, kuka Fahimah? Ki yi hakuri in na miki ba daidai ba, ban iya rabuwa da ke Fahimah zuwa gidan wani, bansan irin kalubalen da zaki fuskanta ba, haka ba zan iya jurar ki wulakanta a gidan aure ba, a dalilin haka ne na yanke shawarar aura wa Uwais ke ba tare da neman shawara ko amincewar kowannenku ba don na san ba za ku taba amincewa ba bisa karan-kanku.
Amma Allah shi ne shaidata kan cewa ALHERI nake nufinku da shi, ba za ku gane hakan ba ku duka sai ranar da bana raye. A yanzu dai ba hadin kanku nake nema ba don abin da nake nema na same shi, burina ya cika. Fahimah kin dauwama cikin zuriata. Dukkanku kuna bukatar lokaci kafin ku tantance aya da tsakuwa, ki kwantar da hankalinki in dai a kan Uwais ne ba zan kai ki gidansa ba sai bisa amincewar zukatanku ku duka.
Ki je ki hada kayanki na sati biyu, gobe insha Allah in an kai masa amaryarsa ni da ke za mu tashi zuwa umrah, ba za mu dawo ba sai bayan sati biyu.
Jiki a mace Fahimah ta mike amma ta kasa ce da Ammi komai.
Idan na yi miki ba daidai ba, idan hukunci na bai miki daidai ba ki yi hakuri ki yafe min Fahimah.
Da sauri Fahimah ta juyo, tausayin Ammi wadda tsufa ya soma bayyana a gare ta duk sai ya kamata. Cikin rishin kuka ta ce,
Ammi, ba ki yi min komai ba. Sannan ta sa kai zuwa dakinta.
Burinta a rayuwa komai ya girmansa a yau ya cika. Mafarkanta sun zamo gaskiya, ta zamo wani bangare na Uwais Shagari, amma abin mamaki ta kasa farin ciki da hakan, watakila don girman kalubalen da ta ke hangowa ne, watakila kuma don ta san auren ba zabin Uwais ba ne, in ma ya sani ke nan. Jin kanta ta ke tamkar wadda ta rako dukkan mata duniya sabida rashin saarta a rayuwa. Gabadaya maganar auren da auren kansa ba ta san a ajin da ya dace ta sanya su ba.
Da me za ta ji ne a rayuwarta? Maraici, rashin asali and finally BORANCI?
Kodayake Ammi ta ce ba kai ta gidan Uwais za ta yi ba, sai ranar da dukkansu suka amincewa hakan. Ranar da ta tabbata ba mai zuwa ba ce, sai dai ta dauwama da sunan matar Uwais, amma auren ba zai taba zama reality ba.
Yadda Fahimah ta ga rana haka ta ga dare a wannan ranar, kitsawa ta ke tana tufkewa sannan ta warware. Ta rasa makomar rayuwarta. A karshe ta sa a ranta cewa, ya kamata ta yarda cewa, duk bakinta da Uwais ke fadi yana gorantawa ita ma mace ce kamar sauran mata, wadda wani namijin bayan Uwais zai iya gani ya ce yana so ya biya sadaki ya dauka ya kai gidansa. In haka ne kenan ya kamata ta martaba kanta....Ta daina kallon kanta wulakantacciya. Ba kuma ta kowacce hanya ba face ta yin gefe da UWAIS daga zuciyarta, shi da duk abin da ya shafe shi. Ta maida komai nasa a bakomai ba, ta maida hankali kadai ga karatun da Ammi ke so ta yi, ta gina wa kanta future yadda duk ranar da babu Ammi za ta tsaya da kafafunta.
Ta dauki aurenta da Uwais a matsayin shifcin gizo in ba haka ba ita ce a wahale. Ta tsaya ta nema wa kanta madafa ga rayuwarta ta gaba, wanda ba komai ba ne san yin ilmi da zai ba ta martabar da kyawun halitta ba ya badawa. Kyawun halittar da ta fi tunanin a kansa ne Uwais bai sonta. "Goddam Black" kamar yadda yake cewa tana alfahari da bakin fatarta.
Ammi ta sha gaya mata Black is beauty a duk lokacin da Yaya Uwais ya ce mata Black, kuma babu mummuna sam a yaya mata sai wadda ba ta martaba kanta ba.
Da kyar barci ya sace fahimah a wannan daren cike da tunanin da ta kwanta da shi.
******
Washegari Ammi da Fahimah suka tashi Umrah zuwa kasa mai tsarki. Ammi ta yi haka ne don ta nesanta Fahimah da Uwais na dan lokaci, ya kuma samu lokaci da matar sonsa yadda ya kamata.
Duk adduar Ammi a Harami da Masjid Nabawy a kan Uwais da Fahimah ne, ita kadai ta san adadin abubuwan alkhairin da ta ke roka musu.
A can Kano, ango da amarya suna ta barzar amarci babu kama hannun yaro. Uwais ya matukar jin dadin tafiyar Ammi da Fahimah, don ba ya so ko da kuskure a samu wanda zai gaya wa Amrah yana da wata matar bayan ita.
Alhaji Umar Dikko ya zuba dukiya a gidan Amrah kamar bai san zafin nema ba. Gidansu komai ya yi acan-acan, soyayya ruwan zuma gangariya tsakanin Uwais da Amrah ba su taba gundura da juna.
Kafin Ammi da Fahimah su dawo Saudiyyah ango da amarya har wata yar kiba suka hada a kumatunansu sabida kwanciyar hankali da samun contentment in life.
Ranar asabar da daddare suka sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano. Fahimah ta yi wa kanta sayayya sosai, haka ta yi wa Talatu tsaraba. Ba yadda Ammi ba ta yi da ita ba a kan ta yi wa Uwais tsaraba ko ta carbi ne, Fahimah ta ki. Yadda ta yi fatali da Uwais daga zuciyarta haka ta ke fatan ta manta da ko sunansa.
Dan halak din shi ya zo daukarsu zuwa gida, ya sha excelcior fara kal, sai walainiya ya ke. Da ganin shi ka ga angon daje kan ganiyar sa. Motarshi kamar a nan ne kamfanin Maison Francis yake. Ga wani farin gilashin PRADA da ya manna ma dogon karan hancinsa. Kallo daya da Fahimah ta yi masa ba ta kara maimaitawa ba, duk da kuwa cewa zuciyarta ta yi mugun raurawa. Sakamakon wata irin ilhama da kamala da aure ya kara wa Uwais, gara ita ta kalle shi sau daya, shi ko sau dayan bai kalle ta ba. Sai da ya mallaki Amrah ya kara gane babu wata sauran diya mace da za ta kara burge shi a duniya.
Babban tashin hankalinsa a kwanakin nan shi ne in ya tuna Amrah tafiya za ta yi ta barshi shi kadai a gidansu, aikinsa kuma ba irin na yawo ba ne duk lokacin da aka ga dama. Ya soma da ya sanin alkawarinsa na barin Amrah ta ci gaba da karatu a jamiar Limkokwing, sai dai ya san bai isa ba, ya yi kadan, yayi tsararo ya daga wannan alkawarin daga muhallinsa.
Amrah ta sangarta shi da abubuwa da yawa a sati uku kacal, ga iya girki, ga tsafta ga shagwaba sannan uwa-uba ta iya bi da shi a shimfida. Duk da karancin shekarunta.
Suna tafe a kan hanyarsu ta zuwa gida daga airport tsakanin shi da Ammi kawai suke hira a motar, Fahimah tamkar ba ta gurin a motar, amma har cikin bargonta ta ke jin tasirin muryar Uwais har tsigar jikinta na tashi, suna isowa gida ko gama parking motar bai yi ba ta bude murfin motar ta yi cikin gida.
Ta gilashin motarsa ya saci kallonta, sanye ta ke da jallabiya kirar Oman ruwan toka da mayafinsu. Kayan sun karbi choculate colour din jikinta sosai. Sannan ta yi dan haske irin na kamawar wanka a jikin mace mai tsafta.
Uwais ya dauke kai daga dubanta yana sakin tsaki a ransa. Mace sai fadin ran tsiya kamar diyar qaruna, nan kuwa diyar kwalin taliyar indomie ce.
Maigadi ya sauke akwatunansu zuwa ckin gida. Da gudu Talatu ta fito tana "oyoyo uwar dakina", ta rungume Fahima wadda ke ta murmushi don ita ba ta kyalkyala dariya sam, murmushi kawai ta ke wanda ke maida ita kamar furen fulawa idan ta yi shi sabida bakin dadashin cikin bakinta da ke bayyana a duk lokacin da ta yi murmushi. Da taimakon Talatu suka kimtsa duk kayan da suka dawo da su a muhallinsu bayan Fahimah ta ware mata tsarabarta.
Fahimah ba ta san cewa Uwais ya gaya wa Ammi washegari zai kawo Amrah ta yi mata barka da zuwa ba. Gajiyar tafiya ya sa ta koma barci bayan sallar asubah, ba ta fito ba sai karfe goma na safe, ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da wando pakistan ruwan dorawa, ta kame kakkarfan gashin ta da ribbon kanta babu kallabi, tana tsaye jikin dining tana decorating wurin da kayan kawata dining area da ta sayo daga Saudiyyah ta ji sallamar mace.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: A hanyarsu ta dawowa Uwais tuki kawai yake ba ya ko kwakkwaran motsi har suka iso gida. Yana yin parking Fahimah ta fice, har tana tuntube saura kadan ta fadi, Uwais ya bita da kallon takaici, dakinta ta shige ta murza key. Ta jingina bayan ta a jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Me ke shirin faruwa ne da rayuwar ta a yau? Ammi na son actualizing wannan auren a lokacin da daga ita har shi Uwais din ba su shirya ba.
A baya ta ce ne sai lokacin da suka shirya karbar juna a matsayin ma'aurata don kansu. Abinda su duka biyun suka tabbatar ba mai yiwuwa bane. Amma yau kwatsam! Ta shammaci kowannen su a lokacin da suka riga suka sakankance cewa auren na su ba mai tabbata bane sannan ba zai je ko nan da can ba.
Yau Ammi ta dauko wata gagarumar rigima wadda baza'a ce rikicin tsufa yayi dalilin ta ba. Don kuwa bata yi tsufan da zata ce ta manta waye UWAIS ba? Kuma kuma yaya matsayin ita Fahimah yake a gare shi?
Ta riga ta gama sakankancewa cewa auren ta da Uwais suna ne kawai, sannan a suna zai kare. Daga ranar da aka daura shi zuwa ranar da zai gaji da ajiyar sa ya bata takardar saki. Yau ina zata tsoma rayuwar ta idan ta bi Uwais zuwa inda bata san kowa ba? A gaban Ammi ma ya ta kare da shi balle a bayan idon ta, karkashin mulkin sa da ikon sa?
Kawai sai ta ji hawaye na zubo mata. Hawayen ba na komai ba ne na tausayin kanta ne. Namiji sai ana rarrashin sa ana kalallamar sa ana nusar da shi a kan ya so ta! Don kawai bata da iyaye kamar kowa! Ko da ya ke watakila Uwais na kin ta sabida kalar fatar ta ne idan ta yi la'akari da irin kalaman da ke fita daga bakin sa akan ta duk lokacin da ya bushi iskar izzar sa. Ita wace irin mara saâa ce a cikin mata? Kuma wace irin kaddara ke bibiyar ta? Daga maraici da rashin asali.... yanzu kuma zuwa BORANCI!
A wannan lokacin wani irin determination (kudiri) ya kutso ya shigi zuciyar Fahimah Shagari.... Determination na self-defence and self-actualization; abin nufi ta tsaya ta san hakikanin kanta, ta kuma kare kanta daga farmakin zuciyarta akan Uwais; kada ta bari soyayyar Uwais dake dankare a zuciyarta ta kassara ta, ta zamo barrier ga farin-cikin ta da cigaban rayuwar ta, ta zubar da kimarta ta diya mace mai daraja a dalilin soyayya.
Zata yi kokari iyakar yin ta, ta ga cewa ko ta ina aka je aka dawo ta baiwa Yaya Uwais mamaki sabani ga tunanin sa; she is not begging for his love. Hakannan komai nasa yanzu ya koma ba komai ba a idanunta (ya daina burgeta). Sannan duk yadda ta kai da son sa a baya, daga lokacin da aka sanar da ita an yi musu aure duk wani infatuation sai da ya kama gaban sa. Su ci gaba da zama a yadda suke a duk inda za su je ba damuwar ta ba ne matukar zata rike determination dinnan nata. Uwais ya rike duk abinda yake takama da shi itama daga yau ta koyi sarrafa kanta akan sa. Abinda Ammi ke fatan ya kasance insha Allah ba zai kasance ba, karewa ma ita yau ta fara period kuma sai ta yi kusan kwana hudu yake daukewa. Kuma an ce tafiyar ta kwanaki uku ce.
Tunanin hakan da ta yi ya sa ta jin wani irin relief a zuciyarta. Ta bar bakin kofar zuwa toilet ta sakar wa kanta shower mai dumi kamar yadda ake a alâadarta kullum kafin ta kwanta barci.
A duk lokacin da tayi hakan zata yi barci mai dadi ne har da saleba.
To yau ma hakan. Domin kwata-kwata ta cire damuwar tafiyar daga ran ta. Sai sake-sake da kintace-kintacen abinda zai faru.
Bayan sallahr asubah ta sake wanka ta shirya cikin koriyar atamparta vlisco, ba ta san takamai-mai karfe nawa za su tafi ba, don haka ta kishingide a kan gado da zummar kafin cikar karfe takwas na safe ta sake bincikawa in ma tafiya yayi ya barta ta sani, tayi abinda ke gabanta.
Ai kuwa barci mai nauyi ya sadado ya yi awon gaba da ita. Don jiya tunani da sake-saken yadda tafiyar ta da Uwais zata kasance kadai bai barta ta yi barci yadda ya kamata ba.
Can! Cikin barcinta ta ji ana buga mata kofa da dan karfi, kamar za'a jijjigeta. âWho is this?" Fahimah Ta tambaya cikin mamaki da mutstsike ido.
Shiru ba amsa, tamkar da dutse take magana, nan jikin ta ya bata ko waye, saukowa ta yi daga gadon ta bude kofar don ganin wanda ke mata wannan bugun kamar ana binta bashi.
Uwais ta gani harde da hannuwa a kirji sai huci yake kamar mesa, ya hade cikin jamfa da wando na wani tattausan voyel sky blue, as usual hular kansa ta nitse cikin tsakiyar sumar kansa. Wani kallo ya yi mata kamar fararen kwayar idanunsa za su fado don harara, sannan ya nuna mata agogon hannunsa.
âAre you awareâ? an lika min ke kuma zaki bata min lokaci ki ka shige daki kina ta barci? Me za mu ci kafin mu bar gida ko ni ki ke jira in je in girka miki?â?
Fahimah ta tsuke baki, sannan ta murguda shi gefe ta rabe ta gefensa ta wuce zuwa kitchen ba tare da ta tanka masa ba. Ya saki baki yana kallonta da madaukakin mamaki har ta shige kitchen, shi ta ke murguda wa baki?
Girgiza kai ya yi ya bi ta kitchen din. Cikin hargagi yace.
âYou Goddam Black, 15 minutes na baki ki sama min abin da zan ci, bana hawa jirgi ban ci komai ba, cikina hautsinewa yake yiâ?.
Fahimah dai bata amsa ba, ta baiwa banza ajiyar sa, sai kokarin kunna heater din dafa ruwan zafi da ta ke yi. Da alama so yake ta tanka ya ji dadin bata mata rai, ya ci mutuncin ta a banza bata da mai tare mata, to ba za ta tanka shi ba. Don an ce karfe daya baya amo.
âIrin ga dan iska din nan ko, ina magana kin bai wa banza ajiyata?â?
Fahimah ta ga in ba ta amsa ba zai iya yin zuciya ya shigo ya makure ta, ko ya samu ya huce haushin manna masa ita da Ammi ta yi, ga shi su biyu kacal a cikin gida babu mai ceton ta. Sai ta ga gara ta tanka, don ya san ta daina tsoronsa yanzu, kuma tana iya mallakar kanta a gabansa. Sannan ba zamansa take yi ba zaman Ammi take yi.
âDon Allah ka sarara min mana! Kafin 15 minutes din ma zan kawoâ?. Ta fada ciki-ciki kamar mai kunkuni. Babu tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba. Tsiwa take so tayi masa amma tana tsoro.
Fatanta ya