Showing 48001 words to 51000 words out of 57616 words
Chapter 17 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
wannan tunanin wahalar ovulation ke damunki, da kin haihu ko kuda ba za ki so ya gifta a tsakaninku baâ?.
Amrah dai ba ta ce komai ba, amma ta ji dadin maganganun Fahimah, ba ta san sanda ta fada ba tsabar bata cikin normal hayyacin ta, kuma tana bukatar taimako daga 'yar uwarta mace koda da shawarar fatar baki ne. Tace.
"Fah-himah I just like you, and i love your simplicity ".
Da sauri fahimah ta girgiza kai tana jin kamar ta bude baki ta gaya mata gaskiya, don ba ta saba rashin gaskiya a rayuwarta ba sam sai yau. Yau din ma don kada ta shiga hurumin da ba nata bane. Kamar Uwais ya san me ta ke shirin yi sai kawai ya bude kofar ya shigo dakin babu zaton su.
Ya dau wankansa as usual ya yi shirin ofis cikin bakaken suit, ya dube su ya girgiza kai.
âDaga ganin wannan zaman naku gulmata ake, kin bar ni zan fita ban ci komai baâ?. Ya fada yana kallon Amrah directly cikin idanunta. Ji ya yi ya kara sonta duk flaws dinta, tunda tana son Fahimar sa.
Fahimah sai ta zame jiki ta bar musu dakin, kofar da ta ke da tabbacin kitchen ce can ta nufa. A gurguje ta dama wa Uwais custard ta zuba madara (peak) ta ruwa gwangwani daya, ta soya plaintain da sauri ta zo ta aje masa a dining. Daidai lokacin suka fito daga dakin nata shi da Amrah, ya ja kujera ya zauna ya soma tsiyaya vanilla custard din a kofin mug na tangaran. Fahimah ba ta tsaya tare da su ba, ta koma kitchen din don ta sama wa Amrah wani abu mai dan gishiri da maggi kuma mai yaji da za ta iya ci kamar yadda ta gaya mata cewa abu mai yaji da maggi kawai taje iya ci..
Farfesun tarwada ta yi mata, Amrah ta ce ta saka tarugu sosai. Haka ta yi ta shan romon da cokali tana gumi tana fyace hanci.
Da rana girki na musamman Fahimah ta yi wa Uwais tuwon semo miyan danyen kubewa da yaji zallar tsokar kaza, ta cire duka kasusuwan ta dagargaza tsokar cikin miyar. Amrah ta ce ba za ta ci komai ba wanda Fahimah ta dafa don bata marmarin tuwo, sai spicy chicken take so, ta kira Uwais tace idan ya dawo aiki ya tsaya ya taho mata da ita daga Chicken Republic.
Amma Fahimah ba ta kyale ta haka ba, sai da ta yi mata dan wake da manja da yaji, ai kuwa Amrah ta yi ta zuqulqula tana shi wa Fahimah albarka.
Ita kuma ta zage ta gyare gidan ciki da bai dinsa, dakin Uwais ne kawai ba ta shiga ba.
Da ya dawo ya kawo wa Amrah kazar. Kallo daya ta yi mata ta ji ta ginshe ta. Ta ce, âHabiby, na ci dan waken Fah-himah na koshi kuma ku nemi mai cin wannanâ?.
Kwanan Fahimah bakwai a gidan gaba daya rayuwar gidan ta yi armashi. Amrah na samun hutu yadda ya kamata Fahimah na kula da cinta da shanta, tsaftar gidanta har ma da walwalarta. Wani irin sabo wanda ya fi kama da na âyan uwantaka ya shiga tsakaninsu.
Uwais ya gaya mata Ammi ke rikonta ba âyar aiki ba ce kamar yadda ya gaya mata a baya, amma ko da wasa bai fada mata Fahimah daga orphanage ta zo hannun Ammi ba. A ganinsa wannan sirrin Fahimah ne wanda daga shi sai Ammi yakamata su sani, don sama wa Fahimah cikakkiyar walwala da sukuni a cikin mutane âyan uwanta.
Uwais ya yi juriya kwarai, don kuwa bai kara attempting zuwa dakin Fahimah cikin dare ba, ya yarda da hujjarta na ce wa Amrah deserves respect, a gaban idonta ko a bayan idonta sabida kyakkyawar zuciyarta da kyautatawar ta..
Sati biyu na cika Fahimah ta soma shirya kayanta don komawa gida, Ammi ta yi waya gobe insha Allah za ta sauka a Kano.
Amrah har da hawayenta da Fahimah za ta tafi, ta hada mata cosmetics designer din AVON set guda. Ita da Uwais da Fahiman suka tafi filin jirgi dauko Ammi. Suna ta hira ita da Amrah, Amrah na fadi mata âI cant' express my kind gratitude, for your being with me, for your kind assistance Fahhimah, ina ma Ammi za ta bar min ke mu ci gaba da zaman mu tare?â?
Uwais ya yi murmushi yana tukin mota zuciyarsa ta masa dadi, ya juya ya ce da Amrah da ke gefensa,
âIta kuma ta yi ta zama kenan ba za ta je gidan nata mijin ba?â?
Amrah cikin zolaya ta ce, âAi don ta ki ne, amma na ce mijin ma ta zo mu aura tareâ?.
Uwais daga jin haka bai iya kara cewa komai ba, ko kwakkwaran motsi bai kara ba, don mamakin Amrah ya gama kashe shi. To amma ya ya za ta ji idan ta ji cewa all these while Fahimah zaman matarsa ta ke yi kamar ta? He is just fooling her? Ko ya ce they are just fooling her?
Daidai lokacin da suka shiga filin jirgin Malam Aminu Kano, tuni su Ammi sun sauka, a reception suka hango ta. Fahimah da gudu ta runtuma ta rungume Ammi. Yayin da Ammin ke fadin,
âAutar Ammi, na yi kewarku. Da fatan na same ku lafiya?â?
Amrah ta iso tana yi wa Ammi barka da zuwa. Ammi ta kama hannunta tana tambayarta karfin jikinta. Daga nan suka karasa mota Uwais ya ja suka tafi, amma wannan karon Ammi ce a gefensa, Amrah da Fahimah suna baya, hira suke sosai. Fahimah na ta bai wa Ammi labarai har suka zo gida.
Baba Talatu ta yi musu girkin tarbar Ammi, Uwais da Amrah ba su jima ba suka wuce, Fahimah na kokarin kaucewa hada ido da Uwais a duk inda Amrah ta ke, haka yanzu da za su wuce ya biyo ta har dakinta yana so su yi sallama cikin gigicewa Fahimah ke korarsa.
âKa yi wa Allah Ya Uwais ka tafi, in yaso ka dawo daga baya, I cannot hurt this beautiful soul!".
Gaba daya ta rude har tana tura shi waje da hannayenta.
Shi abin ma dariya ya ba shi. Ya ce, âZan tafi, amma ki sani kin ci bashi ba dan kadan ba, next haduwarmu biyan bashi ne, DEAL ne. Amrah kuma na gaji da wasa da hankalinta, don haka ki kwarara zuciyarki, soon ba da jimawa ba zan gaya mataâ?.
Fahimah ta ci gaba da tura shi, fatanta kawai ya fita a dakin.
Uwais ya shammace ta ya hade bakunansu, kissing her deeply har sai da alâamura suka soma fin karfin Fahimah. Can cikin tsakar kanta ta jiyo Amrah na fadin.
âHabiby, where are you?â?
Fahimah ta ja baya da karfi, trying hard ta yi pushing Uwais back, amma ta kasa. Wata irin kyakkyawar runguma ya yi mata yana fadin.
âFahhimah don Allah kada ki bar ni saboda Amrah, don na ga yanzu kin fi sonta a kainaâ?.
Fahimah ta gatsina baki, ta ce, âDa can din sonka nake yi Ya Uwais? Ka yi wa Allah ka tafiâ?.
Uwais ya ce, âHummm! A bar kaza cikin gashinta, amma Fahimah na san kin dade kina son mara kirkin Yayan nan naki, dalili na na kara uzzura miki kenan, da kiranki da sunan da zai dinga bakanta zuciyarki don ki cire ni a ranki don na san duk ranar da Ammi ta gane hakan sunana angon Fahimah, ina so ko bana soâ?
To kana naka Allah na naSa, yau ga ni red - handed a dakin Fahhima cikin tafin hanun ta, ina begging for shan minti ana ture niâ¦â?.
Anyway bazan gaji da cewa ba kin burge ni, da ko Ammi bata taba sabin zuciyar ki ba. I salute your courage.
Hannu ta sa ta toshe kunnuwanta tana fadin, âYaya Uwais ka fita ko in yi magana da karfi Amrah ta san kana nanâ?.
âDa kin hutar da ni, don kullum shirya yadda zan fada mata nake yi kwarin gwiwar na subucewa, musamman da na gane tana son ki sosai".
Daidai lokacin Amrah ta iso kwanar dakin Fahimah tana kiran sunansa.
Juyawa ya yi ya fita, ya bar Fahimah tana sakin murmushi, in wani ya ce mata Uwais ne wannan din da gudu za ta karyata ba don raâayal aini abubuwan ke faruwa a gabanta ba.
Lallai shi Allah mai canza alâamura ne zuwa duk yadda ya ga dama, kuma buwayi ne gagara misali, sannan ba abin da ya fi karfin ikonSa.
Ta kwanta a hankali rigigine bisa gadonta tana tariyo dan abin da ya faru tana ta blushing ita kadai, amma wani bangare na zuciyarta ya shiga fargaba, fargabar ya ya alâamura za su kasance when Amrah comes to know the bitter truth din da ba ta sani ba???
******
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ta rasa irin godiyar da za ta yi wa Ubangiji da ya mallaka mata soyayyar Uwais. Amma duk lokacin da Amrah ta fado mata a rai sai ta ji gabanta ya fadi. Ya Uwais ya yi babban kuskure da su duka ba ta san ya za su yi da consequence dinsa ba. Ammi da ma ta ce babu ruwanta, shi da ya boye shi zai warware, wanda ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Ita ba a boye ta yi hukuncinta ba.
A yanzu kam babu tsanar Amrah a ranta don ta yaba da halayenta. Ko mata hudu Uwais zai kara aure a cewarta ba ta da matsala da su, tunda Fahimah ce uwargida, karatun Amrah a wata kasa shi kadai yake ci mata rai.
A karshe kuma ta gode wa karatun na Amrah, don da ba don shi ba ba ta san ranar da Allah zai karkato da hankalin Uwais ga Fahimah ba.
******
Uwais ya sauka a kasar Switzerland lafiya, aka dauke su zuwa masaukin da aka tanadar musu. Thing are perfect ga hutu ga jin dadi, amma rashin iyalinsa ya sa ba ya jin dadin komai. Ita da ma Amrah ya daina sa ta a lissafi don ta gaya masa ya daina takura mata da kiran waya, da jidalallen cikinsa za ta ji mai tsirfar tsiya, ko da karatun da ke gabanta?
A lokacin da ta gaya masa hakan, ransa ya yi matukar baci, ba ta ma tsaya ba ta saurari abin da ya kira ta ya fada mata ba ta fadi hakan, dama ya kira ta su yi sallama ne a kan tafiyarsa Switzerland. Don haka sai kawai ya sauke wayar daga kunnensa ba tare da ya ce da ita komai ba. Yasa a ransa ba zai kara kiran ta ba har ya bar kasar Switzerland.
Kwanaki uku da yin hakan ta kira shi at her leisure time, shi kuma ya ki ya dauka. Sai ta turo text na ban hakuri da kalaman soyayya, ko kula ta bai yi ba, hankalinsa kacokam ya koma kan wadda ta ke da lokacinsa, wadda ita ko karatun ta ke yi ya kira ta za ta tsaya ta saurare shi, ita a kan karan kanta Fahimah tana kiransa idan kewarshi ta dame ta, wani abu da Amrah bata iya ba. Fahimah ta kan kira shi a lokacin da ta tabbata ya bar ofishin su na World bank zuwa masaukinsa.
A wannan dan tsukin Uwais ya tantance da abu guda, gara ka auri matar da ke matukar sonka, a kan ka auri wadda ka ke matukar so. Domin ita wadda ka ke matukar so, in ta gane za ta yi ta wahalar da kai ne.
Ita kuwa wadda ke matukar son ka, ko da daga baya ka zo ka kaunace ta da dukkan zuciyarka, ita a wurinta ka yi mata favour din ta ke kallonta as fortune. Probably zata yi hakuri da kai akan komai cikin kowanne hali. A typical example of Fahimah a gare shi.
Sannan duk abin da yake hangowa a Amrah, sai daga baya ya samu kyal-kyal banza ne, farar fata kam akwai ta da dogon gashi, sannan âyar babban gida ce, âyar manyan 'yan bokon kasa. Amma a mua'amala ta auratayya ya fi samun nutsuwa da satisfaction daga mara kyale-kyalen 'yar marainiya wato Fah-himah.
Su âyaâyan manyan mutanen sai mulki da iko da kansu. Ba kuma yadda za a yi da su. Cikin biyu ne ko daya; ko ka yi hakuri da su as they are ka nema wa kanka wata madafar, ko ka hakura da aurensu ba su da damuwa, domin suna hango wanda ya fi ka a komai. They may find thousands of you....
Wannan ya taimaka gaya wajen dusasar da tauraruwar Amrah daga zuciyar Uwais, ya dai saka a ransa ko me za ta yi masa ba zai sake ta ba. Don kuwa yana sonta har gobe. Amma zuciyarshi na kuna in ya tuna boko ya fi shi muhimmanci a wurin Amrah kuma za ta iya zabar karatun ta a kan aurensa.
*****
Fahimah, ta ci gaba da zuwa makaranta don bayan sun gama exams ba su samu hutu ba zarcewa suka yi da sabon zango. Tafiyar Uwais ta samar mata da nutsuwa domin a da kullum cikin damuwa ta ke da takunkumin Ammi a kansa duk da bata nunawa, wanda ya maida shi Uwais dinsa na baya mara walwala, mara kula kowa.
Zuwan Fahimah cikin rayuwarsa ya canza da yawa daga cikin odd behaviours dinsa, ya fara zama jovial har kafin Ammi ta sanya masa get da kebewa da Fahimah.
Ammi da kanta ta fahimci walwalar da Uwais ya shiga a baya na da nasaba da samun hadin kan Fahimah da ya yi a Sudan, sannan walwalar ta ragu, da ta ce sai ya gama gini, ya kuma gaya wa Amrah gaskiya, sannan zai sake mallakar Fahimah a matsayin matarsa. Ba ta regretting decision dinta, domin ta ga yadda Uwais ya maida hankali a kan gininsa da kuma irin kudin da yake kashe wa ginin ya tabbatar mata Fahimah ta samu kyakkyawan matsugunni a zuciyar Uwais.
Fahimah Shagari, dalibar tsimi da tanadi, ga ta da uwa farfesar tsumi da tanadi, idan suka dawo gida babu abin da Ammi ke yi sai koya wa Fahimah economics, assignment, test da statistics duka Fahimah ba ta da matsalarsu. Da aka yi jarrabawar zango na farko Fahimah 4.50 ta fito da shi.
A hakan ma sai da Associate Prof. Safeeyyah Shagari ta yi wa Fahimah korafi cewa tunanin Uwais ta ke, shi ya sa aka kada ita maki 50 daga cikin CGPA din ta, bata tunanin cewa shi yana can yana kara gina kansa? Zata zauna ta maida kanta baya a kansa.....
Fahimah sai ta yi murmushi kawai, don ita wannan makin ma da ta samu bata zaci za ta same shi ba. Da gaskiyar Ammi duk abinda ta fada ahaka yake. A kullum sallamarsu da Uwais ta ke tunawa which was so emotional; ya nuna mata kauna da soyayya mai tsayawa a zuci, mai kassara diya mace, wadda ta bar ta emotionally disturbed.
A haka watanni uku ke gangara musu da ci gaba da nasara a tare da kowannensu. Dukkansu are goal oriented musamman Amrah is very determined.
Wannan ya sa ta manta da mijin gabadaya, in har ba ta kalli zungureren cikinta bama ba ta tuno shi, shi ma ya yi banza da ita, don duk wata kulawa da yake so yana samu daga Fahimah cikin dare ta waya. Maganganun da Uwais ke wa Fahimah a waya na sanya ta a wani hali na tsananin kewarsa, ta ji ba abin da ta ke so irin ta bude ido ta ganshi tare da ita.
Amrah ta shiga edd dinta ana saura sati biyu Uwais ya dawo daga Switzerland, kuma an yi saâa lokacin suna gab da zana jarrabawa, don haka iyayenta cike da bacin rai suka ce ta taho Abuja, wata shekarar sai ta zana din. Ko kadan ba sa murna da wannan haihuwa ta Amrah ba ta cimma komai a rayuwa ba (a cewar Aunty Wasila).
âKe dabbar ina ce ki ka yarda ki ka dau ciki a wannan lokacin kamar wadda ba ta je makaranta ba?
Ba ki san dan contraception na zamani ba? Ai shi ke nan sai ki yi deferring karatun ki zauna kula da jaririn Uwais, ba ki ganki ba duk kin bi kin tsofe daga aure shekara dayaâ?.
In ji Aunty Wasila ranar da Amrah ta sauka a gidansu da ke Apo.
âHasbunallahu wa niâimal wakilâ?. In ji Jabeer da ke shigowa, âWasila, kina tsoron Allah kuwa? Kina son gamawa da duniya lafiya? Sunnar Annabin ki ke wa wadannan munanan maganganun haka? Ni dai wallahi Daddy ya cuce ku, kwata-kwata hanyar da ya nuna muku ta saba wa addini, da ba a yi auren ba a haife ku? Ko da an haifeku ba aure zaku so hakan? Zina ta yi ta samu cikin ko kuwa da kike mata wannan titsiyen?
To ahir dinki a kan dan Uwais, don wallahi a kan wannan cikin daga ke har Amran zai iya daure ku har sai igiya ta yi rara!".
Wasila ta zumbura baki daidai lokacin da Mamansu ta shigo. Ta ce, âAmrah me ki ke so a dafa miki?â?
Amrah wadda idonta ya cika da hawaye ta ce, âMama ki yi min tsakani da Aunty Wasila, cewa nake ita âyaâya uku gare ta? Ina ruwanta da cikina da za ta ce min dabba a kansa? Aure fa nake yi ba zina ba, ban ga dalilin da za a ce za'a bani query don an ganni da ciki baâ?.
Mama ta kyabe baki, ta ce, âmasu aure manya, ke ki ka ga za ki iya, da ma Daddy ya ce yaron nan ya gama da ke, in ba a yi wasa ba karatun likita sai dai a ga kannenki da shi ban da keâ?.
Amrah ta fashe da kuka, ta ce, ta fasa haihuwa a gidan kada ta haihu su bi dare su kashe mata da, ta fuskanci duk