Showing 45001 words to 48000 words out of 57616 words
Chapter 16 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
ya rungume ta. He then began to kiss her passionately, al'amarin da bai tuke a ko'ina ba sai a tsakiyar gadon barcin su. Hutun da bata samu ba kenan saidai wannan karon bata ji wahalar da tayi tsammani ba, ya tafiyar da komai gently cikin nutsuwa da soyayya.
Ba su suka tafi gidan su Ammi ba sai karfe biyar na yamma.
Ammi girki na musamman ta yi wa Fahimah da kanta, farfesun Zabuwa da ya sha kayan kamshin larabawan Sudan, sannan kunun kanwa mai yaji da zafin sa, ta sa ta a gaba ta ce sai ta shanye, kuma yanka daya ba za ta bari ba. Ba su kara ganin Uwais ba sai karfe tara na dare, don sun je Oumdurman gaida wani kakan Ammi.
Yana shigowa dakin da suke da sallama dauke a bakin sa bayan dawowar su daga Oumdurman. Fahimah ta kara mannewa ta lafe a jikin Ammi gabanta har lugulgude yake. Soyayya kam ta ci gidansu, bata marmarin komai yanzu banda isashshen barci, yanzu Uwaisun kam shi da dodo ba su da maraba a idon Fahimah.
Ammi ta ce, "Har an dawo? Ya ya ku ka baro mutanen Omdourman din?"
"Kowa lafiya Ammi duk suna gaishe ki, na gaji sosai Ammi, Oundurman akwai nisa".
Ammi ta dubi Fahimah da ta bingire a kasa tana barci. Ta ce,
"Ke kuma Fahimah barci haka kamar 'yar goye muna hirar mu yanzun nan?"
Uwais ya yi wani miskilin murmushi don ya san barcin karya ne Fahimah ke yi. Ammi ta soma bubbuga ta,
"Fahimah-Fahimah, tashi mana ku tafi?"
Fahimah ta tashi tana mutsittsikar ido da turo baki ta ce, "Ammi ni a nan zan kwana, wallahi Ammi ban iya takawa na gaji".
Uwais ya kanne ido guda a gaban Ammi, ya ce,
"Ba matsala, sai in dauke ki don dai zuwa mota?"
Kunya ta kama su daga ita har Ammin sai da ta yi da-na-sanin karyar ta, ya mike yana fadin, "Ammi bar abincin nan, mun ci a Oumdurman. Idon na fita kuma, zan sha fresh milk a Fundaq".
Ammi ta ce, "Tashi ku tafi Fahimah kin ji? Kin ga gobe za ku koma gida akwai bukatar ki tattaro kayan ki da kan ki, kada ya manta miki wani abu.
Amma Fahimah fir ta ki tashi, Ammi so ta ke Yaya Uwais ya karasa kashe ta da ranta, saboda cikin al'amarinsa babu daga kafa babu tausayi ko jin lallashi. Ammi ta kada ta raya amma Fahimah ta kafe abinda bata taba yi wa Ammi ba (musu) ta ce ita kam ta zo kenan, Nigeria ma ba ta komawa sai tare da Ammi. Ya dauko mata abinda zai iya ya bar ragowar.
Tausayi ya sa Ammi ta kyale ta, ta kira Uwais wanda har ya shiga mota ta ce su tafi su bar ta, ya taho mata da dukkan kayanta. Za ta lallaba ta gobe su koma gida tare. Bai ce komai ba amma ya hassala, ya ce da Mahdi ya ja motar su tafi.
Cikin daren kuma Ammi ta dauki lokaci tana nusar da Fahimah akan aure, ta ce, "Wannan shi ne ai auren Fahimah da manufar yin sa. Hakuri da juriya za ki sa a ranki, duk wata mace da ki ka gani da 'ya'yanta abin sha'awa sai dai ta yi wannan hakurin ta same su.
A hankali za ki saba kin ji ko Fahimah ta? Lada ne babba ki ke samu a wurin Ubangiji wanda zai miki silar shiga aljannah".
Sosai ta fahimci cewa cikin al'amarin Ammi Safeeyyah babu son kai ko son zuciya, face kauna zallah ta fisabilillah da ta ke mata, shi ya sa ta ke so mata rayuwa da gudan jininta mafi soyuwa a gare ta. Fahimah ta kwana addu'ar Allah ya ba ta lafiya, juriya da tsawon ran da za ta ci gaba da kulawa da bukatar gangar jikin Uwais, da komai nasa, har zuwa ranar da ta daina numfashi.
******
Washegari suka yi sallama da kowa, bayan Ammi ta tsuma 'yarta ta gyare ta tas da gyara irin nasu na Sudanese din asali. Jirgin karfe tara na safe suka biyo wanda zai sauka a Kano.
A cikin jirgi babu irin korafin da Fahimah ba ta sha daga Uwais ba a kan abin da ta yi masa jiya, har da cewa,
"Me ki ka dauke ni ne? Wanda bai iya rayuwa sai da ke ko me? Dana kwana nikadai me kika ga ya same ni? Karewa ma matata da na ke so ta dawo already, don ta bani kulawar da duk nake bukata. Don Allah Fah-himah ki jika abinki ki shanye".
Fahimah ba ta tanka shi ba, amma ji ta yi gaba daya hankalinta ya tashi. Idan da gaske Amrah ta dawo ita mene ne makomar rayuwarta?
Shin za ta iya sake barci a duniya ba tare da Uwais a gefenta ba? Ya sanya ta cikin wata sabuwar rayuwa mai wuyar bari da wuyar mantawa. Ta yarda ashe a can baya So kawai ta ke masa na fatar baki, yanzu ne ta san tana son Uwais har ruhi da bargon jikinta.
Idan kuwa abin da Ammi ta ce gaskiya ne (physical relationship between husband & wife). Alamu ne na so, kuma ba ya faruwa sai da soyayya ko yaya ne, to ta yarda Uwais yana sonta ko da bai furta a fatar bakinsa ba.
Ita kam ai yanzu kalmar kiyayyar Uwais ta daina razana ta, ta daina bakanta mata rai ko da zai kwana yana fadi akan mumbari ta bakin Ammi, domin kuwa har kakannin I love you Uwais ya gaya mata ba tare da ya san lokacin da ya fada din ba.
In haka ne ashe ita ma mutum ce, kuma mace mai daraja kamar kowacce mace duk da kalar fatar tata, ba za ta kara bar wa Amrah miji ita kadai ba.
Da Uwais ya ishe ta da mita da korafinsa da ya ki karewa sai ta tashi tsam ta bar masa wajen, ta koma can wata empty seat a cikin jirgin ta zauna. Tunda ya ambaci cewa Amrah ta dawo ta ji ko muryarsa ba ta son ji, kallonsa ma bacin rai yake sanya mata.
Ya so ya bi ta inda ta koma ya ci gaba da damunta da complain don kuwa ba da wasa ba ya azabtu a jiyan, ya ji haushin abinda tayi masa, yayi hakuri ne sabida Ammi, sai ya hango ta tana share hawaye, duk kuma sai jikinsa ya yi sanyi, domin ya fahimci ko me Fahimah ta ke wa kuka ba zai wuce RABUWAR SU ba tunda Amrah ta dawo.
To amma shin yana da guts na gaya wa Amrah yana da wani auren, auren ma na wadda ya taba kira âyar aikin gidansu? Ko kuwa shin zai iya jure rayuwa yanzu babu Fahimah? Tsakanin ita da Amrah wacece ta fi muhimmanci ga rayuwar sa?
Tambayoyi ne da ba shi da amsarsu, kuma bai san amsar tasu ba. Sannan bashi da mai amsa masa. Har jirgin su ya yi landing a Kano. A nan airport dama ya adana motarsa, ya je inda ya bada ajiyar ya dauka suka wuto gida.
Baba Talatu ce ta bude kofar falo tana musu sannu da zuwa, ta karbi kayayyakin hannunsu, Uwais ya wuce bangarensa, ita ma sai ta wuce nata dakin domin ta yi wanka ko ta warware gajiyar da ke nukurkusarta.
Kafin ta fito Baba Talatu ta shirya musu abinci a dining mai rai da motsi, wanda ta yi musamman domin tarbar su, sinasir ne da waina da miyar egusi wadda ta ji ganyen alayyahu da naman rago. Fahimah sai ta samu kanta da zama ta tsantsara kwalliya ta gani ta fada da kyakkyawar atamfa super Vlisco light blue. Wai aka ce in ba ka yi ba ni wuri, ba za ta kara bari a barta matsayin âyar jiran gida ba.
Uwais ya fito bayan magriba ya canza zuwa kananan kaya, bakar riga ce shirt a jikinsa samfurin Balanciaga da wando chinose, sumar nan ta sha wanki da arganavita ta kara baki sai sheki ta ke. Da Fahimah ta daga ido ta dube shi sai da tsigar jikinta gabadaya ta tashi. Da ta tuna duka wannan kwalliyar ta Amrah ce ba tata ba, sai bacin ran duniya da wani balaâeâen kishi suka zo suka lullube ta.
Uwais gab da ita ya ja kujera ya zauna, kafadunsu na gugar na juna, sanyin kamshin (Maison Francis) har cikin ruhinta. Ta lumshe ido sannan ta bude su a kanshi tana kallon sa da idanun rauni, jin yana take mata yatsun kafa da nashi yatsun. Ya ce,
âMadame, ya ya kin gama shiryawa? Yanzu za mu wuce faâ?.
Fahima ta zaro sparkling eyes dinta a kanshi cikin rashin fahimta, Uwais ya gyada kai cikin tabbatar mata.
âTare za mu tafi Fahimah, gidanki za ki koma!â?.
Sai ta ji tamkar an yi mata rahma, duk da bata da niyyar bin nasa, at least ya nuna yana son zama da ita koda bata bishi ba, tamkar ya yaye mata wani nannuyan dutse daga kirjin ta, duk wata damuwa da wani bacin rai sai ya kau. Ta ji kamar ta rungume Uwais, amma ta kwabi kanta da ta ja ajinta.
Girgiza kai ta yi, âBabu inda za ni Yaya Uwais babu sanin Ammiâ?.
Uwais ya juyo sosai ya sanya fuskar Fahimah cikin tafukansa biyu, ya sumbaci lebunanta keenly, skyblue kwalliyartacikin atampa ta yi mishi kyau ba dan kadan ba, ta kara fiddo da ainahin kalar fatarta mai kyau da ilhamar ta.
Ya ce, âIdan kuma Ammin ta dawo ta ce na barki ke kadai fa?â?
Da sauri ta ce, âBa komai, zan zauna, ai ga Baba Talatu ta dawoâ?.
âAre you sure za ki iya barci?â?
âSure, I wouldâ?.
Sai ga hawaye kuma sun zubo.
Uwais ya sanya babbar dan yatsansa ya lakato hawayen, ya ce,
âWannan fa na mene ne?â?
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Uwais ne a gaba, Fahimah na biye da shi a baya suka ratsa ta tsararrun falullukan Amrah, a falo na karshe ya ce ta zauna don yana kyautata zaton Amrah ta yi barci.
Amma da ya daga labulen bedroom dinta sai ya same ta tana sallah, wadda bai san ta nafila ce ko isha ce ba.
Ya zauna a gefen gadonta har ta idar. Tun tana sallar ya fahimci ta kai hannu ta toshe hanci, tsaki ya yi ya ce,
âAmrah why? Wai a kanki aka fara ciki ne? ko ko naki ne ya fi na kowa tsurfa?â?
Ta sallame sallarta tana kallonshi cikin haushi, ya je ya dade ya yi dare son ransa kuma ya zo yana mata zancen wofi, zuciyar mai ciki da ma a kusa ta ke, ta ce,
âDon Allah fita min a nan Uwais, da kai da gallababben turarenkaâ?.
Yau Uwais din tsura ta fada not Habiby ko Habib-Qalby, ya ce, âTo kin sa na dauko âyar Ammi ko in maida ta ne?â?
Da sauri ta mike tana fadin, âAi ban san tare ku ke ba, ba ka yi min bayani baâ?.
Suka tadda Fahimah a inda ya barta, Amrah da faraâa sosai ta ke mata barka da zuwa, ta dauki jakar kayanta ta ce, âHabiby ya ya sunanta?â?
Irin kallon da ya yi wa Fahimah ya sa ba shiri ta sunkuyar da kanta. Ya ce, âTambaye ta mana? Ai tana jinkiâ?.
Murmushi Fahimah ta yi ta dubi Amrah wadda a take ta ji Allah ya dauke mata kishin Amrah da ke ranta. Ta ce, âSunana Fahimah. Wasu kuma kan ce, Fah-himahâ? (tana nufin Uwais, shi ne mai kiranta da Fah-himah)â?.
âNi ma Fah-himah zan ce, yafi dadi, Fahhimah please taso mu je in raka ki dakin da na ware miki tun safe. Ki kwanta ki hutaâ?.
Fahimah ta mike ta bi bayan ta. Uwais ya bi su da kallo admiringly a zuciyarsa kuma yana taraddadin ranar da gaskiya za ta bayyana ga Amrah, duk sunan da ta kira shi da shi a lokacin daidai ne. Makaryaci? Mahaâinci, mayaudari ko maciyin amanar soyayyah? Heâs ready to face and accept all the names in dai a karshe za ta yi hakuri su hada kai su yi rayuwa mai albarka su ukun.
Amrah will never be enough for him shi ya sani, duk da cewa har gobe ita ce zabin zuciyarsa, muhallin da kowacce ke da shi a yanzu cikin ransa daban ne da na âyar uwarta; duka yana son abinsa, kowacce da bigiren da ta cike cikin zuciya, ruhi da gangar jikinsa.
Amma Fahimah na da wani extra matsayin a zuciyarsa wanda ya wuce soyayyahâ? wanda sexual bond ke karawa tsakanin miji da mata, sama da wannan ita din abin so ce ga mahaifiyarsa da ba ya hada ta da kowa a duniya sannan ta zama wani babban bangare na barin jikinsaâ? abin nufi, a ita ne yake samun nutsuwar da duk da namiji ke son samu a diya mace. Yayin da Amrah har gobe take a matsayin MATAR SO ta likawa a goshi.
Ya yi kokarin ya daidaita matsayin kowacce da na âyar uwarta cikin zuciyarsa a daren yau, sai ya ga cewa daidaiton bai yiwuwa, domin ratar da ke a tsakani mai tsananin fadi da girma ce da ta shallake tunaninsaâ?....Ashe namiji kan iya son wata a lokaci guda, sama da first love dinsa???
Amrah na can tana sharar barci ta yi daidai a kan gado ta baro Uwais kamar marayan da ya rasa uwa don ta roke shi kada ya zo inda ta ke in ba so yake ta amayar da âyan hanjinta ba.
Uwais ya mike tsam yana daure igiyar pajamas din shi cikin ransa yake fadin,
âAna me? Ni ba aminin gwauro ba?"
Dakin Fahimah ya nufa bayan ya leka Amrah ya tabbatar ta yi nisa a barcinta.
Kamar Fahimah ta san haka za ta faru don ta gama gane Uwaisun nasu cikin dan lokaci kalilan, kunya bata ishe shi ba a wannan fannin kam, zai iya janyo mata abin kunya wajen wadda ta dauke ta 'yar uwa, don haka tun sanda zata kwanta ta rufe kofarta ta ciki da key ta kuma barshi a jiki ta yadda ko ya sa nasa ba zai shiga ba.
Ya murda kofar sai ya ji ta gam-gam, wato ya ji ta a rufe, sai ya soma kiranta a matukar tausashe.
âFah-himah, bude min kofar mana, ni ne Uwaisâ?.
Fahimah da ke bisa darduma tana sallolin nafilah don gusar da birbishin kishin da ya cika zuciyarta ta yi sallama, sannan ta matsa jikin kofar cikin damuwa ta ce,
âWani abu ka ke so Ya Uwais?â?
âKi bude na ce, ko ma me ye sai ki jiâ?.
âGaskiya ba zan bude ba Ya Uwais". Ransa ba karamin baci ya yi ba, kuma yana tsoron ya daga murya Amrah ta tashi don haka ya sassauta murya ya ce,
âPlease Fahhimahâ? Iâm begging you in the name of Allahâ?...â?.
Muryar Uwais dake raurawa har cikin tsokar zuciyarta, yadda muryar ke raurawa haka zuciyar ta ke raurawa, weakness na wanda kake so ba karamin rauni bane a gareka, amma ta gwammace ta tsaya a kan gaskiya da adalci, in ita aka yi wa haka ya ya za ta ji? Amrah ba ta san da komai a tsakaninsu ba, sai kokarin kyautata mata ta ke da zuciyarta daya. Ta dauketa kamar kanwar Uwais da ta kawo mata ziyara. Amma sai ta saka mata da dauke Uwais a cikin dakin ta?
âYaya Uwais ka yi hakuri ba fa zan bude ba. Don ban ga abin da ka ke so a nan baâ?..â?.
Muryarsa wani iri don tsananin bacin rai, ya ce, âFah-himah...., amma saboda takaici sai ya kasa karasawa, ya juya ya bar wurin. Dakin Amrah ya koma yana fadin yau sai dai turarensa ya sumar da Amrah in ma suman za ta yi.
Fahimah ba ta san ya suka kare shi da matarsa ba, da asubah Amrah ta hau buga mata kofa, da Fahimah ta ji muryarta sai ta bude, Amrah ta fado dakin tana ajiyar zuciya, at last she escaped! Smell din da bata so. Sannan ta zauna a gefen gadon da Fahimah ta tashi, ta ce,
âZan kwanta a nan don Allah, bana son turaren Habiby, shi kuma ya ki fahimtata ya nisance ni ba da gangan nake yi baâ?".
Ta yi ajiyar zuciya abin tausayi, sannan ta dubi Fahimah cikin rauni "kin huta da ba'a yi miki aure ba Fahhimah, aure takura ne, nauyi ne, jidali ne wallahi ina da na sanin yinsaâ¦â?.
Fahimah ta ce, âKul! Amrah ki daina fadin haka, domin aure umarnin Ubangiji ne kuma sunnar Annabi SAW ne. Ya kuma ce wanda ba ya son sunna ta, to ba ya tare da niâ?.
Amrah ta ce, âAstagfirullahâ? wa'a tubu ilaih, amma duk bayanin da zan miki bazaki gane ba tunda baki da aure, my husband mai yawan takurawa ne, yayin da ni nake tsaa-tsaki, sannan ina fama da kaina, amma ya kasa daga mun kafa ya bar ni in sarara ko kadan.
Yanzu kam na yarda gara ya kara aure, Fah-himah I so much like you, in da aure tsakanin ki da Habiby don Allah ki taimake ni ki aure shi... tafiyarmu ni da shi ba za ta yi tsayi ba in aka cigaba a hakaâ?...don bani da isashshen lokacin sa, yanzu haka na baro komai dake gabana na taho tun daga Malaysia don in ba shi lokacina amma na kasa faranta masa da komai, tunda na zo lafiyata ta ki daidaito.
Shi kuma ya kasa daga min kafa, jiya fada muka yi baram-baram ko barcin kirki yau ban iya na yi baâ¦â?.
Fahimah ta rungumo Amrah a jikinta cikin lallashi, ta ce, âKi yi hakuri Amrah, marriage is not a bed of roses kuma duk soyayya sai ana samun misunderstandingsâ? amma Yaya Uwais is a nice person, duk da ba ni da experience a kan aure na san abubuwan da ki ke fama da su lalurorin karamin ciki ne kawai, da zarar kin samu lafiya ko kusa bazaki so kowa ya rabi Uwaisun ki ba, balle kiyiwa kan ki fatan ya kara aure, kuma insha Allah zai wuce, da zarar cikinki ya yi kwariâ?.
Ta yi shiru sannan cikin murmushi, ta ce.
âAmrah ki ke so ko in ce ki ke fatan wata ta auri Uwais? Ba kya tsoron ta kwace miki shi ne? Ki bar