Showing 51001 words to 54000 words out of 57616 words
Chapter 18 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
ba sa son Uwais ita kuma tana son kayanta.
Mama ta ce, âKi fi ruwa tafiya, muna nan za ki dawo mana in dai namiji ne. Namijin ma irin wannan kallelen mai idanu a tsakar ka, daga ganinshi womaniser neâ?...â?.
Amrah hannu ta sa ta toshe kunnuwanta, ta rasa me Uwais ya yi musu haka, daga Yaya Jabeer sai Aunty Murjanatu ke kaunar aurenta, amma a ce har uwar da ta haife ka?!
Womaniser! Kalmar tayi tsauri da yawa a alaqantata da mutum mai daraja da mutumci irin Uwaiss.
Wannan bakin cikin ya sa washegari ta tattara kayanta sai Kano. Ga shi tana cikin EDD bai kamata ta yi doguwar tafiya ba, amma da ta haihu a gidansu ta gwammace ta haihu a hanya, babu mai taba mata Uwais ta kyale.
Ko da Daddy ya dawo Mama ta gaya masa Amrah ta yi fushi ta tafi, ta fasa haihuwa a gabansu don kawai Wasila ta gaya mata gaskiya, ta kwashe duk yadda aka yi ta gaya masa.
Daddy a take ya dau waya ya kira Amrah, lokacin suna gab da shiga Kano ita da direban gidan su. Ya ce, âAmrah?â?
Ta ce, âNaâam Daddyâ?.
Ya ce, âkada ki sake in kara ganin kafarki a gidana, in kin haihu kuma babu wanda zai zo ki je ga ki dangin miji su yi miki komai da uwarki zata yi miki, ga da namiji nan don soyayya ku wuce Indiaâ?.
Amrah ta bude baki za ta yi bayani, Daddy ya ce, âBana son jin komai, tunda duk abin da muke hango miki ba kya hangowa, weâre talking of your future which is ruined nowâ¦â?.
Kuka Amrah ta fara tana ba shi hakuri da kyar ya hakura, amma ya ce ba za ta haihu masa a gida ba. Amrah ta ce,
âNa ji na yarda, amma don Allah ka yi hakuriâ?.
Ya kashe wayar ya rabu da ita.
Jiki a sanyaye ta isa Kano, sai ta rasa ina za ta dosa, ba ta iya zama gidan ba Uwais, don haka ta ce da direba ya wuce da ita âYankaba.
Ammi da Fahimah na zaune suna karatu a falo, assignment na Fahimah suke solving. Ammi na nuna mata. Sai sallamar Amrah suka ji ta shigo tinkis-tinkis da tirtsetsen cikinta.
Gaba daya suka hada baki wajen cewa, âMaraba da mutanen Malaysiaâ?.
Talatu ta shigo da jakar kayanta, wadda Maigadi ya shigo da ita. Fahimah ta karba sai ta wuce da ita nata dakin. Ammi babu sakewa sosai tsakaninta da Amrah don haka gaisawa kawai suka yi, da tambayar bayan rabo. Fahimah kuwa tuni ta tafi kitchen don hado mata abinci da abin sha.
Har dare Amrah na zuba idon ganin ta inda Uwais zai bullo su wuce gida, amma shiru ka ke ji har karfe goma. Fahimah sai hidima ta ke da ita, dauko wannan miko wannan, da ta ga ta fara hamma daga zaune ta ce,
âAunty Amrah ko za ki shiga daga ciki ki kwanta?â?
Ganin idon Ammi ya sa Amrah ba ta furta damuwarta ta rashin ganin Uwais ba, ta bi shawarar Fahimah, domin sosai take son kwanciyar, suka yi sai da safe da Ammi, sannan ta bi bayan Fahimah zuwa dakinta.
Fahimah tuni ta gyara mata gadonta, ta ce ta kwanta a gadon don ta fi jin dadi ita a kan lallausar bargo da ta shimfida a kasa za ta kwana.
A lokacin ne Amrah ta tambaye ta ko Uwais sai karfe nawa yake shigowa?
Fahimah ta juyo tana kallonta da mamaki, ta kasa cewa komai. Ita ce za ta gaya mata mijinta bai kasar? Abu wajen watanni biyu? To ba sa waya ne?
A karshe ta ce,
âNa ji Ammi ta ce, yana Switzerlandâ?.
Amrah ta zaro ido cikin kidima, Fahimah ba ta bi ta kanta ba ta ci gaba da shirin kwanciyarta.
Wajen sha biyun dare Amrah tana barci wayar Uwais ta shigo wayar Fahima, kuma wayar tana kan bedside daidai inda kan Amrah ke kwance. Hasken wayar ne ya dame ta ta dauka don ta mika wa Fahimah don da alama ta yi barci, amma hoton da ya fito kan fuskar wayar ya sa ta mamaki hadi da bayyanar lambobin da daga gani ka san na kasar Switzerland ne.
Abu biyu ya sa Amrah jin gara kawai ta amsa wayar nan. Don hankalinta ya kasa tsayawa waje guda. Dalilin Fahimah na dora hoton Uwais a kan lambarsa, da irin tune din da kiran ke bayarwa, sannan uwa-uba wane Yaya ne zai kira âyar uwarsa late at night haka? Lokaci ne na masoya da ma'aurata bana âyan uwa ba.
Kawai sai ta amsa wayar ba tare da ta ce komai ba. She just want to confirm it's Uwais ko ta samu nutsuwa.
Muryar Uwais tar-tar cikin yanayin da ke nuna akwai marital intimacy (sexual bond) ya ce, âFahhima na kasa barci, wallahi hakuri na ya kare. Jiya saura kadan in maimaita irin laifina na Sudan, na ji tsoron Allah na ji tsoron fushin ki, musamman da na tuna tsiwar da ki ka yi min a ranar da tsanar dana gani cikin kwayar idon ki, na ce gara in rufawa kaina asiri in kashe ko nawa ne in miki ticket da visa ki zo min ko na kwana uku ne don Allah Fah-himah kada ki ce min a'ah, Iâm missing everything, the luscious and succulent lips, your sweet...â? kalmar karshe da ya fadi ya sa Amrah gigicewa don ko ni ban iya rubutata, wani karfin gwiwa ya zo mata.
A nitse ta ce, âBa FAHHIMAH ba ce, AMRAH ceâ¦â?. Sannan ta kashe wayar silently.
Ta koma ta jingina bayanta a jikin gadon. Abin da ta kasa tantancewa shi ne, da ma tuntuni zaman miji da mata suke yi, ko kuwa farkarsa ce tuntuni suke blackmailing dinta? Ko kuwa Uwais extra-marital affair yake having da âyar rikon gidansu???
Ko da ta ce Fahimah ta auri Uwais, wallahi duk cikin lalurar yaron ciki ne, saboda a lokacin burinta kawai Uwais ya daina kusantarta, don ta daina jin qamshin (Maison Francis). Amma daga baya bayan ta samu ingantacciyar lafiya komawa ta yi tana cewa, âAllah ya sa ban fada da bakin malaâiku baâ?.
âNi Amrah....Amrah Umar Dikko, ni Uwais ya yi wa haka???â?
Hawaye suka soma sintiri a kan fuskarta kafin wani azababben ciwon mara ya zo ya turnike ta. Salati ta shiga yi tana juyi don ba ta san nakuda ba, amma wannan ciwon da ta ke ji yau ta tabbata nakuda ce, amma da ta haihu a hannun farkar mijinta gara ta koma Abuja ko da da rarrafe ne.........
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Washegari Amrah ta wuce Malaysia, da ma sati biyu za ta yi. Satin biyu ma cikin lokacin karatunta ne, ta yanke komai ne don ta samu ta gyara tsakaninta da Uwais, kuma ta samu ta gyara dan kadan ko ba duka ba duk da bai samu wata kulawa a tare da ita ba saboda lalura iri-iri na cikinta.
A daren ranar bayan tashin Amrah daga airport gidan Ammi ya taho. Ammi da Fahimah suna zaune a falo suna kallon shirin Arewa24 Uwais ya yi sallama, hannayensa duka biyun zube cikin aljihu. Idanunsa straight a saitin Fahimah wadda daga amsa sallamarshi ta mike. Ta ba su wuri shi da Amminsa. Ba ta yarda ta kalli Uwais cikin ido ba sabida Ammi, kuma dai ba ta hango komai a tare da shi sai tsagwaron rigima yau, tunda ya koma gwauronsa kamar da.
Ammi ta amsa mishi, ya zauna suna kara gaisawa, ta ce, âYan Malaysia an tashi kenan?â?
Ya ce, âEh Ammi ta tashi yanzuâ?.
Sannan ya sunkuyar da kai cikin jin nauyin abin da zai fada.
âAmmi na zo ne tafiya da Fahhima, sai ta zauna gidan Amrah kafin a karasa nata ginin. Ammi kin ce duk ranar da na shirya karbar aurena da Fahimah da hannu bibbiyu ranar ne za ki ba ni ita.
Yau ga ni da kokon barana Ammi, gwiwa a kasa, ki yi min alfarma ki ba ni Fah-himahâ?.
Haj. Safeeyah ta gyara zamanta tana kallonshi sosai, kamar mai son hango reality na maganganunsa cikin kwarar idanunsa. Daga bisani ta ce,
âUwais, ka gaya wa matarka cewa kana auren Fahimah?â?
Ya girgiza kai, ya ce, âAâah tukunna Ammi, sabida na ga tana gidan, kuma Amrah ba ta gama samun karfin jikinta baâ?.
Ammi ta yi wani miskilin murmushi, ta ce, âTo ba da ni za a yi aikin rashin gaskiya ba, kuma Fahimah ba za ta je gidan matarka da kayanta a ciki da iyayenta suka zuba mata ta yi zaman aure ba.
Har sai ranar da ka zaunar da ita ka gaya mata cewa tare aka daura aurenta da na Fahimah, sannan ka kammala wa Fahimah ginin gidanta ita kadai, don ba za su zauna tare ba. Sannan zan yarda ta tare.
Duk wannan âyar dadin da ka ga suna yi, ina tabbatar maka don Amrah ba ta sani ba ne, da tuni komai ya rushe. Don haka ka je ka gama da wadannan matsalolin na gabanka kafin ka zo gabana da neman daukar matarka.
Sannan Uwais, na hana ka shiga dakin Fahimah daga rana irin ta yau, daga lokaci irin na yau, sai kun koma gidanku, don ni ba tsohuwar banza ba ce, da za ka dinga binta daki a gabanaâ?.
"Yau dai Ammi tsagwaron mugunta ta ke ji!â?.
Uwais ya fada a ransa, gumi na karyo masa ta kowacce kafa mai fitar da gumi a jikin dan adam. Gini kam ya yi nisa amma bai karasa ba ai. Amrah kuma in ba ta waya ake so ya gaya mata ba, cikinsa ya zube bai san ta hanyar da Ammi ke so ya je ya gaya matan ba.
Ya shirya a ransa ne sai ta dawo wannan hutun, nan da watanni hudu, lokacin cikinta ya kusa isa haihuwa.
Ya share gumin da ke faman tsatstsafo masa a goshi. Da dai Ammi zata bari sai gobe ta sa masa wannan takunkumin. Yau ta barshi yayi sallama da matar sa. Yau sati biyu kenan rabon shi da Fahhimah.....Fahhimar da ta zo ta canza akalar rayuwar shi gabadaya ta juya ragamar ta cikin dan lokaci kalilan, gaskiyar magana a yanzu bai iya rayuwa ba tare da ita ba!!!
âAmmi, duk abin da ki ka lissafa zan yi. Amma ki yi hakuri sai Amrah ta dawo hutu. Yanzu zan maida hankali a kan ginin, ki taya ni adduâa Allah ya hore in gama shi cikin dan lokaciâ?.
Yana gama fadin haka ya mike zai fice ko ganin gabansa ba ya yi, imagining yadda zai karar da daren yau babu Fahhimah, bayan har Allah-Allah yake Amrah ta koma ya samu wannan damar, don kuwa ba ta amfana masa komai tun zuwanta sai tsurfa da korafi irin na masu juna biyu. Na Amrah har da karin sangarta a ganinsa, kamar a kanta aka soma ciki. Allah kadai ya san iya burin da ya ciwa daren yau.
Don haka washegari ya bude wuta a kan ginin Fahimah kamar zai shiga ayi da shi, wanda ake yi a Unguwar Sulaiman Crescent. Ya bai wa maâaikatan watanni biyu su kammala komai. Komai da ke account dinsa ya tafi ya shige cikin aikin ginin don so yake a yi mata komai kamar na Amrah.
Ammi zuciyarta kal! Ganin yadda Uwais ya gigice da hukuncin ta. Burinta ta saya wa Fahimah martaba kamar kowacce mace a gidan miji, in ta ci gaba da barinsa yana zuwa yana rage dare ba zai maida hankali ga muhimman alâamuran ba, gini da sanar da matarsa gaskiyar magana. Ita ba girmanta bane wannan boye-boyen da yake wa Amrah. Gara ayi ta ta kare.
*****
Fahimah ta ci gaba da zuwa makaranta tare da Ammi, Uwais sabida haushin Ammi ta ce ba zai kara kebewa da Fahimah ba yanzu sai ya yi kwanaki uku bai zo gidan ba. In ya zo kuma ba ya zama, abinci kawai yake ci ya tafi, in Fahimah na zaune a falon su gaisa yana faman kawar da kai, in ba ta falon ba ya nemanta.
Hakan ya fi komai sauki ga Fahimah don karatunsu ya fara zafi, sai ta maida hankali ga karatu sosai, da tukin mota da Ammi ke koya mata da yamma don ta ce ta fasa na Uwais din, don zai iya amfani da damar ya karya umarninta. Don haka ta zage tana koya wa Fahimah tukin da kanta at her leisure time.
Allah cikin ikonsa kuma da yake ya sa pressure sosai cikin watanni biyu ginin gidan Fahimah ya kammala, har fenti da komai an gama.
A ranar da yake shirin gaya wa Ammi, ya samu takarda daga babban bankinsu na kasancewarsa cikin wadanda banki ya zaba ya tura kasar Switzerland yin wani muhimmin course da World Bank.
Abun farin ciki ne a gare shi domin in ya dawo karin matsayi zai samu, amma da ya tuna tafiyar na nufin nesanta shi da Fahimar da yake ganin ya kusa samu, sai duk murnar sa ta koma ciki.
Yaji kadaicin duniya da damuwar duniya sun lullubeshi kamar shikadai ya saura a fadin duniya.
Na farko dai ba a ba su damar daukar iyali ba, na biyu ko an ba su Fahimah ba za ta samu binsa ba domin tana gab da zana jarrabawarta ta karshen zango. Kwas din na watanni uku ne, kuma su goma kadai suka samu wannan babbar alfarmar. Za su tashi da zarar visa dinsu ta kammala.
A ranar ya zo ya gaya wa Ammi, maimakon ta ga yana murna ta fahimci jikinsa a sanyaye yake. Kuma cikin matukar damuwa yake. Ammi is over-excited domin da ma akwai kyakkyawan shiri da ta ke son yi wa Fahimah wanda a baya ba ta yi mata sosai ba. Gara-gara ma a Sudan ta dan karba ta bata a wajen matar Mahdi. Tafiyarshi zai ba ta damar yin komai a nitse, in ya so da ya dawo sai su koma gidansu.
Ammi ta ce, âWannan ai abun farin ciki ne Uwais, tunda ci gaba ne ta fannin aiki. Allah ya tsare Ya bada nasara. Ita ma Fahimah jarabawa za ta yi, don haka in ka dawo sai ku wuce gidan ku insha Allahâ?.
Sallamar Fahimah da Uwais ta kasance a wani dare na litinin, bayan ya dawo aiki ya zarto gidan, ana i-gobe zai tashi zuwa kasar Switzerland. A kalla ya shafe kwanaki masu yawa bai sanya Fahimah a idanunsa ba, kuma bai neme ta ba, don Ammi gasa shi ta ke ba da wasa ba. In taga lokacin zuwansa ya kusa sai ta tashi Fahimah daga falon ta sata wani aikin. Ita kuma ta kasa ta tsare a falon taki zuwa ko nan da can.
Sun yi sallama da Ammi har zai wuce ba tare da ya tambaye ta Fahimah ba. Ransa a cumkushe. A zuciyarsa yana fadin,
âAmmi ga âyarki nan gabadaya na bar miki har wata uku, sai ki yi ta kullewa a daki. Tunda dai duk kawaici na ba a gani baâ?.
Shi kadai ya san halin da yake kasancewa a ciki duk daren Allah a gidansa ba Amrah ba Fahhimah, kuma ya yanke shawarar kin kiran Fahimah a waya har sai ranar da suka gama masa gashin kumar ita da Ammin ta, don ita ma ta biye wa Ammi ba ta nemansa, ta durfafi karatun makarantar ta, ba ji ba gani.
Amrah ko ko ya kira ta ma yanzu ba ta iya doguwar hira barci zai yi awon gaba da ita. Ko ta ce masa ita karatu ta ke yi ya bari gobe za ta kira shi, sanda ta ke free din, shi kuma yana ofis yana fama da ayyukansa. Don haka in ka ga Uwais a dan tsukin nan har ramewa ya yi, ya fada sosai, ga kasumba ta taru ya ki ya aske ta. Sosai yake ragaita a zuci da gangar jiki.
Bayan sun yi sallama da Ammi zai wuce, sai cewa ta yi.
âBa za ka shiga ku yi sallama da Fahimah ba?â?
Idanun Uwais suka kifta kadan, ta wani fannin tamkar wanda aka aikowa da manzon Rahma, wani kuzari ya da rabon sa da irin shi tun ranar da ya zo daukar Fahimah su tare a gidan sa amma ta gwale shi da takunkumin ta, ya ce,
âAmmi kin yi izni?â?
Da murmushi a bakin Ammi ta ce, âNa yi izni Uwais, ko da ma can ai ban hana ku gaisawa ba a waya ko a falon nan. Na fi so ne dai ta tare a dakinta, sannan ku je ku karata. Amma sallama ai ta zama doleâ?.
Tana gama fadin haka ta wuce zuwa dakinta, ta ce da Uwais, âSaduwar alkhiriâ?.
Ammi na bada baya Uwais ya juya dakin Fahimah da takunsa na sassarfa.
Tana kwance tsakiyar gadonta ta rufe kanta da pillow, amma ba barci ta ke ba, tunanin Uwais ta ke yi da tsawon lokacin da suka dauka ba tare da juna ba alhalin suna gida daya, kuma suna jin muryar juna sau tari cikin gidan, sannan su kan ga juna jefi-jefi.
Ba ta san dalilin Ammi na nesanta su da juna har haka ba, amma ta yarda komai Ammi za ta yi akan su, to za ta yi ne for her own betterment. Itama ta fi yarda Amrah ta san me suke ciki in ya so komai ta fanjama-fanjam, kuma tana bayan Ammi na ba za ta shigar wa Amrah gida ba don ba ta nan.
Da murda kofarsa da sallamarsa ciki-ciki duka ba ta ji su ba. Sai kwanciyarsa a gadon bayanta. Ya sakar mata dukkan nauyin sa. An ce duk nauyin miji mace na dauke shi tsaf ba tare da ta ji nauyin ba ita. Amma Fahimah har âyar kara ta saki sabida nauyin Uwais. Dadi da cewa ba ta tsammaci zuwansa a lokacin ba don ba ta san da tafiyar da ke gabansa ba.
Daga haka Uwais ya canza akalar komai zuwa irin wadda ya fi so a rayuwarsa (romansiyya), wato kasancewa tare da Fahimah cikin nauâikan soyayya irin nasa mai keta zuciya da ruhin Fahimah. Alâamuran da suka biyo baya masu tsauri ne kwarai a tarihin rayuwar auren su. Sai da dukkansu suka samu nutsuwar da suke bukata, Uwais ya maida sittirunsa ya rike Fahimah cikin hannayensa, fuskarta cikin tafukansa.
âIâm going to Geneva Fah-himah, sai bayan watanni uku zan dawo. It will not be easy kin sani. Amma as a man dole in je in nemo muku abinci. Ki kula min da kanki. I will surely miss you and everything