Showing 27001 words to 30000 words out of 57616 words

Chapter 10 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt

bar mata kicin din. Ko ta samu ta saita bugun zuciyar ta. Kada tayi abind ta saba yi a gaban sa.
Tsayuwarsa a wurin na maida ita unease, jikinta ya ki sakewa ya yi aiki yadda ya kamata. Kamar wadda ke cikin sanyin kankara a dalilin kasancewar sa a wurin tare da ita. Daurewa kawai take yi don tsira da determination din ta akan Uwais Shagari.
Amma ga mamakinta Uwais ya ki tafiya, karewa ma shigowa ya yi kitchen din ya haye kan island ya yi zamansa. So yake ya gargasa mata magana ko yaya ne kafin ya yarda ya dauketa su tafi, wadda har ta koma ga mahaliccinta ba za ta mance ba ya sonta ba.
"Yanzu ke kin yarda Ammi ta rusa miki rayuwa da mijin da ba ya sonki, bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba? Me ya sa ba ki yi wata hobbasa don kwatar wa kanki ‘yanci ba? Ba ki da masaniyar ina da mata ne, wadda nake matukar so kamar na ba ta raina?â€?
Tunda ya fara maganar Fahimah ba ta dago ba, firar dankali ta ke, amma da ya zo sentence dinsa na karshe sai ji ta yi ta tafi da tsokar hannunta, wato ta yanke hannunta da kakkaifar wukar da ke hannunta.
“Ina da matar da nake so, kamar na ba ta rainaâ€?.
Wani statement ne wanda shi a wurinsa ba komai ba. Amma a gare ta tamkar digar ruwan dalma ne a kan fatar jikinta. Tana so ta ba shi amsa, daidai da wadda ta dace da munanan maganganunsa sai ta tuna UWAIS ne. Wani kwayan mutum guda daya da zuciya da ruhinta ke so, wanda ta yi wa kanta alkawarin zama da shi da kasancewa tare da shi against all odds koda zai yi ta yankar tsokar naman jikin ta yana sanyawa a miya albarkacin Ammi Safeeyyah - Basudaniyyah. Balle common bakar magana akan matar da yake so.
Sai ta saki wukar da ke hannunta kasa, hade da dankalin ganin jini yana fita. Ta kudire ko dukanta Uwais zai yi cikin gidannan ba za ta soya masa dankalin nan ba, ko dai ya tafi da yunwarsa, ko ya kirawo matar da zai iya bai wa rai ta soya masa daga Malaysia.
Ta kashe komai ta wuce ta gabansa hannun ta nan digar jini ba tare da ta ce da shi komai ba. Murmushin mugunta ya yi, ko ba komai ya ci nasara, ya yi spoiling mood dinta ita ga amarya zata bi miji Ikko, ta samu miji a bagas sabida ba Amrah, kuma gashi ya janyo ta yanke hannu. Sai yaji bai ji dadi ba daga kasan ransa saboda ko kadan ba ya son ganin jini ko yaya daga jikin dan Adam. Don haka ya sauya shawara ya bi bayanta zuwa dakinta ba tare da ta san ya biyo ta ba.


Toilet ta shige ta sakar wa hannun famfo a sink, tana kalon jinin jikin ta na gudu treda ruwan tana hawaye, sai jin motsin mutum ta yi daga bayanta. Da sauri ta juya a tsorace, ashe har ya iso gab da ita sai da ta bigi kirjinsa. Da sauri ta ja baya. Dan farin bandeji ne a hannunsa na nade ciwo da ruwan hydrogen, daya dauko a dakin Ammi, sabida bata wasa da first aid ita, ba tare da ya ce komai ba ya kama yatsan ya zuba hydrogen a kan yankan, sannan ya soma kokarin daurewa da bandejin.
Fahimah, ta kusa suma a wannan lokacin sabida kyakkyawan closeness din da ya shiga tsakanin ta da Uwais. Wanda hakan bai taba faruwa ba koda da kuskure. Ita da Uwais sai kallo daga nesa. Wani irin sassanyar kamshi yake yi na Maison Francis (Baccarat Rouge) dake tashi a hankali daga jikin sa. Shi kuwa Uwais bai yi don wata manufa ba, sai don tunawa da ya yi da kalaman Ammi.
“Fahimah amanar Allah ce tsakaninmu Uwaisâ€? na ba ka amanartaâ€? idan ka cutar da ita kai da Allah…â€?.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ita in wani ne ya gaya mata a baya cewa Uwais na magana haka ma, ba za ta taba yarda ba. He is not that miskili to such an extent kamar yadda ta dauka a baya, kawai dai magana sai ya ga damar yin ta, kuma in ya so yana yin abar sa sosai ko da bazaka bashi amsa ba. Uwais Shagari, ya fara sassauta wa ransa kiyayyar Fahima a bisa dalilai da dama.....
Muhimmi shi ne, ganewa da ya yi ita din is a source of geniune happiness na mahaifiyar sa wadda in ya zauna da ita ko da ba ya kyautata mata in disguise Ammi za ta yi ta farin ciki da shi ne, tareda sanya masa albarka.
Sannan auren su wani abu ne inevitable (wanda ba makawar sa) wanda bazai iya tsallakewa ba, watakila har abada, don ba zai taba iya mikawa Ammi takardar saki ko ta wata mace daban, balle wannan wadda take so kamar ita ta haifa ba.
In haka ne kenan takurawa rai da kiyayyar da babu riba a cikin ta aikin banza ne.
Zai zauna da Fahimah koda har abada ba zaya so ta ba. Sai ta zauna zaman Ladan Noma (as he called it). Tunda haka Ammi ta zaba mata.
A kullum yana tuna dawainiyar da Ammi ta yi da shi tun yana yaro, da dawainiyar ilminsa a bayan ran mahaifinsa ba tare da taimakon kowa ba. Ita ke kaishi makaranta ta dauko shi tun daga primary har secondary bata yarda kowa yayi mata wannan aikin.
Yau ga shi yana ta cin gajiyar ilmin ta ko’ina, sannan ta bar shi ya auri Amrah duk da yakinin da yake da shi na ba ta sonta, amma ta kwatanta adalci ko a fuska ba ta taba nunawa Amrah ko wani ba.
Ammi na da wasu irin principles (doctrines) akan akan karan-kanta, wadanda ta dora Fahimah a kai, wanda su ne ta ke masa kwadayi, amma ya kasa ganewa da gangan. Yana can ga kyale-kyalen da baya lasting. Tana da tabbacin watarana zai gane din, tana raye ko bata raye, cewa Fahimah matar rufin asiri ce kuma babban alkhairi a gareshi, har ma ya zo ya gode mata da dukkan godiyar da zai iya. What he needs most is time ....and closeness ga Fahimah.


Bayan fitarsa Fahimah ta ga ya dace ta sauya sutturar jikinta ko da ba ta yi kwalliyar da Ammi ke so ba, don haka ta yi wankanta a nitse, da Olay shower gel (goats' milk), ta fito ta zauna shafa, sannan ta fiddo wani jan material da aka yi wa fitted gown ta sanya, yana da ratsin golden da baki a jikinsa. Ta yi daurin kai ya zauna cif, sannan ta matsa gaban mudubi tana duba turarukan da Uwais ya ajiye a wajen har guda uku. Ashe sunan turaren Uwais ke nan (Maison Francis, Baccarat Rouge).
Kwarai ta dade tana son kamshin, domin kuwa kamshinsa na mannewa a zuciya ne tamkar maganadisu, musamman ga ruhin diya mace ma'abociyar soyayyar da bata samu martani ba. Ba ta san lokacin da ta kai turaren ga bakinta ta sumbata ba, and it feels like�.. like Uwais din himself ta ji ta sumbata apparently. Wanda hakan ya aika wani irin sako cikin ruhinta, wanda ta ji shi tun daga kwakwalwa har zuwa toe wato babban yatsar kafar ta.
Something like emotion mai narka zuciya, da sanya wani irin daddadan feeling..... Fahimah ta shiga waiwaye ko da wanda ya ga abun kunyar da ta yi (sumbatar turaren Uwais). Ga dukkan taimakon Allah, sai ya kasance babu kowa. Daga ita sai Ubangijin ta kadai, sune kuma kadai suka san adadin son da ta ke yi wa Uwais Shagari. Tana kuma rokonSa Azza Wa Jallah a kan in son da ta ke yi wa Uwais, ba alkhairi ba ne a gare ta to ya yaye mata bakidaya ko ya sassauta mata.
Akuyar cikinta ta yi kukan da ke tuna mata rabonta da abinci tun jiya. And cikinta na da nasa hakkin a kanta ba soyayyar Uwais kadai ba. Wadda ta zamo mafi rinjayen abin da ke consuming lokacin ta.
Idan ta lula a duniyar tunanin Uwais, ba ta sanin cewa lokaci na tafiya, sai ta farga da awannin da ta karar ba tare da ta san me ta ke yi ba. Hormones dinta suna da karfi, da ba su sabbaba mata ciwon tunani a kan Uwais ba.
She then decided to prayâ€? wato ta yanke shawarar komawa ga addu'a akan Uwais Shagari, tunda an ce addu’a maganin komai ce.
Addu'ar data dukufa yi a yau itace. Idan son da ta ke wa Uwais alkhairi ne, Allah ya juyo da hankalinsa kanta cikin gaggawa. Idan ba alkhairi ba ne a gare ta, Allah ya nesanta zuciyarta daga kansa Ya raba ta da wannan koshin wahala.


Karfe biyu aka kawo mata abinci mai rai da motsi taci sama-sama daga nan kuma barci mai dadi ya dauke ta, barci sosai ta yi wanda ba ta farka ba har Uwais ya dawo.


Karar sautin talabijin shi ya sanar da ita dawowarsa. Da ta bude ido ta dubi inda yake zaune yana shan lemun power horse daga shi sai farar singlet da dogon wandon suit din da ya cire. Jikinsa ne ya gaya masa tana kallon shi, ya juya ya sakar mata harara a ran shi yana fadin ta kafe shi da ido kamar mayya, ko sun hada jini da maitar ma wa ya sani ne? Kunya sosai ta ji da ya kama ta kane-kane a cikin kallonsa.
“Are you not praying ne ke? (Ke ba kya sallah ne)? Tunda muka zo ban ga kin dungura goshinki gaban Ubangiji ba, sai kallon mazan mutane kamar kya cinye su?â€?
Fahimah ta tsuke baki da fuska cikin bacin ran kalaman sa, sannan ta mike daga kwanciyar. Ya dan bi ta da kallo tana wucewa ta gabansa, sai ya ji kamshin turaren sa na tashi a jikin ta kadan-kadan.
"Lallai ma yarinyar nan ta fara raina ni". Uwais ya fada a ransa. Amma bai furta mata ba dai in ma ta yi ne don ya tanka. Anyway jan kayan nan sun mata kyau as black as she is, sannan she’s tall, slim and well-structured. Bar ta dai da 'bakin ta' da ke munana ta (dark-skinned). But even her lips are looking luscious, succulent and irresitable to every tensed manâ€?" da sauri Uwais ya shafo sumar kansa cike da fargabar Allah ya sa ba a fili ya fadi wadannan baranbaramar kalaman ba.


Daidai lokacin da ta fito daga toilet fuskarta da damshin ruwa, sai ya ga ruwan ba ya mannewa a kan fatarta sabida sulbinta. Sai digewa yake dis-dis. Da sauri ya kauda kansa da suka hada ido, yana tambayar kansa, me yake kallo ne haka???


Duhu ya shigo, bayan ya yi sallar isha ya ji yana da bukatar fita supermarket, akwai abubuwan bukata da yake son sayo musu. Ya mike ya maida rigar sa, ya dau wayarsa ya sa a aljihu ya durfafi kofa.
Fahimah ta fahimci Uwais fita zai sake yi a daren nan, ba ta san lokacin da ta zari mayafinta ta rufa masa baya ba saura kadan su yi karo a bakin kofa.
“Ke lafiya? Ina za ki haka?â€?
Ai kawai ba ta san sanda ta rike gefen rigarsa ba.
“Zan jira ka a waje ka je ka dawo, dazu bayan ka fita aka yi ta kwankwasa min kofa. Ni gaskiya tsoro nake ji an ce Lagos ana kidnappingâ€?.
Ta fada da iyakar gaskiyarta.
Uwais ya rasa me zai ce, sai ya kalli hannunta da ya rike masa riga gam!
“To cika ni tukunna ko?â€?
Ta sake shi cikin jin kunyar abin da ta yi, har ga Allah tsoro ta ji, ba ta san lokacin da ta yi hakan ba.
Juyawa ya yi ya fita ta rufa masa baya, ya rufe kofar dakin. Suna sauka ta lifter yana kiran direbansu da ke zirga-zirga da su, don haka suka samu direban ya yi parking kofar reception yana jiransu.
“Please take us to the nearest supermarketâ€?.
“It’s done, Sir.â€?
Tafiyar mintuna sha biyar suka yi ya kai su wani supermarket shahararre a nan Ikoyi. Fahimah ba ta yi niyyar fita ba, amma da ta tuna pad dinta saura uku sai kawai ta balle murfin mota ta bi shi a baya ba tare da ya sani ba.
Shi dai sai hango ta ya yi a wani bangare daban na shagon tana daukar abu. Ya yi kamar bai ganta ba ya ci gaba da sayayyarsa. Duk abin da za su bukata da ma wanda ba za su bukata ba sai da ya daukar musu daga nan Lagos har zuwa Sudan. Ta ja gefe ta tsaya tana ta kallon mutane wadanda yawancinsu couples ne da yaransu suke sayayya gwanin sha’awa.
Da ta ga ya doshi wajen biyan kudi, sai tayi maza ta bi shi a baya tana dan bobboye abin da ta dauko.
Daga bayansa ta tsaya, ya yi kamar bai ganta ba. Da aka fara lissafa kayansa ya juya yana amsa waya, sai ta yi wuf! Ta jefa always pad din data dauko cikin kayan.
Da ATM card ya biya aka dauko masa kayan zuwa mota. Suna shiga wayar Ammi na shigo masa.
“Ka ce in ka koma gida za ka ba ni Fahimah kuma na ji shiruâ€?.
“I’m sorry Ammi, mun dan fita ne zuwa supermarket, bari mu karasa masauki zan kira in ba taâ€?.
“To lallai gobe ka duba lafiyar wayar ta, haka kawai Fahima ba ta kashe waya, gara da waya a kusa ko da ba ka nan za ta iya kiraâ€?.
Suna ajewa direba ya ja motar.


A can Khartoum Haj. Safeeyyah-Basudaniyyah sai ta dungura goshinta cikin hali na sujjadah ta godiya ga Ubangiji.
Ko ma dai ya ya ne, ko ba shiri suke ba, ko ba soyayya suke ba, ko babu mu'amalar auratayya a tsakanin su, ta fahimci Uwais ya daina kin Fahimah, ya daina kyararta. Ya karbi auren ta kan ba yadda zai yi. Ya kuma fara daina dagawa kansa hankali akan kiyayyar ta.


Shi yasa katin hannunsa ya bude dakin suka shige. Yana rufe kofar ya dube ta a dage, ya ce,
“You Goddam Black, ina wayar ki? Your Mum wants to talk to you in bana nanâ€?.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Yana gama daure mata hannun ya fice ba tareda ya kalle ta ba, tare da cewa,
“idan kin gama kukan I’m waiting for you outside. Ni ba ni nasa kika yanke ba balle ki kai karata wajen Mamar kiâ€?.


Ta dauki mintuna biyar kafin ta iya komawa hayyacinta. Abubuwa na ta faruwa cikin ‘yan dakikannan kamar a mafarki. Kwakwalwarta ta kasa digesting kowanne daga ciki domin Uwais Shagari ya koma mata tamkar hawainiya.
Bata yi zaton yana da wannan compassion din ko yaya a kanta ba, bata yi zaton zai yi wani action a dalilin fitar jini daga jikin ta ba. Har ya bita da kalaman kare kansa. Ta fahimci dai guilty ne ya lullubeshi kawai.
Hijab dinta ta sanya wani zurmeme da shi sannan ta janyo trolley din kayanta ta da Ammi ta hada mata ta tadda shi a waje. Uwais ya baza shanyayyun lumsassun idanunsa don ganin ina Fahimah za ta zaba don zama. In ta jera da shi a gidan gaba ya zama raini, haka in ta je baya ta zauna ya zamanto shi ne direban ta ya zama rashin kunya da tsaurin ido, ace ya zama direban ‘yar gidan marayu tsintacciyar Ammi? Ga mamakinsa tsayawa ta yi hannayenta dogare da karfen trolley din tana jiran umarnin sa. Wato ya zaba mata wurin shiga da kan sa.


"Bata da azarbabi"


Ya fada calmly daga cikin motar ba tareda Fahimah ta ji shi ba.
“To ai gara in zama direbanki da ki zauna a muhallin AMRAH, don haka shigo bayaâ€?.
Ta kyabe baki ba tare da ya gane ba. Ta rasa me ya sa ta daina jin shakkar sa yanzu, ta fi alakanta hakan da maganganun da ya gargasa mata wadanda suka taimaka gaya wajen gaya mata ta kara martaba kanta a idanun Uwais idan shi bai martaba ta ba, ta daina yarda wata mace ta fi ta don kalar fata kamar yadda Baba Talatu ta ce.
Sai dai kuma ba za ta iya yi masa tsaurin ido ba, don haka ne ta bi umarninsa ta bude booth ta sanya jakarta, sannan ta zagayo ta bude kofar baya ta shige kamar yadda ya umarta.
Tana kallonsa sai da ya karanto addu’ar barin gida, ya shafa, sannan ya ja motar a nitse. Ya kure kira’ar Minshawy cikin suratul Nisa’i. Uwais na jin darajojin da Allah ya baiwa mata da hakkokin su a wurin Ubangiji kasancewar sa masanin tafsiri. Dukkansu zuciyarsu ta nutsu da sauraron karatun nan, tension din bacin-rai da fargaba da ke cikin zukatansu na tafiyarsu tare da juna da Ammi ta hada su ba zato ba tsammani ya ragu 50% a dalilin jin ayoyin Ubangiji mai girma.


Ko da suka iso airport ya nemi inda ya adana motarsa kirar Elantra yadda ko kwana nawa ya yi zai dawo ya tadda ita a wajen lafiya.
Fahimah dai bin Uwais ta ke inda duk ya jefa kafarsa kamar rakumi da akala, tana fama da jakarta da ta dan fi karfin ta domin ya ki karba mata tasa kawai yake ja. Ba su bata lokaci ba suka samu jirgin Bell-View mai tashi zuwa Ikko a yanzun nan.
Uwais don dai ya bakanta wa Fahima sai ya kai ta economy class shi ya zauna a first class seats. Abin da bai sani ba Fahimah ko a jikin ta, don ba ta san wani bambanci tsakanin economy da first class ba. Ita hakan ma ya fi mata, domin zama kusa da Uwais ai ba karamin takura ba ne.


Har suka sauka a Lagos ba ta bawa zuciyarta damar yin wani tunani ba bayan na yadda za ta zauna da Uwais a muhalli guda. Something inescapable, something terribleâ€?...something unavoidable, Ammi ta rigada ta hada tafiya kuma ta gudu ta bar ta, haka ta ke kallon wannan moment din da za ta yi tare da Uwais a wannan dan tsakanin na rayuwarta like eternity moment. Ammi ta kinkimo mata aikin da ba ta taba shiryawa ba (zama da Uwais a muhali guda). Jin dadinta daya tsoron Uwais da ta ke kamar na mala’ikan daukar rai ya ragu sosai daga zuciyar ta. Tana jin kanta ta daidai da daukar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login