Showing 39001 words to 42000 words out of 57616 words
Chapter 14 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
bai san na taho ba. Don Allah ko Yaya jabeer kada ka gaya wa na zoâ?.
Har ransa ya ji dadi, don ta nuna ta yi nadamar abinda tayi masa, amma sai ya ce,
âAmrah currently bana Nigeria, ina kasarmu Sudan, Yayan Ammi ya rasu. Amma in kin sauka ki jira ni nan da kwana uku zan isoâ?.
Amrah ta ce, âKai ma ka san tsoro na bai bari na in iya zama a gidan ni kadai. Allah Ya masa rahmaâ?.
âHakuri za ki yi Amrah, Iâll make sure na dawo in two days. You know how much I missed you babyâ?.
Wani mikakken tsaki Fahimah ta saki, wanda ya sa Uwais saurin toshe wayarsa, gaba daya ma sai ya kashe wayar cike da fargabar ko Amrah ta ji? Tashi ya yi ya kunna wutar dakina fusace, dakin ya gauraye da haske.
âWa ki ke ma tsaki?â?
Daga kwancen da ta ke ta murguda baki, ta ce, âDa wanda ya tsargu da shi nakeâ?.
Uwais ya sanya hannu ya dauke mayafin da ta rufa da shi, ya ce, âFahimah ki ke ko Fahummah? You better be careful da ni don a fuska ne nake da kyau, idan ki ka shiga hannuna za ki san na fi ki rashin tausayi.
Itâs my old principle that I will never rape my wife amma da tuni na goge rainin da na lura ya samu matsugunni tsakanin muâ?.
Fahimah ta mike zaune ta dubi Uwais cikin ido da hasken lantarkin da ya haska kyakkyawar fuskarsa, ta zama tamkar an kara masa hasken fata, ta ce,
âRaini na nawa kuma Yaya Uwais? Ni da na ganka kanaâ?..â?.
Ai ba ta karasa ba ta ji ta kane-kane a jikin Uwais, jikinsa rawa yake sosai with utmost regret to the fullest, a lokacin da yake magana harda taruwar hawaye cikin fararen kwayar idanun sa,
âBelieve me Fah-himah ban taba yi ba, you caused it all, and I repented to Almighty Allah, jiki na kuma na bani ya yafe mini. Shi mai afuwa ne mai jin kan bayin Sa. Ya kike so inyi? So ki ke in halaka? A kan me ki ke so in gaya miki kalmar da ban shirya fada ba? A lokacin da ban shirya mata ba?
Ki ba ni lokaci mana? Ki yarda ba abin da lokaci ba ya canzawa a rayuwar dan adam, kamar yadda Ammi ta ce.
Fahimah I hate you before, ba don kalar fata ko zubin halitta ba; bana son kowa ya rabi Ammina, infact kishi ne da ni mai tsanani tun ina yaro, so nake Ammi ta zauna da ni ni kadai, tayi ta so na nikadai, amma ba don abin da ki ke tunani ba.
A dan zamanmu tare a Lagos, sai na samu alâamura da yawa suka sauya min a kanki Fah-himah. Ganewa da na yi cewa ke din; youâre extraordinarily different da sauran mata, with exceptional qualities ababen so ga duk namijin da ya san ciwon kansaâ? Ina kara rokon ki bani lokaci, kada ki tursasa ni wajen furta abin da ba ni da iko a kansaâ?.
Fahimah ta kwanta shiruu! A jikin Yaya Uwais, tana jin wani irin dadi mara misaltuwa a zuciyarta da ba ta taba jin kwatankwacinsa a rayuwarta ba. Kalaman sa sun gama ratsa ta. Ta kasa cewa komai, ta kuma kasa ko da kwakkwaran motsi sabida yadda kalaman Uwais da zurfin muryarshi ke ratsa ta. Uwais ya yi amfani da wannan damarâ?
It was kind of gentle romance wanda ya gigita duniyar Fahimah Shagari, ta kara dulmiyewa a kaunar Uwais yau, har fiye da tarin shekarun da ta kwashe cikin koshin wahala.....
And it started from thereâ? tafiâ? tafi har tsayuwa ta gagare su. Abu na karshe da Fahimah ta fahimta shi ne, daukarta da Uwais ya yi kacokam a hannun sa. Sauran alâamuran da suka biyo baya masu tsauri da girma ne da suka shallake tunanin suâ? A lokacin da Uwais ya maida Fahimah a layin sauran mata, kuka ta saki mai sauti tana kiran sunan Ammi, kai har Baba Talatu yau ta sha kira, tunda su kadai ta ke da su a duniya.
****
Lokacin da Uwais ya samu nutsuwar da yake matukar son samu kwana da kwanaki, wata da watanni, bai juya mata baya ba, rungume Fahimah ya yi a tsakiyar kirjinsa, yana tambayar kansa was all these not LOVE? Idan ba shi ba ne, mene ne? To ko ma dai ya ya ne ko so ne ko ba so ba ne, shi da Fahimah yau sun zama daya. Duk wani kurarinsa da challenges dinsa a kan Fahimah ya neme su ya rasa, irin matan nan ne da ake kira one in million da sai namiji mai matukar saâa a rayuwa ke sa'ar mallakar su. (Never judge a woman by her skin colour). Inji Uwais Shagari.
Uwais yake fadawa kansa. Ya ke kuma fadawa sauran maza 'yan uwansa, masu ra'ayi da akida irin tasa.
Har aka yi kiran assalatu Uwais tunanin da yake kenan, yana rungume da Fahimah, yayin da Fahimah ta yi kukanta ta gaji, barci ya dauke ta.
Wani irin barci na kwanciyar hankali. Soyayyar shekara da shekaru da ta ke yi wa Uwais yau ta sarrafa kanta ta bada cikakkiyar maâana, maâanar da daga ita har Uwais, babu wanda ya tsammaci girmanta ya kai hakan....fadinta ya kai hakan.... Tasirinta zai kai hakan... haka karfinta da zurfinta ya kai har haka....!!!
*****
WASHEGARI
Har karfe goma sun kasa fitowa zuwa gidan gaisuwa, duk da Mahdi ya zo daukarsu sai komawa ya yi, don Uwais ya ce da shi Fahimah ba ta jin dadi ya je ya dawo wajen azahar lokacin ta ji sauki don ta sha magani yanzu ta kwanta.
Da gaske barcin ta ke tun wayewar gari bayan ya taimaka mata ta yi wanka, ta yi sallah ta sha tea. Shi kuma ya koma kan study table daga shi sai singlet da wando three quarter ya kunna loptop dinsa ya soma rage ayyukansa na ofis.
Daidai lokacin da kiran Amrah ya shigo, sai da ya saci kallon Fahimah ya tabbatar barci ta ke sadidan sannan ya amsa.
âHabiby na sauka a Kano, luckly Yaya Jabeer ba ya gari, don haka ina wajen Aunty Murja, in ka iso sai ka zo ka dauke niâ?.
Ga mamakin Uwais Shagari, duk dokinsa na son ganin Amrah da son kasancewa da ita ya yi decreasing 50% fiye da tsammaninsa. Daren jiya ya samu wata irin gamsuwa a auratayya da bai taba samu ba. Ya kuma gane kyawun fuska ko kalar fata ba shi ne mace ba, matan alfarma daban suke. Daban Ubangiji ke halittar su kawai, don ya baiwa namiji mai tsananin sa'a irin sa.
Shi ya san he's among the luckiest cikin mutanen duniya daga kwanaki bakwai a baya zuwa yau.
âAlright Amrah, see you soonâ?.
Abin da ya ce da ita ke nan, sannan ba tare da ya kara cewa komai ba ya kashe wayarsa.
Amrah ta yi sakatoto da waya a hannu, lokacin da Aunty Murja ta iso wajen ta sameta, ta mika mata kofin da ke hannunta mai dauke da tatacciyar madarar shanu mai sanyi (fresh milk). Murjanatu ta ce, âLafiya dai Amrah?â?
Amrah ta yi rau-rau da ido, idanunta cike da hawaye ta dubi Murjanatu, ta ce, âAunty Murjaj, ni Uwais ya kashe ma waya, alhalin na gaya masa na yo tattaki musamman tun daga Malaysia har Kano don kawai na faranta masa? Na tsallako karatuna cikin hadari mai yawa? Ba don za ki karyata ni ba, wallahi sai in ce miki jiya da daddare..... da muna waya na ji tsakin MACE tsuwww..... cikin kunnena, ya yi sauri ya kashe wayar ba tare da mun yi sallama ba.
Yau kuma very shortly ya amsa min ya kashe wayarsaâ?.
Mu karasa a littafi na 3.
Sumayyah Abdulkadir
07030137870
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Suna shigowa get maigadi ya bude musu suka shiga. Tun bai gama parking ba Fahimah ta bude kofar za ta fice da niyyar ta yi ta kanta. Wannan Uwaisun bata gane masa ba da murmushin sa akai-akai. Ta sa a ranta in ta shige daki yau Uwais bai kara ganinta sai Ammi ta dawo. Amma me? Ta-yi ta-yi ta bude kofar ta ki buduwa. Ya kulle ta automatically.
Juya idanu ta yi tana kallonsa da sigar tambayar dalilin kulle mata kofa. Ya wani lumshe ido a cikin kallonta.
âSaurin me ki ke haka?â?
Fahimah ta dafe goshinta da ke sarawa, ta ce, âKa san ba ni da lafiya, ina so na je na kwanta ne, don Allah ka bude min kofarâ?.
âBa ki ji likita ya ce, I can take care of you ba? Ni kadai ke da maganin ciwonkiâ?.
Fahima ba ta san sanda ta kwalalo ido ba tana kallonsa.
âCiwo na? Wane irin ciwo ne da ni? Zazzabi fa kawai nake yi da ciwon maraâ?.
âDuk ina da maganin suâ?.
âTo ba ni insha in je in kwanta, wallahi kaina sarawa yake yi, kuma kana ta sa ni maganaâ?.
âBiyo ni mu je, magungunan suna daki naâ?.
Ya saki locks din da ya kulle motar da su, wata zuciyar na cewa ta je ta karbo wata na gaya mata wayo zai yi mata, ba shi da wasu magunguna a daki, gara ma ta duba first aid box din Ammi, ba za ta rasa kowanne irin magani ba.
Uwais din nan sai ta yi a hankali da shi, shegen wayonsa da son kansa ya fi karfinsa.
Suna shigowa falo ta nufi dakin Ammi ba tare da ta kalle shi ba, shi kuma ya bi ta a baya, first aid box din ta nufa ta bude tana duba magungunan ciki. Sai jin Uwais ta yi a bayanta, sassanyar numfashinsa na dukan wuyanta. Sannan ya rungume ta ta baya.
âMe ki ke nema ne haka?â?
Ba tare da ta juyo ba murya na rawa kamar yadda jikin ta ma ke yi, ta ce, âMaganiâ?.
âAmma na ce miki ina da su, mu je part dina in ba ki ko?â?
Fahimah ta soma hawaye, because he is dragging her closer, and he began caressing her gently, and the touches are irresistable amma haka ta jajirce ta soma kokarin kwatar kanta.
âYaya Uwais, dakin Ammi ne fa?â?.
âAbin da Ammin ke so kenan, shi ya sa ta bar min ke, ta bar mana gidan daga ni sai ke, don tana so mu zama abu guda. Na tabbata ita ta hana Talatu dawowa. Look Fah-himah, today I disregard all your clumsy excusesâ?...".
Fahimah ta wara fararen idanunta gaba daya tana kallonsa da mamaki, sannan ta kankance su cikin tsiwa ta ce,
âWallahi sai dai ka yi raping din nawa Uwais (as you earlier said), don na san ka fi ni karfi. Amma da amincewata da yardata ba zan taba bada alfarmata ga mijin da na tabbata ba ya sona ba!â?.
Tamkar wanda ta kwara wa kankara haka ya ja birki ya saketa. Tunda kuwa ta yi rantsuwa ya san da gaske take. Kwakwalwarsa gaba daya ta rikice, Fahimah na so ta zauta shi, ta yi amfani da wannan damar ta raba shi ta fice cikin hanzari.
Kafin ta kai daki hawaye sun jika mata fuska; raunin diya mace, weakness na mace kan wanda ta ke matukar so, da tausayin abin da ta ke kauna, ta san da gaske yake yana cikin wani hali da yake tsananin bukatar taimakon matar sa, ita ma kuma tana bukata, Uwais ne fa! Amma da a yi 'a rashin uwa' da itaâ? gara kowa ya mutu da urges ya huta.
Ta dauka zai biyo ta, shi ne dalilin da yasa ta rufe kofar da mukulli ta kuma bar shi a jiki don ma kada ya dauko safayar na Ammi ya cigaba da damunta, amma har dare ya tsala ba ta kara jin motsin shi ba.
Sau uku tana lekawa ta taga ta tabbatar yana nan bai fita ko'ina ba, ta hanyar ganin motar sa, sai ta yi ajiyar zuciya ta koma ta kwanta
Amma kuma barci ya gagara zuwa ga Fahimah a wannan daren, tunanin a wane hali Uwais yake? Ya hana barcin zuwa ya kuma hana ta zaman lafiya.
A daddafe garin Allh ya waye da ita, barcin da ta yi yau kwata-kwata bai yi na awanni biyu ba. Da ta tashi duk sammakon ta ba ta ga motarsa ba, tabbacin ya fice ofis ba tare da ya nemi karin kumallo daga gare ta ba.
Don haka ita ma ta yi shirin shiga makaranta don bada excuse na zuwa Sudan kwana biyu ko uku ga abikan karatunta don su yi mata attendences, amma duk jikinta a sanyaye yake. Tana dai karfafa kanta da cewa hukuncin da ta zartar shi ne daidai, kada ta bari soyayya a inda ba ta da gurbi ta kassara rayuwarta.
Ya jira matar SO ta dawo. Su dora daga inda suka tsaya.
*****
Ta yi wanka ta shiga kicin domin nema musu abin da za su ci. Duk da ba ta da tabbas ko zai ci din? Tunda fushi yake, fushin da ta ke kira na karfin hali wai barawo da sallama. Kai da ba ka son mace, ka fada ka kara, a idonta da bayan idonta, don me ka ke son auratayya ta kasance a tsakanin ku?
Haka kawai ita ma a barta stranded din idan matar so ta dawo babu gaira babu dalili? A hakan ma yaya ta kare da sabbin darussan da ya koyar da ita duk da bata san kan dawar garin ba? Ba ta taba ganin mutum mai son kansa a duniya irin Uwais ba. To ita ma tana son kanta, kuma za ta yi wa rayuwarta gatan da bata da shi in reality, sai ranar da ya furta mata hakikanin kalmar so daga zuciya da ruhi, da kuma fatar bakinsa. Ya janye mummunan sunan da yake kiranta da shi na gorin halitta "Goddam Black".
Yamma lis Uwais ya shigo gidan, a matukar gajiye ya ke ga yunwa da ya dawo da ita, rabon shi da sanya wani abu a bakin shi tun wani dan hot coffee da ya sha da safe a ofis da bai fi rabin kofin mug ba, inda akwai abin da Uwais ba ya yi wa fulako ko zuciya to abinci ne, ko dazu da safe duk da fushin da yake da Fahimah kafin ya fita sai da ya duba ya ga ba ta ajiye komai ba shi ne ya fita, amma shi zai yi fushi da komai ban da cikinsa, sabida yawan excercise din da yake yi yana saka shi saurin jin yunwa.
Yana shigowa dining ya nufa. Luckly ta ajiye lafiyayyar sakwara (pounded-yam) da miyan Ugu wadda ta ji naman rago zuqu-zuqu. A gefe ga jug na lemon carrots da ta hada da fresh abarba, ta zuba kananun kankara a cikin sa.
"Ko da wannan mijin fahimah ya tsira ya tsira". Uwais ya ce a zuciyarsa, yana mai jan kujerar da ya saba zama akai a dining din. Ammi ta yi mata kyakkyawan raino mai matukar ban sha'awa, tarbiyya ingantacciya da kuma tsayuwa a kan raâayi guda. Ya fahimce ta tun jiya, ya fahimci manufarta as the same time ya kuma yaba da jarumtakar ta.
Amma har gobe yana faman cigaba da lalubawa a fadar zuciyarsa bai ji tsayayyen muhalli ga Fahimah ba, balle yayi mata karya wadda ba halin sa ba. Amrah ta bi ta cike kowanne gurbi ita dai barta da son bokonta.
Ta karaso wajen yana cikin cin abincin, sanye da riga da wando na Pakistan ruwan zuma, ta kame kakkarfan gashin kanta a tsakiyar kanta wanda bai da tsayi sai cika da kuma karfi na hausawan usli. Ta lulluba mayafin kayan a kanta. Idanunsu suka hadu, duk sai ta ji kunya ta kamata. Data tuna rashin arzikin data yi masa jiya.
Uwais kallonta kawai yake har ta karaso, ya aje cokalin hannunsa. Ta yi wani fresh da ita, dark-skinned din sai sparkling ta ke yi. Ashe dai a can baya kallon tsoro yake mata, bakin ma, kyau ne, ga wanda ya yi dacen sa.
âKi dau abinda za ki dauka, gobe za mu wuce wajen Ammi, sai ki je ki ba ta bayani cewa kin ki yarda auren ya dore yadda ta ke so, kuma ba daga gare ni ba daga gare ki.
Na yi rantsuwa da Ubangiji idan baki sauya ra'ayin ki ba har muka dawo, mata ta uku zan aura muna dawowa daga Sudanâ?.
Yana fadin haka ya ture plate din gabansa ya mike. Murmushi ya kwace wa Fahimah, beautiful serene smiles, ko mene ne damuwarta don Uwais ya kara aure? Ai kishi na matar so ne, ita ke da damuwa. Ita matar shige ina ruwanta? Ammi kuma in ya ga zai iya tarar ta ya fada mata wannan babbar maganar ai sai ya je ya gaya matan.
Kaya kala biyar ta kara dauka, sai na barci da na amfani, wadanda suka dawo da su daga Lagos ta zuba su a kayan wankin ta, tana shirin kwanciya sai ga Uwais ya shigo.
Ta yi maza ta maida rigar da ta ke niyyar cirewa ta canza da sleepy, ya yi kamar bai ga abin da ta yin ba, ya zauna daga tebir din jikin madubi.
Pajamas ne a jikinshi farare âyan gidan Marks & Spencer. Bakin gashinsa sai sheki yake cikin hasken farin kwan lantarkin da ya haskake dakin.
Ya ce, âSorry, Iâm not here for what you are thinking right now. Na zo ne mu fahimci juna kafin zuwan matata ta uku. Ina son sanin me ye a ranki game da ni Uwais, da har ki ka yarda aka kulla irin wannan auren tsakanin mu ba ki yi kowanne irin protest ba alhalin ba kya sonaâ?.
Fahimah ta lumshe idanunta, wai ita yau Uwais ke wa gorin ba ta son sa! Ina ma ana ciro zuciya a nuna, ta tabbata da Uwais ya yarda duk duniya babu