Showing 30001 words to 33000 words out of 57616 words
Chapter 11 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
kowanne irin challenge daga gare shi, tunda dai ya bi umarnin mahaifiyarsa bai yaudareta ya baro ta a gida a bayan idanun ta ba.
A nan filin jirgin Fahimah ta fahimci tafiyar tasu ta gamayya ce shi da abokan aikinsa. Sai dai mutum daya ne Bahaushe, sauran duk kabilu ne. Wasu cikinsu sun taho da matansu, amma Uwais bai yi introducing Fahimah ga kowannen su ba, su dai sun ganshi tare da mace, kuma da ya ke sun san ya yi aure ba dadewa sai ba su ce komai ba. Domin sama yake da su a mukami, matan biyu sun gaisa da ita, Femi da Ronke, amma yadda ta ga Uwais na harararta sai ta kama kanta bayan gaisuwar ba ta kara kallonsu ko shiga sha'anin su ba.
Da kananan motoci na GT Bank aka zo aka kwashe su zuwa masaukin da aka tanadar musu a (Cascade- Wellness Resort Hotel). Hotel ne mai kyau sosai a Ikoyi ta jihar Lagos. Ta lifter suka bi zuwa dakin su, Uwais ya sa key din da aka ba su ya bude.
Fahimah bata san lokacin da ta yi catching numfashinta dinta da karfi ba, da ta fahimci dakin falle daya ne tal, maâana ba ciki da falo bane bedroom ne guda daya. Amma gadon dakin babba ne sosai yadda sai mutum biyar su kwanta ba tare da daya ya gogi daya ba.
A gefe ga sofa-bed, sai tebirin aiki da study-lamp daga can gefe. Bedside fridge da tv a jikin bango, sai wardrobe ta kayan sawa, bayan wannan babu wani tarkace a dakin, very neat ga rabar A/C na fita ko ta ina da kamshin room freshner mai sanyi, kuma komai dake dakin daidai bukatar kowanne dan Adam ne.
Uwais bai ce wa Fahimah komai ba yana aje trolley dinsa ya yi zaune gefen gado yana latsa wayarsa. Wayar Ammi ya kira don ya ji saukar ta, amma ba ta shiga ba, sai ya aje wayar ya fada toilet. Wanka ya fara yi sai alwallah, ya yi brush sannan ya fito daure da towell iya kugunsa.
Har zuwa wannan lokacin Fahimah na nan tsaye inda ya barta tana sakawa tana kwancewa. Ko da ta daga ido ta dubi Uwais daure da towell saura kadan fitsarin da tuntuni ya cika mata mara ya balle ya zubo. The extra-ordinarily well-built structure, the physique chest, the muscles and masculine appearance su suka taru suka kusa nakasta âyan kananan idanunta.
Fahimah tayi maza ta runtse su gam-gam ba ta kara budewa ba, jikinta na mazari kamar wadda sanyin kankara ke kadawa.
Sauri ya yi ya zura jallabiya a jikinshi don shi ya manta ma tana dakin. Da bai fito a haka ba, kada ta raina shi ko ta kalle wa Amrah miji. Gara ya je ya nemi wani dakin ya kai ta, shi ba zai iya kwana da mace a daki ba Amrah ba.
Ya tada sallah, a ransa yana fadin, idan kafafunta suka tara jini za ta zauna ne. Bayan ya idar, ya kira kan talfon ya yi odar abincin mutum biyu ba tare da ya tambaye ta wanda ta ke so ba. Ya san dai abincin gidansu kullum ganye ya fi yawa (vegetables) don haka abin da ya yi order kenan, sai white rice and stew da farfesu.
Ba jimawa aka kawo, lokacin ta gaji da tsayuwar da runtse idon kamar yadda yayi hasashe ta shiga toilet. A yanayin da ta ke jin jikinta ga gajiya ga takurar period wanka kawai za ta yi ta ji dadi, don haka ta yi wankan, ta kimtsa kanta, ta yi brush sannan ta maida kayan jikinta ta fito.
Samunshi ta yi yana cin abinci. Looking smart and gentle a duk abin da yake yi. Uwais, ba zai daina tafiya da ruhinta ba watakila har gaban abada! Komai nasa mai ban kaye ne ga zuciyarta, ba tun yau ba ta dade tana satar kallon sa in yana cin abinci. Wani irin gaye yake komawa mai yanga idan yana cin abinci amma ba wai ya san hakan ba shi. Actually bai san me ya sa ba, jin haushinta da tsanarta da yake sun dan ragu, but bai da wani feeling ko kankani a kanta.
Ya sa wa ransa ta zame masa dole, dole kuwa ya yi hakuri da ita ya sawa rana juriya in yana son farin cikin Ammi. Ya yarda wholeheartedly Ammi ke son Fahimah wato da dukkan zuciyar ta, da kyar in son da ta ke matan bai rinjayi wanda ta ke masa ba.
Da zamanta shiru ya ishe shi sai ya ce.
âAbincin ma jira ki ke in ce miki ga shi ko? Ashe kuwa za ki kwana da yunwa, look, ki rage wadannan mayun idanun naki a kaina kada ki sa in kwareâ?.
Uwais ya fada ganin ta je can karshen dakin ta zauna a dofane tana kallon sa, ba tare da ta bi ta kan abincin ba.
âMalama, ki yi maza ki ci mu je in kama miki daki, kada matata ta jiyo tsamin jikin nan naki ta wayaâ?.
Wani murmushi Fahimah ta yi, maimakon maganarsa ta bata haushi, he noticed the murmushin, sai dai bai san maâanarsa ba. Bakar magana ya gaya mata wadda kowacce mace ka gaya wa ranta zai sosu. Burin sa har kullum shi ne bacin ranta, muzantar ta da wulakantar ta. To ta daina bari wani abu nasa ya bata mata rai don ba zamansa ta ke yi ba.
Ba ta ci abincin ba har ta yi shirin kwanciya, a ranta tace ka ci kai kadai ka kara zama katoto dama gaka nan masha Allah. Duk da irin kartawar da cikinta ke yi, ta gwammace ta barwa Uwais abincin sa tunda har ya ce tana tsami. Ta ji haushi don haushi amma ko a fuska bata nuna ba.
Uwais kuma bai kara ce mata uffan ba, ya harde bisa gado sai faman kiraye-kirayen waya yake yana zuba turanci kamar bakon Baâireshe. Fahimah ta dauki filo daya ta jefa kan sofa ta rufe kafafunta da katon hijabinta ta yi kwanciyar ta.
Waya ta karshe da ya amsa ta fahimci da matarsa ne, kuma maganar da yake yi ba cikin dadin rai yake yin ta ba. With a bitter tune take fita fiercely. Duk da haka a tausashe.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: âWhatever Amrahâ? whatever makes you to disgrace me ta hanyar tafiya babu izni na. Ga dan iska ko? Wanda bai isa ba, bai isa da matar sa ba don kawai yana son ta, tunda ni baki dauke ni a bakin komai ba ki je ki ji da boko, ni ma in ji da loneliness dina.
Ba'a sayen soyayyah da na sayowa kaina wata, sai dai duk abin da ya faru nan gaba kada ki yi kuka da ni. Ki yi da kan ki. Na fada miki na kara, ban iya rayuwa babu mace tare da ni, this is my hidden nature, ina na akan baka na na ki dawo B.U.K in kina son auren mu ya doreâ?.
Da sauri ya kashe wayar da ya tuna akwai mutum a dakin, shaf ya manta da ita, shi mutum ne mai sirri da ba ya son wani ya ji sirrin aurensa ko yaya yake da shi, balle Fahimah.
Gyaran murya ya yi don ya tabbatar ta yi barci ko ba ta yi barci ba? Ta ji sirrinsa da Amrah? Abin da bai sani ba ta dade da kaiwa birnin Sin a barcinta tun sanda ya fara maganar. Har tashi ya yi ya wuce ta gaban sofa din ya tabbatar barci ta ke don ga numfashinta na sauka a hankali. He felt relieved. Ai in ta ji Amrah ta gudu ta barshi sai ta yi dariya ta kyakayata, ta gane son da yake mata ya fi nata yawa wanda hakan abun kunya ne a gare shi, kuma a zahiri ya dade da fahimtar hakan. Ba ya so ya yarda ne da gangan, ya fi alakanta hakan da raâayin gidansu, âyan boko ne na ga ni kashe ni, wadanda za su iya sadaukar da komai don tsira da profession din su. Soyayya is their last priority.
Shi kuma ba shi ya sanya wa kansa soyayyar Amrah ba, Allah ne ya sanya masa, idan za ta zama cutuwa a gare shi kamar haka, yana rokon Allah ya rage masa. Ko ya cire masa bakidaya
Ya yi nafilfili masu yawa a daren yau kafin ya kwanta. Da asubah yana so ya tada Fahimah sallah yana kwabar kansa shiga shaâaninta. Kulawa ma ai yabawa ce. Ita da kanta ta tashi ta shiga toilet ta yi changing sannan ta koma ta sake kwanciya.
Sai wajejen bakwai na safe ta tashi ta ga Uwais ya tsuke cikin Spanish suit bakake wul, wadanda suka maida shi bature zallah, sai tazar kwantacciyar sumarsa yake yi da kumb yana mulketa da Arganavita. Aka kawo karin kumallo ya karasa ya karbo ya rufe dakin, ya zauna yana ci yana tunanin ya aka yi jiya ya manta bai je ya kama wa Fahimah daki ba? Zuciyar sa ta yi gaggawar ba shi amsa da cewa,
âAmanar Ammiâ?.
What if wani ya je ya cutar da ita a bakon wuri, me zai ce wa Ammin ta?
Don haka ya cire maganar kama mata daki daga ransa sam-sam, zai ta jure hakurin zama da ita. Da ganin bakar fuskarta. Har Allah ya iyakance masa wannan kaddara, ya dauki aurenta matsayin jarabta wadda yake fatan Allah ya ba shi ikon cinyewa, ya sa ya gama da mahaifiyarsa lafiya. Ammin da yake so fiye da yadda yake son kansa.
Yadda Uwais ya dauki aurensa da Fahimah matsayin mafi munin jarrabawa a gare shi, ita Fahima ta dauki aurenta da Uwais ne as a luck by chance, ko Uwais ba zai so ta ba aurensa rumfa ne, mafaka ne, kuma waraka daga tsohon ciwo, tsohon mikin da ya dade yana wahal da ita. Don haka ita ko Uwais ba zai so ta ba, she's now contented and satisfied with everything in life. Ammi ta yi wa zuciyar ta gata, gatan da ba za ta gushe tana mata adduâa ba, tare da roka mata gamawa da duniya lafiya har karshen rayuwar ta.
Da ya so ta, da kada ya so ta, yanzu duk uwar su daya uban su daya a wurin ta.
A âyan kananan shekarunta ta yarda love never fadesâ? wato soyayya bata taba kodewa (son da take wa Uwais na har abada ne) sannan sai ta ga dama ta ke yin kanta. In haka ne kenan ba ta ga laifin Uwais Shagari da ba ya sonta ba, soyayyar ba ta ga damar yin kanta a kansa ba. Tasa soyayyar a kan Amrah ta ke, wanda ko kusa ba yin kansa ba ne.
Ita kuma ta kasance mai yawan yi wa dan Adam uzuri a rayuwar ta, kamar yadda Annabi SAW yayi umarni, don haka komai Uwais zai mata uzuri za ta yi masa, uzuri bayan uzuri sau saba'in, uzuri albarkacin Ammi, da uzuri albarkacin soyayyah.
Ya ci abincinsa, ya kira Ammi a waya, ya ji yadda ta sauka, sannan ya gaya mata su ma sun sauka lafiya a jihar Lagos. Ammi farin ciki kamar ta yi ya ya! Ta sa wa Uwais albarka a waya ya fi cikin carbi, yafi sau shurin masaki. Bai taba jin farin ciki a muryar Ammi irin na yau ba.
He was astonished! Har haka ta ke son sa da Fahimar? Shi kuwa me zai hana shi ya daure ya ci gaba da faranta wa Ammi, in ya so ita Fahimar ta ci gaba da ganin other side din Uwais ita kadai, uwarsa ta yi ta sanya masa albarka irin haka???
"He who has the blessings of a mother....never loss in life".
Ammi ta cancanci samun kowanne irin farin-ciki daga gare shi, sabida bata da kowa sai shi, kuma bata da mai rufawa Fahimah asiri bayan shi, kowa zai auri yarinyar ba zai mata rikon da zai gamsar da Ammi ba, idan aka yi la'akari da asalinta, amma idan shine yasan in reality zai rike auren ta koda a ladan noma ce, sannan ko gunduwa - gunduwa zai dinga yi da ita a bayan idon Ammi, a gabanta ya nuna shi mai kyautatawa ne ga Fahimar, albarka zai yi ta sha kwando-kwando irin wannan a wurin Ammi.
Murmushi ya yi mai sauti, a lokacin da ya gama wannan tunanin, har yanzu Ammina kan layi, tana ta zuba masa hirar mutanen Sudan, ya ce,
âAmmi ta ki cin abinci tunda muka zo, kuma bata magana, ko za ki yi mata magana kada wani abu ya faru a ce laifi na?â?
Ammi ta ce, âBa ni Fahimarâ?.
Fahimah na jinsu, a ranta ta ce, ta inda ya koma ke nan? Hada ta da Ammi? Ina ruwansa da kin cin abincin ta? Cikin sa ko nata? Ita bata son munafurci. Ta lura abinda ya koya kenan. Tana karbar wayar ta yi sallama.
âKin ki cin abinci Fahimah, a wane dalili?â?
Idanunta suka cicciko da kwallah, ta ya za ta iya cin abinci yana gasa mata bakaken maganganun sa masu kona ruhin ta, yana hantara da kyarar ta yadda yake so? Shi cin abinci ai sai da sukunin zuciya ake yinsa, ita kuma zuciyar ta babu sukuni ko kankani. Something deep down inside her is disturbed, she is emotionally disturbed.
A kan me ya kamata ta yi a duniya Uwais ya so ta? Ta laluba ta koâina ta rasa, shi ba irin mazan da wani abu ke jan raâayinsu ba ne, tsayayyu ne a kan raâayin su da akidun su kamar mahaifiyar sa.
Amma daga jiya zuwa yau ta yarda Uwais ya ragewa kansa tsanar ta, tunda har ya iya ya kwana daki guda da ita bai yi amai ba, bai yi bacin ran nan nasa ba. Kuma ko sau daya bai kira ta Goddam Black ba tunda suka bar Kano.
Ammi ta sake maimaita tambayarta jin Fahimah ta yi shiru. Wannan karon ta sassauta murya,
âFahimah, me ya sa ki ka ki cin abinci? Ko akwai damuwa ne? Is he maltreating you?â?
Da sauri Fahimah ta girgiza kai, âBa komai Ammi, lafiya muka zo. Na ji ciwo a hannuna ne kafin mu taho yana dan damunaâ?.
Ammi ta ce, "Zan fada masa ya sa miki magani, ko ku je asibiti a duba. Don Allah ki kula da kwalliya Fahimah, na san ki ba damun ki ta yi ba, ki yi ta yin ta akai-akai, ki zama cikin kamshi kodayaushe, sabida da da yanzu ba daya bane zaman wani kike yi yanzu, zaman samar wa mijin ki hutu da nutsuwa daga ni'imar da Allah ya baki, ki sa a ranki ke amarya ce da ke cin lokacin taâ?.
Maganar Ammi ta karshe ta ba ta dariya, sai da ta murmusa, wai amarya! A'ah muna amarya dai, ita da yake ce wa tana tsami ban da abin Ammi ina ruwansa da wata kwalliyar ta? He may not notice ma idan ta yi tunda ba wani kallon ta yake ba.
Ammi ta ce, âBa abin da ban saka miki cikin kayanki ba na kwalliya da kamshi. Dama ce muka samu Fahimah mu yi amfani da ita, don masu iya magana na ce wa, wai sau daya ta ke zuwa a rayuwaâ?.
Fahimah, ta daga lumsassun idanunta tana kallon kyakkyawa Uwais Shagari na ficewa daga dakin, goye da jakar sa ta kwamfuta ba tare da ya kara bi ta kansu ba daga ita har Ammin, kyau kamar shi yayi kansa, tsaf-tsaf da shi gonin sha'awa wanke hannu ka taba inji Hausawa, miji iya burin kowacce diya mace, kai kace balaraben Kuwait ne ko na Abudhabi ba na Sudan ba, don bashi da duhun kalar su (sudanese) shi a wanke yake tas, bai kara bi ta kansu ba ya fice.
Har ya fita ya tuna wayarsa ce a hannunta, sai ya dawo da sauri. A hankali yadda Ammi ba zata ji ba yace.
âYou Goddam Black, ba ni wayata haka!â?.
Ta mika masa wayar da hanzari, bayan ta ce,
âAmmi sai mun sake kiraâ?.
Yana karbar wayar ya sa a aljihu, ya juya yana fadin, âKo ki ci, ko kada ki ci, ba abin da ya dame ni ba ne fa. Kada ki ji ina gayawa Ammi ki dauka ko na damu ne. Hakkin dake kaina kawai na sauke. Kin gan ni nan idan nas kafa na fita yanzu, sai karfe shidda na yamma zan dawo. Ba zaman mace na zo yi ba da aka lika min ke.
Sai ki zauna ki ta gadin daki tunda haka Ammi ke so. Na sa a kawo miki lunch karfe biyu, bayan shi in wani ya buga kada ki bude. Iâve my keys with meâ?.
Fahimah ta yi masa shiru, ya sa kai ya fice da sassarfa don he is almost late. Yau ne za su fara seminar din da ta kawo su a babbar shiyyarsu ta GT da ke birnin Ikko.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Uwais ji ya yi kamar kwarankwatsa ta fado a kansa, sai ya soma ja da baya idanunsa a kanta, sai kuma ya juya da sassarfa ya dauki wayoyinsa da mukullin kofar ya juya zai fice.
Da wani zafin nama Fahimah ta riga shi kai wa bakin kofar ta babbake ta da hannunta.
âBabu inda za ka je Ya Uwaisâ¦â?
Wata uwar harara ya zabga mata da idanunsa da suka rikide kamar na wanda ya sha Dagga.
âIdan ke uwata ce sai ki hana ni fitaâ?.
âIâm not your mother, but a good daughter to her, amma zan iya gaya mata tabbas. Wallahi ka fita sai na gaya mata yanzunnan ka tafi neman mataâ?.
Duk halin da Uwais yake ciki sai da Fahimah ta ba shi dariya, amma ya gintse bai yi ba.
âTo shin ina ruwanki in ma na je neman mata? Na ga dai ba ke zan debo cutar in shafawa ba matata mai hada jiki da ni zan shafawaâ¦â?.
âWhatever!â?
In ji Fahimah,
âIta ma âyar uwata ce a musulunci, zan taya ta kiwon rigimammen mijin taâ?.
Maganarta ta yi wa Uwais dadi har cikin kokon ransa. Bai san sanda ya kama hannayenta biyu ya rike cikin nasa yana murza yatsunta cikin wata irin siga.
âFah-himah, a woman can care for her husband, ko da tana period din, in dai da gaske kina taya Amrah kiwon rigimammen mijinta, to ki taimake ni!â?.
"Ni BLACK?"
Tambayar ta subuto daga bakin Fahimah