Showing 18001 words to 21000 words out of 57616 words
Chapter 7 - FAHIMAH Book 1 Complete pdf Writing by Takori kabara .txt
daya. Anya Amrah ba zamu sake shawara ba? Nace me zai hana tunda bakiyi nisa da fara karatun nan ba a shekarar farko kike ki hakura, na nema miki admission a BUK, Ammi na acan take bazaki sha wahalar samun admission ba.
A ganina Amrah kasancewar mu tare yafi komai muhimmanci, mu shirya welcoming our incoming babies...... Amrah i'm sorry na yi alkawarin da na zo ina tantamar yiwuwar sa, i can't live without a wife Amrah, bansan irin ragaitacciyar rayuwar da zan yi ba. In kin amince Daddy ba zai ce komai ba tunda rayuwar mu ce mu biyu ba tasu ba.....".
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Idanun Amrah har wani kanakancewa suka shiga yi sabida bacin rai, tace "Habiby, ka san abinda kake fada kuwa? BUK? Who? Ni Amran? Amran da na sani Amrah Umar Dikko? In ma wasa kake tun wuri ka bari kafin Daddy ya ji ka". Ta mike cikin fushi ba tare da ta dauki komai daga sayayyar da ya yi mata ba ta nufi dakin ta.
Tana shiga daki mahaifin ta ta kira, tana kuka ta gaya masa duk abinda Uwais ya ce. Alh. Umar Dikko murmushi yayi irin na manya da suka san halin dan adam. Yace.
"Ke ba tantabara sarkin soyayya ba? Duk Yayyen ki wacece tayi aure kafin ta ci karfin karatun ta sai ke? Kin ga farar fata kin rude kin yarda da dadin bakin sa. Abinda baki sani ba mu maza duk halin mu daya bama iya rayuwa babu mace. Kafin ya aure ki ba abinda bazai ce ba, amma yanzu tunda kin zama nama sai yadda yayi dake.
Tun farko ma me ya kai ki kula shi har kika bari soyayya ta shiga tsakanin ku kina level 1? Inda kin bi tsarin dana yi miki tun farko da hakan bata faru ba.
Amma tunda bisa yarjejeniyar nan muka amince aka yi auren ni da iyayen sa to yayi kadan wallahi. Gobe zan turo direba kawai ki biyo shi ku taho, daga nan Abuja ki wuce Malaysia, in zai iya auren ya jira ki as promised, in bazai iya ba babu dole fa a rayuwar nan Amrah... your future is your life, kafin kiyi tunanin farin cikin namiji think of your future, think of yourself first, kafin kowa ya biyo baya.
Your husband only wants to destroy your future......" Amrah bata iya ta karasa sauraron abinda Daddyn ta ke fadi akan Uwais ba ta kashe wayar ta. Ta san Uwais yana son ta, kuma son ne yasa yake son kasancewa da ita, amma is it true that he wants to destroy her future??
Tambayar da bazata iya yiwa Uwais ba, domin yanada kima a idanunta da madaukakiyar daraja, saidai bazata yarda ta bari ya kassara burin rayuwar ta ba don amfanin kansa.
Yau ma kowa a dakin sa ya kwana. Everyone of them is entitled to his opinion. Uwais ya tafi aiki a washegari ba tare da Amrah ta bashi karin kumallo ba kuma batare da ya ganta ba.
Wajejen karfe biyu na rana yana fama da ayyuka a kwamfutar ofishinsa sakon Amrah ya shigo masa.
"On my way to Abuja, daga can zan wuce Malaysia, See you soon... so much Love.
-Amrah.
Al'amarin da ya daurewa Uwais kai, ya kasa koda motsi akan kujerar sa. Bai taba hango matsala kwatankwacin wannan zata kasance tsakanin sa da Amrah ba. In yayi la'akari da cewa auren so da kauna suka yi dukkannin su. Amma Amrah har zata iya yanke wannan hukuncin ga auren sa ba tare da ta ji ko dar ba? Lokaci na farko da ya ji yayi fushi matsananci da Amrah, fushi kuma ba na wasa ba. Ya sa a ransa zai daure ba zai kara neman ta ba ko a waya har sai ya ga iya gudun ruwan su ita da mahaifin ta.
Don tsananin bacin rai da ya koma gida sai ya samu kansa da janyo trollies yana hada kayan sa, gara masa ya koma gidan Ammi da ya zauna gwauro har tsayin wata hudu. Ko ba komai zai dinga samun abinci. Amma yau da wata ce ta yi masa haka ba Amrah ba, zai hakura da auren ta ne kawai. Amma Amrah zata ci alfarmomi har guda biyu; alfarmar son da yake mata da kuma mutuncin dake tsakanin sa da Jabeer.
Ammi na falo tana karatun 'Bulugul Maram' din ta. Sanye da shudiyar laffaya, da butar shayin ta da tambulan a gefe, sai ganin maigadi tayi yayai sallama yana shigowa da akwatunan Uwais, yana wucewa da su part din sa.
Ta saki baki tana kallon sa a lokacin da yake shigowa. Fuskar nan tayi jawur, ta nan take gane fushin Uwais ko bacin ransa tun yana yaro. Bata ce komai ba har ya zo ya samu wuri ya zauna daga gefen kafafun ta.
"Ammi masa'ul khair"
Tana cigaba da kallon sa ta amsa fuskar ta ba yabo ba fallasa, sannan tace "wadannan akwatunan fa? Ko balaguro zaka yi?" Ya girgiza kai cikin shanye bacin rai, don ya san Ammi ba wai tana farin ciki da auren sa da Amrah bane kawai ba yadda zata yi ne kuma tana so ta bashi hakkin sa, shi yasa ta yarda ya aure ta. Don haka dole ya rufawa Amrah asiri don dorar da dangantakar su. Yace.
"Babu komai Ammi. Amrah ta koma makaranta ne, sai bayan watannni hudu zata samu hutu, shiyasa na dawo gida kawai don kadaici zai dame ni, babbar matsala ta abinci".
Ammi cikin mamaki tace "makaranta a ina?" "Limkokwing, Malaysia" Ammi ta rasa abinda zata ce, daga bisani ta ce "dama ka san tana karatu a wata kasar ka aure ta? Ko kuwa sabon zance ne?" Uwais ya sunkuyar da kai, sai yanzu yake ganin wautar kansa, sannan yace "eh Ammi" sai kawai ta gyada kai ta ce "Allah ya bada nasara".
Har wata ajiyar zuciya Uwais ya saki don bai zaci Ammi zata gajarta zancen a haka ba. Shi kuma baya son zancen yayi tsaho har ya kai ga fada mata cewa Amrah ta tafi ne ba tare da iznin sa ba.
Haj. Safeeyah tace "bari in sa Fahimah ta gyara maka dakin, don tun bayan tafiyar ka babu wanda yayi amfani da sassan, na san yayi kura sosai, Talatu bata nan na aiketa kasuwa".
Ba tareda ta saurari me zai ce ba tasa murya tana kiran FAHIMAH. Uwais sai ya sunkuyar da kai, sannan ya ji gaban sa ya fadi, da ya tuna wai itama zaman matar sa take. Zaman shi ta ke yi. Don shi sam ya manta da ita da existence din ta.
Fahimah ta fito daga kicin dauke da madaidaicin tray data shiryowa kanta abinci zata ci, ta shigo falon tana amsa kiran Ammi ba tareda ta san Uwais yana nan ba. Dai-dai lokacin da Uwais ya dago kai. Sexy eyes din sa suka sauka akan Fahimah. Ita kuma bata tsammaci ganin sa a falon ba, don haka farantin dake hannnun ta da duk abinda ke kai ta saki a kasa ba tareda ta sani ba.
Idanun Uwais na da matukar tasiri ga mental well-being din ta, ta yadda a duk lokacin da ya dubeta da su take neman hankalin ta da nutsuwarta ta rasa.
Komai dake kan farantin ya kife, tangaran sun fashe sannan jikin ta ya hau bari. Ammi takaici ya ishe ta na yadda Fahimah bata iya mallakar kanta a duk lokacin da ta ga Uwais kamar wadda ta ga mala'ikan daukar rai, tace.
"Yau nake ganin sakarci, sai ki dauko tsintsiya da mopper ki share, ke ba makauniya ba balle ace tuntube kika yi, kiyi maza ki kwashe kije ki gyara masa sassansa".
Ta juya a sanyaye ta koma kicin don ta dauko tsintsiyar. Uwais mikewa yayi yana sakin dan karamin tsakin da Ammi bata ji ba. "Zan je wajen Jabeer na dawo Ammi, kafin a gyara dakin". Ammi tace "Rehlah Sa'eedah" wato a dawo lafiya.
Bayan fitar sa Ammi ta bishi da kallo sannan ta yi murmushi ta maida duban ta ga Fahimah wadda ke durkushe tana tsaftace wurin data yi messing, ta kasa dagowa har Uwais ya zo ya wuce ta gaban ta. Ammi a ranta tace "muje zuwa dai, ai sannu - sannu bata hana zuwa ai, sai dai a dade ba'a je ba".
*****
FAHIMAH A DAKIN UWAIS
Wannan ne karo na farko data taba shigowa dakin Uwais a rayuwar ta, da farko kasa tabuka komai tayi, domin ji tayi gabadaya kuzarin jikin ta ya kare, koda yayi watanni baya dakin kamshin tsadadden turaren sa 'Maison Francis' bai bar sanyaya dakin ba. Babban hoton sa window size cikin kayan aikin sa na GT shi yafi daukar hankalin ta domin yayi kyau ba na wasa ba a cikin hoton.
A jikin bed-side wani dan karamin hoton ne cikin frame da ya sha adon zuciya, fuskar sa ce data Amrah a ciki kamar zasu sumbaci juna. A hankali ta kai hannu ta dauki hoton a tafin hannun ta tana share kurar jikin sa da gefen gyalenta, tana kallon su da wani irin mixed feelings da ya fi kama da "kishi mai nukurkusa zuciya". Kishin da bata taba ji akan Amrah ba sai yau, ganin yadda ta maida Uwais jazur, ga 'yar kiba yayi, tabbacin yana samun gamsashshiyar soyayyar mace. Mai mace kamar Amrah yaushe zai taba waiwayar ta?
Amma me? Mayaudariyar zuciyar ta sai ta ci gaba da bata hope da courage na cewa wata rana irin haka na zuwa....ranar da zata ga fuskarta haka gab da ta Uwais, watakila closeness din har ya fi haka. Duk da haka bata jin kin Amrah a ranta domin ta yaba da yadda ta karbeta a ganin ta na farko da ita.
Ba abunda ke bukatar gyara a dakin sai kura da ko'ina yayi, don haka ta hau karkade komai tana gogewa tayi shara ta gyara abinda duk ya kamata ta tsaftace, sannan ta wanke masa toilet wanda yake fari kal shi ko kurar ma bai yi ba fari kal yake tabbacin a baya yana samun kulawa sosai.
Da ta kammala ta feshe dakin da 'air freshner' din 'raspberry' ta shimfida masa sabon bedsheet mai kauri da Ammi ta bata ta shigo da shi sannan ta juya zata fita.
Kamar wadda aka yiwa umarni sai ta sake juyowa, ta kalli hoton sa dake kafe, sannan ta runtse idon ta ta juya ta fita.
"Na gama Ammi!"
Ta fadawa Haj. Safeeyah dake zaune tana lazumi, mace ce mai yawan ibadah da bata bari lokacinta ya wuce a banza. Kai ta gyada mata. Sai Fahimah ta wuce kitchen ta tadda Baba Talatu don ta taya ta shirya abincin Uwais. Ko dama can tare suke girkin su muddin Fahimah tana gida.
Suna cikin aikin Baba Talatu ta dube ta sosai ta ga kullum kara ramewa take yi. Ta san dole Fahimah ta kasance cikin damuwa sai dai ta boye hakan a ranta, don bata taba ji ko ganin Aure irin nata ba. Har yau ta kasa gane manufar Ammi ta hada wannan baudadden aure, ita Fahimahn tana nan a gefe kusa da uwar sa, shi yana can tare da matar da yake so suna more kuruciyar su. Anya ko Fahimah bata son Uwais hakan bazai ke damun ta a karkashin zuciya ba? Koda yake Ammi tace jami'a zata fara, ta san Fahimar su da son karatu, watakil in ta fara zuwa makarantar zata samu abin debe kewa. Baba Talatu ta nisa ta ce.
"Uwar daki na, daga yau ke kadai zaki dinga dafa abincin ubandaki na, sannan ke zaki dinga kai masa, gyaran dakin sa da kula da komai nasa a gidannan ya dawo wuyanki domin da ke yafi dacewa har zuwa lokacin da zai bar gidannan".
Fahimah tayi mata kallon "sannu sarkin kankanba". Sannnan ta ce "shin Baba Talatu meye gami na da shi din?" Dariya Talatu tayi tace "wai ai naga aikin neman lada ne da neman aljannah, kiyi don neman dacewa da aljannah ba don komai ba" da sauri Fahimah ta girgiza kai "ban iya shishshigi ba, kuma bazan fara yanzu ba. Ayyukan neman lada yawa gare su. In ya ga dama ya bi matar sa. Ni ki daina alaqanta ni da Ya Uwais, don babu komai tsakanin mu bayan 'yan uwantakar musulinci da Ammi ta hada, kuma ita nake fatan ta cigaba da wanzuwa a tsakanin mu har karshen rayuwa ta.
Baba Talatu ta yi murmushi ta ce "Fahimah har yanzu ke yarinya ce, amma yaya zaki nade hannu a kirji ki koma gefe ki barwa kishiya miji? Miji fa aka ce Fahimah ba saurayi ba! Ai kowanne li'irabi kike dashi ki ajiye shi a gefe ki yi hobbasar kwatarwa kanki 'YANCI don tabbatar da martabarki ta diya mace.
Ni ban yarda wai wannan farar tsadar ta fi ki komai ba, mace sunan ta mace, kowacce irin kala ce ita, bahaushiya, balarabiya, ba'abziniya, bafullatana ke har bayerabiya duk daya muke.
Balle ma Fahimah ke kike ganin kan ki a baya don baki da hasken fata irin ta ubandaki na, amma bakar mace ai ita ce mace ta alfarma, shi kansa ya san hakan sai don dai wani dalili nasa na daban amma.....".
Zancen duk ya gundiri Fahimah, tace "Baba Talatu chapter closed, inda aka san darajar ka acan ne zaka yi rawa a baka kudi, a inda ba'a san darajarka ba kuwa maimakon ka samu kudi, kana iya karewa da dan banzan duka!".
Uwais da ya je bai samu Jabeer a gida ba sai Murjanatu, ta gaya masa Jabeer yana Abuja, zurfin ciki irin na Uwais yasa bai tattauna komai akan matsalar sa da Amrah da Aunty Murjanatu ba duk da ya san kusancin dake tsakanin su. Maimakon ya koma gida sai ya samu gefen hanya ya gangara ya tsaya, ya kashe motar gabadaya yana kallon wayar sa da kiran Amrah ke ta shigowa akai-akai ba kakkautawa. Zuciyar soyayyah na azalzalarsa da ya dauka.....zuciyar maza na hambarewa. Duk son da yake yi wa Amrah dole ta yi abinda zai nuna mata shi ba irin mazan da mace ke juyawa bane don kawai yana son ta.
Ya fi karfin mintuna ashirin a wurin yana tunanin abinda zai yiwa Amrah ya rama bacin ran data sanyashi, kin amsa kiranta is not enough. Amma ga mamakin sa ya kasa daukar wani matakin bayan wannan. Amrah ta riga ta yiwa zuciyar sa illah bai da wani katabus a kanta.
Da kyar ya jawo motar ya dawo gida, bai tadda kowa a falon ba duk sun shige daka, ya wuce dakin sa kansa tsaye. Wani irin gyara da dakin ya samu da sanyin air fresh da Fahimah ta fesa su suka yi masa sallama, wadanda suka cakude da rabar iyakwandishan. Sai lokacin ya tuna ya ji sanda Ammi ke fadin Fahimah ta zo ta gyara masa daki. Tsaki yayi yana fadin "da abinda tafi dacewa kenan ai (aikatau) ba matar masu gida ba".
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Washegari da safe Fahimah ta shirya masa breakfast, sabida Talatu ta yi sammako zuwa kauyen su Jahun 'yar ta ta haihu. Kunun gyada tayi masa fari kal mai gardi sai kosan dankalin turawa da ruwan shayin da ya zamewa al'ummar gidan duka farillah.
Ya fito cikin casual - dress din sa na suit din ma'aikatan bankin GT misalin karfe bakwai dai-dai na safe. One thing shine baya wasa da cikin sa sabida fadin kirjin sa (physique) da motsa jiki da yake yi da Asubah yasa baya iya fita ba tare da ya karya ba.
A jikin dining din ya sameta tana jera abincin, rigar barci ce a jikin ta da 'yar hula a kanta ta dora zanin atampa a saman rigar. Yana zuwa ya ja kujera ya zauna, ba tareda ya dubeta ba. Juyawa tayi ta bar wurin jin zata sake yin barin tangaranm ita kuma tayi alkawarin ta daina bada kanta gaban Uwais. Yayi tsammanin zata gaishe shi ne ya baiwa banza ajiyar ta. Ga madaukakin mamakin sa sai ta juya zuwa dakin ta ba tareda ta ko kalle shi ba.
"Kin rufawa kan ki asiri".
Ya fada yana tsiyaya kunun a kofi. Ko daga kyan kunun a ido ya tabbatar zai yi gardi a baki. "Kin taimaki mijin ki na gaba (idan Uwais ya sake ki) da kika tsaya kika iya girki. Don zaman Ammi kike yi ba nawa ba. Banda abun Ammi wannan Blakin ai sai ta dinga firgita mutum cikin dare. Gara da ta rike abar ta a gefen ta bata yi gigin kawo masa ita gida ba. La-shakkah da Amrah ta samu Kuku. Don bazai taba bude baki ya iya cewa Amrah yana da wata macen a duniya bayan ita ba. Bai yaudari Amrah ba, don da gaske har cikin zuciyar sa bai da wata mace bayan ita.
Sama-sama ya ci abincin ya wuce dakin Ammi, tana zaune bisa darduma tana azkar din ta na safiya. "Na fito Ammi, sai na dawo. Sabahul khair". Daga masa kai ta yi ya juya ya fita.
****
Yau Fahimah zata fara registration, don haka tare suka tafi da Ammi, kuma fannin da Ammi ke koyarwa shi ta zabar mata, don tace a fannin ne kawai zata iya dinga taimaka mata a gida wato tsimi da tanadi (economics).
Kasancewar yanzu abu ake na sanayya, Fahimah bata sha wahalar samun gurbi fannin na tsimi da tanadi ba kamar sauran dalibai, duk da wahalar da yakeyi, tunda tana da uwa a gindin murhu.
Da taimakon Ammi ta fara registration, kullum da safe tare suke tafiya, yau da suka fito akan titin su na komawa gida Ammi ta ce "Fahimah, is high time ki fara koyon tukin mota don ki dinga taimaka min kina taimakon kanki, tunda Surajo ya tsufa baya iya gani sosai, yanzu kuma ke matar aure ce, bai kamata ga mijin ki zaune a gida in dauko wani kato ya dinga