Showing 1 words to 3000 words out of 70255 words
® *_HASKE WRITERS ASSO_*
( _Home of expert & perfect writers_)
*ALWASHI....!*💍
_(Labarin Hafsat)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to MISS XOXO_
_Sakon fatan alkhairi gareki k'anwata Feedohm marubuciyar ZAN RAYU DAKE,ina yimiki fatan alkhairi aduk inda kike, indeed i have no words to thank u, am deeply grateful....! The first page is belong 2 u dear!_
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI.
*1*
****Gidane na marayu mai d'auke da tangamemen gate sannan ga katanga babba zagaye da gidan wanda tsawonta ma abin kallone,haka shima cikin gidan yake wawakeken gaske mai dauke da gine gine masu yawa wadanda suka hadar da ofisoshin ma'aikatan gidan da kuma wurin kwanan marayun da kuma duk wani abu na bukatarsu,
Duk inda ka hanga yarane zaune sunyi group group, masu wasa nayi sannan masu hira sunayi yayinda wasu kuma suke yan aikace aikacensu na yau da kullum,
Wasu yanmata ne guda biyu acan gefe su kadai wadanda akalla shekarunsu zasu kai shekaru 23,
Daya daga cikinsu tayi tagumi tana sanye da kodadden hijabi da wata kodaddiyar atamfa ajikinta haka itama dayar kayan jikinta duk sun gajiya,
"Hafsat wai wannan tagumin da kikayi na menene? Yau naga gaba daya yanayin naki sai ahankali tamkar wata marar lafiya..." Daya daga cikin yanmatan tafada bayan ta dafa kawar tata,
"Amina wallahi lafiyata kalau kawai dai ina tunanin makomar rayuwarmu ne acikin gidan nan, ba kasafai mutane suka fiya kulawa damu ba, hatta gwamnati tayi watsi da rayuwarmu sai lokaci zuwa lokaci take tunawa damu..." Wadda aka kira da suna hafsat tayi magana cikin karyewar zuciya,
"Amma dai hafsat wannan ai ba bakon abu bane awajenmu duba da tsawon shekarun da muka diba acikin wannan gida gashi har yau Allah bai kawo wanda zai daukemu ya fitar damu daga cikin gidan nanba ko muma mazamo yaya kamar kowa.."
"Amina kenan tayaya zamu zamo yaya kamar kowa alhalin babu wanda yasan asalinmu, Allah ne kadai yasan tushenmu dan haka kinga maganar amaida mu 'yaya ma bata taso ba.."
"Hmmm babu komai koma dai yayane Allah yana tare damu..."
"Kai yanmatan nan kutaso kuzo muje.." Muryar daya daga cikin ma'aikatan gidan marayun ta ratsa kunnuwansu wanda hakane yayi sanadiyyar katse musu hirar da suke yi,
Mikewa sukayi suka karasa inda take,
"Yawwa kuzo muje, wannan bawan Allahn ne yauma yakawo muku agaji kamar yadda yasaba..."
Batare da sunyi magana ba suka bi bayanta, gaba daya an tattaro yaran gidan antarasu wuri guda gefe kuma wata babbar motace anata sauke kaya daga kanta wadanda suka hadar da buhunhunan kayan abinci da tufafi,
Wuri amina da hafsat suka samu suka tsaya suna kallon irin uba uban kayan da ake saukewa,
Kowacce acikinsu addu'a take acikin zuciyarta kan Allah yasakawa koma wanene wannan mutumin da alkhairi domin yajima yana yi musu hidima,
Kayan da aka sauke daga kan wannan katuwar motar ba dan kadan bane domin bayan kayan abinci da kayan sawa harda barguna da katifu,
Suna nan zaune sunyi tsuru suna ganin tulin kayan da aka kawo musu har aka kammala sauke kayan nan wakilin wanda yabada kayan akawo ya mike yadanyi jawabi,
_Kamar yadda muka sani kuma muka saba, wannan bawan Allah Wanda mukafi sani da suna baya goya marayu akoda yaushe yana iya kokarinsa wurin ganin ya kyautatawa rayuwar marayu sannan kuma ya sadaukar da dukiyarsa wurin taimakon musulunci, kamar yadda nadade ina fada muku shi wannan bawan Allah matashine ba tsoho ba kawai dai Allah ne ya albarkaceshi da halin manya dan haka muyita yimasa addu'a akan Allah ya albarkaci rayuwarsa da dukiyarsa da kuma iyayensa...._
"Amin..."
Dukkan jama'ar dake wurin suka amsa cikin farin ciki domin wannan bawan Allah ba karamin taimako yake yiba saboda kusan agarin ma shine lamba daya wurin taimakawa rayuwar marayu.
Saida aka gama rabawa marayun kayayyakin da aka kawo musu akan idon wakilin wannan bawan Allahn dake basu gudun mawa wanda suka dade da rada masa suna da baya goya marayu,bayan gama rabon kayan tsaf sannan wakilin baya goya marayu yatafi, sukuma yaran kowa ya kinkimi kayanshi ya nufi wurinda zai adana su, haka suke gudanar da rayuwarsu cikin wannan gida wanda a lokuta mafiya yawa sukan shafe sama da watanni biyu batare da sun samu wani tallafi ba indai ba wannan bawan Allahn ne ya aiko musu ba gashi kuma duk wannan hidimar da yake yi musu basu taba ganinsa ba balle har su gane kamanninsa.
***
Kamar bazai taka k'asa ba haka yake tafiya, sanye yake cikin jar t shirt mai dogon hannu yasha d'amara da jar belt wadda ke d'amare ajikin bakin trouser din dake jikinsa, duk da wai ahakan sauri yake amma baisashi sauya salon tafiyar tashi ba,bak'in face din dake idonshi yadan gyara bayan ya maida hankalinsa kan agogon azurfar dake d'aure a tsintsiyar hannunshi, kamar koda yaushe fuskarshi babu alamun fara'a atare da ita,
K'ofar da zata sadashi da falon mahaifiyarshi ya bude ya shiga fuskar nan kamar zaice wayyo Allah dan tsananin fushi,
Ganin babu kowa aciki yasashi kara yin gaba, awani tsararren falo wanda aka tanada musamman domin hutawa ya isketa, tana zaune saman kujera daga ganinta bazata haura shekaru 45 ba aduniya, farace jajur mai dan jiki, tana sanye da wani leshi mai tsadar gaske, wuyanta da hannuwanta gamida kunnenta duk gwala gwalai ne sai walwali suke, haka yan yatsun hannunta ma duk sunsha zubunan gold,gefenta kuma wata yar matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekaru 23 tana kwance tayi matashi da cinyar matar,
Sallama yayi wadda ba lallai su iya jiba domin aciki ciki yayita,
Dukkansu hankalinsu yana ga drama din da suke kallo atashar tauraron dan adam wanda har saida ya zauna sannan suka farga dashi.......
*_Ummi Sha® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI.....!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Miss Xoxo_
*2*
***Fuska cikeda annashuwa mahaifiyar tashi ta kalleshi cikin fara,a yayin da shikuma sai faman cijar lebenshi nakasa yake yi fuska babu annuri,
"Yusleem.... Har anshigo?"
Mahaifiyar tashi ta tambayeshi da fara,a akan fuskarta,
Saida yasake hade rai idanuwansa na bisa screen din hadaddiyar wayar dake hannunshi sannan ya amsata dakyar,
"Ehh Mami..."
Wata fara,ar tasake yi sannan tayi magana,
"Nima dama tun dazu nake jiranka kazo saboda ina son ka sama mana visa nida surayya zuwa kasar chairo zan kaita medical check up..."
Shiru yayi batare da ya amsa ba yaci gaba da latsa wayarshi, idan da sabo to kowa nagidan ya saba da wannan mummunar dabi'ar tashi tayin shiru idan ana yimasa magana, ko mahaifiyarshi ce tayi masa magana sai yaga dama zai amsa gashi da shegen girman kan tsiya kamar shi yafi kowa,
Saida ya dauki fiyeda mintuna goma sannan ya daga manyan idanuwanshi wadanda suke tamkar kwai domin round eyes gareshi,surayya kanwarshi ya kalla wacce ke kwance akan cinyar mami tana sanye da English wears riga da skirt bakake kanta babu dan kwali,
Baiyi magana ba yasake mayar da kanshi kan screen din wayarshi,
"Mami...am dama ina son infada miki.."
Tattaro hankalinta gaba daya Mami tayi zuwa gareshi,
"To yusleem ina jinka.."
"Mami nasaki khadija yau da safe.."
Zaro idanuwa Mami tayi gamida dafe kirji, surayya kuwa dake kwance akan cinyarta zunbur tayi ta mike zaune, dukkaninsu kallonshi suke cikeda tuhuma gamida zargi iri iri,
"Nashiga uku ni siyama, innalillahi wa inna ilaihir raji'un...." Mami tafada tana tafa hannuwanta,
"Haba yusleem wai kai wanne irin mutum ne? Anya kuwa ba aljana ce ta aureka ba? Karfa ka manta ko watanni uku cikakke ba ayiba da bikinku kaida khadija amma shine yau kazo kake fada min wai ka saketa?
Yusleem mai ka dauki aure ne? Ka daukeshi ne a matsayin wasa, ko kuma abin wasa ko wasan yara?
Yusleem duk fa wannan dukiyar da kake ganin kana da ita bazata taba iya siya maka darajar da aure zai siya maka ba...!"
Dan jan numfashi tayi sannan ta dora,
"Kana yaronka dakai amma acikin shekaru biyar kayi aure sama da guda goma, haba yusleem wannan wacce irin mummunar dabi'a ce, ka mayar da sakin aure ba komaiba,saki da Allah ma baya sonsa amma kai kuma shine ka mayar tamkar sana,arka,
To agaskiya nidai nagama gajiya da wannan halin naka na auri saki, babu damar ka zauna da mace na koda shekara dayane?"
"Gaskiya Yaya bamuji dadin wannan labarin ba, yanzu anty khadijan ma ka saketa?"
Surayya ta fada idonta dauke da kwalla,ko kallonta baiyi ba bare tasa ran zai bata amsa,
Fada mami tasoma balbala masa ta inda take shiga bata nan take fitaba,
"Ni narasa gane kan wannan hali naka yusleem, kwata kwata baka dauki aure da daraja ba, sam baka son zama da mace, wannan wacce irin rayuwa ce,
Kuma bafa kowa kake watsawa kasa a idoba face ni tunda nice nake aura maka matan, yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?"
Dan kishingida yayi kadan ya tsurawa wayarshi ido batare da yace komai ba,
"Dakai nake magana kayi min shiru, ka fada min dalilinka na auri saki, akalla ba a kasaru ba yusleem ka auri mata dai dai dai har guda goma sha..., baka da lafiya ne ko yaya?"
Saida ya dan shafi sajen fuskarshi sannan ya kalli mami,
"Mami ni lafiyata kalau sannan dama ai ban taba cewa ga wacce nake so ba, duk matan da nake aure kece kike samo min su ki aura min.."
"Wacce irin magana kake fada min yusleem? Dan bakai kagansu kana soba shikenan bazaka zauna dasu ba? Wannan dalilinne yasa ka dauki auri saki ba abakin komai ba?
Sau nawa ina baka dama domin ka fito da matar da kake so in aura maka amma sai kayi biris da maganar, kuma ni ai aganina nagama yimaka duk wani gata wanda yadace ace uwa tayiwa danta domin na nemo maka mata yan mutunci, yan asali, masu aji wadanda suka dace dakai amma daga karshe duk dai labarin iri dayane cewa ka sakesu, yanzu kaduba kaga yarinyar nan khadija da ka saketa ka rabu da ita, yarinya ce mai hakuri mai nagarta mai sanin ya kamata, yarinya kyakkyawa yar asali yar mutunci yar kawata hajiya fa'iza,ko wata biyar ba ayiba da bikinku amma kasaketa..."
Dan tsagaitawa mami tayi tana dubanshi cikeda bacin rai, har tsawon mintuna biyar babu wanda yasake magana acikinsu,
"Yusleem wai da me kake takama ne da har kadauki auri saki ba abakin komai ba?
Idan dan kyawun dakake dashi ne yasaka kake yin haka to ya kamata fa kasani akwai wadanda suka zartaka kyau amma basa yin haka,
Idan kuma dan arzikin dakake dashi ne to kasani akwai big millionaires suna nan ba irinkaba young millionaire ba kuma basa aikata wannan wulakancin dakake yi,
Inkuma kuruciyar da kake tare da itane yasaka yin wannan cin mutuncin to wallahi ka gaggauta farkawa daga wannan dogon baccin da kakeyi domin akullum shekarunka sake yawa suke bawai raguwa ba.."
Shiru mami tayi cikeda bacin rai tana huci saboda babatun da tagama yanzu,
Mikewa yayi sannan yayi magana ahankali,kamar mai ciwon baki yace,
"Kiyi hakuri mami.."
Ko amsa masa batayi ba yasaka kai yafice daga cikin falon, nan mami da surayya suka rakashi da idanu....
_*Ummi Shatu*_👌🏻[12/14, 9:21 PM] Ummu A'isha: ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to MISS XOXO_
*4*
aishaummi.blogspot.com
***Tashi mami tayi tabi bayan hajiya fa'iza zuwa dakin da khadija ke kwance tagama cin kuka ta koshi dan tsabar kuka yanzu ko hawayen ma bata iyayi,
Zama mami tayi agefen gadon da khadijan ke zaune ta dafata jikinta asanyaye,
"Khadija kiyi hakuri kinji, insha Allah komai zai daidaita sannan zaki koma gidan mijinki"
D'aga jajayen idanuwanta wadanda suka rine tayi ta kalli mami,
"Mami bazan iya komawa gidansa ba, nahakura da aurenshi, bazan sake iya zaman aure dashi ba wallahi"
Gaban mami ne yashiga dukan tara tara saboda jin abinda khadija tafada,
"Khadija wani abu yayi miki?"
"Mami ni babu abinda yayi min kawai wulakancinshi ne bazan iya cigaba da jurewa ba"
Dafata mami tasake yi,cikin sigar lallashi tace,
"Nasani khadija, kuma nasan kinada hakuri amma daurewa zakiyi kisake yin wani hakurin ki koma dakinki..."
"Mami bazan iya komawa ba wallahi nidai nahakura"
"To kuma khadija idan Allah ya kaddaro da rabo a tsakaninku fa? Bana son ayi gaggawar yanke hukunci daga baya kuma azo ana dana sani"
Sai a lokacin hajiya fa'iza mahaifiyar khadija tayi magana,
"Ai hajiya siyama maganar rabo a tsakaninsu ma babu shi saboda tunda akayi auren bai taba shiga dakinta ba, ko kallo bata isheshi ba bare har ya kulata"
Tagumi mami ta rafka taci gaba da sauraron bayanin da hajiya fa'iza take yimata na irin zaman da yusleem yayi da khadija ta rufe maganar da cewa,
"Kawai dai muyi addu'a Allah yasa hakane mafi alkhairi, nanda sati biyu kuma zamuzo mu kwashe kayanta ki fada masa"
Ita dai mami jiki babu kwari ta mike bayan tagama bawa khadija da mahaifiyarta hakuri, jakarta ta dauka ta fita ranta babu dadi zuciyarta cike da bacin rai, wannan karon kam yazama dole ta nunawa yusleem fushinta akan abinda yajima yana aikatawa na sakin mata babu gaira bare dalili, babu laifin tsaye babu na zaune.
Har kofar gida hajiya fa'iza ta rakata suna cigaba da bawa juna hakuri musamman ma mami da take ganin laifin na yusleem ne domin shine yake nema yaja mata lalacewar zumuncinsu da matar da suka dade atare,
Mota Mamman driver ya bude mata tashiga ta zauna ya rufe suka tafi domin tuni hajiya fa'iza tajima da shigewa cikin gida.
Da tunani kala kala acikin zuciyarta suka karasa gida, cikeda damuwa take zayyanewa surayya abinda yafaru, suna tsaka da yin maganar sukaji shigowar yusleem,
Bai karaso cikin falon ba yatsaya a dining area, sanye yake da jar t shirt mai gajeren hannu sai black trouser, kamshin turaren lailatul abyad da na real oud ne yake tashi daga jikinsa, fuskarshi tayi fes sai annurin kyaune yake fita daga gareta,
D'aga murya Mami tayi tayadda tasan zai iya jiyota,
"Kai..."
"Na'am ma..." Ya amsa yana kokarin bude jeren flasks din dake ajiye asaman table din,
"Zo nan.." Mami tafada bayan ta daure fuskarta, fasa diban abincin yayi ya tasamma cikin falon inda su Mami suke.
***
Rayuwar Hafsat haka taci gaba da tafiya agidan marayu, yanzu haka ta maida hankali sosai wurin koyon sana'o'in hannu domin ana zuwa akoya musu, musamman aka ajiye musu wadanda zasu rinka koyar dasu,
Cikin lokutan da babu yawa ta kwarance wurin sak'a sannan tafara iya dinkin keke,haka kawarta Amina itama tana yi daidai gwargwado,
Kullum cikin yin sak'a suke itada Amina suna warwarewa sai su sake saka wani abun nadaban kamar hula, safa, ko riga,
Yau ma kamar kullum suna zaune a inda suka saba zama suna yar hirarsu kowaccensu tana rikeda koreshi tana yin saka,
Hirarsu ce ta katse saboda gano wasu manya manyan motoci da sukayi suna kokarin shigowa cikin harabar gidan,
Amina ce ta zunguri Hafsat da hannunta,
"Hafsat yauma da alama munyi baki, watakila mai girma governor ne yakawo mana ziyarar bazata.."
"Nima dai abinda nake tunani kenan Amina, koma dai menene kinga tashi muje ayi damu kin san bahaushe yace wai gani ya kori ji..."
Mikewa sukayi atare kowaccensu ta tukunkune zaren kulunta da koreshi suka nufi inda suka hango mutanen gidan suna tafiya....
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/14, 9:21 PM] Ummu A'isha: ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to MISS XOXO_
*5*
aishaummi.blogspot.com
***Ahankali yake ratsawa har zuwa cikin falon mami inda suke zaune itada surayya,
Tunda yaga fuskarta yasan tana cikeda bacin rai,
Zama yayi acikin daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake girke acikin falon,
Tamkar basarake haka yajingina da jikin kujerar ya kishingide,
"Yusleem kana son inyi maka mugun baki..?"
Mami tafada ahasale cikin fada, shiru yayi bai amsa ba hakan yasake tunzurata, cikin tsawa tasake yin magana,
"Ba dakai nake yin magana ba?"
Dan kallonta yayi,
"Mami laifin me kuma nasake yi?"
"Ban saniba, ohhh watonma tambayata kake me kayi? Harma ka manta abinda kayi kenan..?"
Jijjiga kai mami tashiga yi ta maida dubanta ga surayya wacce ke zaune tana jinsu,
"Lallai surayya gaskiyarki ne dole sai an binciki kwakwalwarsa, kinji yanzu wai tambayata yake me yayi, watonma shi har ya manta, dole ka manta mana tunda ka cimin mutunci a idon duniya, sannan ka nunawa duniya ban isa dakaiba, ka cuci yar mutane ka mayar da ita bazawara.."
Nunashi da yatsa tayi,
"To wallahi kaji tsoron Allah yusleem, ina fada maka kaji tsoron Allah domin wallahi bazai barka ba indai kaci gaba da wannan mummunar dabi'ar taka ta auri saki"
"Mami yanzu shikenan anty khadijan tatafi bazata dawoba?" Surayya tayi tambayar tana kallon mami,
"Surayya ai babu macen da za ayiwa irin wannan wulakancin ta yarda tasake dawowa, yayanku bashida hali mai kyau mugun mutum ne.."
Da sauri ya kalli mami, sai lokacin yayi magana,
"Mami muguntar me nayi? Ita khadijan ce tace miki ni mugune?"
Kallonsa mami tayi cikeda masifa,
"Ai basai ta fada minba, kai yanzu acikin halayenka har sai wata tafada min? Acikin halayenka wanne ne bansani ba?
Kai cikakken mugune, miskili, mai shegen tinkahon tsiya da girman kai,
To bari kaji infada maka, komai tinkahon mutum da girman kansa idan yashiga wurin matarsa kaskantar da kansa yake komai sarautarsa da kudinsa, amma kai hatta matarka wannan shegen kasaitar taka da girman kai kake nuna mata.."
Shiru yayi bai sake maganaba, yayinda mami taci gaba da zuba masa fada har saida tayi mai isarta sannan ta sassauta,
"Yusleem nakasa gane damuwarka, tun kana karami kai mutumne mai zurfin ciki, amma ai bakada wanda zaka iya fadawa damuwarka sama dani da na haifeka, idan wani abune yake damunka kasanar dani.."
"Nifa lafiya lau nake mami, babu abinda yake damuna" yabata amsa,
"Karya kake, tayaya zan yarda dakai bayan kana yin abu irin na marassa lafiya, tunda bazaka fada minba to ya zama wajibi agareni inkaika adubaka, yanzu maganar zuwa chairo da nayi maka dazu to harda kai zamuje, zan kaika kaima su bincika min kwakwalwarka agani domin inajin kasamu tabin kwakwalwa a wannan accident din da kukayi da mahaifinku.."
Murmushi