Showing 6001 words to 9000 words out of 70255 words

Chapter 3 - ALWASHI BOOK 1 COMPLETE by Ummi Aisha .txt

23 Dec 2024

3910

bedroom dinta bai sake cewa koda uffan ba,


Yadade zaune acikin falon kafin ya mike ya fita, washe garin ranar yan uwan tsohuwar matarshi khadija suka zo suka kwashe kayanta kaf basu bar koda cokali ba,


Ita kuwa mami shirye shirye nema masa aure taci gaba dayi, tuni har tabada sautin ahado masa lefe tun daga kasar dubai, amma har yau yusleem bai san koda kalar yarinyar da Mami keson aura mishi ba,


Neman auren saida yayi karfi sosai sannan Mami tace ya shirya yaje yaga yarinyar,


Baiyi musu ba yace to zaije amma kuma baije dinba, shiru shiru baije gidansu nusaiban ba har aka wuce sati biyu, kiranshi Mami tayi tace yazo ya sameta,


Lokacin da yatashi daga office yawuce kiran da mamin keyi masa, a falo ya sameta itada sa'ade mai yimata kitso da kunshi domin Mami irin matan nanne yan gayu shiyasa koda wasa bazaka taba cewa itace ta haifi yusleem dinba domin jikinta bai nunaba gayunta ya boye tsufan,


Zama yayi acikin daya daga kujerun falon yazaro wayarshi yasoma latsawa,


Gaidashi sa'ade mai kitso tayi ya amsa dakyar, saida mami ta sallami sa'aden tatafi sannan ta juya ta fuskanceshi.


"Yusleem meya hanaka zuwa wurin matar da zan aura maka? Tunfa rannan nace maka kaje ku gaisa amma shine bakaje ba?


To lallai lallai kaje yau"




"Mami yarinyar shekararta nawane? Tayi 22?"


Girgiza kai mami tayi, "banajin zatafi 20 gaskiya"


"To agaskiya Mami ni tayi min kankanta da yawa, ina laifin ma yar 23 zuwa 25,amma kawai ni akawo min wata karamar yarinya tazo tana yimin yarinta.."


"Kajishi sai kace wani abun arziki yake yiwa matan idan ankai mishi, ina ruwanka da kankantarta? Kaida duk aure auren nan da kayi bana jin akwai mace kwaya daya da zakace kunyi rayuwar aure da ita, duk fa sakinsu kake yi kafin wani abu yashiga tsakaninku..."


Kawar da kanshi yayi bai kalli bangaren da mamin takeba,


"Koba haka bane..?"




"Mami wai sune suka fada miki hakan?" Yafada yana kallon wani wuri,


"Kai kasani dai,nidai kaji abinda nafada maka yau dinnan kaje wurinta ku gaisa"


Bai amsa ba yatsiri danne dannen waya,


"Wai idan ana yimika magana sai ka hau danne dannen waya, kaji abinda nafada?"


"Naji mami..."


"Ba maganar kaji bane, dama ai nasan kaji, so nake ka aikata abinda nasaka, sannan idan kasan kanada matsala ka fada min tunda wuri sai in nemo maka magani..."


Sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi, shi baya son yaji mami tana irin wannan maganar,


"Kaji abinda nace?"


"Naji, mami dan Allah kibar maganar nan nifa lafiyata kalau"


"Yusleem ai dole inyi wannan maganar domin tazama dole, idan ba marar lafiya ba wanne namiji ne za arinka aura masa kyawawan yanmata yazauna yana kallonsu sai ankwana biyu ka sakesu? Nidai har yau ina nan akan bakana nacewar kana tareda aljana dan haka ya zama wajibi inci gaba da nemar maka mafita"


Sajensa yafara shafawa kansa asunkuye idanuwansa akasa,


"Yanzu katashi kaje kaci abinci inyaso sai ka karasa gida ka shirya kaje can gidansu nusaiban"


Tashi yayi yaje yahau kan dining ya dan fara dudduba abubuwan da aka dafa, tuwon shinkafa da miyar ganye ya saka yadan ci ya mike, har lokacin mami na zaune acikin falo, lekata yayi yai mata sallama yafita,


Shi dai adole zaije wurin yarinyar nan, yasan tunda mami takafe akan sai anyi auren nan to ko me zaiyi bazata fasaba ba, da wannan tunanin yashiga cikin gidansa yaje yayi wanka ya shirya,


Kananan kaya yasaka dark blue din t shirt mai gajeren hannu da bakin jeans, fuskar nan ahade babu alamun fara'a,kamshin turaren albahrainil madina ne ke ta faman tashi daga jikinsa,


Saida yayi sallar magrib a masallacin dake kofar gidanshi sannan ya dauki mota yafita lokacin gari yasoma dan yin duhu,


"Mtswwww.." Yaja dogon tsaki, tsakin yayi tayi yana bin kwatancen da mami tayi masa har yasamu ya gano gidansu nusaiba,


Yana hakimce acikin motarshi ya tura yaro ya kirata, gidan yaketa bi da kallo yana daga cikin motar, gidan ba wani babba bane sai dai rufin asiri,


Yana daga ciki azaune ya hango ta tana fitowa daga ciki, kawar da kanshi yayi daga kallonta sannan kuma bai fito daga cikin motar ba har ta karaso,


Glass din motar ya zuge yayi kasa dashi yana kallonta fuska ahade....






*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_






_Dedicated to MISS XOXO_






*9*






aishaummi.blogspot.com






***Fuska adaure yusleem ke karewa nusaiba kallo aranshi yana mamakin wai shine zai auri wannan yar karamar yarinyar domin shi aduk matan da mami ke aura masa ma babu wacce take kasa da shekaru 23,


Muryar nusaiba ce ta katse masa tunaninsa,


"Ina wuni..?"


Sai da yayi kamar bazai amsa ba sannan ya amsa gaisuwar tata da kyar,


Daga nan yayi shiru itama shiru din tayi domin bata da abin cewa, kallonshi nusaiba keyi yana cikin mota a zaune ita kuma ya barta awaje atsaye saboda tsabar mulki,


Wayarshi ya dauka yafara latsawa zuwa can ya dan kalleta kamar wanda akayiwa dole,


"Sai anjima..."


Glass din motar yayi sama dashi nan ta matsa tabashi wuri yaja motarshi yayi gaba, bin motar da kallo nusaiba tayi acikin ranta tana yaba kyawun siffarshi amma kuma akwai iya tsare gida da dan karen wulakanci nan da nan taji auren nashi ya fice mata arai,


Shikam yusleem tun lokacin da yabar gidansu nusaiba yayi watsi da maganar aurenta domin gaba dayanta bata yimasa ba,


Bai samu zarafin zuwa gidan mami ba sai washe gari da yamma,


Acikin bedroom dinta ya sameta tana yin waya da su khalifa,


Wuri yasamu yazauna akan stoll din mudubinta yana kallonta,


Sallama tayi dasu khalifa ta juya tana fuskantarshi,


"Barka da hutawa mami.."


"Yawwa sarkin taurin kai.., yanzu kai haka dama ake yin zance? Kaje ka tisa yarinya agaba da harara, fuskarka adaure kamar mala'ikan mutuwa.."


Zamanshi ya gyara,


"Mami shiyasa nace maganar auren nan kibarshi kawai, yanzu ahakura da maganar auren wannan yarinyar, ki bani lokaci zanyi miki magana da kaina kuma da kaina zan gabatar miki da yarinyar da zan aura.."


Shiru mami tayi tana dan nazari,


"To yanzu baka jin idan nace afasa iyayenta zasu yimana kallon kananan mutane? Kuma ma duk ba wannan ba, kai dinnan ba tabbas garekaba, nasan ko na baka shekara azuwan ka fito da matar aure ba lallai ne ka iya yin hakan ba"


"Mami kidai bani damar ki gani nidai burina yanzu ki hakura da maganar auren nan wallahi yarinyar nan tayi min karama kofa surayya batayi ba ashekaru.."


"Ehhh to, bari dai sai nayi shawara"


"To shikenan mami Allah yasa ki amince da bukatata.."


"Ai bukatar taka ne bata alkhairi bace amma tunda ka dage zan duba nagani.."


"To mami.."


Mikewa yayi yafita Mami ta rakashi da ido ita yanzu tausayi ma yake bata saboda takamaimai ba asan abinda ke damunsa ba,


Aminiyarta hajiya fa'iza ta Kira wato mahaifiyar khadija matar yusleem tada wacce yasaka,


Shawararta mami ta nema dangane da auren da take nemarwa yusleem, ajiyar zuciya hajiya fa'iza ta ajiye sannan cikin sanyin murya tafara magana,


"Hajiya siyama nidai aganina ki rabuda yaron nan karki sake yimasa wani auren har nan da wani lokaci,


Abinda yasa kikaji nace haka shine, kinga dai nafarko sakin auren da yusleem yakeyi yayi yawa kuma hakan yana haifar da bacin sunansa acikin al'umma sannan kuma suma yaran da yake sakin kinga yana rage musu wata kima da daraja a matsayinsu na yanmata domin koda babu abinda yataba shiga tsakaninsu tofa da zarar ya sakesu sunansu zawarawa sannan iyayensu kamar fa anshiga hakkinsu shiyasa ni nake ganin ahakura da batun auren nan inyaso sai kici gaba da lallabashi har yasamu ya sanar dake matsalarshi..."




Itama mami ajiyar zuciyar ta sauke,


"Hakane hajiya fa'iza, hakika gaskiya kika fadi shikenan insha Allah zanyi yanda kikace"


"Babu komai siyama,Allah dai yabamu mafita"


"Amin ya Allah"


Sallama sukayi mami ta katse wayar, tabbas tasan abinda hajiya fa'iza tafadi gaskiya ne shiyasa ma ta kuduri niyyar zuwa gidansu nusaiba da kanta domin tayiwa iyayenta bayani,




Aranar da yamma taje gidan, lokacin da ta shiga dama ta iske Baban nusaiban da mahaifiyarta sun sakata agaba sai fada suke ta inda suke shiga bata nan suke fitaba saboda tace bazata auri yusleem ba ita tsoranshi takeji,


"Ko zaki mutu kuwa dolenki sai kin aureshi.." Inji mahaifin nusaiba, ganin mami yasa suka dakata daga fadan da suke yiwa nusaiba, nan mami ta sanar dasu anjanye maganar aure amma dukiyar aure wacce aka kai anbar musu,


Bacin rai da tashin hankalin da iyayen nusaiba suka shiga ba kadan bane itada dai mami nan tayi musu sallama tatafi tabarsu da mita.




***


"Hajiya kubra dan Allah ki hakura kidaina kukan nan haka, haba kamar wadda aka yiwa mutuwa? Karfa ki manta tafiya ba mutuwa bace"


Dago da jajayen idanuwanta tayi tana kallon mai gidan nata wanda ke zaune kusa da ita,


"Haba Alhaji, dole nayi kuka ai, yanzu bazan sake ganin amal ba sai nanda shekara daya.."


"Haba hajiya kubra sai kace yarinya, ya kike abu irin na yara ne, ai naga ga waya nan akoda yaushe zaku rinka gaisawa.."


Cigaba da kukanta tayi bata amsa ba, yana shirin sake yi mata magana wayarshi dake aljihunsa tafara ringing nan yacirota yaduba, ganin Wanda ke kiran nashi yasashi saurin mikewa yana kallonta"


"Hajiya kubra ina zuwa, Alhaji Abubakar ne yazo,dama munyi dashi zaizo yanzu, ina zuwa"


Bai jira amsarta ba yayi azamar ficewa daga cikin bedroom din nata yafita zuwa part dinshi...






*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*






_Dedicated to MISS XOXO_








*10*




aishaummi.blogspot.com






***Gidan Alhaji sa'id tawagar mai girma mataimakin gwamna suka wuce direct, hafsat tana zaune abayan mota sai zazzare ido take yi domin bata ma san inda suka nufa ba kasancewar ba fitowa sukeyi ba,




Wani kayataccen gida taga sun shiga wanda ya tsaru mutuka fadin girman gidan kuwa bata baki ne,


Bude mata kofar motar akayi tafito tana bin gidan da kallo,


Wurinta alhaji sa'id ya karasa bayan sunyi sallama da aminin nashi wanda tuni har tawagar tashi tafara fita daga cikin gidan,


Atsorace hafsa take binsa da kallo saboda rashin sabo gashi kuma uwa uba bata taba ganinshi ba,


"Zo mu karasa ciki.." Yace da ita lokacin da yakarasa kusa da ita,


Kamar kurma haka tayi domin bata iya amsawa ba illah bin bayanshi da tayi tana mai cigaba da karewa gidan kallo,


Tana biye dashi abaya har zuwa cikin wani hamshakin falo wanda ya kayatu mutuka da kayan alatun more rayuwa,


Tunda suka shiga cikin falon alhaji sa'id yake kwallawa matarshi kira,


"Hajiya kubra.... Hajiya kubra...,hajiya kubra ko bakya kusa ne?"


Amsawar da yaji hajiya kubran tayine ya dakatar dashi daga kwalla kiran da yake yi mata, falon tafito tana magana muryarta adashe saboda kukan da ta dade tanayi,


"Alhaji gani, har kun dawo?"


"Mun dawo kuma munyi farar tafiya tunda harda tsaraba nakawo miki.."


Hafsat ya nuna mata da yatsanshi, ido ta zaro ta bude baki cikeda mamaki domin da lokacin da ta fito sam bata lura da Hafsat dinba sai yanzu da ya nuna mata ita,


"Alhaji a ina kasamo amal? Dawo da ita kasa akayi?"


Dan murmushi alhaji sa'id yayi, "kidai kalleta dakyau kigani.."


"Alhaji ai naganta, amal ce, ai bai kamata kace adawo da itaba tunda karatunta karuwarmu ce gaba daya.., amal meyasa kika dawo?"


"Hajiya kubra wannan fa ba amal bace mai kamada amal ce, ganin kin tada hankalinki kina neman tayar da nawa hankalin shiyasa na Kawo miki ita.."


Sai a lokacin hajiya kubra tafara bin Hafsat da kallo tun daga kafarta zuwa kayan dake sanye ajikinta, ko shakka babu wannan ba amal bace amma kuma bata da banbanci da amal din sai ko gayu da wayewa wadda amal din zata fita dashi amma hatta kalar fatarsu da komai iri dayane kawai hutu da jin dadi fatar amal zata nunawa ta Hafsat,


"Ikon Allah baya karewa,tabbas wannan babu abinda zai hanani karbarta a matsayin amal domin kamar tasu ta isa.." Hajiya kubra tafada tana takawa har izuwa wurinda Hafsat ke tsaye nan tashiga kare mata kallo,


"Yawwa tunda bukatata tabiya shikenan dama burina ki cire damuwar dake ranki akan amal ki karbi wannan amadadinta"


"Alhaji ina kasamo min ita? Wallahi yarinyar nan batada maraba da'yata.."


"Hajiya kubra zanyi miki bayani daga baya saboda kinga yanzu lokacin sallar magrib yakawo kai, amma abinda nake so dake shine wannan yarinyar nakawo miki ita amana duk da cewar nasan zaki kula da ita tamkar yar da kika haifa saboda tayi kama da jininki amal, yanzu kije kibata duk abinda ya kamata.."


Narai narai da ido hajiya kubra tayi ta kalleshi,


"Amma dai alhaji ba aro aka bani itaba ko? Saboda bana son itama kwana biyu azo ace za arabani da ita"


"Kisha kuruminki hajjaju wannan yarinyar babu abinda zai rabaki da ita domin tazama'yarki halak malak.."


Farin cikine ya bayyana akan fuskar hajiya kubra wanda har saida takasa boye hakan,


"To alhaji, amma naji dadin wannan maganar,nayi mutukar farin ciki.."


Juyawa yayi yanufi kofar fita, cikin farin ciki hajiya kubra ta kama hannun Hafsat tana kallonta,


Tana rikeda hannunta har suka fice daga cikin falon suka shiga wani tafkeken dakin bacci wanda ke dauke da Italian bed pink colour,haka komai na cikin dakin kalarshi pink domin hatta bed sheet din dake shimfide akan gadon pink colour ne,


"Ya sunanki?" Hajiya kubra ta tambayi Hafsat har lokacin tana rikeda hannunta,


Sai a lokacin Hafsat tayi magana tun shigowarta gidan,


"Sunana Hafsat.." Tabata amsa,


"Hafsat, kamarku daya da tilon 'yata kwaya daya amal shiyasa lokacin da naganki naji ina sonki har cikin zuciya..., nan dakinta ne ina so ki daukeshi a matsayin naki, kiyi amfani da duk wani abu wanda kika ganshi acikin dakin nan ko kuma cikin gidan nan.."


Sakin hannunta hajiya kubra tayi tajuya tafita, kan Hafsat adaure tafara bin dakin da kallo tana yaba irin haduwar da yayi domin kamar akasar turai, kan gadon ta kalla nan taga wasu jibga jibgan teddies guda biyu a jingine, kan mirror din dake cikin dakin kuwa kayan make up ne jere tamkar wani dan karamin shago,


Kananan frames ta hango guda hudu ajiye akan bedside drewar nan ta nufi wurin domin tahango kamar akwai hoton wata budurwa ajiki, nan ta nufi wurin da Sauri......








_*Ummi Shatu*_👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_






*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*






_Dedicated to MISS XOXO_






*12*




aishaummi.blogspot.com






***Gaban frames din hafsat ta karasa da sauri ta mika hannu ta dauki guda daya ta kura masa idanuwa tafara kallo,


Gabanta ne yafara faduwa zuciyarta tana bugawa da karfi da karfi Wanda har saida ta kaita da zama asaman gadon dake gefenta,


Ko shakka babu badan rayuwarta agidan marayu tayita ba to da zata iya yarda da cewar wannan ta jikin hoton itace, sake kallon hoton tayi akaro na biyu wanda yarinyar jiki ke sanye da english wears pink din riga da farin wando, kanta sanye da hula pink colour,


"Ikon Allah..." Tafada ahankali tana mai sake dauko wani hoton tafara kallo, nan ta lalace wurin kallon hoton batare data kosa ba.




Kasa koda zama hajiya kubra tayi illah kaiwa da kawowa da take ta faman yi dan tsananin farin ciki, tabbas wannan wani al'amari ne daga Allah Wanda shi kadai yabarwa kansa sani,


Ganin zama yagagara yasata fita ta nufi part din alhaji, shima shigowarsa kenan daga masallacin dake kofar gidansa,


Zama tayi akan kujerar dake makotaka da tashi,


"Alhaji nidai kaganni tsabar farin ciki nakasa zaune nakasa tsaye.."


Murmushi alhaji sa'id yayi,


"To in banda abinki hajiya menene abin kasa tsaye da kasa zaune? Yanzu ina ita yarinyar take?"


"Alhaji dole inkasa zaune in kasa tsaye mana,ai farin cikin da nake ciki bazai barni inyi hakaba, tace min sunanta hafsat, tana can dakin amal nakaita tayi wanka ta shirya sai tafito muyi dinner.."


"Hakan yayi daidai hajiya kubra,nidai abinda nakeso dake shine dan Allah ki rike yarinyar nan bisa amana duk danasan zaiyi wuya ki gallaza mata tunda bata da maraba da amal to amma wani lokacin ku mata ana ganin kamar kunfi kowa tausayi da rauni sai dai akan gallazawa yaran da ba nakuba kunfi kowa nuna rashin tausayi da rashin rauni, dan Allah ki riketa amana tunda kinga daga gidan marayu na daukota wannan yana nuna cewar ita maraya ce..."


"Haba alhaji ai basai kayi min wannan nasihar ba domin ko wanine yakawo min wannan yarinyar wanda bakai ba wallahi zan kula da ita..."


"Nasani hajiya kubra, Allah yayi miki albarka, yanzu ina tunanin ai tagama ko?"


"Ehh to bari indubo ingani"


Tashi tayi tafita takoma part dinta, dakin amal ta tura tashiga nan ta iske hafsat zaune ta kurawa hotunan amal ido ko kifawa bata yi,


"Hafsat..." Ta kira sunanta bayan takarasa kusa da ita, dagowa hafsat tayi ta kalleta,


"Na'am"


"Ya bakiyi wanka kin canja kayan jikinki ba? Tashi ki shiga bathroom kiyi wanka indan kin fito ga drewar din kayan amal nan ki duba duk wanda yayi miki kisaka.." Ta karasa zancen tana nuna mata drewar din da dan yatsanta,


"To" hafsat ta amsa har lokacin tana cike da mamaki domin ganin abubuwan dake faruwa take yi tamkar acikin mafarki,


Fita hajiya kubra ta sake yi ganin haka yasa hafsat tashi ta shiga cikin bathroom din, komai wanda ake bukata akwaishi acikin bathroom din babu bata lokaci tayi wanka ta fito, man da zata dan shafawa fatarta ta shiga nema domin duk wadanda ke kan dressing mirror din lotion ne dan haka dakyar tasamu wani me dan kama da Vaseline tashafa,


Gaban drewar taje ta bude nanfa mamaki yacikata domin kayane iya ganinta shake acikin drewar din,


Wata doguwar riga kalar ruwan hanta ta zaro da dan kwalinta tasaka ta dauki hijabinta tayi salla,tana saman abin sallar azaune a inda aka kebe musamman domin yin salla hajiya kubra tasake shigowa fuskarta dauke da murmushi,


"Hafsa kin idar ne?" Tajiyo muryar hajiya kubra na tambayarta,


"Ehh na idar.." Tabata amsa tana kokarin mikewa,


"Yawwa to taso kizo muje wurin alhaji"


Bin bayanta tayi suka fita, tiryan tiryan tana biyeda ita har suka shiga falon alhaji sa'id Wanda ke zaune yana kallon labarai a tauraron dan adam,


Ganinsu yasashi rage volume din tv din ya fadada murmushinsa yana kallonsu domin sai yake ganin kamar hajiya kubra ce da amal suke dososhi kamar yadda suka saba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login