Showing 30001 words to 33000 words out of 70255 words
sallar isha sannan ta iya mikewa,dakin duhu didim yake saboda babu wuta ga uban sauro banda zafi da yake addabarsu,
"Gaskiya yaya yusleem muyi sallar nan muje mu samo abinda zamu ci daga nan sai mu taho da maganin sauro.."
Suna idar da sallar suka fita, gasasshiyar kaza Hafsat tace asiya nan yusleem ya kalleta,
"Yanzu fa ba lokacin cin abin dadi bane, kibar kazar nan muje shagon can mu sai gari da sugar.."
"A'a yaya yusleem, gaskiya gari bazai shiga ba wallahi, mudai siyi kazar.."
Son ranta yabi suka siyo gasasshiyar kazar daga nan suka karasa shago suka siyi maganin sauro da candle guda biyu da ashana sai sabulun wanka give sinki daya da soson wanka da brush da maclean sai man shafawa Vaseline,
Gida suka koma ya kunna candle din ya ajiye sannan ya kunna musu maganin sauro,
Kasancewar yunwar tasu taci ta cinye yasa baifi rabi suka ci kazar ba, Hafsat ce tafara tashi ta bude trolley dinta ta dauki zani tadauki soso da sabulun wanka da brushes dinsu da maclean ta shiga bathroom, wanka tayi tafito ta dauki kayan baccinta takoma cikin bathroom din,Riga da wando ne red colour masu santsi, rigar tana da dan guntun hannu yayinda wandon yake dogo,doro hijabinta tayi akan kayan tafito tahau kan katifa ta kwanta,
"Bari nima inje inyi wankan tunda kin fito" yusleem yafada tareda tashi tsaye ya shiga cikin toilet din, yajima aciki kamar wanda zai sake fata dama Hafsat tasan dadewarshi a wanka shiyasa tafara shiga,
Saida yayi kusan minti 30 sannan yafito yana rikeda rigarshi yana tsane ruwan kanshi,
Gaban kayansu ya karasa ya bude trolley dinshi yaciro yar t shirt da boxer,
Ta dan hasken candle din da suka kunna Hafsat take kallonshi lokacin da yake kokarin sauya kayan jikinshi,
Rufe idanuwanta tayi saboda wannan shine karo nafarko da zata kwana dashi akan katifa guda daya,
Juyowa yayi ya kalleta bayan yaje ya dauke kakkauran labulen kofar dakin yabar mai shara sharan,
"Ko ke bakya jin zafin ne?"
"Inaji mana yaya yusleem, wallahi akwai zafi kila hadari ne agarin"
Candle ya dauka yakarasa gefen katifar yazauna,
"Bama kila bane ga gari nan anata yin walkiya, kalli waje ki gani"
Sai lokacin talura da ashe asaitin kofar daki ta kwanta nan ta mirgina takoma barin da yake,
"Anan zan kwanta, kai kakoma can barin"
Tashi yayi yakoma bayan yakashe candle din,duhu didim dakin yayi,
"Shine ni kika turo ni kofar daki ko inyaso abin tsoron idan yazo ni ya kamani"
Murmushi tayi ta zare hijabin dake jikinta,tana jinshi ya kwanta agefenta bayan ya matso da filonshi jikin nata filon sabanin da dayake ajiye acan karshen katifa.....
*_Ummi Shatu_*👌🏻© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to MISS XOXO_
*30*
***Dukkaninsu shiru sukayi kowa da abinda yake tunani acikin zuciyarsa,
"Nanah..." Taji yusleem yakirata, dan juyawa tayi acikin duhun ta kalleshi,
"Yaya yusleem menene?"
"Babu komai dama nayi zaton ko kinyi bacci ne"
Juyawa tayi ta dan gyara kwanciyarta,
"A'a banyi ba"
"To kiyi.."
Lumshe idanuwanta tayi,
"Saida safe"
"Allah ya tashemu lafiya"
Shiru suka sakeyi wanda har bacci ya dauke Hafsat amma shi yusleem sam yakasa baccin inbanda sake sake babu abinda zuciyarshi keyi masa, yasaka wancen ya kunce yasaka wancan har garin yayi tsit dare ya raba bai iya yin bacci ba,
Hafsat kuwa cikin barcin da takeyi tafara wani mafarki marar dadi domin wasu manyan mutane tagani suna bin yusleem aguje kowannensu rikeda katuwar wuka mai kaifi sai kyalli take zuwa can yusleem din ya fadi daya daga cikinsu ne ya cimmasa ya daga wukar zai daba masa tayi firgigit ta farka,
Cikin duhun tafara lalubenshi akan katifar amma bata jishiba hakan yasata rudewa,
"Yaya yusleem,yaya yusleem...!"
Shiru tayi sakamakon jin ya amsa daga bakin kofa inda yaje domin saukar da labulen dakin domin yanzu garin yadauki sanyi duk da ba ayi ruwa ba amma wata iska mai sanyi ake kadawa,
Karasowa yayi kan katifar, tun kafin yakarasa hawowa taje ta rirrikeshi,
"Yaya yusleem babu abinda yasameka...?"
Riketa yayi ya kwantar da ita awurinda take kwance dafarko,
"Menene yafaru nanah? Lafiya lau nake.. Mafarki kikayi?"
Hannuwanshi ta makalkale cikin nata,
"Yaya yusleem wani mummunan mafarki nayi wallahi..."
"To ai mafarki ba gaskiya bane nanah, ki koma kiyi baccinki kinji..."
D'aga mishi kai tayi kamar yana ganinta tareda tallafe kumatunta da hannunshi guda daya,
Duk da taga azahiri babu abinda ya sameshi amma sai takasa komawa baccin, shi kanshi yusleem din shima yakasa yin barcin,
"Yaya yusleem.."
"Na'am..."
"Tunda mun kasa yin bacci katashi muyi alwala muyi sallar nafila watakila sai Allah ya amsa ya rangwanta mana masifun da suke tunkaro mu..."
"To nanah, bari natashi naje.."
Saurin rikeshi tayi, "yaya yusleem mu tafi tare"
Taren suka shiga toilet din kasancewar duhu ne alwala sukayi suka fito suka fara sallolin nafila wanda har saida suka yi sallar asuba sannan suka kwanta bacci, bacci sukayi sosai sai 12 saura sannan Hafsat ta farka, yusleem takalla wanda ta rirrikeshi yana kwance agefenta,
Tashi tayi tashiga wanka har tafito ta shirya bai tashiba tunanin abinda zasu karya dashi tafara, mikewa tayi tashiga bathroom ta dauko bucket domin debowa yusleem ruwan wanka,
"Nanah ina zaki..?" Taji yace da ita idanuwanshi suna rufe,
"Ruwan wanka zan debo maka..."
Tashi zaune yayi,
"Dauko wani bucket din inbiki mu debo tare"
"Kabarshi zan debo"
Tashi yayi dakanshi yaje yadauko bucket din yabita domin ita tuni tajima da fita, kamar jiya yauma matan gidan suna zazzaune akofar dakin daya daga cikinsu, ganin Hafsat tafito duk sai suka maida kallonsu gareta, gaishesu tayi kamar jiya sannan takarasa bakin rijiyar,
Gugar yusleem ya karba daga hannunta,
"Kawo inzuba miki.." Yayi maganar ahankali duk da dama maganarshi bawai cika karfi tayiba,sakar mishi tayi yafara janyo ruwan yana zuba mata acikin bucket din,
Ganin hankalin matan ya komo garesu yasa duk taji ta tsargu musamman ma dataga kamar sunfi karkata ga kallon yusleem, saida ta jirashi ya cika nasa bucket din sannan suka dauka suka tafi,
Acikin bathroom din tabarshi bayan ta ajiye ruwan tafito,
Keken sakarta ta kinkimo ta zauna agefen katifa tasoma saitashi domin so take tafara yin sakar kayan sanyi, jin tafiyar yusleem yasata juyawa ganinshi tayi babu riga sai iya boxer dan haka tayi saurin maida kanta ta sunkuyar,
Kanta yana sunkuye har yagama shiryawa yasaka kayanshi yadawo kan katifar ya Zauna,
"Yaya yusleem ga guntun naman jiya can bari indauko mana.."
Kafin yabata amsa har tatashi taje ta dauko,
"Kaga cewa nayi ko inje insaida kujeru na sai insiyo zaren bulu da sauran kayan da zamu bukata, kaga dole sai mun siyo risho da kayan abinci.."
Shiru taji yayi baice komai ba, dagowa tayi ta kalleshi,
"Yaya yusleem bakace komai ba"
"Nanah gaskiya akaina bazaki rabu da kayanki ba, karki saida ko cokali naki"
Murmushi tayi,
"To ai ba saboda kai zan siyarba, saboda nida kai zan siyar"
"To ban goyi baya ba"
"Shikenan tunda baka amince ba"
"Ba amincewa ne banyiba kawai dai idan narabaki da kayanki ne banyi miki adalci ba"
"To magana tawuce,yanzu kasan me? Kafadawa mami cewar zakayi tafiya ta gaggawa zuwa wani state din mai nisa saboda kasan zata nemeka idan kuma har ta nemeka bata sameka ba hankalinta tashi zaiyi, idan tayi maka maganata kace tare zamu tafi kaga hankalinta zaifi kwanciya sannan tunaninta bazai taba Kawo mata cewar da akwai matsala ba.."
"To amma iyayenki fa? Sukuma me zan fada musu"
"Sudinma hakan zan cemusu munyi tafiya zuwa wani gari mai nisa, koma kawai muce Niger muka tafi.."
Hadaddun wayoyinshi dake ajiye akasan trolley dinshi hadeda laptop dinshi yadauko ya kunna,
Number mami yayi dialing babu bata lokaci ta dauka, dakyar ya saita nutsuwarshi yayi mata bayani bayan sun gaisa, fatan alkhairi tayi musu daga nan sukayi sallama,
"Nima bari inkira Ummi infada mata kaga shikenan daga nan mun gama da matsalar gida sai mu fuskanci wata rayuwar kuma"
Tata wayar itama ta dauka ta kira Ummi ta sanar mata daga nan takashe wayar amma shi yusleem tashi wayar abude yabarta saboda yasan abokan harkarshi zasu nemeshi.
Misalin karfe 2 narana ta dauki dan madaidaicin food flask, fita tayi domin yusleem bacci yakeyi, tsakar gida taje inda matan nan ke zazzaune ta tambayesu inda ake sayar da abinci,
"Me kike so? Kawo amir yasiyo miki" inji wata mata wacce ahaife da alama bazata girmeta ba,
"Yawwa nagode dan wanke nakeso"
Naira dari tabayar yaron yatafi siyo mata, daki takoma tazauna tana lissafi domin kudin da yayi saura yanzu baifi dubu goma sha daya da yan canji ba gashi kuma bukatunsu nada yawa domin basuda kayan abinci kuma zasu cikawa mai gidan haya kudinsa gashi tana son ta siyo zaren saka,
Yanke hukuncin zata sayar da kujerunta kawai tayi batareda yusleem yasaniba, jin muryar amir yana sallama yasata tashi taje ta karbo abincin ta danka mishi naira goma,
Bata tashi yusleem ba saboda tasan daren jiya bai samu bacci ba har saida ya tashi dan kanshi lokacin karfe 3:32 na yamma,
Dan waken tasa musu suka ci bayan sun gama tace mishi zata fita kasuwa domin siyo zaren kulu da dan abubuwan da ba arasa ba, acikin dakin tabarshi tafita,
Direct wurin wasu kafintoci tawuce tayi musu tallen kujerunta sukace zasu siya amma sai sun gansu nan tace to zuwa gobe zatazo suje sai sugani,
Daga nan kasuwa tawuce tasiyo zarirrukan kulu kala kala sannan ta siyo musu dan karamin risho ta hado musu kayan tea da babban bread guda daya,
Ana kokarin yin sallar magrib tadawo gida, akan katifa tasamu yusleem yana zaune,
"Sannu nanah.."
"Yawwa yaya yusleem sannu nabarka kai kadai ko"
Murmushi yayi, "ai kece da sannu"
"Kaga abubuwan da nasiyo, ga risho amma kalanzir dinne na dari biyu kawai nasiyo nasan zai ishemu mu rinka dan dafa ruwan zafi"
Tausayinta yaji yakamashi saboda irin rayuwar da suka samu kansu aciki yanzu wacce yasan shine silar jefata aciki,
"Allah yayi miki sakayya da gidan aljanna.." Shine abinda yafada kawai ya mike yashiga toilet domin yin alwala,
Tea tadafa musu da daddaren suka sha suka kwanta, wayarshi ce ta hau vibrating nan yadaga,
"Yusleem kayi gaggawar kashe wayarka domin su oga nemanka suke ido rufe, idan baka kashe wayarka ba zasuyi tracing wurinda kake..." Wannan shine abinda kunnuwan yusleem suka ji wanda bai gane ko muryar waye ba kitt yaji wayar takatse nan yakashe wayar gaba daya,
Sam baya son Hafsat taji bare hankalinta yatashi nan yaki fada mata gaskiyar abinda yake faruwa domin tun lokacin data fita suke fafatawa shida abokan harkar tasa domin sun ce mutukar yace yabar wannan harkar to sai dai wani bashi ba saboda sun san tona musu asiri zaiyi,
Jin baice komai ba yasa Hafsat bata Kawo komai acikin ranta ba daga karshema tashi tayi ta kunna candle tahau keken sakarta tafara saka kayan sanyi na yara, sai wurin 12 sannan ta hakura ta kwanta.
Washe gari dakyar da dabara yusleem yabarta tafita, wurin masu siyan kayan nan da sukayi alkawarin siyan kujerunta ta nufa daga can suka wuce gidan yusleem nada tabude musu sukaje suka gani, ganin kyawun kayan da irin tsaruwar gidan sai masu siyan kayan suka nemi fasawa domin gani suke kamar karya take banata bane ko kuma ba mallakinta bane dakyar tashawo kansu akayi cikini dubu 50 suka siya duk da kayan sun wuce haka,
Fita sukayi da kujerun tamayar gidan ta rufe ta nufi kasuwa da kudin, komai da tasan zasu bukata na kayan abinci saida ta siya musu, data gama siyayyar kuwa adaidaita sahu ta nema ta zuba kayan yakaita har kofar gida.
Yusleem na kwance agefen katifa bayan ya kammala dafa musu ruwan zafi wanda zasu sha tea sai gata tashigo niki niki da kaya, manyan idanuwanshi yazuba mata,
"Daga ina haka?"
"Ina zuwa yaya yusleem ai zan fada maka"
Tashi yayi ya taimaka mata suka karasa shigo da kayayyakin,
Kudin hannunta ta ajiye ta zare hijabin jikinta ta zauna,
"Yaya yusleem nagaji sosai gashi ina jin yunwa"
"Bari inhada miki tea.."
Kafada ta makale,
"Gaskiya ni bazan sha tea da wannan uban zafinba, tunda ga kayan abinci sai ka dafa min abinci inci"
"To ai baki fada min a inda kika samo wadannan kayan abincin ba.."
"Zan fada maka kafara bani abinci inci tukunna mana"
"Nifa ban iya girki ba sai dai kiyi guiding dina"
"To fara kunna risho din ka mayar da ruwan zafin can ka dora.."
Kamar yadda tace haka yayi, yanayi tana kwatanta mishi har yadafa musu farar taliya yasoya mai,
Acikin filet ya zuba musu yakai gabanta inda take kwance, hannunshi ya mika mata amma sai tayi kamar bata ganiba ta tashi zaune cikeda kunya,
Saida suka gama cin abincin sannan ta fada mishi duk yanda akayi,
"Yanzu ga 10 thousands din wannan alhajin cikon kudin hayarshi idan yazo sai abashi, wannan kuma 9 thousands din sai mu ajiye.."
Rasa abinda zaice yayi yatsaya kawai yana kallonta saboda yasan acikin mata dari dakyar za asamu irinta guda goma, Hafsat tayi masa halacci acikin rayuwarsa, ta rufa masa asiri, tayi sanadiyyar fitarshi daga cikin halaka, gashi tana zaune dashi a lokacin da bashida madafa har tana salwantar da abubuwan data mallaka saboda shi,
"Nanah banida bakin da zan gode miki illah..."
Tashi tayi tabar dakin ta wuce toilet saboda bata son yayi mata godiyar abinda tayi,
Cikin dare ta tasheshi tana makale da cikinta saboda wani irin ciwo mararta keyi mata, riketa yayi acikin duhun da suke yana tambayarta menene,
"Yaya yusleem cikina ne yake ciwo"
"Ciki kuma? Sannu to yi hakuri"
"Bani ruwa insha.."
Ruwa ya Kawo mata takarba tasha takwanta, candle ya kunna yajata jikinshi yadora kanta akirjinshi ya rungumeta yasoma rarrashinta hannunshi yakai kan cikin nata nan tayi saurin ture hannun,
Kwanciya luff tayi ajikinshi sakamakon duk gabobinta ciwo suke yimata, tambayar duniya yayi mata akan tafada mishi abinda yasa mata ciwon cikin amma tayi shiru saboda kunya takeji tace mishi period pain ne,
Ajikinshi ta kwana har asuba tayi sai lokacin tasamu saukin ciwon da marar tata keyi bacci yadan dauketa kwantar da ita yayi ya nufi toilet,
Sai wurin karfe 6 sannan tatashi daga baccin nan tarasa yadda zatayi tana son tafada mishi kuma tana kunya, komawa tayi ta kwanta ta kalleshi,
"Yaya yusleem kira min amir dan gidan maman amir.."
"Meya faru?"
"Aikenshi zanyi.."
"Toh bari naje"
Tashi yayi yafita ita kuma ta rakashi da ido...
*_Ummi Shatu_*👌🏻© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to MISS XOXO_
*31*
****Bai wani jima da fitaba sai gashi yadawo, kusa da ita yakarasa ya tsugunna agabanta,
"Su maman amir din basu bude kofar su ba inaji basu tashiba.."
Gyada mishi kai tayi taja bargo zata lulluba, rike bargon yayi,
"Kitashi kiyi salla mana kafin kisake kwanciya"
Shiru tayi masa tasake yunkurin lulluba, kara maimaita maganarshi tafarko yayi,
"Ba yanzu ba.."
Ganin ta dage taki tashi yasashi rabuwa da ita tasake lulluba takoma barci, gefenta yaje ya kwanta,
K'arfe 8 tafarka ta kalli yusleem wanda ke gefenta akwance,
"Yaya yusleem dubo min ko su Maman amir din sun tashi.."
Tashi yayi yafita jim kadan sai gasu sun dawo tareda amir din,
"Yaya akwai biro awurinka?"
"A'a babu"
"Amir jeka wurin ummanka kace tabani aron biro da yar paper kaji"
Tafada tana ciccije lebenta, fitar amir tasa yusleem komawa wurinta,
"Har yanzu ciwon ne?"
Daga mishi kai tayi,
"To ko asibiti zamuje?"
"A'a"
Shigowar amir yasa sukayi shiru dukkaninsu, karbar takarda da biron tayi tana daga kwance ta rubuta mishi abinda zai siyo mata ta kalli yusleem,
"Yaya yusleem bashi dari biyu acikin kudin nan"
Tashi yusleem yayi yadauko kudin yabashi, sake gyara kwanciyarta tayi ta tukunkuna har amir yadawo kasancewar yusleem yana tsaye bakin kofa yasa amir bashi ledar pad din,karba yusleem yayi ya leka cikin ledar, sai yanzu ya fahimci abinda yake damunta,
Tana kokarin tashi domin yin wanka ya dakatar da ita,
"Tsaya indafa miki ruwan zafi sai kiyi wankan dashi zaki fi jin dadin jikinki"
Komawa tayi tasake kwantawa shikuma ya dora mata ruwan zafin bayan ya kunna risho,
Bathroom yashiga ya dauko bucket yazo ya juye mata ruwan aciki yakai mata cikin toilet tareda sirka mata shi,
"Ga ruwan wankan can nakai miki, tashi kije kiyi"
Dakyar ta tashi tajuya ta dan kalleshi ganin ba ita yake kalloba hankalinsa yana kan ruwan da zai sake maidawa ya tafasa yasata saurin tashi bayan taja zanin wankanta tashige cikin bathroom.
Bata dade sosai ba tafito lokacin har yusleem ya kammala hada musu abinda zasu karya dashi, kallonshi take kasa kasa saboda duk yau atakure take,shi kansa ya fahimci haka shiyasa ma yajuya mata baya bayan ya kwanta bisa katifa,
Ganin baya kallonta yasata dan sakewa tashirya tasaka wata blue din atamfa dinkin riga da skirt wanda dayane daga cikin irin dunkunan da mami tayiyyi mata,
Zama tayi abakin katifa wanda yayi sanadiyyar juyowar yusleem,
"Kin gama?"
"Uhm" tabashi amsa,
Tashi yayi ya debo mata tafasasshen ruwan zafi acikin cup,
"Kisha wannan ruwan zafin zai dan rage miki radadin ciwon da marar taki keyi"
"Ni ba ciwon Mara nakeba ciwon cikine"
Murmushi yayi ya mika mata cup din,
"Ashe dai ke dinma kin iya karya ban saniba, meye hadin period da ciwon ciki? Ai nazaci mahaifa a mara take ba acikin cikiba ko ke taki acikin ciki take?"
Karbar cup din tayi tasoma kurbar ruwan zafin batare da tayi magana ba har saida ta shanye,
"To ga abinci kuma taliya"
Girgiza masa kai tayi ta kwanta babu jimawa sai bacci, rasa abinda zaiyi yayi saboda dama idan tana ido biyu ne suke yin yar hira, shi dinma kwanciyar yayi tun yana yan tunane tunane har bacci ya daukeshi,
Hafsat ce tafara farkawa yanzu taji dadin jikin nata sannan kuma ciwon ma yaragu sosai sai kadan kadan, ganin yusleem din bacci yake yasata zuba abincin ita kadai ta danci tana gamawa yatashi, fita tayi tace mishi zataje wurin maman amir,
Dayake mata babu wuyar sabo tunda taje suke hira da maman amir din kasancewar itama mijinta baya nan dama kuma police ne,
Yau duk taki sakewa ta zauna wuri daya da yusleem saboda kawai yagane abinda ke damunta, da tashiga dakin zata fice takoma wurin maman amir shi kanshi yusleem din ya lura da ita,
Tun azahar da tashiga wurin maman amir sai yamma lis tadawo wannan dinma dan wanka zatayi ne, yana kwance ta shigo taki kallon inda yake tadauki abinda zata dauka tashiga wanka bakar ledar da tasaka pad din data cire da rana taga ya dauke yadora akan window din bathroom din, acikin toilet din tashirya dan haka koda tafito iya kaya kawai tasa tashafa dan mai tagama tafita.
Wasa wasa