Showing 57001 words to 60000 words out of 70255 words

Chapter 20 - ALWASHI BOOK 1 COMPLETE by Ummi Aisha .txt

23 Dec 2024

3905

lokacin da yakoma gida bai sameta afalo ba iya hafsat kadai yatarar tana zaune tana kallon wani Indian film kites,


Jiki asabule yazauna akusa da ita ya mika mata maganin ta karba tana kallonsa bayan tahada ledar maganin da hannunsa ta ruke,


Jingina da jikinta yayi ya ajiye kansa bisa kafadarta......






_Gaisuwa mai tarin yawa ga besty na Phertymarh Xarah._








*_Ummi Shatu_*👌🏻




© *HASKE WRITERS ASSO.*








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*








_DEDICATED TO MISS XOXO_








*55*






***Hular kanshi ta cire tasoma shafa sumarshi ahankali, dan lumlumshe ido yafara yana sake nanuka jikinta domin wani kamshine yake fusgarsa,


"Yaya yusleem lafiya kuwa?" Tace dashi tana rike hannunshi,


"Lafiya lau baby, kamshinki ne yake neman tada min da hankali..."


Saurin juyowa tayi ta kalleshi,


"Meyayi? Ko kamshinsa ne baiyi maka ba?"


Murmushi yayi yadafa kafadarta,


"Easy, ba abinda nake nufi kenanba, tsananin dadin kamshinshi ne ke neman juyar min da kwakwalwa..."


Murmushi tayi ta tureshi ta tashi tanufi dakin mami domin kai mata maganin da yasiyo mata,


Mintuna kadan tafito ta dauki ruwa roba daya tasake komawa, wannan karon ta dan jima sannan tafito, amike taganshi kwance kan doguwar kujera,


Durkusawa tayi akasa ta dora hannuwanta ajikin kujerar,


"Ba yanzu zaka shiga ka kwanta ba?"


Hannuwanta duka ya riko yajata kan ruwan cikinshi,


"Gani nayi kinje wurin mami kinyi zamanki shiyasa na kwanta anan..."


"To ba gashi nafito ba"


Yana kokarin kai hannunta guda daya bakinshi mami tafito,


Tashi hafsat tayi gaba daya kunya tagama lullubeta domin tasan mami tagansu, sum sum tawuce cikin bedroom batare da tayi magana ba,


Zaune yatashi yana kallon mami wacce tawuce dining area batare da ta kalli wurin da yakeba,


Handset dinta yaga ta dauko wanda da alama mantata tayi awurin,


"Sannu mami, yajikin naki"


"Yawwa sannu, dasauki"


Mami tace dashi tareda wucewa bedroom dinta, yajima zaune awurin kafin ya mike ya nufi bedroom wurin hafsat, tana gaban mirror daure da zani tana shafa wasu dadadan turaruka, khalta maryam,da musk altahara,


Ajiye mata ledar maganinta yayi yatsaya kawai yana kallonta,


Juyawa tayi ta kalleshi itama,


"Ya yusleem ya akayi?"


Hannunta yariko cikin nashi yazauna agefen gado ya zaunar da ita ajikinshi,


"Yau basai kinsa sleeping dress ba" yarada mata acikin kunnenta, kunyace ta rufeta, dan dukan kirjinshi tayi ahankali, ta cusa kanta agefen wuyanshi,


"Kaga dazu ma haka kasani naji kunya"


"Da nayi me?"


"Da ka sa mami tazo taganmu mana"


Mikewa yayi ya kwanta ya kwantar da ita ajikinshi yana murmushi,


"Ai ba laifina bane"


"Laifin waye?"


"Laifinki mana"


"Laifina fa kace"


Lumshe idanuwanshi yayi yana sake matseta ajikinshi,


Sun jima ahaka zuwa can bata san meya faruba sai ji tayi ya sassauta rungumar dayayi mata yafada kogin tunani,


Kin bari yayi ta fuskanci cewar akwai abinda yake damunsa nan ya lallabata bacci ya dauketa, kwantar da ita yayi yatashi zaune yayi shiru yana nazari,


Jin zaman ya gundureshi yasashi tashi tsaye yafara kai kawo acikin dakin, sam yau bayajin bacci sannan yarasa dalilinsa na damuwa da lamarin hafsat yar gidan alh musa, haka kuma yana jin wani irin abu mai kamada tausayi tausayi yana yimasa yawo akirjinsa gameda ita,


Kukan da yaga tatafi tanayi shine yafi komai tsaya masa arai,kusanma shine makasudin rashin baccinsa, yarasa ta inda zaibi ya bullowa wannan al'amari domin shi dai ara'ayinsa baida niyyar kara aure, yafi son ya zauna da Hafsat ita kadai ya nuna mata soyayyar da sauran mata basu samuba to amma kuma ita rayuwa kana nakane Allah yana nashi kuma komai mukaddarine daga gareshi,


Bude idanuwanta tayi nan taganshi tsaye yayi shiru abisa dukkan alamu baiyi bacci ba,


Sauka tayi ahankali daga kan gadon tanufi wurinshi, dafa kafadarshi tayi nan yayi saurin juyowa yana kallonta,


"Ya yusleem...., meke damunka? Menene ya hanaka bacci? Tunanin mekakeyi?"


Kago murmushin dole yayi yasa tausasan yan yatsunshi ya kamo nata,


"Babu abinda nake tunani baby nah, baccin ne naji yaki daukata shine kawai nataho nan nake dan zagayawa"


Murmushi tayi ta dan sake yin kasa da muryarta,


"Kafada min gaskiya dai, kodai?"


Murmushin shima yayi mata ya dauketa cak yanufi makwancinsu da ita,


"Kema kindai san idan nace miki bata damuna karya nake yimiki...."


Mayar da fuskarta gefe daya tayi tana murmushi aranta tana tunanin abinda zaije yazo duk ranar da aka tabbatar masa da yagama samun lafiya domin shima taga kamar fitinanne ne,


"Yanaji kinyi shiru?"


"Ehh bacci nake son komawa"


Mirginata yayi takoma kasa yayi pillow da kirjinta, tun tana dan shafa sumarshi har yaji shiru alamun tayi bacci, shikam dakyar yasamu ya iya bacci cikin wannan dare.


Tunda wannan maganar ta shiga tsakaninsu da Hafsat shikenan bai sake ganinta ba koda yaje gidan sai dai kusan kullum yana ganin massage dinta taturo mishi,


Bayan kamar sati biyu da faruwar al'amarin da wani yammaci yaje gidan bayan sun gaisa da alh musa yafito ya hangeta tsaye jikin motarshi tana wasa da key din motarta wanda da alama dawowarta kenan taga motarshi,


Dan hade rai yayi yanufi wurin,


Ganinshi haka yasata yin dan murmushi,


"Ya yusleem menene abin bata ran? Dama kawai tsayawa nayi mugaisa sannan in tambayi lafiyar takwarata da na yaranta"


Batare da yasaki fuskarshi ba yace,


"Tana lafiya"


Bashi wuri tayi ta tsaya tana kallonshi bata kara maganaba yashiga motarsa yafita daga gidan, yana cikin driving yaji karar shigowar text massage,


_Ya yusleem insha Allah sai na aureka kuma zakace nafada maka..._


Cilla wayar kan kujera yayi yaci gaba da driving dinshi bayan yagama karanta sakon.


Akasalance ya karasa gida,babu kowa afalon mami dan haka kai tsaye yawuce cikin bedroom dinta nan dinma bata nan sai lokacin yatuna da cewar baiga motarta ba lokacin da yashigo, dakin hafsat yawuce ita dinma bata ciki, fitowa yayi yana tunanin to kodai tareda mamin suka fita da wannan tunanin yakarasa cikin bedroom,


Zaune yaganta tana goge mishi kananan kayanshi data wanke ta kunna laptop dinshi tana sauraren wakar dayake muradin so wadda kusan koda yaushe sai yajita,


Tsaye yayi yana kallonta yana dan murmushi domin yasan bata san yashigo ba,


Ahankali ya sadada yarufe mata ido da hannuwanshi ai kuwa ta kurma wani uban ihu tana salati,


Dariya ce taci karfinshi ya fada jikinta yanayi bayan ya bude mata idanuwan,


Kashe iron din tayi tahau dukanshi, hada hannayenta duka guda biyun yayi ya rike yana yimata dariya,


"Allah ya yusleem sai nafawa mami abinda kayi..."


"Yi hakuri hafsat, ke dince kika bani dariya sosai"


"To bakaine ka tsorata ni ba"


"To kiyi hakuri, kinga anjima dama ina son ki rakani anguwa"


Fadada murmushinta tayi,


"Tom shikenan, yanzu bari inhada maka ruwan wanka idan ka shirya sai muje kaci abinci"


"To tashi ki hada min"


Tashi tayi tashiga bathroom kafin tafito yayi sauri ya cire kayan jikinshi yabita ciki dole sai tare sukayi suka fito tanata kumbura fuska,


"Shikenan bazan karaba tunda bakya son ladan, kiyi hakuri"


Kin kallonshi tayi yayinda shikuma ya kafeta da nashi manyan idanuwan, bai san daliliba bakar fatarta tana yimasa kyau,


"Gaskiya koda ace mata hudu zanyi to duk bakake zan aura"


Dan harararshi tayi taci gaba da shafa masa mai,


"Kullum kuma sai kaita ganin kala daya babu canji?"


"Ehh mana ai tafi kyau"


Shiru tayi masa takarasa shiryashi takoma shirya kanta, kananan kaya yasa dark blue din t shirt da blue din jeans iya gwiwa,


Tattarawa sukayi suka nufi part din mami lokacin tadawo tana zaune tana waya dasu Abdul wadanda zasu dawo wani satin,


Zama sukayi takawo masa abinci yaci sannan suka yiwa mami sallama suka fita,


Ac ya kunna musu acikin motar ya rufe gaba daya glasses din ya kunna wata waka ta turanci _you are my African queen..._,ahankali wakar take tashi yanabi yana makale da hannun hafsat guda daya acikin nashi yana driving da dayan,


Wata hamshakiyar unguwa tamasu fada aji taga yakaisu, wani tangamemen gida suka shiga mai manya manyan part har guda hudu sannan kowanne upstairs ne,kuma daga can gefe B/Q ne,


Nafarkon yabude suka shiga nan taga tangamemen falo da kitchen da store sai dining area, saman kuma bedrooms ne guda biyu masu dauke da bathroom acikin kowanne,


"Kinga gidan da na sai mana zamu dawo nan bada jimawa ba domin har nabada asiyo furniture's,nafi son ina dawowa daga Cairo insauka anan"


"Wai amma gidan ya hadu yaya, ga girma komai awadace.."


Murmushi yayi yariko hannunta suka fito, "kin dai k'i zancen ko?"


Murmushi tayi,


"To amma yanaga part din guda hudu?"


"Daya namu, daya na mami, daya nasu Abdul"


"To dayan fa?"


"Na amarenki"


Duka takai mishi,


"Allah kabari"


Dariya yayi yabude musu motar suka shiga batare da sun shiga sauran part dinba domin gaba daya parts din tsarin gininsu da komai iri dayane,


Saida suka gama yawonsu agari sannan suka koma gida.




Washe gari hafsat gidan umminta tatafi tawuni acan, misalin karfe 2 narana mami nazaune tana yin lunch taji sallama, har cikin falon mai sallamar tashiga sai faman budada kamshi take nan ta durkusa tagaida mami,


"A'a tashi ki zauna, sannu da zuwa"


Saida mami ta gabatar mata da abinci da abubuwan sha sannan ta dubeta da fara'a,


"Sai dai kuma ban ganeki ba" inji mami,


"Ehh ai momy baki sanni ba, sunana hafsat kuma ni yar gidan alh musa ce ubangidan ya yusleem"


Sake fadada fara'arta mami tayi ta dubeta....




_Fans kuyi min uzuri zakuji ni shiru kwana biyu saboda wani uzuri da ya taso min na gaggawa amma insha Allah nanda sati daya zaku cigaba da jina ina fata zaku yimin afuwa..._






*_Ummi Shatu_*👌🏻


© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_







*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








_*Na*_
*_UMMI A'ISHA_*






_DEDICATED TO MISS XOXO_






*Fans ina mai mutukar baku hakuri dangane da jina shiru da kukayi kwana da kwanaki hakan yafarune ba ason raina ba sai tarin hidimomin da suka shamin kai, ban san ta inda zan fara baku hakuriba, indeed i have no words to apologize you saboda nasan kuna mutukar ji da alwashi domin kun nuna min hakan kullum cikin amsa wayoyinku da karbar sakonninku nake dan haka ina mutukar godiya kuma ina mika gaisuwata agareku, insha Allah hakan bazata sake faruwaba, ina yimuku fatan alkhairi aduk inda kuke,duk wata masiyiyar alwashi tayi alfahari da page din yau domin mallakinta ne, i heart u all.*






*56*






***Sake fadada fara'arta mami tayi tadubeta cikin murmushi tace,


"Allah sarki ya kika baro mahaifiyar taki da yan uwanki, duk suna lafiya ko?"


"Lafiya lau suke..."


"Madalla, ai kin kyauta da kika zo" inji mami,


"Ah babu komai wlhi ai an zama daya..."


Sun dan jima suna hira kafin hafsat tayiwa mami sallama tatafi, har waje mami ta rakata wurinda motarta take saida taga tafiyarta sannan takoma ciki.




K'arfe 6 yusleem yatashi daga aiki, Hafsat yakira daidai lokacin da yaje gaban motarshi,


"Ya yusleem..."


"Uhmmm, matata kina ina?"


Murmushi yaji tayi saboda sunan da ya kirata dashi,


"Da waye yace ba matarka bace?"


Cikeda alamun gajiya yabude motar yashiga ya zauna amma baiyi mata key ba,


"Nidai nasan matatace koda wanima zai ce ba tawa bace, dan Allah kina ina? Wallahi agajiye nake sosai"


"Ina gidan Ummi"


"Wai har yanzu dama baki koma gida ba?"


"Ai yau anan zan kwana"


Yar dariya taji yayi,


"Yanzu zanzo in daukoki ki shirya"


Yafadi yana daura sit belt ajikinshi,


"Ko baka zo ba ma ai zan dawo anjima"


"A'a ban yarda ba, gara inzo indauki abata intafi da ita ina jinta agefena"


Murmushi tayi tace "sai kazo" tareda katse wayar,


Mintuna ishirinne suka kaishi gidan, awaje ya tsaya ya kirata babu jimawa sai gata tafito rikeda jakarta da wata leda yar babba,


Bude mata kofar yayi tashiga ta zauna, mika hannu yayi ya rufo kofar yana kallonta, gaba daya wani kamshin dadine yaji ya cika cikin motar,


"Ummi tana gaisheka..."


"Ina amsawa, kefa? Bakya gaidani ko kina gaisheni?"


Murmushi tayi ta rike hannunshi wanda ke yawo acikin rigarta,


"Ina gaisheka, dan Allah kabari"


Murmushi yayi yatada motar yasoma tuki yana kallonta,


"Na fuskanci duk ranar da kikazo gidan Ummi bakya son komawa gida da wuri,meyasa?"


"Hirarce ke yin yawa bata karewa shiyasa" tafada tana murmushi,


Yan yatsunta taji ya kama,


"Me kike sha'awa yanzu mubi insiyo miki?"


Lumshe ido tayi, "Duk abinda kake kwadayi nima ina so"


Murmushi taji yayi kasa kasa yace,


"Ni ke naketa kwadayin samu kuma nagagara, kefa?"


Dauke kanta tayi ta mayar gefe saboda abinda taji yace, murmushi yayi ya dan kalleta,


"Yanaji madam tayi shiru?"


"Muje gida kawai basai mun tsaya ko inaba"


"Dama ai gidan zamuje"


Shiru tayi saboda yagama kashe mata bakinta, ita da zarar yayi mata magana makamanciyar wannan sai taji duk bata da bakin yimasa magana,


Juyawa yayi ya kalleta, "menene wannan haka mai kamshi ummi tabaki?"


"Turaren wutane da humra aka kawo mata daga Sudan shine tabani..."


"Ta kyauta kuwa dan naji kamshin irin wanda nake so ne"


Kawar da maganar tayi tahanyar cewa,


"Yaushe zaka je chairo dinne?"


"Zamuje dai, ai tare zamu tafi yanda muna dawowa mami zata fahimci cewar andace nagama warkewa".


Murmushi kawai tayi masa batare da tace komai ba saboda idan taci gaba da biye masa kunya zai ta sata tanaji,


Wurin wani mai sayarda balangu da tsire taga ya tsaya nan yafita yaje ya siyo yadawo, ledoji biyu yariko ya mika mata,


"Amshi wannan, na mami daya namu daya..."


"To angode, Allah yakara budi"


"Amin, me zaki bani tukwici?"


Shiru tayi masa takai hannu zata kunna radio, dora nasa hannun yayi akan nata yana lalubo mukunnar radio din,


"Ko babu abinda zaki bani? Naji bakice komai ba"


"Uhmm"


"Uhm fa kikace? Lallai, to ashe bazaki cimin balangu na ba tunda hakane"


Kallonshi tayi tasaki dan murmushi,


"Dama bada zuciya daya ka siyo ba kenan?"


"Wallahi da zuciya biyu nasiyo, kici balangu ki bani tukwici"


Rasa abinda zata fada masa tayi dan haka taja bakinta tayi shiru, shikuwa sai sake nanatawa yake yi dahaka har sukaje gida,


Part din da yake yawuce yayinda ita kuma tawuce part din mami, mamin nazaune tana lazimi da alama sallar magrib ta idar, ciki Hafsat tawuce taje ta dauro alwala tafito, saida ta idar da sallar sannan suka gaisa da mami ta fito da kayan da Ummi tabata da kuma naman da yusleem yasiyo,


Tuwo da miya tazubo musu ita da mami,sun fara ci kenan yusleem yashigo,


"Mami ni baza ajirani ba inzo shine kuka wareni"


Murmushi mami tayi,


"Kai ai kayi girma da yawa Yanzu babu mai wani riritaka"


Samun wuri yayi yazauna kusa da mami yana murmushin shagwaba,


"Gaskiya mami a'a"


"Basai kayiba kuma" inji mami,


Dariya Hafsat tayi ta dan kalleshi nan suka hada ido dama shidinma ita yake kallo,


"Am yawwa kafin namanta, dazu wannan yarinyar Hafsat tazo yar gidan alh musa..." Mami tayi maganar tana kallon yusleem,


Saida yaji gabanshi ya fadi saboda jin abinda mami tace,


"Mami lafiya? Meya kawota gidan nan? Tace miki wani abune?" Duk ya jerowa mamin wadannan tambayoyin lokaci guda,


"A'a ni babu abinda tace min, kawai dai zuwa tayi agaisa, akwai wani abune tsakaninka da ita da kake tambayar me tace?"


Kallon hafsat yayi amma ita bashi take kalloba tuwonta kawai take ci sai dai gaba daya tasauya ta danyi wani iri tana sauraronsu, ita dama bata sawa ranta cewar ita kadai zata zauna dashi ba tunda tasan watakila shima akan kansa nan gaba zai bukaci kara auren,daurewa tayi tai watsi da duk wata damuwa taci gaba da cin tuwonta batare data bari bacin rai ya ziyarci zuciyarta ba,




Kallon mami yusleem yayi bayan ya tsame hannunshi daga cikin kwanon tuwon da suke ci,


"Mami ni banida wata alaka da ita, kawai dai abinda nasani shine ina zuwa gidansu wurin mahaifinta kuma tana girmamani"


"To ai shikenan hakanma yanada kyau, Allah ya rufa asiri.."


Bai amsaba yasaci kallon Hafsat, balangun da yasiyo musu yaga tabude tafara ci,


"Baby nanah babu ko bisimilla?"


Murmushi yaga tayi tatura masa gabanshi,


"Haba ya yusleem taya zan hanaka bayan kaine ka siyo, gashi muci"


Tashi mami tayi tawuce domin wanko hannunta, ganin haka yasashi rage murya,


"Nidai sai dai kibani abaki..."


Tun kafin yarufe bakin nashi ta dauki naman tasaka mishi, murmushi yayi yarike hannunta,


"Yawwa matata..."


Dariya tasaki saboda jin abinda yace,


"Ni kana bani dariya idan naji kafadi haka, wai waye da yace ba matarka bace?"


"To laifine dan nasake jaddadawa?"


Hannunta tazare daga cikin nashi saboda jin tahowar mami,sake rage murya yayi,


"Ya kamata fa kitashi muje mu kwanta saboda yau jina nake asama sama..."


Sunkuyar da kanta tayi batare data tanka mishiba har mami takaraso cikin falon ta nemi wuri ta zauna,


Hira sukeyi kadan kadan shida mamin yayinda ita kuma hafsat ta tattare kayan da suka ci abinci tafita dasu bayan tagama cin naman dayake gabanta,


Dawowa falon tayi itama ta zauna tana kallo sannan tana dan sauraren hirarsu mami wadda yanzu akan dawowarsu Abdul ne,


Da ido yusleem yake yiwa Hafsat alamun ta tafi bedroom zai biyota,


Makale kafada tayi, kallonta yayi yadan jijjiga kai alamun zan kamaki ne, murmushi tayi gamida yimasa gwalo, hakan da tayine yabashi dariya,


Gani yayi sam bata da niyyar tashi domin lokacin har karfe 9:30 tayi gashi mami itama yau hirar takeji saboda tana nan zaune bata motsa ba,


Dan gyangyadin da taji yana fusgarta ne yasata tashi badan tasoba tawuce bedroom, binta da kallo yusleem yayi har ta shige,


Wanka ta shiga bata dauki lokaci ba tafito tana daure da towel din surayya wanda dakyar ya ritsata saboda dan jikin da tayi,


Humrar da ummi tabata yau ita tabude tasoma shafe jikinta babu bata lokaci dakin gaba dayanshi ya gauraye da daddadan kamshi,tana rufe kwalbar yusleem yaturo kofa yashigo, da sassarfa yakaraso gareta sakamakon kamshin da yakaiwa hancinsa ziyara ya ratsa har cikin kwakwalwarsa.......








_*Ummi Shatu*_👌🏻


© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_






_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*








_DEDICATED TO MISS XOXO_








*57*






***Wata lafiyayyiyar runguma yayi mata bayan yacusa fuskarsa awuyanta yana sinsinarta,


Towel din dake jikinta tarike gam yayinda shi kuma yasake tsananta rukon da yayi mata,


"Ya yusleem...."


Kasa amsawa yayi illa gyada mata kai da yayi alamun yana jinta,


"Ya yusleem kabarni inshirya...."


Sake kankameta yayi yana janta ahankali har suka dangano da gadon dake cikin tsakiyar dakin,


Makaleta yayi sosai ajikinsa ya shimfidar dasu nan yasake bada himma wurin isar mata da sakonnin da yafara bata tun suna tsaye, sosai yau taga ya fice daga hayyacinsa sakamakon yakai makura wurin bukatarta, wani zazzafan numfashi yake fitarwa yana sauka ajikinta,


Sun dauki lokaci mai tsawo cikin wannan yanayin wanda shi yusleem jinshi kawai yake yashiga wani wahalallen hali maimakon yasamu relief daga azabtuwar da gangar jikinshi da rushinsa ke ciki, badan yana jin tausayinta ba kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login