Showing 66001 words to 69000 words out of 70255 words
tafada tana daga kishingide akan gado,
"Mami nashiga tsaka mai wuya, bazan iya auren wata maceba inbanda Hafsat, Hafsat itace sirrina she's my everything, Hafsat itace macen da tasoni tsakani da Allah, tasha wuya ta, tashiga kuncin rayuwa saboda ni, Hafsat itace macen datafi cancanta insota kuma inrayu da ita koda kuwa zataci gaba da tsanata da kyarata,
Mami bazan iya rabuwa da Hafsat ba sannan bazan iya yimata kishiya acikin wannan halin ba, mami zan cigaba da zama da Hafsat ahaka koda hakan na nufin rayuwata zata kare cikin kunci da damuwa da bakin ciki saboda abaya Hafsat ta zabi zama cikin kunci da talauci saboda ni, Hafsat itace tayi min sanin da ko mahaifiyata bata yimin shi ba, sannan ta lullube sirrina bayan ta maidani cikakken mutum nagari...."
Zaune mami tatashi tana sauraren yusleem,
"Yusleem duk naji bayananka kuma nafika son zamanka da hafsa amatsayin mata, idan baka manta ba nice nan nanemo maka ita a lokacin da baka santa ba kuma na jajurce har sai da tazama matarka, to yanzu tunda lalura tashigo ciki yana da kyau kasamu nutsuwa tahanyar auren wata matar..."
"Mami i can't, wallahi bazan iyaba, bazan iyaba mami, mutukar nayiwa Hafsat kishiya tana cikin wannan halin ban kyauta mata ba, kamar yadda ta zauna dani acikin halin lalura to nima yazama wajibi inzauna da ita aduk halin data tsinci kanta, mami naci ALWASHIN zama da Hafsat ahaka kuma zan yi iya bakin kokarina wurin nemo mata lafiya domin hakan kadai shine zai bayyanarwa da duniya matsayinta da muhimmancinta agareni..."
Hawaye na bin kumatunsa yajuya yadafa mami,
"Mami ko kin san da ni dan luwadi ne? Mami da ni gay ne wanda bansa komai agaba ba face rashin tsoron Allah da aikata kazantar da Allah yai hani da ita, mami Hafsat da idonta taganni ina aikata luwadi amma ko uwar data haifeta bata fadawa ba haka tazauna dani, to danme yanzu ni zan kasa zama da ita? Mami akan me? Why....?, mami babu aurefa tsakanina da khadija domin saki 3 nayi mat"
Mikewa yayi tsaye nan wani jiri mai karfin gaske ya kwasheshi, sai gashi akasa, mami dake zaune ta daskare awurin takasa ko motsi saboda jin maganganun da yagama fada mata yanzu, dakyar tatashi tafita takira su Abdul, akan gadonta suka dorashi takira Dr Nabila domin abashi taimakon gaggawa,
Wani matsanancin ciwon kai yakeji tunda yafarka, bude idanuwansa yayi wadanda suka yimasa nauyi,
"Mami bazan auri kanwar Hafsat ba, bazan auri Hafsat ba, bazan auri khadija ba domin babu aure atsakaninmu saki 3 nayi mata mami, idan ku kun manta ni ban manta ba, cikinsu babu wanda zan aura mami, zanci gaba da zama da matata har mutuwata, wallahi mami bazan iya auren wataba, mami dan Allah kije ki dauko min Hafsat, ni ina son zama da ita koda zata cigaba da tsanata...."
Wadannan surutan yai tayi baiyi shiru ba, kowa dake cikin dakin shiru yayi yana saurarensa, saida mami taji yana shirin sake bada labarin da yabata dazu sannan tayi saurin zuwa tazauna tarufe masa baki da hannunta tana fadin,
"Ya isa haka yusleem, yi shiru zanje zan kawo maka ita, kayi hakuri..."
Karin ruwan dake hannunsa ya kalla sai yadafe goshinsa domin baya zama yaci abinci sam tunda yaga halin da Hafsat ke ciki wanda wannan kadai ya isa ya sashi rashin lafiya,
Rarrashinsa mami taci gaba da yi har tasamu allurar da aka yimishi tasoma aiki aijikinsa nan bacci ya daukeshi,
Nan suka koma falo suka barshi acikin bedroom din yana bacci, mami kam duk jikinta yamutu yayi sanyi kalau saboda jin labarin da yusleem yabata wai ada shi gay ne amma ita bata taba saniba? Lallai indai hakane to ta tabka babban kuskure abaya domin indai uwa tagari ce zata kasance mai bibiyar al'amuran yaranta da sanin abokan mu'amularsu da wurinda suke zuwa da kuma dabi'unsu,
Tabbas yanzu kam zata goyawa yusleem baya kamar yadda yaci ALWASHI na rayuwa da hafsanshi ita kadai kwal agidansa, tagumi ta rafka wanda har bata jiyo maganar da surayya ke yi mata,
"Mami inata magana, tunanin me kike yine...?"
Firgigit tayi ta kalli sury,
"Wallahi surayya tunanin yayanku nakeyi domin yana cikin wani hali..."
"Allah zai bashi lafiya mami, kidaina daga hankalinki, me za adafa masa?"
"Kiyi masa faten wake da kifi da ganye, tunda kinga baya cin abinci sosai..."
Tashi surayya tayi tafita zuwa kitchen ita kuma mami taci gaba da zama bayan ta rafka tagumi.
Misalin karfe 10 yusleem yafarka har lokacin kansa bai daina wannan azababben ciwonba, mami ya kalla da kannensa wadanda ke zaune,
"Mami tana ina?"
Soma kwantar mishi da hankali mami tayi, dakyar ta lallabashi yaci abinci yakoma bacci,
Bar mishi dakin mami tayi takoma bedroom din surayya suka kwana tare.
Sai da yusleem yayi kwana uku akwance, akwana na hudu yadan samu lafiya har ya samu yafito daga bedroom din mami yazauna a falo, aranar mami taje gidansu Hafsat domin taho da ita nan Ummi ke fadawa mami shawarar da suka yanke na aurawa yusleem amal kanwar Hafsat domin ta maye gurbinta, jijjiga kai mami tayi taceda Ummi,
"Hajiya kubra ni ina ganin kar asoma yin haka domin yusleem ahalin yanzu yanuna min babu wadda zai zauna da ita idan ba Hafsat ba, mu hakura kawai muyita addu'a har Allah yabata lafiya, yanzu haka ma ni zuwa nayi domin natafi da ita..."
"To shikenan hakan yayi ai duk dayane da amal din da Hafsat din domin nice nan duk na haifesu, amma maganar komawar Hafsat adan bamu lokaci domin muna son muyi mata magani na gida, sannan yanzu haka ma andorata akan wasu addu'o'i wadanda nake yimata kullum safe da daddare, insha Allah da zarar ta soma samun sauki zamu dawo masa da matarsa..."
"To shikenan Allah yasa mudace, Allah yabata lafiya, shima yanzu yana can akwance bashida lafiya amma yadan soma warwarewa"
"To Allah yakara masa lafiya..."
"Amin" inji mami, nan mamin tayiwa Ummi sallama tatashi domin tafiya,amal dake labe ajikin labule akofar dakinsu tana sauraren duk abubuwan dasu mami suka tattauna akai wasu hawaye ne na bakin ciki suka shiga zarya da Kai Kawo akan kumatunta, cikin bedroom tawuce dagudu tana kuka, Hafsat dake zaune akan gado tabita da kallo ta zuba mata ido, cikin toilet amal tashiga tarufo kofa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya wanda ita kadai tasan ko kukan me takeyi.
Daga gidan hajiya kubra mami gidan su khadija tawuce taje tasamu kawarta hajiya fa'iza suka tattauna dangane da maganar da sukayi na komawar khadija anan mami tabata hakuri tasanar da ita cewar yusleem bai aminceba yace saki uku yayiwa khadija abaya kuma bashida niyyar kara aure zai cigaba da jiran matarsa har tasamu lafiya,
Murmushi hajiya fa'iza tayi sannan tace,
"Ayya wallahi mun sha'afa ne, ashefa babu aure atsakaninsu yanzu tunda saki 3 ne, Allah yasa haka shiyafi alkhairi to"
"Amin hajiya fa'iza" ummi ta amsa,
Duk da khadija tana zaune awurin bata ko damuba balle aga sauyin fuska atare da ita, mami ta dan jima agidan sannan tatafi,
Lokacin data koma gida afalo tasamu yusleem yayi wanka yasa green din t shirt da farin trouser yana zaune yana cin biscuit da fresh milk, zama mami tayi tafada masa duk yanda sukayi da su hajiya kubra da hajiya fa'iza,
"To mami yanzu saura abu daya, dan Allah kisamu lokaci kije gidan alh musa kifada masa bawai kin auran yarsa nayiba, inada mata kuma yanzu ni hankalina ba akwance yake ba..."
"Shikenan insha Allah zuwa gobe sai inje"
Sanyi yaji aransa domin yanzu wannan matsalar yasamu damar kawar da ita.
Bayan sallar isha yatafi gidansu hafsat saboda kwana ukun nan da yayi batareda yaganta ba yayi mutukar jigata,
Kayan kwalam da makulashe ya siya mata sannan yakarasa gidan, dukkansu suna falo banda Hafsat din wacce yanzu zaman daki ya zame Mata doka,
Bayan ya gaisar dasu Ummi ne ummin tace yashiga, tashi yayi yashiga wurin Hafsat wacce bata gajiya da bacci domin yanzu ma shi takeyi,
Zama yayi agefenta yana kallon fuskarta wadda duk da acikin halin rashin lafiya take amma tayi kiba, gashin kanta atsefe,
Fuskarta yake shafawa ahankali, dayan hannun kuma yarike hannunta daya, amal tana tsaye akofar daki tana kallonsu hawaye nabin kumatunta suna wanke mata fuska, jin alamun fitowarsa yasata saurin barin wurin tafada bedroom din Ummi.
Kwanaki sunci gaba da tafiya ahaka Hafsat har yanzu sai dai godiyar ubangiji amma sauki bai samuba, koda yaushe yusleem yana kan hanyar zuwa gidansu, har umarah yaje ya iyo mata addu'a akan Allah yabata lafiya,
Wata ranar alhamis dukkaninsu suka tafi dubota kamar yadda suka saba shida su mami, sury, Abdul da khalifa,dama duk sati sai sunje dubota duka gidan amma shi yusleem arana ma sai yaje gidan sau hudu duk da bata son ganinshi,
Suna falo azazzaune bayan angama gaggaisawa alh sa'eed na kokarin fita yafasa sakamakon sallamar da sukaji anyi, kowa maida hankalinsa kan kofar shigowa cikin falon yayi domin ganin wacce ke sallamar,
Hafsat mori ce tashigo fuskarta akumbure duk ta kukkuje an nadeta da bandeji, haka kanta ma an nannadeshi da bandage, hannunta daya yasha bandeji sannan an sakaleshi ajikin wuyanta alamun karaya, kafarta duk auduga amammanne,
Yusleem takalla tayi magana cikin dasasshiyar murya irin ta marassa lafiya,
"Yusleem gashi..."
Kowa bin abinda ke hannunta yakeyi da kallo domin wata bakar ledace marar kyan gani,
"Daga gidanku nake aka ce min kun taho nan shine nabiyoku nan din, wannan shine asirin da akama matarka gashi ka dauka ka kona shi yanzun nan mutukar kana son ta warke..."
Ajiye ledar tayi tajuya zata fita yusleem yayi gaggawar shan gabanta, bai yi la'akari da daddaujewar dake jikin fuskarta ba ya dauketa da mari, dafe kuncinta tayi da hannunta mai lafiya hawaye nabin kumatunta,Murmushin karfin hali tayi ta kalleshi,
"Nidai gashi nan na ajiye maka, kadauka ka kona da hannunka domin mutukar bakai ka kone wannan asirin ba to matarka zata dawwama har abada acikin hauka....".
*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI....!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_DEDICATED TO MISS XOXO_
*63*
***Kowa acikin falon tsitt yayi banda khadija da amal wadanda suka zazzaro ido suke kallon Hafsat mori,
Da wani gudu amal tataso tazo ta cukumi wuyan Hafsat mori tana jijjigata,
"Kece kika haukata min yar uwa ko? Wallahi bazamu yarda ba sai kema na haukataki...."
Yusleem ne ya bambareta yacireta daga rikon da tayiwa Hafsat din,
Khadija kuwa dake zaune har lokacin idanuwanta awaje suke, cikin daga murya tace,
"Gaskiya Hafsat kinyi asara, kirasa hanyar da zakibi ki cutar da baiwar Allah saita hanyar haukatata?"
"Ai bata kyauta ba kuma Allah ya isa tsakaninmu da ita..." Ummi tafada tana kwalla,
Mami dai bin kowa take da kallo tama kasa magana, banda surayya wacce tayi jugum tai tagumi tana kallon kowa,
"Duk dai yanzu abar wannan maganar, kai yusleem kayi yanda tace kadauka kaje waje ka kona..."
Juyawa Hafsat tayi zata tafi yusleem yayi saurin fincikota wanda har saida tatafi taga taga zata fadi,
"Babu inda zakije har sai nakona asirin nan sannan sai nakira hukumar yan sanda nayi report sunzo sun tafi dake domin wallahi bazan taba yafe miki ba har sai munyi shari'a dake...."
Wani murmushi Hafsat tayi irin ko ajikina dinnan tawuce kan kujera ta zauna, wata uwar harara khadija ta wulla mata,
"Andaiyi asara, wallahi sai kin je prison tunda kika cutar da baiwar Allah haka kawai..."
"Ba nace ya isaba? Kar nasake jin maganar kowa, kai yusleem dauki muje..." Alh sa'eed yafada yana nunawa yusleem kofa, tare suka fita dashi suka zagaya bayan gidan suka kunna wuta suka kona abun, nan wani bakin hayaki yaringa fita har yazama ja daga nan yakoma kore daga karshe yazama fari tass,
Saida sukaga yadaina hayaki alamun yagama konewa kurmus sannan suka koma ciki, abin mamaki suna shiga cikin falon saiga Hafsat tafito daga cikin daki dafe da kanta,yusleem ta zubawa ido tana kallonshi cikin wani irin shauki na so,
Kowa ita yake kallo ganin haka yasata karasawa tsakiyar falon ta matsa kusa da amal ta zauna wacce tafara hawaye tun ganin fitowar Hafsat din,
Waya yusleem yazaro daga cikin aljihunsa zai kira police alh sa'eed yayi gaggawar dakatar dashi,
"A'a yusleem, katsaya dai mubi komai ahankali mu warwareshi, kabari tafada mana dalilinta nayin haka.."
"Babu wani dalili abba kawai shirmene da hauka da mugunta irin nasu na mata...."
"Kadai bari muji daga gareta"
Juyawa ga Hafsat mori abban yayi,
"Baiwar Allah kiyi mana bayanin abinda yafaru, ni bana son zuwanki wurin hukuma domin hakan tozarcine ga rayuwarki..."
Wani shu'umin murmushi Hafsat mori tayi sannan ta daga kanta sama alamun tunani.....
*FLASHBACK*
Afusace yaja motarsa yabar harabar gidan bayan yagama gasa mata bakaken maganganu yanda yaso,
Cikeda mamaki baki abude take binsa da kallo har ya bacewa ganinta,
Ahankali taja kafarta tabar wurin tashiga cikin gida kasa tabuka komai tayi dan haka tawuce cikin dakinta ta zauna agefen gado,
"Anyiwa matarsa asiri? Kuma yana zargina da aikata hakan?"
Sunkuyar da kanta tayi daga nan kamar wacce aka tsikara ta mike ahanzarce tadauki key din motarta tafita duk da agajiye take, kai tsaye asibitin da aka kwantar da Hafsat kafin asallameta tanufa,
Dakyar tasamu ganin Dr zayyad ta hanyar dan uwanta Dr sufyan domin cousin brother dinta ne, bata samu damar barin asibitin ba sai misalin karfe 9 nadare,
Agajiye liss takoma gida lokacin kowa dake gidan yakwanta bacci,
Zama tayi akan teburinta na karatu wanda yake cikin dakinta ashirye kamar libry, mintuna kadan tatashi tashiga wanka tafito, ruwan Lipton kadai tasha tasake zama awannan teburin tana faman bincike acikin wasu tuma tuman littattafai har karfe 3 nadare tadauka zaune tana faman bincike sai 4 saura sannan ta kwanta,
Washe gari da sassafe ta tashi tashirya tafita ko karyawa batayi ba,
Unguwar Garara ta nufa nan tasamu dakyar ta binciko gidan da take nema, wani dan karamin gidan kasa tashiga tana kwada sallama, daga can wata yar dattijuwa ta amsa mata bayan tafito, gaisawa sukayi,
"Baba nazo wurin Malam audu ne mai gidannan"
"Lale lale, sannu da zuwa sai dai kuma yafita yatafi gona amma kijirashi yanzu zai dawo" Yar dattijuwar tafada tana kokarin shimfida mata wata yar guntuwar tabarmar karauni,
Zama Hafsat mori tayi tazaro wayarta wacce take tamkar faranti dan tsananin girma nan takunna ta tashiga latsawa,
Tsawon mintuna talatin sai ga alh audu yashigo sabe da fartanya akan kafadarsa,
"Yawwa Malam sannu da zuwa dama tun dazu bakuwa take jiranka"
Ajiye fartanyar yayi yana murmushi,
"Allah mai iko, lale da bakuwa..."
"Yawwa sannu da zuwa Malam..."
Zama yayi akan wani dan dutse wanda ke kafe abakin kofar dakinsu,
"Sai dai kuma yarinya ban ganekiba, daga ina?"
Murmushi Hafsat mori tayi,
"Baba ni sunana Hafsat m mori, ni kwararriyar lawyer ce mai zaman kanta, nazone domin ina neman wasu bayanai daga gareka saboda zamuyi wani aiki dakai, dan Allah baba kabani hadin kai, kataimaka min"
"To yarinya bawai ki nayiba amma wanne irin aikine wadannan, sannan wadanne bayanai kike nema daga gareni?"
"Baba abaya kayi aiki agidansu wani Matashi wanda ake kira da yusleem, shin baba zan iya sanin alakarka dashi wannan matashi? Tsawon wanne lokaci kadauka agidansu kana aiki? Shin yanzu kanada wata alaka dasu ko babu? Wanne irin bayani zaka yimin dangane da halayya ko dabi'un shi yusleem din"
Gyara zama Malam audu yayi yana kallon Hafsa,
"To yarinya nidai tsawon shekaru 4 nadauka ina aiki agidansu shi yusleem, sannnan nabar aikine agidan shekaru uku baya..."
"Ko menene dalili baba?"
"Ehh saboda girma yakamani shiyasa mai dakina tanemi da indawo gida inzauna inhuta haka"
"To baba yanzu kenan bakada wata alaka dasu?"
"Ehh gaskiya babu amma duk da haka wata rana nida mai dakina mukan shirya mu ziyarcesu"
"To baba mai kasani dangane da yusleem?"
"Yaron kirkine mai ganin girman manya, har nabar aiki agidansu ban taba ganin ya yi wani abu wanda bai kamata ba..."
"Har yanzu baba da kake ziyartarsu ko sau daya bakaji wani mummunan abu dangane dashiba?"
"Gaskiya banjiba"
"To baba lokacin daka bar aiki waye yakarba?"
"Malam ilu ne yakarba"
"Yanzu yana ina?"
"To inajin dai acan kauyen madaci yake domin shima yanzu yabar yimusu aiki"
"To baba nagode, idan nasamu lokaci zan dawo, nagode madalla"
"Ah babu komai yarinya, sai kin dawo"
Sallama tayi musu tafita, tana fita matar Malam audu ta dubeshi,
"Malam wannan yarinya da tambaya take? Aba kamar na'urar nasara?" Dariya dukkaninsu sukayi shida ita,
Da fitarta motarta tabude tashiga bata zame ko inaba sai kauyen madaci domin ayau dinnan take son ganin Malam ilu.
Tasha mutukar wahala Kafin tasamu gidan malam ilu, lokacin da tasamu gidan tashiga baya nan yatafi kasuwa sai matanshi da yaranshi, kasuwar tabishi wurin da yake sayar da kayan masarufi,
Acikin rumfarsa ta zauna ta fara gabatar masa da kanta, dukkan tambayoyin da tayiwa Malam audu shi tayi masa yana bata amsa har akazo wurinda take son ji domin tanan ne kadai zata samu saukin binciken da take yi,
"Malam ilu tun lokacin da kake zaune agidansu yusleem baka taba ganinshi da wani hali ko dabi'a wadda take bata gariba?"
"Ehh hajiya gaskiya nidai ban sanshi da wani hali marar kyau ba amma dai wata rana ina cikin falon mahaifiyarsa domin karbar albashi na naji ya bugo mata waya amma banji abinda yaceba nadai ji ita tanata fada tana cewa baya son zama da mata domin wannan itace mace ta goma da ya aura yasaki acikin kasa da shekera biyu... To wannan dai itace matsalarshi ina jin amma bayaga wannan agaskiya ban sanshi da wani mummunan haliba..."
"Nagode baba ilu sai nasake dawowa akaro nabiyu domin da yuyuwar zan kara dawowa"
"Shikenan yarinya Allah yadawo dake"
Sallama sukayi tashiga motarta tafita lokacin misalin karfe 1:30 narana, inbanda yunwa babu abinda takeji saboda ko breakfast batayi ba tafito da sassafe,
Kai tsaye gida tawuce tana zuwa tashiga kitchen tazubo abinci, tana zama hajiya mahaifiyarta nashigowa,
"Hafsat ina kikaje ne yau tun safe?"
Murmushi tayi takalli hajiyarta,
"Hajiya ina wani bincike ne akan wani case da zanyi..."
"To ai ku dama lauyoyi kullum aikinku kenan investigation, bakuda wani batu sai wannan, Allah yabada sa'a amma ina fata case din ba akan kisan kai bane ko maita dan bana sonki da karbar irin wadannan case din domin hatsarinsu yawa gareshi..."
"Bashi bane hajiya amma zanyi miki tambaya, hajiya mutumne yakeda matarsa sai tafara ciwon hauka kuma ance asirine to da yataba auren wasu matan kafin ita, dan Allah waya kamata azarga?"
Shiru hajiya tayi zuwa can tace,
"To zato dai zunubi ne amma babu tabbas ko acikin kishiyoyinne wata tayi mata asirin.."
"Hakane hajiya nima abinda nake tunani kenan amma dai bari zan bincika"
Abincin da take ci ta ajiye tawuce bedroom dinta, wanka tayi tai salla tazura wata bakar doguwar riga tayi rolling fuskarta babu