Showing 9001 words to 12000 words out of 70255 words

Chapter 4 - ALWASHI BOOK 1 COMPLETE by Ummi Aisha .txt

23 Dec 2024

3902

akowanne dare domin yin hira,


"Alhaji...,labarai kake kallo?"


"Wallahi kuwa hajiya, keda 'yar takine?"


"Ehh amma har yanzu dai banga alamar zata sake ta saki jiki damu ba saboda ganinmu take baki agareta" hajiya kubra tafada fuskarta da yar damuwa,


"To wannan kuma dama ai sai ahankali,kin san ai yau tafara ganinmu,sai asannu ko Hafsat?" Yakarasa zancen cikin barkwanci,


Hafsat kam shiru tayi takasa koda kallonsu, sai dai wani lokacin ta dan saci kallonsu ahaka har lokacin sallar isha yayi nan alhaji sa'id yafita masallaci yabarsu a cikin falon nashi,


Anan Hafsat da hajiya kubra sukayi sallarsu,suna nan zaune har alhaji sa'id yadawo dan haka hajiya kubra ta mike domin gabatar musu da abincin dare,


"Hafsat zo muje kitchen.."


Mikewa Hafsat tayi suka fita zuwa cikin kitchen wanda kallo kawai Hafsat ta bude ido tanayi saboda ita ba taba ganin irin shi tayiba,


Akan babban faranti hajiya kubra ta jera flasks din abincin nan Hafsat din ta karba ita kuma hajiya kubra ta debi filet da sauran abubuwan da suka kamata,


Zama Hafsat tayi bayan ta ajiye farantin, acikin dan madaidaicin filet hajiya kubra ta zuba musu abincin, tuwon semo miyar danyar kubewa,


"Hafsat zo muci abincin.."


Matsawa hafsa tayi tasa hannu ita a zatonta iya ita da hajiya kubran ne kadai zasuci amma sai taga sabanin haka domin shima alhajin saka hannu yayi saboda al'adarsu tare suke cin abincin tare dashi da hajiya da amal, Hafsat ji tayi kaunarsu ta fara darsuwa acikin zuciyarta, duk da cewar taki dan sakin jiki dasu amma hajiya kubra sai sakota take acikin hirar tasu dahaka suka kammala cin abincin.


Suna falon alhaji sa'id azaune har misalin karfe 9 nadare lokacinne hajiya kubra ta mike ta kalli Hafsat,


"Hafsa taso muje ki kwanta naga kamar bacci kikeji ko?"


Dan murmushin yake Hafsat tayi ta tashi ta kalli alhaji sa'id,


Dan rissinawa tayi, "Alhaji saida safe"


Cikeda fara'a ya amsa tabi bayan hajiya kubra suka fita,


"Abba zaki rinka cewa alhaji kinji, nikuma ummi saboda haka amal ke kiranmu, kinga tunda yanzu kema mune iyayenki.."


Hajiya kubra tace da ita akan hanyarsu ta zuwa part dinta,


"Tohh Ummi.."


Dadi hajiya kubra taji jin Hafsat ta kirata da Ummi,


Sai da safe Hafsat tayiwa hajiya kubra tashiga daki,zama tayi akan gado tana mai bin dakin da kallo.....








*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_






_*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*








_Dedicated to MISS XOXO_






*13*






aishaummi.blogspot.com






***Kasa bacci Hafsat tayi illa tunanin rayuwarta da take ta faman yi,


Ji tayi kamar ta fashe da kuka a sakamakon fadowa ranta da kawarta Amina tayi,


Duk da tasan abin atayata farin cikine saboda canjin rayuwar data samu amma duk da haka tana jin radadi acikin zuciyarta na rabuwa da gidan marayu da tayi domin tariga da ta saba da mutanen ciki,


Wadannan tunane tunanen da tarinka yi sune suka hana idonta bacci har aka fara kiran assalatu, a kunnenta aka shiga sallar asubah nan ta tashi tashiga bathroom ta dauro alwala tafito, salla tayi tareda addu'o'i masu yawan gaske, anan inda tayi sallar anan bacci ya kwasheta.


Misalin karfe shida da rabi na safe hajiya kubra ta shiga cikin dakin ganinta kwance tana bacci yasata juyawa tafita batare data tasheta ba domin ta fahimci cewar tayi sallar asubah,


Hafsat dai bata samu damar tashi daga wannan baccin ba mai cikeda mafarkai iri iri wadanda takasa tuno koda guda daya daga ciki lokacin data farka, ba ita tatashi ba sai misalin karfe 10 zuwa da rabi, hajiya kubra kuwa ta leka dakin yafi sau akirga,


Zama tayi tana bin dakin da kallo kamar yanzu ne tashigo ciki, daga bisani ta sauke idonta kasa ta mike, fita tayi acikin falo ta hango hajiya kubra tasha kwalliya cikin wata shadda kamfala tana faman jejjera abin Karin kumallo akan dining table,




Sam hajiya kubra bataji fitowarta ba har saida tayi magana,


"Ummi ina kwana.."


Cikeda farin ciki hajiya kubra ta juyo ganin Hafsat atsugunne yasata kamo kafadunta ta tada ita tsaye tana murmushi,


"Lafiya lau Hafsat, sai yanzu aka tashi? Ai na shisshiga dakin kinata bacci"


Murmushin yake Hafsat tayi,


"Ummi akwai abinda za ayi ne?"


"Kamar mefa Hafsa na?"


"Na aikin gida.."


"A'a Hafsa babu abinda za ayi, har ankammala gyara gidan ai, inada ma'aikata na masu yimin komai da kika sani, girki ne kadai nake yin abuna dakaina, yanzu kije kiyi wanka ki shirya ki fito mu karya lokacin abbanku shima ya fito"


"Toh" ta amsa tareda juyawa takoma cikin daki, wanka tayi ta shirya ta fito zuciyarta cikeda mamaki na irin tarba da soyayyar da hajiya kubra ke nuna mata wadda abisa dukkan alamu zata riketa amana kamar itace ta haifeta,


Atamfa ta saka dinkin riga da zanine pieces kalar atamfar kalar ruwan hoda, hijabinta da tazo dashi tasa ta fita,


Lokacin data fita tuni har su hajiya kubra sun hau kan table suna jiranta, durkuwa tayi tagaida Alhaji sa'id,


Fuska asake ya amsa gaisuwarta yakare maganar da fadin,


"Tashi, tashi, zo ga kujera ki zauna"


Mikewa tayi taje ta zauna akusa da hajiya kubra wacce tafara kokarin hadawa Alhaji tea,


"Hafsa babu wasu hijaban ne akayan amal naga kinata saka wannan?"


"A'a ban duba ba"


"To ai kuwa inajin tabar hijabai dan bata tafi da komai nataba duk agida tabarsu..."


"Ashe yar uwarta tabarwa bata saniba" Alhaji sa'id ya karbe zancen,


Dariya hajiya kubra tayi,


"Ai so nake idan ta sai sim ta kira inyi mata albishir"


"To ai kuwa da dai nine naso inyi albishir dinnan amma naga kina nema ki rigani.."


Dariya sukayi dukkaninsu inbanda Hafsat wacce dan murmushi kawai tayi,


Abinsu gwanin sha'awa suna karyawa suna hirarsu har suka kammala nan Alhaji sa'id ya mike yana gyara babbar rigar dake jikinsa domin wurin aiki zai fita,


"Adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya" Hafsat tace dashi tana rakube ajikin kujera,


"Amin Hafsat, nidai abinda nakeso dake shine ki saki jikinki ki dauka cewar nan gidanku ne sannan kuma mu iyayenki ne, kinji? Allah yayi miki albarka"


"Amin, amin..." Hajiya kubra ta amsa tana murmushi,


Juyawa yayi yafita hajiya kubra tana biye dashi ganin haka yasa hafsat tattare kayan da sukayi amfani dasu wurin karyawa ta nufi kitchen, tana tsaka da daurayesu hajiya kubra ta dawo daga rakiyar da ta yiwa alhaji,


"Ahh hafsat ai ban sakiba, waye yace ki wankesu? Nafada miki akwai masu aiki zasu yi har wanke wanken"




"Babu komai Ummi nima gani nayi babu abinda zanyi shiyasa nace bari in wanke.."


"To shikenan ai kin kyauta, ke baki da son jiki ba irin amal ba, amal bata son motsi nan da can koda yaushe tana nade akan gado kamar wata mage.."


'Yar dariya Hafsat tayi taci gaba da wanke wanken yayinda ita kuma hajiya kubra taci gaba da bata labari akan amal wannan yasa Hafsat sake fahimtar cewar ba karamin so hajiya kubra ke yiwa yar tata ba domin magana daya biyu sai ta sako zancen amal,


Tsaf Hafsat ta gyare kitchen din bayan ta kammala wanke wanken, falo suka koma suka zauna suka fara kallo atashar tauraron dan adam,


Wannan zaman da suka yi shine yabawa Hafsat damar sakin jiki sosai da hajiya kubra domin ta dan warware suna yin hira har tana bata labarin irin yanda rayuwarta ta gudana agidan marayu.....






_Fatan alkhairi ga masoya masu bibiyar labarin..!._




*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_






*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*






_Dedicated to MISS XOXO_






*14*




aishaummi.blogspot.com








***Sosai hafsat ta sake da hajiya kubra domin hatta girkin rana tare suka yi suka shiryashi akan table saboda alhaji sa'id yana dawowa cin abinci daga office,


Har dare suna tare suna hira afalon alhaji sa'id wanda kusan rabin hirar ta amal ce, yauma kamar jiya atare suka fita ita da hajiya kubra suka yiwa alhaji sai da safe,


Yauma saida tayi karfin hali sannan tasamu bacci ya dauketa domin har lokacin tana kewar gidan marayu da kuma kewar kawarta amina,


Washe gari da safe suna kan table suna karyawa amal ta kira mahaifinta,nan hajiya kubra ta shiga murna domin bakinta yaki rufuwa,


Mikawa hajiya kubra wayar Alhaji sa'id yayi bayan sun kammala gaisawa shida amal din, cikin farin ciki hajiya kubra ta fara yiwa amal albishir na zuwan Hafsat gidan, Hafsat tana zaune tanaji bata dai jiyo abinda amal din taceba kawai dai taga hajiya kubra ta mika mata wayar tana fadin,


"To shikenan bari abata.."


Karbar wayar tayi ta kara akunnenta nan taji muryar amal din kamar zata fasa mata dodon kunne dan tsananin kara,


Tamkar dama sun san juna haka suka gaisa gamida yin sallama,


Cikin fara'a Alhaji sa'id ya mike domin fita adawo lafiya Hafsat tayi masa, zama tayi shiru bayan fitarsu shida hajiya kubra,tunani tafara aranta na yanda kowa agidan ke sonta da kaunarta tabbas ta yarda Allah shine kadirun ala man yasha'u domin ya sauya rayuwarta ya kuma juyata acikin lokaci kankani,


Yanzu kam ta warware sannan tagama sakewa da hajiya kubra, abu dayane kawai ke damunta shine kewar Amina tare da sauran jama'ar da ta dade da sani arayuwarta,


Haka dai ta rinka boye damuwarta taci gaba da zama tareda su hajiya kubra har tayi sati biyu agidan, kullum da daddare sai hajiya kubra ko Alhaji sa'id sun kira amal angaisa da ita, ita kuwa idan aka bata wayar domin su gaisa amal cewa take tana ta dokin ganinta saboda taji yanda su umminta ke zuzuta tsananin kamanninsu da Hafsat din,


Duk da cewar tana jin dadin zaman gidan kuma babu abinda ta nema tarasa amma hakan bai hanata shiga damuwa ba, tana yawan tuna rayuwarta ta baya wadda tayita acikin rashin gata da rashin galihu sannan uwa uba cikin maraici,wannan dalilin ne yasa take burin ta bada tata gudun mawar domin aganinta wannan wata damace ta samu wurin taimakon yan uwanta marayu,


Ganin kamar tana cikin damuwa yasa hajiya kubra tambayarta koda akwai abinda ke damunta, bata boye mata ba ta sanar mata da gaskiyar bukatarta na son zuwa kaiwa kawarta Amina wacce ke gidan Marayu ziyara,


"To ai duk wannan mai sauki ne Hafsat, idan kin shirya kiyi min magana sai insa driver yakaiki.."


"Toh Ummi nagode madalla Allah yasaka da alkhairi, Allah ya..."


Dakatar da ita hajiya kubra tayi,


"Bana son godiyar nan Hafsat, duk abinda nayi miki kaina nayiwa, yanzu me zaki kaiwa kawar taki?"


"Ummi girki kawai zanyi mata inkai mata domin wallahi hatta abinci wahala yake mana acan.."


"To shikenan gashi nan sai ki zabi abinda zaki dafa mata,duk abinda zaki bukata da akwai kuma kin san wurinda yake.."


Daga haka hajiya kubra ta juya tawuce cikin falo domin lokacin acikin kitchen suke Hafsat tana wanke wanke saboda sam bata son zama batare da tayi dan wani aiki ba,


Shinkafa da miyar kaji Hafsat ta dafawa Amina cikin manyan food flaks guda biyu, wanka tayi ta shirya cikin wata shaddar amal kalar ruwan toka,farin hijab tasa tafito ta iske hajiya kubra zaune tana karanta wani English novel,


"Hafsat anfito?"


"Ehh Ummi nashirya"


"To driver yana waje yana jiranki, yanzu idan kin tafi sai yaushe zaki dawo?"


"Ummi zan dan jima saboda kinga rabona da Amina an kwana biyu.."


"To shikenan sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya.."


"Amin" ta amsa tareda fita ta shiga kitchen ta debi girkin da tayiwa aminan tafita compound din gidan inda salisu driver yake jiranta,


Har wani nushadi takeji yau haka kawai saboda zataje taga Amina da sauran mutanen dake gidan marayun.




****


Tunda yusleem yaji mami tace masa anjanye maganar aurenshi shikenan yasaki jiki yayi watsi da maganar bai kara bi takanta ba amma ita mami abun yana nan aranta domin har yanzu kullum cikin tanadin kayan aurenshi take, duk inda taji ankawo kaya masu kyau ko masu tsada na mata sai ta siyo kuma zata nuna masa tace matarsa ta siyawa wacce zai auro nan gaba, shidai baya magana sai dai yayi shiru amma kuma shine zai biya kudin kayan da ta siyo wannan kam ko nawane baya shayin biya kuma bai taba musu ba,


Yauma hakance tafaru lokacin da ya shigo gidan ya isketa afalo ita da wata mata wacce ta Kawo mata kaya daga dubai, wasu dogayen riguna ne masu adon stones ajiki hadaddu,


Daga rigunan mami taci gaba dayi tana jujjuya su, bayan sallamar da yayi bai sake yin magana ba yasamu wuri ya zauna,


"Yusleem kaga rigunan nan daga dubai aka kawo kuma sunada kyau nayi sha'awarsu mutuka ko zaka siyawa matarka..?"


Yaji sarai abind mamin tace amma bai amsaba, kasancewar tasan halin abinta yasata daukar kala biyu, ja da kuma baka mai adon golden ajiki,


"Gashi na daukar maka guda biyu, duk guda daya 35 thousands ahakanma ragi tayi min amma bahaka take sayarwa ba.."


Gyada kai yayi har lokacin baice komai ba saboda shidai baiga amfanin kayan nan da mami ta dage taketa siya ba,


Saida mai kayan tatafi sannan yadubi mami wacce ke zaune har lokacin tana ta dudduba rigunan tana yaba kyawunsu,


"Wai mami dan Allah meye amfanin wadannan kayan da kiketa siye?"


"Amfaninsu? Amfaninsu kake tambaya? Kaifa mukayi dakai zaka nemo matar aure, ko kamanta? Ai zuba maka ido nayi ka gama zagaye zagayenka ka Kawo min wacce kakeso idan kuma hakan ya faskara to ni bazan gajiya ba wurin sake nemo maka wata.."


Shiru yayi ya lumshe manyan idanuwansa tareda jingina da jikin kujerar da yake zaune batare da yayi magana ba....








*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*






*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_






_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*






_Dedicated to MISS XOXO_






*15*








***Lokacin da Hafsa takarasa gidan marayun ba karamin dadin ganinta Amina tajiba domin bata taba tsammanin sake yin tozali da itaba acikin rayuwarta,


Kebewa sukayi suka samu kasan wata bishiyar darbejiya suka zauna suka fara tattaunawa,


"Hafsa har kinyi kyau, ki ganki yanda kika sauya lokaci daya" Amina tace da Hafsat tana bin jikin Hafsat din da kallo,


"Amina kema insha Allah canji yana nan zuwar miki ai tunda mukayi hakuri da rayuwar da muka samu kanmu to da izinin Allah zamu dace da samun babban rabo.."


"Hmmm abar kaza dai kawai acikin gashinta hafsa, yawwa baki bani labarin yanda akayi ba rannan da kika tafi.."


Kwashewa duk yadda akayi hafsat tayi tafadawa amina da irin gatan da take samu yanzu,


Sun dade suna hira domin sai da la'asar liss sannan hafsat tatafi nan dinma kamar kada su rabu da amina saida hafsa tace ai zata rinka zuwa akai akai sannan hankalin amina ya kwanta.


Lokacin da hafsat takoma gida har alhaji sa'id yadawo daga office yana zaune a falon hajiya kubra shida ita bayan ya kammala cin abinci kasancewar yau bai dawo yin lunch ba,


Sallama tayi tashiga bayan sun amsa mata,


"Hafsa yau kuma ziyara aka kai?" Alhaji sa'id ya tambayeta yana murmushi,


"Ehh Abba" tabashi amsa,


"To ai yayi kyau, kin kyauta mutuka wannan ya nuna min cewa bazaki manta dasu ba duk abinda kika zama nan gaba"


"Ai da alama kam hafsat bazata manta dasu ba" hajiya kubra ta karbe zancen ta hanyar bawa alhajin amsa,


Zama hafsat tayi acikin falon tana sauraren hirar da su alhaji keyi wanda basu suka tashiba sai da sukaji anfara kiran sallar magrib.




Satin hafsat uku agidan amma kai idan kaganta zakace wata uku tayi domin tayi kiba tayi bul bul sosai, domin tana samun kulawa sosai daga iyayen rikon nata ga gata da suke nuna mata kamar sune suka haifeta,


Malamai guda biyu musamman alhaji sa'id ya daukosu domin su rinka koyar da ita karatun boko da na Arabic, sannan kuma yayi mata register a wata center ta mata wacce ake koyar da sana'o'i saboda tana son tasake samun kwarewa sosai akan sakar da ta iya,


Wadannan abubuwan da tasaka agaba sune suka saka bata da lokacin kanta yanzu koda yaushe tana da abinyi amma hakan bai hanata ware lokaci na ziyartar kawarta amina ba,


A fannin sakar ma tafi maida hankali domin hajiya kubra tafada mata cewar idan har ta gwanance to zata siyo mata keken saka kuma tanada shagon saida kayayyaki zata bata jari tafara saka kaya ana kaiwa shagon ana sayar mata wannan dalilin ne yasa ta bada himma sosai har ta samu kwarewa kamar yadda hajiya kubran keso,


Satinsu shida aka yayesu domin sun iya sosai, alkawarin da hajiya kubra ta daukar mata ta cika ta hanyar siyo mata keken saka harda sabuwar wayar hannu dambasheshiya mai kyau kirar kamfanin LG,


Murna wurin hafsa sai wanda yagani, samun keke da tayi sai yasake rike lokacin ta koda yaushe tana kai tana aiki acikin satittika kadan ta saka kaya masu yawan gaske, kayan sanyi na yara da towel da safa da hula,


Diban kayan akayi aka kai shagon hajiya kubra na kasuwa acikin satin aka Kawo kudin kayan domin har sun kare,


Kiranta hajiya kubra tayi itada alhaji sa'id domin suji ra'ayinta dangane da kudin,


"Hafsat kudin naki ajiyewa zakiyi a banki ko kuma wani abu zaki siyo ki ajiye?" Alhaji sa'id ya tambayeta,


"Abba ba ajiyewa zanyi ba, kaya nakeso insiya inkaiwa gidan marayu gudun mawa" tabashi amsa idonta yana kallon kasa,


Murmushi Alhaji sa'id yayi,


"Allah sarki hafsat hakika ke tagari ce kuma kinada hankali da nutsuwa, Allah yayi miki albarka, yanzu abinda za ayi shine, gobe idan Allah yakaimu zan hadaki da driver sai yakaiki kasuwa ki siyi duk abubuwan da kike ganin zaki siya sai kuje ki kai musu.."


"Allah yabaki lada ya biyaki da gidan aljanna kinji.." Hajiya kubra tayi magana cikin marerecewa,


Tashi hafsa tayi tafita domin malamin dake koyar da ita karatun arabi duk yamma yazo yana jiranta.


Washe gari kamar yadda alhaji sa'id ya alkawarta haka yasa driver ya dauketa yakaita kasuwa tayi siyayya wadda saida ta karar da kudin tass ko kwandala baiyi saura ba, daga nan gidan marayu suka wuce, koda sukaje kuma akaga irin gudun mawar da takai saida kowa yayi mamaki domin kayane na amfanin yau da kullum irinsu sabulun wanka da na wanki, omo, sugar, man shafawa da makamantansu,


Rungumeta Amina tayi tana kukan farin ciki tareda yi mata addu'ar alkhairi, bama Amina kadai ba kowa addu'ar da yake yi mata kenan....








*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*






*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*






Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login