Showing 27001 words to 30000 words out of 70255 words
mai tsarki ya sanar damu nau'o'in azabar da ya tanadarwa duk wani wanda ya kasance yana aikata irin wannan halayyar...."
Tausassun hannayensa yakai yadora akan nata har lokacin dai idanuwansa suna kan fuskarta sannan sun juye daga farare zuwa jajaye,
"Ba laifina bane, karki ga laifina, komai yana faruwa ne da dalili, wallahi irin rayuwar da na tsinci kaina abaya ta kunci, talauci, tsangwama, tsana da kuma kyara itace tayi sanadiyyar fadawata cikin wannan mummunan halin..."
Kallonta yayi da jan idanuwanshi tareda kwantar da kanshi bisa cinyarta yanajin zuciyarshi tana yi masa zafi wanda bai taba jin irinsa ba,
"Yaya yusleem nikuma sai nake ganin wannan ba dalili bane ko hujja da har zaka jefa kanka cikin halaka..."
"Wannan daliline mai karfi NANAH...."
"Nikuma agareni ba dalili bane domin wannan abun da kake aikatawa yafi dukkanin abubuwan da ka zayyano muni,haba yaya yusleem kamanta labarin wani mutum da annabi yafada mana mai tsawaita tafiya yana mai gizo mai k'ura k'ura yadaga hannayensa zuwa sama yana cewa ya ubangiji ya ubangiji amma annabi yace ba a amsa masaba saboda abincinsa haramun ne,abin shansa haramun, tufafinsa haramun sannan yayi guzuri da haram...."
Dago da kanshi yayi ya kalleta sakamakon jin saukar hawayenta akan wuyanshi,
"NANAH arayuwar baya na tsinci kaina cikin mawuyacin hali, mahaifinmu Alhaji Ahmad Mela mu Goma Sha biyar ya haifa sannan matanshi uku kowacce tanada yara biyar,
Ya mutu ya barmu tun muna kanana, acikin yaransa mu ukune manya daga Shu'aib sai Mukhtar sai ni, dukkaninmu kanmu daya, kasancewar dama gidan ba azaman lafiya yasa tun rasuwar mahaifinmu kowa ya kama 'yayanshi yarike bayan anraba gado,kuma kin san zumuncin yanzu yanda yake na ganin ido ne,
Nanah a lokacin wallahi duk da ni yarone ban wuce shekara 24 ba ina yin iya bakin kokarina wurin nemowa mahaifiyata da kannena abinda zamuci amma mami bata gani kullum cikin kusheni take da zagi cewar ni banida zuciya zan bari wai talauci ya kasheta,
Nayi iyakar iyawata ganin na fahimtar da ita amma taki fahimta ita kawai burinta lokaci daya inyi kudi inzama millionaire dan kawai ta bawa kishiyoyinta haushi,
Idan kinga irin sana'o'in danayi makaskanta sai kin tausaya min, har turin baro wallahi nayi, na saida pure water, nayi kanikanci,nayi jiran shago duk wai dan inrufawa kaina da yan uwana asiri amma mami bata gani koda yaushe bata da magana sai nacewa, ita bazan burgeta ba muddin ban tashi nanemo kudi duk inda yake nazama mai kudiba,mami duk tabi ta tsangwameni ta tsaneni akan kawai ban zama mai kudiba,
Da wannan kananan sana'o'in nasamu nakammala degree amma abin haushi babu aikin yi dole nakoma gareji naci gaba da gyaran mota,
Sau da dama ku mata kune kuke cusawa mutum ra'ayin da baiyi niyyaba nanah, a lokacin idan nasiyowa mami abu nakawo mata ko atamfa ko takalmi sai ta raina kiri kiri zata nuna min ban burgeta ba kuma bata ji dadiba wani lokacin ma har takara da fadin "ni ba irin wannan harkar tsiyar nakeso kayimin ba, ni so nake karinka Kawo min kaya masu tsada akwati akwati yanda nima zan fantama, amma kai kullum abubuwa ba arziki kaki katashi kayi arziki yanda mahaifinku ya mutu bai bar muku komaiba kaima haka zaka mutu baka bar komai ba?"
Irin Wadannan maganganun da mami kemin sune suke tsaya min araina inji zuciyata takasa samun nutsuwa saboda ni aganina ina iyakar kokarina amma komai nayi bata gode min kuma bazata samin albarka ba,
Acikin wannan yanayin wan mahaifinmu yabani yarsa Rahina in aura, sam Rahinan bata sona saboda kawai banda abin hannu sai rufin asiri,
Dakyar ita da uwarta suka amince akayi auren saboda babu yanda zasuyi, bayan aurenmu da Rahina nashiga matsanancin hali saboda zan siyo mata kayan cefane in aiko mata dashi daga gareji amma wallahi nanah yanda aka Kawo kayan nan haka zan dawo insamu kayana tabarshi awurin bata taba ba, idan abin lalacewa ne to sai dai ya lalace, bazata yimin girki ba idan nayi magana tace ita bazata dafawa matsiyaci abinci ba mai k'ashin tsiya wanda bashida rabon arziki,
Bazata yi sharaba,baza tai wanke wanke ba babu abinda takeyi abinci ma mahaifiyarta ce ke aiko mata daga gidansu batare da mahaifinta yasaniba, kullum idan naje gaida mami dakyar take amsawa, idan nadawo gida Rahina ta tareni da masifa da bakaken maganganu wani lokacin ma sai tace bazan shiga dakinta ba ita ubanta bai siya mata gado da katifa dan matsiyaci ba dama kuma tunda akayi auren bata barni na kusanceta ba domin kullum da wuka akasan pillow take kwana wai duk ranar da nayi yunkurin zuwa inda take sai ta kasheni,
Kullum a falo nake kwana ita kuma tana cikin daki wata rana ma idan bata gadamaba rufe kofa take sai dai inkwana awaje idan nafadawa mami sai ta goyi da bayanta tamkar ba itace ta haifeni ba, duk da irin wannan abubuwan da Rahina kemin bai hana zuciyata fara sonta ba amma ita hankalinta ba akaina yakeba domin haka mahaifiyarta zata zo har gida su hadu su zageni tass suna kirana da matsiyaci marar arziki,
In takaice miki zance daga karshe sakani agaba sukayi saida nasaki Rahina duk da ina sonta ashe wani mai kudi tasamu suke soyayyarsu da aurena, aranar da nasaketa sukazo suka kwashe kayanta Hafsat nayi kuka irin kukan da ban tabayiba domin ina sonta duk da rashin kyautatawar da take yimin,
Kwana biyu nadauka agida ban fitaba saboda damuwa, da daddare ina kwance ni kadai adaki na dauki wayata nashiga facebook nan naga wani yaturo min da friend request babu bata lokaci nayi accepting,
Bayan mun gaisa yake cemin a ina nake nafada masa, sai yacemin wai ina dan harkoki nace masa ehh to ana dan tabawa saboda ni ban gane abinda yake nufiba haka mukaci gaba da yin hira yace shi dan majalissa ne awani gari yakamata inje in sameshi,
Wallahi nanah ban taba sanin mutumin nan bana kirki bane saboda nayi tunanin ko aiki zai bani tunda nafada masa nagama karatu babu aikin yi,
Sallama nayiwa mami nashirya natafi wurinsa da takardu na amma koda naje sai labari yasha banban lokacin da yanuna min karara abinda yake son yi dani ashe gay ne ban saniba, a lokacin ban aminceba amma koda nazauna nayi tunani nahango irin tsangwamar da mutane kemin akan bani da arziki da irin halin ko inkula da mami ke nuna min da kuma yadda aka rabani da rahina sai kawai na amince shiyasa nace miki amafi yawan lokuta ku mata kone kuke zama silar faruwar komai domin dayawa daga cikinku bakuda godiyar Allah burinku kawai mutum yayi arziki batareda kun damu da sanin halalcin arzikin ko haramcinsa ba,
Kwanana uku awurinshi aranar da zan dawo yabani wata kyakkyawar mota banda tsabar kudi dubu dari biyar,
Tunda mami taga nafara arziki shikenan tahau murna tana cewa burinta yakusa cika sukuma mutane sai cewa suke Allah ne yayi min nasibi dare daya ya azurtani, wallahi nanah ko sau daya mami bata taba tambayata a ina nake samun kudiba ita kawai tunda nace mata wani uban gida nasamu yake buda min shikenan tahau murna tana saka min albarka,
Kuma har yau dinnan da nake miki magana mami bata taba tuhumata akan arzikin da nake dashiba gashi kuma acikin lokaci kankani na mallaki komai na jin dadin rayuwa kama tun daga gidaje, kamfanoni, motoci da komai da kika sani na jin dadin rayuwa domin mutanen dake cikin harkar nan masu fada ajine daga senators sai Reps sai Governors...."
Zamowa daga kan bedside drewar din Hafsat tayi tazauna dirshan akasa cikeda tashin hankali, matsawa kusa da ita yayi yasake dora kanshi akan cinyarta yafashe da wani kuka mai ban tausayi,
"Yaya yusleem daina kuka dan Allah, shi Allah mai yawan gafara ne domin yace yana gafarta zunabai gaba daya komai yawansu mutukar muka tuba kuma muka nemi gafararsa, nidai dan Allah so nake kabar aikata wannan dabi'ar domin bata dace dakai ba, kazanta ce, masu aikatata sun tabe duniya da lahira.."
Hannunta yakama ya matse cikin nashi,
"Nanah na daina, amma nasan rayuwata tana cikin hatsari domin wallahi sawa zasuyi akashe ni saboda zasuga kamar zan tona musu asiri ne kuma mafi yawansu manyan mutane ne.."
"Yaya yusleem insha Allah babu abinda zai sameka, insha Allah Allah zai kareka..."
Baiyi magana ba illah kukan da yaci gaba dayi mai tsuma zuciya,
Rarrashin duniya Hafsat tayi masa amma baiyi shiruba, ranar haka suka kwana azaune ido biyu har gari yawaye,
Alwala yayi yafita masallaci idanuwansa akunbure sunyi jajur, ita kanta Hafsat din kukan da tayi ba kadan bane,
Acikin sujjadarta kuwa tajima tana yimasa addu'a, tana zaune akan abin sallar tayi tagumi ta jingina da jikin gado sai gashi yashigo akusa da ita ya zauna yajingina da jikinta, hannu tasa ta rungumeshi,
"Yaya yusleem kadaina kukan nan haka dan Allah.."
"Hafsat wallahi natsani kaina, natsani rayuwata, ni yanzu mutuwa kawai nake s...."
Saurin rufe masa baki tayi,
"Yaya yusleem babu kyau fatan mutuwa, karkayi sabo dan Allah kayi shiru.."
"Nanah mami ta illata rayuwata, bata min adalciba.."
Sake rufe masa baki tayi, "kadaina fadin haka, mami mahaifiyarka ce bata cancanci haka daga gareka ba domin tafi kowa sonka.." Shiru yayi baice komai ba saboda jin abinda tace.
Haka suka ci gaba da zama har rana tafito karfe 12 narana yayi, tashi Hafsat tayi taje kitchen ta dafa musu indomie da kwai ta hado tea takawo musu, ko kallon abincin yusleem baiyi ba bare tasa ran zaici, ta rarrasheshi iya rarrashi amma yace bazai iya ciba,
Haka suka wuni da yunwa har dare,
Yau ma bacci baiga idonsu ba sai jikin asubah ya daukesu yana kwance akan cinyarta.
Karfe 8 nasafe suka farka, salla sukayi tace bari takawo masa tea, girgiza mata kai yayi alamun bazai sha ba, dawowa tayi tazauna akusa dashi takamo hannunshi,
"Yaya yusleem haka zaka zauna jiya bakaci komai ba yauma kaki ci?"
"Nanah bazan iya cin komai ba musamman ma wanda aka siya da wannan kazamin kudin ..."
"To idan nabada aka siyo maka wani abun nadafa maka zaka ci?"
Girgiza kai yayi alamun a'a, tashi tayi taje cikin drewar din gadonta ta dauko dari biyar,
"Wallahi wannan ba irin kudin ka bane, ranar da naje gidane Abba yabani 5000,gashi zan bawa mai gadi ya siyo maka indomie indafa maka"
Baiyi magana ba tasaka kai tafita, tunda tafita bata dawo cikin dakinba har sai da tadafo indomie din,
Agabanshi tazauna ta diba takai saitin bakinshi, kawar dakai yayi,
"Please yaya yusleem..."
Dakyar yayarda yayi 5 spoon daga haka bai karaba, ita kanta cokali biyu kacal tayi tabari tature gefe.
Har kwana uku suna cikin wannan hali yusleem dai dai da ruwan gidan yaki sha bare yaci abinci, aranar tun sassafe yafice daga gidan batareda yasanar da itaba, bashi yadawo ba sai la'asar,
Tana falo tayi tagumi yazo ya sameta, hannunta yakama ya matse cikin nasa,kallonshi tayi cikin tausayawa domin har ya dan fada yayi wani iri kamar bashiba,
"Yaya yusleem ina katafi haka tun safe,lafiya kuwa?"
"Zan fada miki, yanzu kitashi kije ki debo kayanki gidan nan zamu bari, yau bazamu kwana agidan nan ba.."
"Lafiya?" Ta tambayeshi tana zaro ido,
"Kidai je ki kwaso kayanki kifito mu tafi, nasayar da gidanne bama shi kadaiba komai nawa da kika sani nasayar.."
"To me zakai da kudin?"
"Nasaka acikin asusun marayu, yanzu banida ko kwandala nanah, banida komai yanzu, su kansu kayan sawata wallahi dan babu yanda zanyi dasu ne amma da bazan kara sakasu ba.."
Hawayen dake makale acikin idanuwanta sune suka silalo tajuya ta nufi cikin bedroom dinta,
Lokacin da tafito rikeda babbar trolley dinta shima har ya fito yana kulle part dinshi, jakarta yakarba yahada da tashi yaja suka fita,
A bakin gate taga wasu mutane guda 3 suna jiransu, kulle gidan yayi da wani babban padlock yamika musu key din yarike daya awurinshi domin yafada musu da sauran kayansu aciki,
"Ina mai gadin kuma?" Ta tambayeshi,
"Na sallameshi tun safe"
"To yanzu ina zamuje?"
"Allah ne yasani domin nikaina ban saniba gashi nafada miki babu ko naira daya atare dani domin hatta account dina na rufeshi..."
Trolley dinsu yasoma ja yayi gaba nan tabi bayanshi suka fara tafiya batare da sunsan inda zasuje ba.....
*_Ummi Shatu_*👌🏻© *HASKE WRITERS ASSO.*
*ALWASHI....!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to MISS XOXO_
*29*
***Bin bayanshi tayi suka fara tafiya batare da sun san inda zasuje ba har saida suka danyi nisa da gidansu sannan Hafsat ta dakatar dashi,
"Yaya yusleem yanzu ina wai muka nufane takamaimai?"
"Ai nafada miki ni kaina banida masaniyar inda zamuje..."
"To tsaya inkira ummi inada kudi awurinta sai inje in karbo kaga ko babu komai zai dan rage mana wani abun.."
Shiru yayi baice komai ba illah tsayawa da yayi akarkashin wata bishiyar mangwaro,
Wayarta ta zaro tasoma kiran Ummi, saida suka gaisa sannan tayi mata maganar kudin kayan sanyin da ta saka kashi biyu,
"Hafsat kin san ban fiya son in ajiye kudi agida ba amma anyi sa'a ga dubu talatin zan bawa Salisu yakawo miki yanzu..."
"To shikenan Ummi dan Allah kice yayi sauri saboda amfani zanyi da kudin yanzun nan..."
Sallama sukayi ta katse wayar takarasa kusa da yusleem ta tsugunna,
"Yi dan hakuri kadan yanzu ummi zata aiko min da kudin"
Daga mata kai yayi baiyi maganaba da alama miskilancin ne ya motsa kuma hakan bazai rasa nasaba da irin damuwar da yake ciki ba,
Bayan kamar mintuna 15 suna zaune sai ga motar gidansu ummin tana dosowa da sauri hafsa ta tashi ta tsayar da salisu driver ta karbi kudin tana kallonsa sam bata son ya fahimci wani abu bare idan yakoma yafada,
"Kaga nima baki nayine yan uwan mijina ne suka zo daga can wani kauye kuma baya nan shine zan basu kudin mota"
"Allah sarki to Allah ya kiyaye hanya"
"Amin"
Saida taga bacewar motarsa sannan takoma wurin yusleem wanda ke zaune shiru yana tunani,
"Yaya yusleem tashi mutafi to.."
Mikewa yayi yaja akwatunansu suka fara tafiya,
Adaidaita sahu suka samu suka tare bayan sun fara tafiya mai adaidaitan ya tambayesu wurinda zai kaisu,
"Bawan Allah idan akwai unguwar da kasani wacce za a iya samun dakin haya ayanzu kawai kaimu can..." Inji Hafsat,
"Ahh za asamu mana hajiya, unguwar da nake akwai gidajen haya sosai bari muje..."
Yar tafiya mai tsawo kadan sukayi sai gasu cikin wata unguwa, kallon yanayin unguwar dukkansu suke yi domin da alama ta talakawa ce saboda ko titi babu gashi gidajen awani cunkushe suke babu tsari,
"Yawwa ga gidan alhaji Bashari yanada gidajen haya har guda uku bari inyi muku sallama dashi"
"Yawwa mun gode"
Kafin dan adaidaita sahun ma yafita saiga mai gidan yafito,
"Yawwa ga alhajin ma"
Fita Hafsat tayi mai adaidaita sahun yana biyeda ita,
"Alhaji barka da yamma, dama wadannan ne suke neman dakin haya.."
Dan jimm alhajin yayi sannan yace,
"Ai inajin dukka gidajen nan akwai mutane aciki.."
"To alhaji yanzu ya za'ayi?" Inji Hafsat,
"Yawwa natuna jiya wani yafita sakamakon transfer da akayi masa ta aiki amma gidan ba anan layin bane a layin gabane"
"Alhaji nawane kudin dakin"
"Dubu ishirin ne"
"To shikenan yanzu zamu baka dubu goma, nanda kwana biyu sai mu cika maka"
"To babu laifi, babu laifi Kawo"
Kirgar kudin Hafsat tayi tabashi suka koma cikin adaidaita sahu suka nufi layin da gidan yake,
Fitowa sukayi suka shiga cikin gidan nan suka ganshi babba domin dakuna sun kai goma sha biyar can gefe kuma rijiya ce gefenta wasu mata ne kimanin su 8 zaune suna hira masu kitso kuma sunayi,
Dakin da zasu zauna aciki gashi nan abude duk sumintin ya dan farfashe,kayansu suka shigar ciki takalli dan adaidaita sahun,
"Bawon Allah a ina zamu samu motar da zata debo mana yan kayayyakinmu?"
"Hajiya nima ai ina yin dakon kayan, bari inje indauko akori kura.."
Fita yayi ita kuma ta tsaya tana karewa dakin kallo wanda yake da dan girma amma ba canba, gabanta ne yafadi sakamakon tunawa da tayi da matan da ta hango atsakar gidan ita fatanta daya Allah yasa ba bathroom guda daya bane agidan,
Ji tayi andafa ta, ahankali ta juya, yusleem tagani,
"Tunanin me kikeyi?"
"Yaya yusleem fata nake Allah yasa bathroom din gidan nan ba guda daya bane"
"Idan guda dayane mezai faru?"
"Takura zamuyi, kuma bana son idan kafito daga wanka mutane suyita kare maka kallo.."
Kafadarta ya dafa yayi mata nuni da hannunsa bayan yadan saki murmushi,
"Kinga bathroom nan acikin dakin nan.."
Sai lokacin ma ita takula da kofar bathroom din amma sam da hankalinta bai kai nanba, zuwa tayi ta bude nan taga bathroom din dan kuf dashi,
"Wannan dinma duk da haka babu laifi.." Tafada acikin zuciyarta.
Babu jimawa dan adaidaita sahun nan yadawo da mota ta diban kaya fita tayi suka koma gidansu ta bude tashiga yan kayayyakin da tasan zasu bukata ta debo musu irinsu kwanukan cin abinci tukunyar girki, bargo, bedsheet,labule sai katifarta sannan bata bar keken sakarta ba shima ta hado dashi,
Wurin biyar da rabi suka koma gidan hayar nan aka sassauke kayan ta biya kudin diban kaya Dubu biyar, har ciki mai adaidaita sahun nan ya taimaka musu suka shigar da kayansu,
Share dakin tayi ta karkade ko ina suka shigar da katifar ta shimfidata wacce ta cinye fin rabin filin dakin gashi babu ko leda atsakar dakin sai simintin dake shimfide kawai,
Yar madaidaiciyar dardumar data dauko musu ta shimfida agaban katifar sannan ta shimfida bedsheet akan katifar tajera musu filillika guda biyu,
Yusleem ta kalla wanda ke kokarin kafa musu labule,
"Yaya yusleem bari indebo ruwa inwanke mana toilet din.."
"Kibari ingama sai na debo"
"A'a kayi wannan din idan kagama sai ka yi alwala kaga fa ko salla bamuyi ba"
Bucket ta dauka ta fita taje bakin rijiya inda matan nan ke zaune,
"Sannunku.."
"Yawwa sannu da zuwa.." Matan suka fada har suna hada baki,
Ruwa taja ta cika bucket din ta dauka ta koma daki, wanke toilet din tayi tasake komawa ta debo wani ruwan ta cika daya bucket din sannan ta ciko wannan din ta ajiye,
Alwala sukayi sukai salla,
Kan katifa taje ta kwanta saboda gajiyar da take tareda ita, shikuma yana kan carpet azaune yana tunanin rayuwa domin ko a mafarki bai taba tunanin wai zai yi irin wannan rayuwar ba amma dayake Allah shine mai cancanja al'amura sai gashi rayuwa ta canja ya tsinci kanshi acikin wannan halin,
"Yaya yusleem baka jin yunwa ne?"
Juyawa yayi ya kalleta,
"Inaji amma sam bana sha'awar cin komai"
"Duk da haka daurewa zakayi kaci, bari ayi sallar magrib sai mufita mu samo abinda zamu ci"
Har bayan sallar magrib Hafsat takasa tashi saboda gajiyar da tayi, saida akayi