Showing 60001 words to 63000 words out of 70255 words
yana tsoron kar ya cutar da itaba da ayau dinnan ba gobeba babu abinda zai hanashi zama cikakken ango,sake kankameta yayi yana faman jujjuya kanshi,
Shiru Hafsat tayi tana saurarensa cikeda jin tausayinsa, dakarfi da karfi take jin fitar numfashinsa har yasoma fita ahankali ahankali dahaka har yadawo fita normal sai lokacin ya iya barin jikinta ya matsa gefenta amma har lokacin yana makale da hannunta kamar wadda za adauke masa ita,
Jin yadan sassauta rikon da yayiwa hannuwanta yasata zaton cewa bacci ya daukeshi,tashi tayi ahankali tawuce bathroom, ruwa takama tadawo tadauko rigar baccinta tasaka takoma kusa dashi ta kwanta tana faman runruntse idanuwanta saboda irin dakumar da yayiwa kirjinta har wani irin radadi takeji yana damunta,
Dakyar ta iya yin bacci awannan dare, shikam yusleem tunda yasamu bacci ya daukeshi bashi ya farkaba saida asuba wannan dinma Hafsat ce ta tadashi, wata wawiyar mika yayi sannan yashiga bathroom din, yajima aciki kafin yafito domin saida yayi wanka,
Lokacin da yafito Hafsat tana zaune akan abun salla tana lazimi, kallonta yayi yai magana ahankali,
"Bari naje part din can..."
Rike kafarshi tayi saboda bata son yafita domin zasu iya haduwa da mami afalo,
"Dan Allah ya yusleem karkaje kayi sallarka anan..."
Murmushi yayi yasake rage murya kamar wanda baya son wani yaji abinda zai fada,
"Wallahi kayana bazasu yi salla ba saboda gaba daya sun baci..."
Cikashi tayi batare da ta kalleshi ba, wucewa yayi yaje yabude kofa yafice, aranta tanata addu'ar Allah yasa kar mami tafito taganshi, kwanciya tasake yi bayan ta kammala addu'o'in da takeyi,
Baccine yasake daukarta saboda jiya bawani mai yawa tayiba, ba ita tatashiba sai karfe 8 nasafe, wanka tayi tashirya cikin doguwar riga tawani jan material, turarrukan jiya tafesa ta hade jikinta da kamshi mai dadi tafita.
Abangaren yusleem kuwa dakyar ya iya komawa bacci bayan ya idar da salla, juyi kawai yarinka yi akan gado daga karshe wani wahalallen bacci ya daukeshi, karar wayarshi ce ta tasheshi lokacin karfe 8 saura nasafe,
Hannu yamika yadauko wayar idanuwanshi arufe, muryar Hafsat mori yaji tana magana cikin kasalalliyar murya da alama ita dinma daga baccin ta tashi,
"Ranka yadade ina fata ban tasar dakai ba a bacci?"
Batare da yabude idanuwanshi ba yayi magana,
"Meya faru? Dama ina son yin magana dake.."
Shiru tayi, jin baiyi magana ba yasata fadin,
"Ina sauraronka"
"Meya kawoki gidanmu jiya? Hafsat nafada miki fa inada mata, bakya tunanin zuwanki yana iya haifar da matsala tsakanina da iyalina? Dan Allah na rokeki karki sake zuwa gidanmu..."
Bai jira abinda zata fadi ba yakashe wayar kittt, daga nan tashi kawai yayi yashiga toilet yayi wanka yafito yanaji Hafsat mori nata kiranshi awaya amma yayi fuska yaki kallon koda wayarne,
Farin wani lallausan yadi yasaka yasha turare yadauki wayarshi yafita da hularshi ahannu, a tsakiyar falo ya hango Hafsat tana shirya jaridun mami akan centre table ita kuma mamin tana kitchen ita da kuku, wucewa yayi bayan sun gaisa da mami yashiga cikin falon, da kafadarshi yadan bugeta, murmushi tayi batare data juyo ba saboda tagane cewar shine domin kamshinsa yasanar da ita,
"Morning Nana hafsat"
"Morning ya yusleem" ta amsa mishi bayan ta dago amma bata kalleshi ba,
"Kinga irin wahalar da nasha dazu da asuba bayan nabar dakinki? Acikin week dinnan gaskiya zan koma chairo, wallahi nagama kaiwa karshe atakura"
Shiru tayi masa acikin ranta tana hangowa fitinar da yusleem zaiyi duk ranar da yagama samun lafiya,
"Yanaji kinyi shiru? Ko bakya son nawarke ne?"
Murmushi tayi tadago tana kallonsa saboda jin abinda yafada,
Kafin tayi magana tajiyo mami na kwalla mata kira daga kitchen, gefenshi ta raba tawuce batare data sake kallonshi ba,
Kayan breakfast tadauko tazo ta ajiye ta zuba mishi, da kallo yake binta yana kurbar tea din dake hannunshi amma yana lura da ita sai wani dan yayyatsina fuska takeyi, saida ya kammala breakfast din sannan yaja hannunta zuwa bedroom,
"Nanah meyake damunki naga alamun damuwa atare dake?"
Shiru tayi tasunkuyar da kai,
"Fada min Mana"
"Babu komai"
Murmushi yayi yakai hannu jikinta dasauri tarikeshi,
"Ya yusleem dan Allah kayi hakuri.."
Murmushi yayi yajuya yafita saboda ya fahimci abinda ke damunta, cikin falon tabishi tasameshi tsaye rikeda hularshi, karbar hular tayi tasaka mishi yajuya yafita, tana jiyoshi yana yiwa mami sallama domin har lokacin tana cikin kitchen saboda tafara shirye shiryen tarbar yan makaranta wadanda zasu dawo.
Wurin mami taje suka cigaba da aiki tare bayan ta kammala yin breakfast, har azahar tayi suna cikin kitchen suna aikace aikace zuwan khadija ne yasa Hafsat barin kitchen din suka shiga falo,
Yar hira suke tabawa bayan hafsat ta gabatarwa da khadija abinci shinkafa da doya da miya,
"Amarya ta ango" khadija tace da hafsat cikin wasa,
"Yanzu ai kece amarya khadija" hafsat tafada tana murmushi,
"A'a kedin dai"
"Zancen kike so" inji hafsa, maganar yusleem tajiyo acikin kitchen yana cewa mami,
"Yunwa ce ta dameni shine nadawo inci abinci"
Murmushi hafsat tayi saboda tasan ba gaskiya bane abinda yafadawa mami shidai kawai fitinarsa ce tadawo dashi, cikin falon yashigo ganin khadija yawani hade rai sama sama ya amsa gaisuwarta yawuce cikin bedroom,
Tashi hafsat tayi tashiga kitchen, abinci tahado masa ta dauka ta nufi cikin bedroom din har lokacin khadija tana zaune tana cin abincinta,
Kwance taganshi agefen gado idanuwanshi alumshe, ajiye abincin tayi taje kusa dashi,
"Lafiya kuwa ya yusleem?"
Bai bata amsaba illa kamota da yayi ya sadata da jikinsa ya kwantar da ita, fuskarta zuwa wuyanta yake sinsina da fuskarshi,
"Ni dama nasani" tafada acikin ranta,
Cigaba da birkitata yayi har zuwa tsawon wani lokaci dakyar ya iya barinta ya tashi domin cin abincin da ta Kawo masa saboda zai koma office,
Zuba mishi tayi ya dauka yafara ci yana kallonta,
Sunkuyar da kanta tayi taki kallonshi, dan murmushi yarinka binta dashi har yagama,
Fitowa sukayi bayan ya gama cin abincin nan taga khadija bata nan da alama tafiya tayi, saida ta rakashi har wurin motarshi taga tafiyarshi sannan takoma ciki.
Cikin yan kwanakin gaba daya busy hafsat take itada mami saboda aikace aikacen da suke yi na karbar baki, ranar laraba da yamma su Abdul suka dawo shida khalifa,
Bakin mami kasa rufuwa yayi sai murna take tana fadin "saura yar autana surayya itama tana tafe"
Tunda su khalifa suka dawo sai hafsat ta dauke kafarta da zuwa part dinsu wurin yusleem duk da cewar har yanzu yana nan adakin Abdul sukuma samarin sunyi skwatin adakin khalifa kafin akoma sabon gida,
Duk da bata zuwa amma shi kowanne daren duniya adakinta yake kwana,
Dawowar su Abdul da sati biyu itama surayya tadawo, murna hafsa tashiga yi harda rungume surayya nan suka kafa dandalin hira har karfe 11 nadare,
Wasu hadaddun English wears surayya tadawo dasu akwati guda, kallonta hafsa tayi tana murmushi,
"Wai ke sury bakida kayane sai wadannan...?"
Dariya surayya tayi,
"Wallahi ban iya saka wasu kayan inba wadannan ba, ke nifa atamfa da sauran kayan gargajiya gumi suke sani, ga uban nauyi shiyasa ma bana iya sawa"
"Amma kuwa kin hadu da aiki" inji Hafsat,
"Babu wani aiki, kema ai nakawo miki tsarabarsu kisa ki kashe ya yusleem"
"Bakida kunya..."
Karar wayar hafsa ce ta katse musu hirarsu,
"Ya yusleem ya akayi?"
"Zo ina jiranki awaje"
Tashi hafsa tayi bayan ta dauki hijab, kallonta surayya tayi tana murmushin shakiyanci,
"Saida safe kenan"
"Ahh kin manta sai jibi" hafsat tafada tareda ficewa daga cikin dakin, hannunta yakama lokacin da tafita yanufi part dinsu khalifa,
"Ya yusleem..."
"Bana son gardama"
Shiru tayi har suka shiga falon, su Abdul din suna zaune kowannensu dauke da laptop dinshi suna danne danne, kunya ce ta kamata hafsat saboda ganinsu abdul amma shi ko ajikinsa, sakata yayi agaba suka wuce ciki yamaida kofa ya rufe harda sa key,
"Haba ya yusleem..."
Bai kulata ba yacire rigar jikinshi ya kwanta,
"Idan kin gama mitar sai kizo ki kwanta.."
Yace da ita bayan ya lumshe idanuwanshi, ta dan jima atsaye daga karshe dai taje gefenshi ta kwanta, dama kamar jira yake yajawota jikinshi ya kwantar.
Koda asuba hanata tafiya yayi bai barta tatafiba sai da gari yawaye,ai kuwa tasha tsokana awurin surayya dan tun tana mayar mata har dai tayi shiru ta rabuda ita daga karshe tace,
"Bari yayan naki yafito sai nafada masa"
Jin haka yasa surayya yin shiru tabar zancen, tun daga ranar kowanne dare sai yazo ya tisata agaba yatafi da ita baya barinta tadawo sai gari yawaye,
Yau kam takasance weekend suna zaune adaki ita da surayya, sury tana karatun novel a wattpad ita kuma tana gyara farcenta tana sanye da hijab ajikinta duk da acikin dakine domin wata yar karamar rigace ajikinta pink colour da yar karamar skirt iya cinya, kwata kwata bata saba irin shigar nanba surayya ce tasata dole saida tasa gashi bahaushe yace zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai, knocking akayi sannan aka shigo yusleem ne yana sanye cikin kananan kaya,
"Zo Hafsat..." Yace da ita yana kallonta, kasancewar babban hijab ne ajikinta yasata tashi tabishi,
"taho min da ruwan zafi"
Acikin kitchen suka tsaya ta dauki ruwan zafin suka fita, part din su Abdul suka shiga, dukkansu suna falon suna kallo,
"Kai me kuke yi?" Yusleem ya tambayesu,
"Yaya kallo muke" inji khalifa,
"To ko ku koma daki ko kuma ku fice ku koma part din mami"
Yana kaiwa nan yawuce cikin daki Hafsat tana biye dashi tana ji kamar kasa ta tsage ta nutse dan tsananin kunya.......
_Fatan alkhairi ga aminiyar kwarai maryam qaumi (Mrs.......),the above page is urs dear...!_
*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_DEDICATED TO MISS XOXO_
*59*
***Hankalin surayya ne yayi masifar tashi saboda ganin yanda jini yake zuba daga goshin hafsat, gaba daya goshinta duk ya fashe idanuwanta akafe alamun ta suma,
Kafin surayya tayi wani yunkuri taji sallamar Khadija wacce ta manta phone dinta a dining area tasaka charge kafin tatafi, ganin yanayin da Hafsat ke ciki yasanya Khadija rudewa cikin hanzari suka tarairayeta suka fita da ita zuwa motar Khadija agaggauce surayya tafada part din Mami tana kwalla mata wani matsanancin kira,
Mami suna zazzaune afalonta nakasa itada su khalifa suna jiran zuwan yusleem yasauka suje su daukoshi suka fara jiyo kiran da surayya keyi wanda da alama ba lafiya ba,mamice tasoma mikewa wacce ke sanyi cikin wata lafiyayyar exclusive,
"Surayya lafiya?"
Kankame Mami tayi jikinta yana rawa,
"Mami anty Hafsat ce tafado daga upstair bakiga yanda taji ciwoba..."
"Tana ina?..." Mami ta tambaya cikin rawar baki,
"Gata can amotar anty Khadija zata kaita asibiti"
"Tsaya nazo muje"
Dukkansu suka tafi asibitin Dr sufyan wanda shine mafi kusa fiyeda sauran asibitocin,
Har lokacin jinin dake fita daga goshin Hafsat bai tsayaba duk yabata cikin motar Khadija da jikin mami wacce ke rungume da ita,
Emergency aka shigar da ita har lokacin bata farfado ba, kowa acikinsu shiru yayi yana tunani,
Babu wanda ya iya matsawa nan da can acikinsu har saida yusleem yakira khalifa yace ya karaso amma yanata kiran Hafsat da mami bai samesuba sukuma Abdul da Surayya,babu wanda ya dauka,
Alama mami tayiwa khalifa da yace gasu nan zasuzo su daukeshi yanzu, hakan kuwa khalifa yafada masa sukayi sallama,
"Khalifa jeka kadauko shi amma dan Allah karka sanar dashi abinda yake faruwa, idan kunje gidan kace masa muma unguwa muka tafi amma ba jimawa zamuyi ba saboda bana son hankalinsa yatashi"
"To shikenan mami..."
"Ka bashi abinci yadiba yaci"
Fita khalifa yayi yanufi airport domin dauko yusleem yabar su mami zaune a reception suna ta jajanta abinda yafaru da hafsat wanda har yanzu tana nan kamar yadda aka kawota bata farfado ba acewar likita sai sunyi mata allurar bacci tasamu bacci nawasu awanni,
Koda khalifa yaje daukar yusleem tuni har yusleem din yafito yana saurarensu, duk yabi yadamu saboda rashin samun Hafsat da mami awaya,
Koda wasa khalifa bai fadawa yusleem abinda yake faruwaba har suka karasa gida,
Part dinsu zaije khalifa yayi gaggawar dakatar dashi,
"Yaya kazo kafara cin abinci mana a part din mami kafin su dawo..."
Fasa zuwa nasu part din yayi yawuce na mami saboda dama girke girken da Hafsat tayi duk can aka kai,
Zama yayi ya debi abincin yaci yayi alwala yai salla saida ya idar sannan khalifa yace yatashi suje wurinsu mami domin ta kirashi awaya tace suje,
Tunda yaji abinda khalifa yafada yasan akwai abinda yake faruwa dan haka ya kalleshi,
"Khalifa waye baida lafiya? Mami ko Hafsat?"
"Yaya dukkansu lafiya suke kawai kazo muje dai kagani..."
Binsa yusleem yayi bai kara cewa komai ba amma aransa yanata tunanin to waye baida lafiya agidan? Da wannan tunanin suka karasa asibitin Dr sufyan,
Mami da Abdul da sury suka samu domin ita khadija tatafi gida tadawo amma da tare suke tun lokacin da aka kawo Hafsat din,
Tunda yaga kowa baiga Hafsat ba jikinsa yabashi Hafsat ce batada lafiya, wurin mami yaje fuskarta dauke da alamun damuwa da tashin hankali,gashi duk jikin gyalen mami jini ya babbatashi,
"Mami.... Me.... Yasameta..?"
Tashi mami tayi cikin sigar kwantar da hankali ta dafashi,
"Karka daga hankalinka yusleem bawani abu bane dan buge goshinta tayi shine likita yabata gado domin yadubata amma insha Allah ma nasan nanda jimawa idan tatashi zai sallamemu..."
Ajiyar zuciya mai nauyi yasauke domin sai yanzu yasamu yar nutsuwa da mami tayi masa wannan bayanin.
Cigaba da zaman jiran farfadowarta suka zauna sunayi amma shiru har la'asar tayi koda suka tuntubi likita sai sukace allurar da akayi mata ne yasata yin bacci mai nauyi,
Duk yusleem yashiga cikin damuwa, dakyar yaje masallaci yayi salla yafito, lokacin da yake tahowa ya hango khadija tana packing din motarta aharabar cikin asibitin, jin wayarshi tasoma kara yasashi dubawa sunan hafsat musa yagani nan yaja dan siririn tsaki ya maida wayar aljihu batare da ya dauka ba,
Karasowarshi tayi daidai da fitowar khadija daga cikin motarta nan suka gaisa tayi masa sannu da zuwa sannan ta jajanta masa akan abinda yafaru, tare suka shiga ciki wurinsu mami suka cigaba da zaman jiran tashin Hafsat amma ba ita tafarka ba sai bayan sallar magrib,
Gaba dayansu suka shiga cikin dakin kowa yana kokarin yimata sannu,da ido duk take kallonsu tana dafe da goshinta wanda yake nannade da bandeji, yusleem ne ya nufeta yana yimata sannu tareda kokarin kai hannu jikinta, cikin wata irin kara da karaji ta dakatar dashi fuskarta kunshe da tsanarshi gamida jin haushinshi karara,
Kowa dake cikin dakin saida mamaki ya lullubeshi, tashi zaune tayi tana binsu da kallon tsoro daya bayan daya kamar wacce taga doduna,
"Hafsat sannu, duk zafin ciwon ne hak..." Inji mami, sai dai amma tun kafin mamin takarasa Hafsat ta toshe kunnenta ta callara wata kara wacce ta karade asibitin,
"Bana son ganinku kufice daga dakin nan..."
Yusleem wanda zuciyarshi keta faman tafarfasa yana tambayar kansa meyake faruwa, juyawa yayi yafita yanufi office din likita wanda shine on duty yau wato Dr zayyad,
Tare suka koma cikin dakin da Hafsat take wato emergency inbanda kara da buge buge babu abinda takeyi, kowa yayi tsumu tsumu yana kallonta, cewa likitan yayi dukkansu sujira awaje, jugum mami tayi banda yusleem wanda yama kasa koda maganane sai jan da idanuwanshi sukayi kamar gauta,
Khadija ce ke dan kokarin basu baki amma baya ga ita babu wanda ke iya magana acikinsu.
Haka suka cigaba da tsaiwa cikeda alhini kowa zuciyarsa babu dadi duk sunyi jungum jungum, suna gani likita yazo yawuce babu wanda ya iya binsa domin duk acikin damuwa suke,
Karfe goma saura suka sake komawa wurinta lokacin ta tashi daga baccin da tayi na bayan magrib,
Cikeda kulawa mami takarasa gefenta tazauna, awani iri take kallon mamin kamar yau tafara ganinta,
"Sannu Hafsat tashi kici abinci kinji..."
Sake bin mami da kallo tayi kafin tamaida kallonta ga kofar shigowa inda surayya tashigo rikeda basket din abinci sai khalifa da Abdul wadanda ke biyeda ita yusleem kuma yana bayansu,
Runtse ido tayi tasaki wata razananniyar kara tana nuna yusleem da yatsa,
"Sannu Hafsat, meke damunki ne? Kiyi hakuri kinji"
Hawaye ne suka soma zuba daga idonta,
"Bana son ganinku, bana son ganinku musamman ma shi...."
Mamakine yakama mami ta riketa,
"Yi hakuri kici abinci..."
Ki tayi har saida yusleem yafita daga dakin sannan aka dan fara samo kanta.
Damuwa sosai yusleem yashiga saboda ganin abubuwan da Hafsat keyi idan har taganshi kamar wacce taga wani dodo haka take zama, tagumi yayi idanuwanshi jajur,
Bayan fitar yusleem mami ta debo abincin a filet da spoon ta mika mata,
"Yi hakuri ki karba kici kinji hafsat..."
Kallon mami tayi,
"Sunana Hafsat? Yaushe aka saka min wannan sunan?"
Idanuwan mami cikeda kwalla takai spoon din bakinta batareda tabata amsaba ba,
Cikin lallashi da lallami mami take bata abincin tana ci kamar wata karamar yarinya, kowa acikin dakin tsuru tsuru yayi yana jin yanda Hafsat ke tayiwa mami wasu tambayoyin shirme,
Dai dai lokacin da mami tagama bata abincin nurse tashigo ta bata magani tasha, watsar da maganin Hafsat tayi ta toshe kunnuwanta ta zuba wata kara nan mami tayi saurin riketa tasoma rarrashi, dakyar da sudin goshi ta karbi maganin tasha tana daddafe goshinta wanda ke nannade da bandeji,
Inbanda shirme babu abinda takeyi kamar wacce ta bugu, da haka aka samu barci ya dauketa, saida tayi bacci sannan su mami suka fita daga cikin dakin, jin cewar tayi bacci yasa yusleem shiga wurinta,
Tunda yadawo sai yanzune yasamu yazo kusa da ita datayi bacci, agefenta ya zauna yakai hannu ya kamo nata idanuwanshi fal kwallah.......
*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI....*💍
_(Labarin Hafsat)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
_DEDICATED TO MISS XOXO_
*60*
***Hannunshi yasa yadafa goshinta yana jin wani tausayinta yana ratsashi domin abin atausaya mata ne duba da irin kaddarorin da suke ta samun rayuwarta,binta da kallo yarinka yi saboda ganin yanda tasauya gaba daya, fatar jikinta sai sheki da kyalli take banda wani laushi da tayi, gashi kanta yasha kananan kitso masu mutukar kyau banda jan lallen da aka zana mata atafin kafarta da hannuwanta, ko ba afada masa ba yasan shi tayiwa wannan tanadin sai gashi kuma kaddara ta afku,
Yana nan zaune kusa da ita har su Mami suka shigo,
"Yusleem zo kutafi gida kaje ka kwanta ka huta inyaso gobe da safe sai kadawo..."
Girgiza kai yayi,
"Mami kuje kawai ni zan zauna inkwana awurinta"
"A'a yusleem kai da kadawo daga tafiya ai kana bukatar hutu, jeka ka huta ni zan kwana awurinta"
Tamkar zai fashe da kuka haka yamike yafita,