Showing 63001 words to 66000 words out of 70255 words

Chapter 22 - ALWASHI BOOK 1 COMPLETE by Ummi Aisha .txt

23 Dec 2024

3907

dukkaninsu tafiya sukayi Mami kadai aka bari awurinta ta kula da ita.


Koda yusleem yaje gida kasa bacci yayi inbanda juyi babu abinda yakeyi wai duk irin burin da yaciwa ranar nan tayau yatashi a iska, goshinsa yadafe saboda wani irin radadi da kansa ke faman yimasa, kwanan zaune yayi har asuba tayi idonsa biyu Wanda damuwa ce fal ranshi musamman ma idan yatuno yanayin da Hafsat ke shiga aduk lokacin da taganshi,


Sai bayan da yayi sallar asubah sannan yasamu bacci ya dan daukeshi, karfe 8 saura yatashi yashiga part din mami, dakin sury yashiga ya tadata domin ta taya kuku su hada abincin da zasu kai asibiti domin da wuri yake son suje,


Karfe 9 daidai yafito bayan yayi wanka yashirya cikin kananan kaya, idanuwan nan nashi sunyi ja gashi sun dan canja daga halittarsu domin rashin bacci,


Shida surayya ne suka tafi asibitin a motarshi, suna tafe ahanya yana yiwa sury tambayoyi dangane da yadda abun yafaru har Hafsat taji irin wannan ciwon,


Lokacin da suka shiga cikin asibitin tuni har Khadija ta rigasu zuwa takai shiryayyen breakfast dinta, acikin filet ta zubawa Mami sannan ta zubawa Hafsat taje wurinta tana bata, tana tsaka da bata dinne su yusleem suka shiga, daga dan baya baya yatsaya yana leken Hafsat saboda ganin yanda fuskarta da idanuwanta suka kumbura tamkar an bubbugeta awurin,


Tun kafin taganshi yayi saurin komawa yafice daga cikin dakin, yana tsaye yanata kaiwa da komowa Mami tafito ta sameshi, durkusawa yayi yagaida ta sannan yatashi fuskarsa fal damuwa,


"Mami kodai wani asibitin zan canja muku ko kuma infitar daku outside? Wallahi rashin lafiyar nan ta hafsat ta tsaya min arai saboda irin yanda naga bata koda son ganina ne, why?"


Dafashi Mami tayi ita dinma fuskarta cikeda damuwa banda yar kwallar da taciko mata idonta,


"Yusleem ni kaina abin ya daure min kai, saboda jiya bamuyi bacciba daga ni har ita inbanda buge buge babu abinda takeyi daga bacci ya dauketa zakaga ta zabura tafarka tamike tana buge buge, dakyar bacci yadauketa bayan wata nurse tazo tayi mata allura..."


"To wai Mami kunyi magana da Dr din?"


"Har yanzu likita baice damu komai ba tukunna..."


"Ai kuwa yakamata ya sanar damu domin musan abinyi, bari idan yashigo zan tuntubeshi inji"


Tsayuwa suka cigaba dayi awurin har su Abdul suka karaso daidai lokacin Dr zayyad yashiga emergency wurin da Hafsat take, saida ya kammala duba marassa lafiya sannan yafito, bin bayansa yusleem da Mami sukayi zuwa cikin office dinsa,


Zama dukkanninsu sukayi suna fuskantar juna,


"Am Dr dama muna sone muji menene takamaimai abinda yake damun patient dinmu? Saboda har yanzu mu mun kasa fahimtar condition din da take ciki tunda tana behaving kamar wata wacce ta tabu...."


"Agaskiya patient dinku tana cikin wani irin yanayi wanda har yanzu muma bamu gama tabbatar da abinda muke zargi ba, amma dai abinda nasani shine, buguwar da tayi akanta kamar yaso ya taba lafiyar kwakwalwarta da tunaninta, acikin kai akwai wani abu da muke kira a turance da...."


"Dr buguwar da tayi har nawa take da za ace brain dinta ya tabu?" Yusleem yafadi cikin fushi,


"Calm down abokina...." Dr zayyad yafada yana dafashi,


"Buguwar da baiwar Allahr nan tayi bafa kadan bace kamar yadda kuke tunani, tunda kunce daga steps din bene tafado tarinka buguwa, wannan buguwar itace ta gurbata mata tunaninta amma insha Allah zata samu lafiya tunda muna bata magungunan da suka dace da ita"


Ajiyar zuciya mai karfi yusleem ya ajiye ya sunkuyar da kai, sam yakasa magana sai Mami ce tayi magana suka karasa maganganun da likita daga nan takamo hannunshi suka fito, sury da Khadija dasu abdul suka samu zaune a reception, bai tsaya awurinsu ba ya nufi wurin Hafsat tana kwance idanuwanta arufe kanta babu dan kwali, da sauri yaje yadauki dan kwalin zai daura mata saboda ganin dakin harda maza aciki, bude idonta tayi ai tana ganin yusleem tafasa wata uwar kara tafara buge buge kamar wata zautacciya, Mami ce tashigo ganin abinda ke faruwa yasata tura yusleem waje tace yafita, dan kwalin ya mika mata,


"Mami ki rufe mata gashinta kinga akwai maza awurin"


Murmushi mami tayi takarba takoma ciki saboda tasan kishine yasashi fadin haka amma inbanda haka matar da bata da lafiya ina ruwan wani da ita kowa yana takansa,


Saida mami ta lallabata sannan tafita wurinsu yusleem, kallonsu tayi,


"Ya kamata mukira iyayen Hafsat mu sanar dasu koba hakaba? Bai kamata muyi musu shiruba bamu sanar dasu rashin lafiyar yarsu ba, ya kamata mu sanar musu tunda wuri susan halin da ake ciki..."


"Gaskiya kam afada musu susani...." Acewar khadija,


Waya mami ta dauka takira hajiya kubra tasanar mata amma ta boye mata lalurar hafsat din domin gudun shiga cikin tashin hankali,


Shiru sukayi dukkaninsu bayan mami ta kammala yin wayar.


Bayan kamar mintuna 30 sai ga hajiya kubra itada Alh sa'id, kowa fuskarsa awurin kunshe takeda damuwa da bacin rai, mamice tayi musu jagora zuwa wurin Hafsat din nan suka isketa tana bacci duk tafita hayyacinta,


Dawowa reception din sukayi suka zauna suka cigaba da jajanta abun,


Sai daf da sallar azahar sannan Khadija tayi musu sallama tatafi,sukuma suka cigaba da zama, shima yusleem yana wurin azaune Hafsat mori sai faman kiranshi awaya take tayi bai daga ba ita kuma son ganinshi take domin ji take kamar ta shekara bata ganshiba,


Ganin ta dameshi da kira yasashi tashi ya matsa gefe ya daga wayar akufule,


"Sweet yusleem me yak...."


Tun kafin takarasa ya katseta cikin fada,


"Wai menene kiketa kirana ne? Baki san abinda yake damunaba kinbi kin uzzura min da kiranki marar amfani..."


"Ayya yusleem kayi hakuri dan Allah, meke damunka?"


"Babu ruwanki da abinda ke damuna, kawai dai ki saurara min haka..."


Daga haka yakatse wayar ya maidata cikin aljihu yakoma wurinsu mami ya zauna.




Karfe 2:30 narana khalifa da sury sukaje gida domin dauko abinci saboda kuku yayiwa Mami waya yace yagama, kafin su dawo har Khadija tazo asibitin da wani babban basket shake da abinci, nan Mami tashiga yimata godiya saboda irin dawainiyar da taketa yi akansu,


"Mami ai babu komai, Hafsat tawuce haka agareni, tazama tamkar yar uwata ba kawata ba, fatanmu dai Allah yabata lafiya..."


"Amin,amin, Allah yakara zumunci" inji hajiya Kubra,


Sai da la'asar tayi sannan mami tatafi gida ita da yusleem, wanka mami tayi sannan ta debowa Hafsat wasu kayan, bayan sallar magrib suka koma asibitin shima yusleem din yasake wanka yasaka kananan kaya blue din jeans da farar t shirt ta polo,


Suna zuwa wurin su hajiya Kubra suka sanar musu da cewar ansauyawa Hafsat daki an kaita wani daki nata ita kadai, mami da yusleem ne suka nufi dakin wanda yake dauke da gado guda daya aciki,


"Asauya mata kayan ko?" Inji mami,


"To mami"
Mika masa tayi tafita, ahankali yazauna agefenta yafara kokarin cire mata rigarta ahankali, duk da yana cikin damuwa saida yayi ta maza sannan ya iya jurewa yasaka mata rigar, skirt din jikinta yacire yasa mata wani, yana cikin gyara mata dan kwaline mami tashigo, wani kamshine ya bayyana tareda mamaye cikin dakin,


"Yusleem kunyi bakuwa, Hafsat ce tazo duba Hafsat"


Dagowa yayi nan idanuwansu suka sarke da na juna, Hafsat mori yagani sanye cikin bakar abaya,dan hade rai yayi sannan yayi magana,


"Ok sannunta da zuwa"


Har wurin Hafsat din suka karasa, sai yau ma ita Hafsat taga matar tashi, kallonta ta danyi na wasu yan mintuna daga nan tayi musu fatan Allah yabata lafiya ta juya tafita, kasancewar da driver tazo sai ga drivern yashigo hannunsa niki niki da kayayyakin dubiya, kowa dake zaune awurin bin kayan yake da kallon mamaki.....






_Fatan alkhairi ga dumbin masoyana masu karanta wannan labari musamman ma yan kungiyar haske writers, haskakkun marubuta masu haskawa aduniyar rubutu....._








*_Ummi Shatu_*👌🏻


© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_






*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*








_DEDICATED TO MISS XOXO_






*61*






****Wani takaici yusleem yakeji kamar zaiyi me dan bacin rai, tashi yayi yabi bayan Hafsat tana tsaye jikin motarta tana yin waya tabashi baya,


"Gaskiya aiki yayi kyau, nagode madalla, ladan aiki kuma sai na zo...."


Daidai lokacin yusleem yazo wurinta, afusace yake kallonta,


"Me yakawoki nan? Waye yasanar dake inda muke da har kika samu kikazo? Nifa Hafsat kifita daga hanyata domin banida bukatarki acikin rayuwata, kin takura min, wai ni kadai ne namiji da zaki bi ki damu?"


Tunda yafara wadannan jawaban batayi maganaba illa binsa kawai da takeyi da kallo tana dan murmushi, sai da yagama sannan tayi magana,


"Allah yahuci zuciyarka, ai ban san zuwana zai haifar da matsala ba da bazan zoba amma kayi hakuri insha Allah hakan bazai sake faruwa ba sannan daga yau dinnan ni Hafsat ina mai farin cikin sanar dakai cewar kamar yadda kace bakai kadai ne namijiba to zanje injira har insamu rabona....",


Tana kammala fadin haka tabude bayan motarta tazauna taja tarufe kofar da wani mugun karfi alamun yin fushi, nan driver yaja suka wuce daga harabar cikin asibitin,


Komawa ciki yusleem yayi zuciyarsa dankare da bacin rai domin ji yake komai na duniyar yagama isarshi,


Haka suka cigaba da jinyar Hafsat amma kuma kullum abun babu sauki har suka shafe satittika a asibitin, Khadija kuwa tareda ita ake jinyar Hafsat domin kullum tana asibitin, ganin sauki bai samuba yasa aka sallamesu daga asibitin domin su koma gida, damuwa sosai yusleem yashiga saboda har yau baya iya zuwa koda kusa da Hafsat ne mutukar idonta biyu sai dai idan bacci take shine zai samu ya rabeta,


Gidansu aka kaita domin hajiya Kubra tace gara itama mami tahuta saboda dawainiyar asibiti da tasha, duk da yusleem bai soba haka ya hakura domin yana ganin kamar za anisanta shi ne da farin cikinsa,


Batun Hafsat mori kuwa tun daga ranar yusleem bai kara ganin kiranta ba bare sakonta kamar yadda tace.


Ranar da aka tafi da hafsat gida yusleem yakasa zaune yakasa tsaye, kiranshi mami tayi tace yadebi kayan Hafsat nasawa yakai gidansu inji hajiya Kubra,


Kala biyar kacal ya diba saboda baya son tadade bata dawo ba,


Zuciyarsa babu dadi ranshi abace yanufi gidan su Hafsat din, lokacin da yaje an idar da sallar magrib dan haka saida yatsaya a masallaci yayi salla sannan yashiga cikin gidan lokacin da yashiga hajiya kubra na falo azaune hannunta rike da carbi Hafsat tadora kanta akan cinyarta tana tofa mata addu'a idanuwan hafsat din alumshe,


Jin sallamarsa yasa Hafsat kokarin tashi daga cinyar Ummi, saurin dakatar da ita Ummi tayi taci gaba da tofa mata addu'a, ahankali yusleem yashiga cikin falon yazauna, runtse idanuwanta hafsat tayi saboda bata son koda ganin yusleem ne, juye juye tafara yi da kanta tana ciccije lebe, ganin haka yasa Ummi tasar da ita tsaye takamata suka shiga bedroom dinta, kwanciya tayi akan gado sannan ummin tafita falo wurin yusleem,


Sauka kasa yayi yagaida ta fuskarsa dauke da damuwa,


Itama hajiya kubran cikin damuwar ta kalleshi,


"Yusleem kadai sake kara hakuri kaji, hakika Hafsa tana cikin mawuyacin hali, ni nakasa gane kan wannan ciwon nata kamar yadda asibiti suka kasa fahimtar komai, shiyasa ma ni nake wani tunani domin kamar abin akwai alamar tambaya aciki duba ga irin yanayin lalurar tata, kodai akwai wata ko wani wanda wani abu yahadasu ko kuma kai yahadaku shine akabi ta wata hanya aka cutar da ita Hafsat din..."


Shiru yusleem yayi zuwa wani lokaci kafin yadago ya kalli Ummi,


"Hakane Ummi insha Allah zan bincika domin akwai wanda nake zargi.."


"To Allah yasa adace, Allah yabata lafiya"


"Amin" yusleem ya amsa, nan yaci gaba da zama har isha tayi,


Sama sama ya danci tuwon da ummi takawo masa daga nan yatashi yashiga wurin Hafsat,


Akwance ya sameta tana bacci tunda lalurar nan tasameta koda yaushe acikin bacci take, zama yayi akusa da ita ya dafata yakamo hannunta,


"Hafsat bazan iya nisantarki ba kamar yadda kike so, bazan iya zama batare dake ba, kiyi min wannan alfarmar kibarni na rab'u dake ko zanji sanyi, ko zan samu sassauci araina...."


Kwallar dake kokarin sauka a kumatunsa yagoge, cigaba da mammatsa mata hannunta yayi sannan yatashi yafita bayan yayi kissing din goshinta.


Tunda ummi tayi masa wannan maganar suka shiga neman magani babuji babu gani amma kuma har lokaci mai tsawo ba adaceba domin duk mai maganin da aka kai masa Hafsa sai yace bai gane abinda ke damunta ba, gashi yusleem yana son yafitar da ita kasar waje amma su ummi sun hana sunce ciwon kamar ba na asibiti bane,


Abubuwa duk sun taru sunyi masa yawa nan aka hakura aka zubawa sarautar Allah ido amma ana neman maganin duk inda akaji labari.


Yau kimanin watanni uku kenan da fara rashin lafiyar Hafsat, cikin satin yusleem yayi tafiya ta kwana biyu koda yatafi duk hankalinsa atashe yake domin yafi son kullum yarinka ganin Nana hafsanshi,


Kwananshi biyar yadawo, aranar da yadawo Alh Musa mori yayi masa waya yace yana son ganinshi, bai jeba saida yafara biyawa ta gidan su Hafsat domin idanuwanshi suna masifar son ganinta saboda kwana biyun nan da bai ganta ba ji yake kamar anzare masa lakka, shi sai yanzu ne da bata da lafiya yagane cewar yana mutukar kaunarta,


Tunda yashiga gidan yajishi gaba daya ya canja sai wani kamshi yake,


Cikin falon ya tasamma nan ya tarar da Ummi zaune sai Hafsat akusa da ita tasha english wears pink colour, riga da skirt, ta kama kanta da wata hula baka mai santsi, murmushi yai mata ga mamakinsa sai yaga itama ta maida masa da martani, nan ta mike tafita, suna cikin gaisawa da Ummi sai gata tashigo rikeda babban tire takawo masa juice da bottle water,


"Sannu...." Yace ahankali can kasan makoshinsa,


"Yawwa..." Ta amsa tareda yimasa murmushi, hamdala yafara yi acikin ranshi domin wannan kadai ya tabbatar masa da cewar hafsanshi tasamu lafiya,


Maganar Ummi ce takatse masa tunaninsa,


"Yusleem dama alh nason ganinka, tunda kazo bari inyi masa magana..."


Wayarta ta dauka takira alh sa'eed cewar yusleem yazo, shikuwa yusleem sai kallon Hafsat yake yanata faman aika mata da sakonni kala kala ta idanuwanshi, ita dai sai dai tayi murmushi ta sunkuyar da kanta.


Mintuna kadan alh sa'eed yashigo cikin falon yasamu wuri ya zauna, sauka kasa yusleem yayi ya gaidashi, bayan sun gaisa alh sa'eed yayi gyaran murya yace,


"Alhamdulillah ala kulli halin, yusleem damu dakai mun san komai daga Allah yake,sannan duk abinda yafaru da bawa mukaddari ne daga Allah, nasan kayi namijin kokari wurin ganin matarka Hafsat tasamu lafiya amma abin yaci tura, to duba da irin yananin da take ciki shine muka taru muka yanke wata shawara,


Muna son kasaki Hafsat inyaso ka auri yar uwarta *AMAL* domin basu da banbanci ko awurin halitta..."


Cikin sauri yusleem yadago yakalli abban su Hafsat,


"Abba, wanne irin saki kuma? Wacece amal?" Bakinsa yana rawa yayi wannan maganganun,


Nuna masa amal abba yayi da yatsa,


"Gata nan kusa da hajiya Kubra"


Arazane yusleem yakalli wacce ada yake tsammanin hafsanshi ce, tabbas ko shakka bayayi wannan Hafsa ce tawarke duk da yaga takara fari sosai, to kodai wasa abba yake masa?


"Abba dan Allah karka cemin wannan ba Nana Hafsat bace..."


"Yusleem wannan amal ce yar uwar Hafsat, tare muka haifesu, yan biyune, Hafsa tana cikin daki..."


Dasauri yatashi yanufi dakin dan bai yarda ba, yana shiga yahangeta kwance tana bacci kamar yadda tasaba, da sassarfa yakara kusa da ita ya tsugunna yakamo hannunta kawai sai yafashe da kuka tamkar wani karamin yaro, dakyar yayi ta maza ya tsaida kukan yatashi yafita yana kallon amal wacce ko kadan batada maraba da hafsanshi,


"To yusleem yanzu dai kaje gida kuyi shawara da mahaifiyarka domin yabawa mukayi da nutsuwarka da kuma kokarinka shiyasa muka musanya maka da amal amadadin Hafsat...."


"To abba bari naje..."


Shine kawai abinda ya iya fadi yatashi yafita, kansa yawani yimasa nauyi da haka yaja mota yanufi gidan alh Musa mori domin sai waya yaketa yimasa,


Acikin falonsa ya tarar dashi zaune shida matarsa, da fara'a suka karbeshi bayan sun gaisa alh Musa yadubeshi da fara'a yace,


"Yusleem, nasan kasan irin matsayin da nabaka na dan da kamar nine na haifeshi, sannan na doraka akan dukiyata fiyeda yadda na dora yayana na cikina, to kayi hakuri zan sake dora maka wani nauyin akaro na biyu, domin zan aurar da yata Hafsat agareka mutukar ka amince...."


Yusleem ji yayi hankalinsa yatashi, gaba daya jikinsa babu kwari domin indai da halacci to da kunya yadubi idon alh Musa yace baya son yarsa ta cikinsa,


"Yusleem yanaji kayi shiru...?" Inji alh Musa,


Sake sunkuyar da kai yusleem yayi, ya ce,


"To alh nagode, Allah yasaka da alkhairi, yanzun ne sauri nake domin agida ana jirana, bari naje"


Sallama sukayi yafito zuciyarsa nawani irin tafarfasa cikin sa'a sai ga Hafsat ta danno motarta cikin gidan tana makale da waya, hade rai yayi yaje har gaban motarta yabude kofa ya kalleta cikeda tsana,


"Dama saboda kina son in aureki shiyasa kika yiwa matata asiri? To wlhi kiyi gaggawar zuwa ki karya asirin nan domin bazan taba aurenki ba, ni bakiyi minba bana sonki, mace daya nake so itace matata...."


Tafiya yayi yabarta baki bude mamaki bayyane akan fuskarta,


Aguje yake tafiya har yakarasa gidansu, part din mami yashiga, tana cikin bedroom dinta tana hutawa dan haka yabita ciki, agefen gadonta yazauna,


"Yawwa yusleem gara da Allah yakawoka, yanzun nan hajiya fa'iza tatafi mun gama yanke magana da ita zaka mayarda Khadija dakinta kafin Allah yabawa hafsat lafiya..."


Shiru yayi ya tallafe kansa da hannayensa wanda yake juya masa ga wata hajijiya dake daukarsa.......






*_Ummi Shatu_*👌🏻


© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_






*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_






*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*






_DEDICATED TO MISS XOXO_






_Fatan alkhairi gareki kanwata takaina ASMY B ALIYU, alkhairin Allah yakai miki aduk inda kike._






*62*






*Gaisuwa ga dunbin masoyana masu karanta littafin alwashi musamman ma masoyan yusleem & Hafsat, hakika banida kalmar da zanyi amfani da ita wurin mika muku sakon gaisuwata gashi kuma yawanku yasa bazan iya lissafo sunayenku ba amma akoda yaushe kuna nan acikin zuciyata...*






***Tsawon mintuna biyar yusleem yana rikeda kansa yakasa tabuka komai domin ji yake tamkar kansa zai rarrabe gida dari dan tsananin ciwo,


Wasu zafafan hawayene suka fara zubowa daga idonsa,


"Yusleem yanaji kayi shiru...." Mami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login