Showing 18001 words to 21000 words out of 70255 words
bai gantaba tana jin tsoron kar yaganta ya rainata yace batayi masa ba domin tasan dama auren hadin mami ne,amma shikam bata tunanin akwai wata ya macen da zata ce baiyi mataba,
Yusleem kuwa tunda ya Lula yatafi bai dawoba gyaran gidanshi ma wanda za ayi sai yaronshi na office yasa yatsaya akai akayi aka gama aka gyara gidan tsafa aka sake fenti,
Saida biki yarage saura kwana takwas sannan yadawo lokacin hatta kannenshi su Abdul da surayya har sun zazzo daga makaranta, mami taso tayi masa fada amma kuma dayake acikin farin ciki take sai ta shareshi taci gaba da harkokinta,
Surayya kam kanwar yusleem tattarawa tayi takoma gidansu Hafsat saboda acewarta ita abangaren amarya take ba bangaren ango ba, Hafsat ba karamin dadi tajiba domin dama ita kadaici kwal agidan take harkokinta domin Alhaji sa'id bai bar amal tazo ba duk da tayi niyyar zuwa amma yahana,
Surayya ce taraka Hafsat akayi mata komai kama tun daga kunshi gyaran jiki da gyaran kai wanda duk mami ce tadauki nauyin yin hakan,
Ana igobe daurin aure yusleem yaje gidansu Hafsat din wanda wannan dinma mamice ta tilastashi, kamar zaiyi kuka yashirya yatafi bayan sallar isha,
Surayya yayiwa waya tana dauka taji yace,
"Ke turo min wannan yarinyar"
Sarai surayya tagane abinda yake nufi amma sai tayi fuska tace,
"Uhm yaya wafa?"
"Oho miki" yafadi tareda katse wayar,
Kallon Hafsat tayi tana murmushi,
"Angonki ne yazo yana waje yana jiranki"
Saida gaban hafsa yafadi saboda jin abinda surayya tace,hijabi tadauka ta kalli surayya,
"Zo ki rakani dan Allah"
"Zan dai kaiki amma ina zuwa dawowa zanyi"
"Nayarda"
Fita sukayi gaba dayansu, afalo suka iske su ummi ita da jama'arta wadanda sukazo suna yan aikace aikace,
Kanshi yana durkushe akasa yana latsa wayarsa dan haka ko fitowarsu bai ganiba bare yaga zuwansu, surayya ce ta kwankwasa masa glass din dake saitinshi hakan yasashi yin kasa da glass din yana kallonta, gaban Hafsat ne yashiga dukan tara tara haka kawai domin gani tayi yusleem yafi kyau afili kuma tabbas shine mutumin da yake taimaka musu lokacin da tana gidan marayu domin yataba zuwar musu sau daya sun ganshi,
"Ina wuni.." Hafsat tace dashi tana kallon kasa,
Ko kallonta baiyiba ya amsa da "lafiya"
Daga haka babu wanda yakara magana acikinsu ganin haka yasa surayya tajuya zata tafi dominated tabasu wuri nan yadakatar da ita yadauko rafar yan dubu dubu guda daya ya mika mata yaja motarshi yayi gaba,
Hafsat ji tayi ko ajikinta balle abin ya dameta,
Washe gari aka daura auren Hafsat da yusleem da misalin karfe 2 narana akan sadaki naira dubu hamsin.
*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to MISS XOXO_
*22*
***Aranar da aka daura auren aranar alhaji sa'id yace aje akai Hafsat gidanta duk da hajiya kubra bata so hakaba domin ita taso ace sai washe gari za akaita amma tunda ga abinda alhaji sa'id yace dole babu yadda ta iya dan haka aka fara shirin kai amarya dakinta,
K'arfe 9 daidai aka fito da Hafsat din daga sashen alhaji sa'id bayan ya kammala yimata nasihar da ta dace duk wani uba yayiwa'yarsa a lokacin da za akaita gidan miji, haka itama hajiya kubra ba abarta abaya ba wurin yiwa Hafsat fada akan tabi mijinta kuma ta kyautata masa,
Inbanda kuka babu abinda Hafsat keyi domin tasan su hajiya kubra sunyi mutukar kokari akanta kuma sun taka muhimmiyar rawa acikin rayuwarta wanda har abada bazata manceba kuma bata da abinda zata iya biyansu da shi,
Wata tsadaddiyar mota ta alfarma kirar Lexus new series 2017 aka bude mata tashiga, nan kannen hajiya kubra suka sakata atsakiya yayinda surayya kanwar yusleem tashiga gaban motar,
Direct gidan mami aka wuce da ita inda mamin nacan ita da jama'arta suna zaman jiran zuwansu,
Yanayin farin cikin da mami ke ciki abin bazai misaltu ba domin kana ganinta zaka gane irin dunbin farin cikin da take ciki,
Har tsakiyar bedroom dinta aka shigar da Hafsat wacce ke tukunkune cikin wani babban mayafi dark blue kalar leshin dake jikinta,
Rungumeta mami tayi tana fara'a,
"Barka da zuwa cikin zuri'ata 'yata,ubangiji Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina da duk wani sharri daga gareku, Allah yabaku zuri'a dayyibah, nidama tun can a matsayin 'ya na daukeki kuma yanzun ma kina nan ahaka baki sauya ba, insha Allah zamu rikeki amana"
Jin abinda mami tafada yasa kawayenta dake baibaye da ita sakin guda,basufi minti talatin agidan mami ba aka wuce da Hafsat gidanta wanda ke can wata unguwa da ake kira da babbar inuwa domin gaba daya mazauna unguwar shaharrun mutane ne wadanda sukeda hannu da shuni,
Shi kanshi yusleem fadin girman gidansa da tsarinsa abune mai wahala domin gidan yatsaru iya tsaruwa,
Cikin babban bedroom dinta aka shigar da ita ta zauna akan gefen makeken gadonta samfurin Italy,
Saida yan Kawo amarya suka fita sannan Amina kawarta da surayya suka shiga cikin dakin,
"Amarya kinsha kamshi, nidai bari inje intafi.." Inji Amina,
Dago jajayen idanuwanta Hafsat tayi ta kalleta,
"Haba Amina bazaki bari angwayen suzo ba?"
Dariya surayya tayi tareda bararrajewa akan gadon,
"Waye zai Kawo miki angwaye? Indai yaya yusleem ne Allah shi kadai zai zo gidan nan garama kibarmu muje mu tafi, nidai dama kin san gobe da sassafe zanyi miki asubanci..."
Jin abinda surayya tace yasa Amina tashi tsaye,
"To shikenan bari intafi, Hafsat sai nadawo ganin gida lokacin kin dawo cikin nutauwarki domin nasan yanzu bakya tareda ita..."
"To Amina nagode, Allah yabar zumunci, nagode"
Tashi surayya tayi tabi bayan Amina suka fita tare,
Tsuru Hafsat tayi tana bin dakin da kallo wanda yasha furniture's na alfarma kalarsu dark purple, duk tsoro yabi ya cikata saboda babu motsin komai agidan, ta wuri daya hankalinta ya kwanta shine tasan akwai masu gadi acikin gidan wanda yanzu haka suna can gate suna aikinsu,nan tazauna taci gaba da zuba idon ta Inda zataga shigowar angonta.
K'arfe 10:30 yusleem yashiga gidan mami kasancewar yan biki suna nan basu tattafi ba yasa gidan inbanda hayaniya babu abinda kakeji kamar dare baiyi ba,
Fitowa mami tayi wurinshi ta tsaya tana kallonsa, gaba daya ta fahimci bashida wata walwala,
"Yusleem..." Ta kira sunanshi tana kallonsa,
"Na'am.."
"Kasan abinda nakeso dakai? Na hadaka da girman Allah yusleem ka rike Hafsat amana, dan Allah karka cutar da ita, sannan ka taimaka ka rufa min asiri karka sakar musu 'ya, yusleem idan ka aikata daya daga cikin wadannan wallahi bazan yafe makaba sannan ka nemi wata uwar amma baniba, Allah yayi maka albarka ya baka zuri'a tagari"
Hannayenshi duka suna cikin wandon farar shaddar dake jikinsa yana tsaye yana jin mami har ta kammala,
Gyada kai yayi batare da yace komai ba ya sunkuyar da kai,
"To kaje katafi mana"
"Ehh yanzu zan tafi, inasu Abdul suke? Ko shi ko khalifa wani yazo muje yayi dropping dina saboda dama shu'aibu yaron office dinane yakawo ni kuma yawuce"
"To bari nakira maka daya daga cikinsu, ina zuwa"
Juyawa mami tayi ta nufi sashen samarin,da khalifa tafara yin arba dan haka shi takirawo ta nuna masa yusleem a inda yake tsaye ya cire hularshi yana lanlankwasa ta,
Batare data koma wurinshi ba tawuce zuwa ciki shikuma khalifa ya nufi wurinsa daga nan wurin da aka tanada domin adana motoci sukaje khalifa yadauko guda daya yusleem yabude yashiga suka fita daga cikin gidan,
"Yaya ka siyi yan abubuwanne?"
Kallon khalifa yusleem yayi,
"Mefa?"
"Wai da yaya ina nufin dan nama haka da sauransu.."
"Kaima yanzu bakada kunya kamar Abdul ko?" Yafada yana kallon titi,
"A'a yaya bahaka bane,nayi tunanin ko kamanta ne shine natuna maka"
Bai sake cemasa uffan ba har sukaje gidan nan yabude kofa yafita ya nufi ciki yana takawa ahankali.....
*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to MISS XOXO_
*23*
***Ahankali yaci gaba da takawa yana tafiya tamkar wani marar lafiya ko kuma wanda yake jin tausayin kasar,
Hularshi yatura baya zuwa keyarshi ya zuba hannuwanshi acikin aljihun wandonshi domin wani dan dari dari yakeji,
Babban falon dake girke atsakiyar part din guda biyu yabude yashiga, hanyar da zata sadashi da bedrooms din Hafsat yabi har ya isa ga dakin da take ciki,tana kishingide ta dan fara gyangyadi amma ba bacci takeyi ba,
Ahankali yatura kofar dakin yashiga, daga bakin kofa ya tsaya bayan yasake zuba hannuwanshi acikin aljihun wandonshi,
Dan gyaran murya yayi kadan wanda hakan yayi sanadiyyar bude idon Hafsa ta tashi zaune da hanzari,
"Zo...." Shine kawai abinda yace da ita cikin sanyayyiyar muryarshi yajuya yafara tafiya, tashi tayi tasauka daga kan gadon tabi bayanshi,
Saboda irin yadda yake daga kafa dakyar yana tafiya ahankali yasa harta cimmashi awani dan madaidaicin corridor, cikin falonta suka shiga,
Kan dining ya nuna mata,
"Ga abinci can idan kina jin yunwa.."
Daga haka bai sake cewa komai ba yajuya yafita ya nufi part dinshi,
Cikeda mamaki Hafsat take binshi da kallo, lallai wannan yusleem din ba kanwar lasa bane yanzu dama akan kawai zai nuna mata abinci ne yasa yatasota?
Kan dining table din takarasa, bakaken ledodi ne cikeda fruits daya ledar kuma kaji ne gasassu guda uku sai juice da fresh milk,
Dan yunwa kam tabbas tana jinta domin rabonta da cin abinci tun lokacin da aka fara hidimar bikin nan bata iya zama taci abinci ta koshi ba,
Zama tayi ta bude ledar tafara yagar kazar tana ci saida taji ta koshi sannan ta mayar ta rufe ta tashi,
Bedroom dinta takoma tashiga bathroom ta wanke hannunta da bakinta tadawo ta kwanta, Sam bata kara jin duriyar yusleem ba har asuba tayi gari ya waye,
Wanka tayi ta shirya tayi kwalliya tasaka wani jan Swiss material,
Fita tayi zuwa falo tana bin ko ina da kallo domin dukiyar da aka zuba afalon da shi kansa tsarin falon ba kadan bane,
Haka taci gaba da zama shiru har surayya tazo, shigowa tayi tana dauketa kulolin abinci,
"Amarya bakya laifi.." Surayya tafada cikeda tsokana,
"Ni dan Allah zubo min abincin nan inci yunwa nakeji"
"Ai dole kiji yunwa amaryar mu, yanzu kuwa zan Kawo miki.."
Kitchen ta shiga ta dauko filet tazubo mata wainar shinkafa da miyar agushi wacce taji kaji domin inbanda kamshi babu abinda takeyi,
"Ga abinci, ina yayan? Ko bai tashiba?"
Shiru Hafsat tayi saboda ita bata sanma me zatace ba domin rabonta da ganinshi tun jiya da daddare,
"Duk yunwar ce ne ta hanaki magana?"
Murmushi Hafsat tayi ta gutsuri wainar tafara aikawa cikinta, kan dining table surayya takoma taje ta kinkimo ledar kajin da yusleem yakawowa Hafsat jiya,
"Ai wannan baku ci bama, kun tsaya jin kunyar juna ko? To ni bari inci"
Hafsat najinta bata tankaba domin ita yusleem yayi bala'in daure mata kai saboda ko atarihi bata taba jin angon da yayiwa amaryarshi hakaba, ace kazar ma bata da darajar da zai dauka yakai mata har sai ya kirata tazo ta dauka da kanta,
Abincinta taci ta koshi ita kuma surayya tana faman yagar kazar da ta rage jiya, bayan sun gama ne surayya tajata,
"Zo muje kiga sauran bedrooms din"
Fita sukayi daga falonta suka shiga corridor din da zai sadaka da dakunan baccinta wadanda suke guda biyu ajere sai can gaba dasu daga karshe wata kofa ce itama daban, bayan sun gama dudduba dakunan ne suka shiga wannan kofar, wani lafiyayyen falo Hafsat tagani mai mutukar kyau wanda yasha kaya masu tsada sannan akwai wata babbar kofa wacce tafita tawaje har zuwa kan wata katuwar balcony,
Coffee & milk colour ne gaba dayanshi sai wani kamshi yake na musamman,
Zama surayya tayi acikin daya daga cikin kujerun falon,
"Wash kafata, kinga bedroom din can leka kigani saboda wallahi nikam nagaji.."
Batare da tunanin komai ba Hafsat ta nufi bedroom din ta murda kofar ta shiga, dakine babba wanda girmansa zaiyi girman falo, wani babban royal bed ne agirke aciki sai kamfacecen mudubi da sauran kayayyaki, kamar ance ta kalli gefenta tana kallon wurin taga wata babbar kujera mai kamada dan karamin gado, yusleem ne kwance akai ya rungume pillow akirjinsa idanuwansa arufe abisa dukkan alamu bacci yake yi,
Tafi minti biyu tana kallonshi kafin tajuya zata fita harta bude kofar taji maganarshi cikin muryarshi mai mutukar sanyi da zaki,
"Zo nan..."
Cikin tsoro ta waiwaya ta kalleshi, bude idanuwanshi yayi yana kallon sama bai kalleta ba,
Mayar da kofar tayi ta rufe takarasa inda yake,
"Gani.."
"Menene ya kawoki?"
"Babu komai.."
Shiru taji yayi baiyi magana ba sannan har lokacin bai daga ido ya kalleta ba maimakon hakama sai yajuyar da kanshi da yayi yana kallon wani wuri,
"Ina kwana..?" Tace dashi saboda tunawar da tayi bata gaidashi ba,
"Lafiya.." Taji ya amsa,
Tana nan tsaye shiru bai sake yimata magana ba dan haka tajuya tafita,
Gani tayi surayya bata inda tatafi tabarta, wucewa tayi takoma part dinta acan ta iske surayya ta kunna makekiyar tv din dake manne abangon falon ta kamo tashar zee world,
Ganinta yasa surayya fara yin dariya kasa kasa,
"Amarya da alama dai jiya yaya bai gayyaceki dakin nashi ba shiyasa har nakaiki baki san can bane"
Zama Hafsat tayi tana yamutsa fuska,
"Dama kin san dakinsa ne shine kika ce inshiga ko?"
Dariya surayya tayi,
"To ba gashi kinyi gaisuwar safe ba.."
Kyaleta Hafsat tayi batace komai ba amma yanzu ta fahimci miskilin mutum Allah ya hadata zama dashi,
Haka suka cigaba da zama itada surayya har yan uwan hajiya kubra suka zo suka tafi suna tafiya yan uwan mami da kawayenta suma suka zo, duk wanda yazo gidan sai yasa albarka kuma sai yaji yayi sha'awarsa domin yayi sosai, amma wasu daga cikin kawayen mami da sukazo suka ga gida sannan suka ga Hafsat saida tausayinta yakamasu domin sun san itama kwana nawane yusleem zai tarkatata yakorata da saki dai dai dai dai har uku.
Har dare surayya tana gidan sai bayan sallar isha dasu khalifa suka zo tace zata bisu tatafi,
Hafsat kallon samarin tayi wato Abdul da khalifa duk da bata taba ganinsuba amma tasan dai kannen yusleem ne domin ga kama nan sai dai duk cikinsu shine fari domin har surayya batafi Hafsat din fariba shikuwa yusleem farine sol,
"Kinga kannen yaya, yakika gansu? Sunfishi kyau ko?"
Murmushi Hafsat tayi, "ke kika sani"
Gaisawa sukayi daga nan sukai mata sallama suka tafi,
Tunda suka tafi kuma tazauna shiru ita kadai daga karshema taji tsoro yafara shigarta dan haka ta tattara takoma bedroom dinta tayi shirin bacci ta kwanta.
Tun daga wannan ranar bata sake saka yusleem acikin idonta ba,kullum tareda surayya suke wuni har dare, da haka har tayi sati daya agidan,
Rabonta da ganin yusleem kuwa tun ranar da surayya tazo last wanda yashigo falon yace mata gobe kukun da yasamo mata zai fara zuwa tace a'a zata rinka girkinta da kanta, juyawa yayi gurin surayya tatashi ya maida ta gida, tun daga ranar Hafsa bata kara ganinshi ba gashi yanzu surayya bata nan sati biyu kenan da tafiyarta Kaduna gidan kanwar mami,
Haka take wuni ita kadai babu abokin hira, bata san fitar yusleem ba bare tasan dawowarsa.
Ranar alhamis da safe misalin karfe 11 saiga mami tazo gidan,
Da murna Hafsat ta karbeta, bayan sun gaisa mamin ke tambayarta yusleem din tashi tayi tafita tace bari ta kirashi,
Faduwa gabanta yafara yi lokacin data doshi dakin nasa, ahankali ta tura ta shiga, tayi sa'a kuwa yana nan,
Yana kan gado akwance yana bacci,
"Yaya... Yaya.." Tafara kiranshi, bude idonshi yayi, kallo daya yayi mata ya maida idanuwanshi ya rufe,cikin sanyayyiyar muryarshi mai dadi yace,
"Menene?,idan ina bacci ba a tashina"
"Mami ce tazo shine tace inkira ka,amma kayi hakuri"
Ganin bashida niyyar amsa mata yasata juyawa zata fita, har takai bakin kofa taji muryarsa,
"Zo.." Komawa tayi wurinshi,
"Bude drewar dinnan ki miko min t shirt dina"
Budewa drewar din tayi ta dauko masa t shirt guda daya ja ta mika masa,
"Ajiye anan"
Ajiyewa tayi ta juya zata fita,
"Kinga..."
Dawowa tasake yi,
"Kin iya dafa tea?"
"Ehh na iya"
"Ki dafa min, kicewa mami ina zuwa"
Da "to" ta amsa tajuya tafita tana mamakinshi acikin ranta domin sam bashida alkibla tarasa gane inda yasaka gaba......
*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to MISS XOXO_
*24*
***Wurin mami Hafsat takoma tafada mata cewa yusleem din yace yana zuwa daga nan ta tashi ta shiga kitchen domin dafa masa tea din,
Dama indai fannin girki ne to bata da matsala domin zaman da tayi agida bawai zama tayi ta zuba ido sai dai adafa abata taci ba, tare suke yin komai da hajiya kubra, wata rana ma ita kadai ce keyin girkin,
Dankali ta fere ta soya masa bayan tagama dafa tea din sannan ta dan jajjaga kayan miya kadan ta yimasa sos din kwai, akan babban faranti ta dauki kayan tafita,
Zaune ta iskesu shida mami ya sunkuyar da kai yana zaune akan kujerar dake facing din ta mamin abisa dukkan alamu wata maganar suke yi mai muhimmanci, agabanshi ta ajiye tiren tajuya ta koma kitchen ta dauko na mami ta Kawo mata itama ta ajiye, sai binta da kallo mamin keyi cikin farin ciki tana yi mata sannu,
Ganin kamar maganar da sukeyi mai muhimmanci ce yasata kin zama awurin dan haka tana kammala ajiye musu abincin ta juya takoma kitchen ta hada yan kayayyakin da tayi amfani dasu tasoma wankewa,
Acan falo kuwa koda Hafsat ta fita mami kallonshi tayi,
"Yusleem anya kuwa kana zama tareda yarinyar nan kuyi hira kuyi wasa da dariya a matsayinku na ma'aurata?"
Sunkuyar da kai yayi,
"Mami me kika gani?"
"To ai gani nayine kamar tana dan dari dari dakai, dan ko lokacin da nace ta kiraka saida naga tayi wani dan jimmm"
Murmushi ne ya kwace masa saboda abinda yaji mami tace wanda har hakan yayi sanadiyyar ajiye cup din dake hannunsa,
"Mami kenan, wallahi babu komai kuma ki tambayeta kiji"
"Ehh ai zan tambayeta din, amma kasani wallahi muddin naji kana takura mata ko wani abu mai kamada haka to sai ranka ya baci..."
Murmushi yayi ya dauki shayin yaci gaba da kurba domin ba karamin dadi yayi ba kasancewar da kayan kamshi Hafsat ta dafashi shiyasa in banda kamshi babu abinda yake yi,
"Kaci dankalin mana gashinan, kai mai son dankali.." Yaji muryar mami tana yimasa