Showing 21001 words to 24000 words out of 70255 words

Chapter 8 - ALWASHI BOOK 1 COMPLETE by Ummi Aisha .txt

23 Dec 2024

3901

magana, shifa sam bai taba cin a abincin Hafsat ba, bama wannan ne abin mamakin ba abin mamakin shine har yau baisan kamanninta ba domin ko kallon minti 1 bai taba yimata ba bare har yaga yadda take,


Bude flask din data zubo masa dankalin yayi yadiba a filet yadebi sos din yadora akai yafara ci,


Yana ci suna maganar da suka fara da mami har saida ya cinye dankalin domin baifi kwaya biyar ba wanda yabari acikin flask din,


Hafsat kam tana kitchen bayan tagama aikinta ma wuri ta samu ta zauna saboda bata son taje tasaka su mami agaba ta hanasu sakewa suyi zancen da suke,


Tana zaune akan kujera ta jingina da jikin deep freezer taji kamshin turarensa na oud abyad,sam bataji shigowarsa ba bare tafiyarsa,


Akanta ya tsaya kamar wani soja yana kallon wani wuri,


"Me kikeyi?"


"Aiki nagama yanzu shine nazauna ina hutawa.."


"To zo.."


Yace da ita tareda juyawa yayi gaba, tashi tayi tabi bayansa tana kallon irin yanda jar rigar da yasaka ta kara haskashi,


"Hafsat kizo ki zauna ki huta mana, inata kiranki bakiji ba,sannu kinji, tunda nazo gidan nan baki zauna ba sai aiki kike tayi..."


Murmushi tayi saboda jin abinda mami tace, akasa ta zauna kusa da kujerar da mamin ke kai,


"Mami ai aikin bashida yawa..."


"Duk da haka dai Hafsa ai kina kokari, gashi kin hadu da miji mai tsirfa Wanda ba kowanne abinci yake ciba, kin ganshi nan haka yake kamar wani marar lafiya sam bashi son cin abinci..."


"Uhm.." Kawai Hafsat tace ta danyi murmushi domin ita kwata kwata ma yusleem bai taba cin abincinta ba,


"Bari intashi inje intafi, akwai ta wurin da zan biya dama cewa nayi bari inkaraso inganku, Hafsat ai babu matsalar komai ko?"


Takarashe maganar tana dafa kafadar hafsa,


"Wallahi mami babu komai.."


"A'a hafsa idan da wani abu ki fada min saboda nasan halin yusleem sarai, bahagon mutum ne koni da na haifeshi ban fiya gane mishi ba.."


"Allah mami babu komai da ace akwai wani abu ai zan fada miki.."


"To shikenan, taso muje akwai abinda nakawo miki"


Mikewa mami tayi itama Hafsat din ta tashi, kallon yusleem mami tayi,


"Kai kayi zamanka basai ka tasoba saboda ina son zan ganta ita kadai.."


"To mami asauka lafiya" yusleem ya amsa mata yana kokarin kishingida ajikin kujerar da yake zaune,


Kama hannunta mami tayi suka fita,


"Hafsat kikace babu komai? Idanfa akwai wani abu ki sanar dani"


"A'a mami babu komai"


"Baya takura miki?"


"Wallahi mami babu abinda yake min"


"To shikenan dama haka nake son ji, bari ga wani sako da na Kawo miki,turare ne na tsugunno tun daga chadi wata kawata ta aiko miki dashi,ki tsugunna akai kamar saura awa biyu ko uku kafin kije dakinsa"


Jin abinda mami tace yasa hafsa taji kunyar duniya ta rufeta,


"Hafsat ai ni babarki ce menene abin kunya? Ki dauka haifarki ne kawai banyi ba amma babu abinda bazanyi mikiba a duniya"


Karbar turaren tayi tana yiwa mamin godiya,


"To mami nagode Allah yakara girma"


"Amin, ai babu komai Hafsat"


Har gaban motar mamin tarakata ta bude ta shiga, tana tsaye har saida taga fitarta sannan ta juya ta koma ciki,


A wurinda suka fita suka bar yusleem yanzun ma anan ta tarar dashi ya kwanta akan doguwar kujera ya kunna tv yana kallon ball, har zata wuce tatafi bedroom dinta taji k'asa k'asa yace,


"Zo nan.."




Dawowa tayi tazo inda yake,


"Gani..."


Shiru yayi mata baiyi magana ba, tafi minti biyu atsaye, ganin yaki magana yasata fadin,


"Intafi ne?"


"Tafi in bazaki rage tsawo ba, kinzo kin wani tsaya min aka.."


Zama tayi akujerar dake makotaka da tashi,


"Bani inga abinda mami tabaki.."


Kallon mamaki ta wurga masa nan taga idanuwanshi suna kan tv,


"Ni babu abinda tabani.."


"Karya kike yi.."


Shiru tayi saboda jin abinda yafada domin dama tun lokacin da zata shigo ta cusa kullin turaren acikin zaninta,


"Muga hannunki.."


Dagasu tayi babu komai aciki,


"Idan baki baniba tashi zanyi in cajeki fa"


"Ehh nayarda.."


"Tashi kije"


Mikewa tayi tawuce bedroom dinta taje ta bude drewar din madubinta ta jefa aciki tafito ta shiga kitchen.


Girkin rana ta dora ta dafa shinkafa da taliya da miya, abin mamaki har ta kammala girkin ta fito daga cikin kitchen yusleem yana nan awurin da yake kwance yana kallon ball da alama yau babu inda zaije domin ko shirin fita baiyi ba,


Kan dining table taje ta jere abincin data girka tazo inda yake kwance akan doguwar kujera,


"Yaya ga abinci angama"


Kai kurum ya daga mata alamun yaji, bedroom dinta tawuce taje ta watsa ruwa tayi alwala domin taji anfara kiraye kirayen sallar azahar,


Bayan ta shirya ne ta koma falon, yusleem baya ciki amma ga filet nan da spoon alamun ya danci abincin data dafa,


Murmushi tayi taje ta zubo abincin tadawo ta zauna tana cin abincin tana kallo, tun da yafita kuma shikenan bata sake jin duriyarsa ba har akayi kwana biyu,


Jin shirun yayi yawa yasata nufar part dinshi domin dubashi,


Lokacin da ta shiga atsaye taganshi gaban mirror yana gyara necktie din da yasaka da alama shirin fita yakeyi domin lokacin karfe 9:30 nasafe,


Sallama tayi ya amsa mata aciki ciki batare da ya kalleta ba,


"Ina kwana yaya.."


"Lafiya" yabata amsa,


Shiru tayi ta tsaya tana kallonshi, sanye yake cikin bakaken suit yasaka blue din t shirt mai kwala ta ciki,


Agogon azurfa na Gucci yadauka ya daura ahannunshi yafesa turare ya zo ya raba ta gefenta yawuce batare da yayi mata magana ba,


"Adawo lafiya..." Tafada ganin yayi hanyar fita,


Bata fita daga cikin dakinba saida ta gyarashi ta wanke toilet ta goge ko ina sannan ta rufe tafita,


A falonta tasamu surayya baje tana jiranta,


"A'a saukar yaushe?"


"Jiyan nan nadawo shine naga bazan iya zamaba har sai nazo naganki"


"Sannu da dawowa, kin jima da zuwane?"


"Ehh to nadai fi 20 minutes amma abinda yasa ban damuba shine naga kina turakar mai gida..."


Murmushi Hafsat tayi mai ciwo,


"Surayya yaya yusleem narasa wanne irin mutum ne shi wanda sam bai damu da iyalinsa ba..."


Katseta surayya tayi,


"Da jira kikeyi yadamu dake? Tab ai bari kiji wallahi garama ki tashi daga wannan dogon barcin da kikeyi domin yaya yusleem yanada manyan matsaloli,


Bafa akanki yafara aureba kuma wallahi sakin mata yake, auri saki gareshi dan babu wacce ya taba aura tayi shekara agidansa shiyasa nake son ki zage ki kamashi ahannu dumu dumu kuma wallahi karki raga masa ki azabtar dashi idan kika tsaya jin tausayinsa kika raga masa sunanki sorry domin shi azabtar dake zaiyi..."


Jin abinda surayya tace ai Hafsat bata San lokacin data zamo daga kan kujerar da take zaune ba tadawo kasa,


"Auri saki fa kikace?"


"Tabbas domin ya auri mata sunfi goma sha..."


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.."


"A'a nifa ba fada miki nayi dan ki tada hankalinki ba, kawai fada miki nayi dan ki tashi atsaye kisan duk yanda zakiyi ki karkato da hankalinsa gareki"


Tagumi Hafsat tayi tana lazimi acikin zuciyarta......








*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*






_Dedicated to MISS XOXO_








*25*








***Tagumi Hafsat tayi tai shiru tama rasa abin cewa domin bata san ta inda zata faraba,


"Baiwar Allah karki tashi hankalinki, nidai kawai abinda nakeso kisani shine yaya yusleem fa ba dutse bane mutum ne dan haka duk taurin kansa wata rana dole ya bukaci mace, dan haka daurewa zakiyi ki zage kiyita shisshige masa har yazo hannu kin gane ai?


'Yar rangwadar nan, kwalliyar nan, tsabtar nan..." Surayya tafada tana dariya,


Kallonta Hafsat tayi idanuwanta har sunyi ja,


"Surayya kenan da alama baki gama fahimtar yayan naki ba, yaushe ma ya zauna agidan bare har insamu damar yi masa wadannan abubuwan? Kedai kawai Allah yabani mafita"


"Amin, zaima baki cikin ikonsa"


Haka suka cigaba da tattauna maganar har tsawon wani lokaci,yauma kamar koda yaushe saida da daddare sannan surayya taja motarta ta tafi,


Tafiyarta yasa Hafsat jin gidan yayi mata tsittt, part din yusleem ta shiga baya cikin falon dan haka ta nufi bedroom dinshi nan dinma baya ciki, har zata fita tajiyo motsin ruwa acikin toilet alamun wanka yake nan tajuya tafita,


Bata kara sashi a idonta ba tun daga ranar,dan haka kullum wunin kadaici takeyi wannan dalilin ne yasa tayiwa Ummi waya tace a Kawo mata keken sakarta domin ko babu komai zai rinka dan debe mata kewa idan babu abinda takeyi sai tarinka hawa tanayi,


Washe gari hajiya kubra taje gidan takai mata keken da sauran kayan da zatayi amfani dasu wurin sakar, wannan shine karo nafarko da ummin taje gidan nata shiyasa murnarta takasa boyuwa,


Ita ason ranta ma ummin ta zauna ta wuni amma fur taki ko minti talatin batayi ba tatashi zata tafi,


Bin bayanta Hafsat tayi ta rakata anan hajiya kubran ke fada mata cewar ai yusleem sau biyu yana zuwa gida gaishesu bayan bikin, mamaki ne ya kama hafsa saboda bata zaci zai iya zuwaba duk da tafi zaton cewar mami ce zata tilasta shi yaje, sallama sukayi da ummin tatafi ita kuma takoma cikin gida.


Samun keken sakar nan akusa da ita shine dalilinta yanzu na rage zaman tunani duk da wani lokacin tana ganin anya kuwa rayuwarsu ita da yusleem zata yiyu ahaka? A matsayinsu na mata da miji ace sai suyi kwana 3 basu ga junaba, sannan bai damu da yaci abincinta ba balle har magana ta shiga tsakaninsu,


Gama wannan tunanin keda wuya ta mike ta nufi falonshi, baya ciki dan haka takarasa dakin baccinsa can dinma baya nan amma ga laptop dinshi nan a ajiye akan gado, karasawa tayi ta dauke laptop din ta gyara gadon daga nan ta zarce da gyara dakin gaba daya,


Bathroom tashiga nan taga ya jika kananan kayanshi acikin bocket da dukkan alamu so yake su jiku yasa acikin washing machine yawanke domin tasan bazai taba yin wanki da kansa ba tunda itama da ba kowan kowaba an ajiye mata injin wankin sai dai ita bata ma fiya amfani dashiba tafi ganewa tayi abinta da kanta,


Tsayawa tayi ta wanke masa kayan tass tadauka tafita ta shanya, tana cikin shanyawa yadawo yana sanye da kananan kaya jeans da t shirt,


Binshi cikin falon tayi bayan ta kammala shanyar kayan,


"Sannu da zuwa..."


"Yawwa..." Ya amsa mata aciki ciki daga nan bai kara koda kallon bangaren da takeba bare tasa ran zaiyi mata sannu na aikin da tayi masa,dan haka tawuce takoma part dinta,


Wadannan abubuwan dake faruwa sune suka hanata bacci adaren yau har misalin karfe daya idonta biyu, tanata juyi tajiyo kamar alamun tafiya atsakar gida a tsorace ta tashi taje gaban window ta daga labule tafara lekawa ahankali, kasancewar tsakar gidan akwai haske tal kamar rana shiyasa tasamu damar hango yusleem din wanda ke kokarin bude kofar motarshi,


"Ina yaya yusleem zaije acikin daren nan?" Ta tambayi kanta,


Kafin ta iya bawa kanta amsa tuni har yashiga motar mai gadi ya bude masa yafice, ita tsoro ne ma ya kamata domin duk atunaninta agidan mami ne wani abu yafaru nan takoma ta zauna jugum tanata nazari amma motsi kadan sai tatashi ta leka ko yadawo amma shiru,


Haka takasa bacci sai sake sake da haka har asubah tayi a lokacin ne taji dawowarshi da kamar taje wurinshi taji abinda yafaru sai dai tafasa,alwala taje ta dauro tazo ta tada salla.


Misalin karfe 8 tashiga falonshi bayan taci kwalliya cikin wata dark purple din shadda,


Kwance ta sameshi yana bacci akan doguwar kujera yana sanye da farar t shirt da bakin boxer, karasawa dakinshi tayi ta gyara masa tafito, lokacin da ta fito kuma yana zaune yana danna wayarshi, gaisheshi tayi ya amsa daga nan yaci gaba da abinda yake yi, jin baice mata komai ba yasata fita takoma falonta taci gaba da harkokinta,


Tana kan kekenta tana karasa hada rigar data fara jiya taji sallamar Amina kawarta, da murna ta tari aminan wacce ke daga kafa dakyar domin cikinta yadan fara tsufa,


Ba karamin dadin ganin aminan tajiba nan suka baje a falonta suka hau hirar yaushe gamo, wuni cur Amina tayi mata sai yamma ta tafi,


Haka taci gaba da zaman kadaici agidan domin surayya ma takoma makaranta kuma bazata sake dawowa ba har saita kammala, yau watanta biyu da wani abu agidan kuma tunda tazo bata taba fitaba shiyasa yau ta kuduri niyyar tambayarshi zuwa ganin gida,


Yana kokarin fita tayi gaggawar tsayar dashi, tsayawa yayi batare da yajiyo ba,


"Yaya dama yau ina son zuwa gidanmu ne"


"Allah kiyaye hanya, idan kin shirya akwai driver"


Daga haka yayi gaba abinshi, shiryawa taje tayi tafito tana dauke da rigunan jariran da ta saka wanda zata tafi dasu takaiwa Ummi domin asayar mata,


Kamar yadda yusleem yace haka ta tarar da driver yana zaman jiranta nan ya dauketa yakaita gida, murna wurin hajiya kubra abin ba acewa komai nan tashiga yin nan nan da ita, Hafsat ba ita tabaro gidanba sai dare domin saida tajira alhaji sa'id yadawo suka gaisa,


Daren yauma kamar rannan kasa bacci tayi can taji fitar yusleem daga gidan agogo ta kalla karfe 2 saura na dare,


"To wai shi wannan ina yake zuwa cikin talatainin dare haka?"


Sake saken zuci tayita yi har saida asuba takawo kai, awannan lokacin ne taji dawowarsa azamar sauka daga kan gadonta tayi tanufi part dinshi da sauri domin tana son taga awanne yanayi yake,


Acikin falonshi ta buya a bayan labule, ahankali taji ya bude kofa yashigo, lekashi tayi nan taganshi acikin nutsuwarshi yake ita tayi zaton zata ganshi cikin maye ko makamancin haka, zama yayi ya bude wani dan karamin akwati nan taga kudi fall kuma duk daloli ne ba naira ba,


Mayarwa yayi ya rufe ya tashi yashiga bedroom dinshi, sadadadawa tayi tafita takoma dakinta tana tambayar kanta to daga ina yaya yusleem yake?


Wasa wasa kullum cikin dare sai taji fitarsa kuma bashi zai dawoba sai aubah ashe dama can haka yakeyi sanine batayi ba saboda lokacin da zai fita tayi bacci shiyasa har yaje yadawo bata saniba, kasa gane inda yake zuwa tayi domin fitar tasa kusan kullum ne tamkar ibada kuma baya tashi fita sai tsakiyar dare,


Yau kam ta daura aniyar binshi taga inda yake zuwa domin tunaninta yanzu yafara bata cewar ko yaya yusleem dan fashi ne?


Hana idonta bacci tayi har karfe dayan dare tana jira taji motsin fitowarsa amma shiru, karfe biyu shiru har da rabi duk shiru, hakura tayi ta kwanta nan bacci ya dauketa can cikin baccinta taji dirin motarshi agigice ta tashi ta leka abin haushi wai sai ganinshi tayi yafito daga cikin mota alamun yadawo daga wurinda yaje,


Da haushin wannan abun ta wuni da yamma sai gashi ya shigo cikin part dinta yana sanye cikin farar shadda mai mutukar kyau da tsada dinkin tazarce sai jar hula da yasaka,hannunsa daure da agogon fata fari kafarshi kuma yasa farin takalmi half cover tsaf dashi fadin irin kyan da yayi abun ba acewa komai,ita bama tafiya ganinshi da dogayen kayaba sai dai idan ranar juma'a ce tayi wannan kam yanasa manyan kaya amma idan bahaka ba kullum cikin kananan kaya yake,


"Zanyi tafiya zanje America daga can zan wuce India saboda akwai likitan da zan gani acan,idan akwai abinda kike bukata ki duba cikin bedroom dina akwai kudi..." Yace da ita cikin muryarsa mai sanyi,


"Allah ya kiyaye hanya yadawo dakai lafiya"


Bai amsaba yajuya yafita,bayan tafiyarshi part dinshi taje ta shiga bedroom dinshi tahau binciki wai ko zataga wata alama wacce zata tabbatar mata da gaskiyar abinda take zargi amma babu abinda tagani haka ta hakura ta mayar da dakin ta gyara ta fita,


Washe garin tafiyarshi mami ta turo driver ya dauketa can ta zauna har tsawon sati 2 sai ana gobe zai dawo sannan takoma gidanta kuma sosai taji dadin zama tareda mami domin tana mutukar kaunarta tareda kulawa da ita,


Tunda yadawo take bibiyarsa tana fakonsa saboda so take sai tagane inda yake zuwa cikin dare da abinda yake yi, kullum bata bacci har tsawon kwana biyar da dawowarsa saida ta sakankance ranar da tayi bacci aranar ya fita daf da asuba kuma sai gashi yadawo,


Wani haushine ya cika mata ciki gashi kuma tun daga ranar bai kuma fitaba, duk da haka bata hakura ba haka taci gaba da saka masa ido,


A wata ranar lahdi har zata kwanta sai tajiyo motsinsa, tashi tayi ta sadada tafita har yabude motar zai shiga ko me ya tuna oho sai yafasa yanufi ciki amma dai yabar motar a bude, ganin haka yasata lallabawa tabude bayan motar tashiga ta makure ta buya,


Tafi mintuna talatin aciki bai dawoba, tana shirin fita sai taji alamun tahowarsa nan takoma tasake makalewa ta yadda bazai ganta ba,


Shiga cikin motar yayi yatadata ahankali ya murza ya doshi gate din fita.......






_Sakon fatan alkhairi ga yan group din Duniyar littattafan Hausa, tabbas kunfi kowa son alwashi..._






*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_








*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_








_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*






_Dedicated to MISS XOXO_








_Kuna ina? Members na zauren karatu group, wannan page din yau nakune ku kadai domin jin dadinku, soyayyarku gareni ta musamman ce, ina yinku kamar yadda kuke yina....!_








*26*






***Sake lafewa Hafsat tayi a lungun kunjerun baya wato wurinda ake ajiye kafa, tana jinsa yana driving din yana dan jan karamin tsaki, titin emirs palace yahau,


Gaba daya garin tsitt yake babu motsin kowa sai haushin karnuka wadanda idan sun ji motsi suke kaurewa da yi,


Wayarshi ce tadanyi kara nan taga ya dauka yakara a kunnensa, cikin sansanyar muryarshi taji yace,


"Am on my way...." Wani dan tsakin yaja bayan ya kammala wayar ya ajiye,


Haka yaci gaba da yin driving ahankali shi kadai atsakiyar titi domin hatta jami'an tsaro masu yin patrol sun gama aikinsu sun tafi,ita mamakinshi ma takeyi ganin ko tsoro bayaji shi kadai a titi kamar aljani,


Wata hadaddiyar atishawa ce ta tahowa Hafsat batare data shirya ba nan tayi hanzarin toshe bakinta da hancinta amma duk da haka saida yar kararta ta fita,


"Atshhh..."


Jin sautin yasa yusleem wanda ke yin driving dan juyowa nan tayi saurin sake kwantawa abayan kujerar, maida kallonsa titi yayi yaci gaba da tukinshi,


Jin alamun yatsaya yasata dan dago kanta domin ganin ko inane, bata san ko ina bane amma tana dan iya jiyo maganganun mutane, dukar da kanta tayi har saida taji fitarsa sannan ta dago tafara kallon wurin,


Wani babban hotel ne mai tsananin kyau wanda yakeda fiyeda hawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login