Showing 30001 words to 33000 words out of 133269 words
Chapter 11 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt
ambatonshi a matsayin uban diyarki, kikace kin amince, yanzu kuma kice muje gurinshi? Karki manta yace ya gama aikinshi kanki rana kawai zaki jira, yace duk randa kika zo mishi da maganar diyarki zai kwance komai da ya kulla kinga kinyi jiran banza, Shekara 5 ta tafi a banza, komai ya tashi a banza, ke dai kiyi hakuri yanzu, gobe ki koma Jos a fara ma Mama maganin hausa zaa dace".
Kuka Shafa'atu kawai take, Washegari da Asuba tayi Sakkon komawa garin Jos ranta 6ace, ta na dawowa da kwana daya Mamarta tace ga Garinku nan, ta girgiza da mutuwar Mahaifiyarta ta sha kuka son ranta tana tausayin kanta da na kaninta Hudu, basu da kowa, basu da komai.
Rayuwa ya mata zafi, dole ta rayu kafin Burinta ya cika, dole ta zama karfin Annah da Hudu, dole duk su rayu, mikewa tayi tsaye ta fara Abincin Saidawa kamar yanda sukeyi a da, kasancewar ta iya Girki, kuma akwai Tsafta ya sa take samun Customers. Kuddirinta na nan, ranta chunkushe, Ganinta Ali zaki ne yayi sanadiyar mutuwar Mahaifiyarta, da ya taimaka mata, da amma Uwar ta aiki da ta warke, Ta k'agara Shekaru 10 su cika ta fanshe Bakincikinta.
Bayan Shekara Goma
18/10/2008
Yau take Sallah a gurin Hajiya Shafa'atu, kwalliya ta ci ta sa tsaddaden leshin da Allah kadai ya san inda aka samu kudin dinkawa, harta lalle sai da aka K'unsa mata, yanda ka san Sabuwar Amarya.
Da karfe 1 na rana Annah ta shigo dakinsu, tace "wai ni Mummy ina Baban nawa? Har yanzu bai iso ba?"
Shafa'atu ta fara girgiza kafarta, ita fa a ganinta ko garin yau be idasa wayewa ba zata ga Alinta, gashi har an fara kiraye kirayen Sallah.
Ba ta so ta sa shakku a Aikin Mallam, Shekaru 15 tayi tana jiran Ranar nan, ga ranar tazo, gashi ranan ya mata kama da sauran ranakun da suka shude, ba wani abu special game da ranar yau, ko dai tayi wauta da sakaci da ta yarda da maganganun Mallam? Ko Annah bata amsa ba ta ciro wayarta ta latso Er Rabi, Er Rabi na dauka ta fashe da kuka.
Yau waya kala kusan 10 sukayi, Er Rabi tace "Yaya ne? Ya iso ne?"
Shafaatu ta fashe da kuka tace "wani isowa? Har yanzu shiru, sai da nace miki zanzo Katsina kila gidan ya mai wahalar ganewa, er Rabi ya zanyi? Ko dai mallam ya wanke mu ne?"
Er Rabi tace "ke dai baki da hakuri, ki bari ranar yau ta kare mana kafin kiyi korafi, kinsake hakuri, kar ki sake kirana sai yazo" dif Er Rabi ta kashe waya, ran Shafaatu a bace.
ABUJA
Zuciyarshi ke mishi Zafi tun bayan Sallahr Asuba, Ji yake kamar a na yankar Naman jikinshi. Meeting sukayi , amma be fahimci komai ba.
Meke damunshi? Ya tambayi Zuciyarshi.
"SHAFA'ATU"
A takaice zuciyar ta amsa mai.
Yana son ganinta, ta na ina? Tayi aure? Akwai auren wani a kanta? Ta mutu? Da sauri ya girgiza kanshi da ke barazanar tarwatsewa, tunanin Mutuwarta na neman dauke mishi numfashi, in ta mutu sai ya bita, in kuma tana da aure ko zaiyi yawo tsirara sai ya raba auren nan ya dawo kanshi, zai biya Mijin da duk wani k'addara tashi.
"Ina zan fara nemanta?" Ya tambayi zuciyarshi.
JOS ta amsa mai, kamar ana karanto mishi abunda zaiyi haka yake ji, kurum ya kira PA dinshi yace a siya mishi ticket din Jirgi zuwa Jos, haka ko a kayi, a gurguje suka isa Airport, suka nufa Jos bayan Mintuna da basu kai 50 ba suka isa Jos.
Akwai Convoy din da suka zo tarbenshi, be manta Unguwarsu ba, ya gaya ma driver cikin 30mins suka iso Unguwarsu Shafa'atu.
Kamar ana ingizashi ya fada Gidan, ko Sallama babu, abunka da me jira, ta na zaune tsakar Gida, tana ganinshi ta mik'e tsaye, murna ya sa ta fashewa da kuka, da niyarta in yazo ta dan gasa mai gyada a hannu ta ja aji, amma ganin yanda ya shigo, ta manta da duk wani bacim rai da ya taba kunsa mata a rayuwa, Son shi ya goge mata komai, daga inda yake ya choge tsaye, hankalinshi ya dan tashi ganin ta na zubda hawaye kai ya girgiza mata tare da ware hanayenshi Biyu, da gudu ta fada jikinshi ya rungumeta gam yana samun wani irin natsuwa.
Murya a dishe yace "Shafata, ina kikaje kika barni cikin kewanki, Shafata me na miki kika barni?" Kiyi hakuri kizo mu cigaba da Zamanmu, Ina sonki, kece wacce na fara so a rayuwata" ganin yanda yake sake rungumeta ya sata cewa "Yarinya na kallonmu,Alhajina ai Sakina kayi, Saki Uku ma" da sauri ya tureta yace "Inji Ubanwa yace Sakin ki nayi? Nifa ban sakeki ba, ta ya zan rabu da rayuwata? Baki da labarin kece Rayuwata".
Dan tabe baki tayi tace "Ya kayi da Shekaru 15 da suka wuce?" Yana son yin dogon tunani amma ya kasa cewa yayi "Ni bansani ba, kar ma ki tambayeni, abunda na sani shine, san karashe rayuwata dake, ba zan taba bari kiyi man Nisa ba".
Wani Farinciki ya ziyarceta, dadi kamar tayi tsalle, "Shafata, Katsina zan tafi dake, ba zan iya kwana ba da ke ba, yau dare yayi, gobe zamu dau hanyar KT kinji?"
"To wa ya ce maka zan bika? Ina da Auren wani a kaina" ganin yana neman haukacewa tayi saurin cewa "Wallahi wasa nake maka hahaha" kamar yayi kuka yace "kina son wahalar dani ne? Ki zo mu tafi Masaukina" Cike da shagwaba tace "Auren fa? Ba zaa maida ba?"
Yace "Yanzu kuwa zaa maida, Da anyi sallahn maghrib sai a daura" Dadi kasheta, nan ta mishi introducing Annah a matsayin diyarta da Babanta ya mutu, Hudu kuma kaninta.
Yace "duk baki da damuwa, Annah Diyata ce, Hudu kuma kanena, dukkansu na dauki nauyinsu na tsaya musu, tare zamu tafi dasu".
Godia tayi mai sosai, bayan Sallahn Maghrib aka daura Aurensu sadaki dubu dari 5, a ranar duk basuyi kwanan Gidansu ba, sai a kayattacen Hotel dake Jos.
Washegari da Sassafe suka hau Jirgi suka nufi Kano, daga Kano suka hau Mota zuwa Katsina.
Suna isa KT ya bada Umurni a kai Annah da Hudu Shopping Mall suyi siyayyan Kaya.
Shikuma suka nufi Gida tare da Amaryarshi.
^^^^^^^
Kiraye kirayen Sallahr Azahar akeyi, ashe ta dade a wurin Dan Makaho, ita ina ta lura lokaci ya ja? Wuri ta samu ta buga tagumi, tana ta nazarin Labarin danMakaho, wayarta tayi k'ara Jay ta gani a gaban screen.
Numfashi ta ja ta saki ta dauka wayar da Sallama "Labeenah, ina kika shigane? Nayi missing dinki sosai" In Ina ta fara "Eh wallahi lecture mukeyi, nima nayi missing dinka"
"Yaushe zaki ban lokaci na zo Katsina?" Murmushi tayi tace "duk lokacin da kazo, ina maraba da kai"
Hangoshi tayi daga inda take, ya dawo dauke da wani abu a hannu, mancewa tayi da Wayar da take ta mike zuruf ta kuka tsallaka fasasssun Blocks din ta bishi daki har ta kusa bashi tsoro.
"Ke wai meyasa baki da hankali ne? Ta ya zaki ta shigo min daki ne? Wato ba kiji warning din da na miki ba ko?"
Baki ta tabe ta kalli ledar hannunshi, Bread ne sai Sardines, tace "ni karashen labarina nazo ji"
"To ba zaa bada ba"
Wuri ta samu ta zauna harda daura kafa daya kan daya tace "gama ci dai".
Tsaki yayi, gardama da ita aikin banza ne ya bude Kifin gwangwaninshi, ya na dangwala mai din da bread yana ci, be kulata ba, ita kuma latsar wayarta kawai take.
Daga waje kuwa Blocks aka kawo da Cement da Yashi zaa fara aiki.
"Kina ji ba?" Da ya gama kenan, da sauri ta ajiye wayar tace "eh ina jinka.
"Jikin Mancy Rawa kawai yake, rik'ota nayi na mata garkuwa da kafada na" ban bi ta kan Dalo da ke kuka ba, Mancy ta zare jikinta daga gareni tayi hanyar cikin gida duk sai muka bita.
A parlo muka tsaya inda muka ga Baba da Anty Shafa'atu suna magana, ce mishi take ita ba zata iya zama a dakunan nan ba, bata san surkullen da ke ciki ba, kafin ya bata amsa ya hngo mu, Baba na ganinmu kamar an aiko mai da mutuwa, dif annurin fuskarshi ya dauke, ya ja hannunta ya fita, muma muka bishi riiiiiii,
Mancy ta dan Matsa kusa dashi tace "ka riga da ka furta, ba aure tsakaninmu, aure ya k'are, ina so na san me na maka da na chanchaci Saki Uku gaban Yarana?" Kamar jira yake ya hau kan Mancy da duka, hankalina ya tashi na shiga tsakaninsu, na janye Mancy ina ma Baba Kallon Mamaki.
"Ki fitar min A Gida Maryama, ki kwashi yaranki ki bar min Gida bana son ganinku ku duka, na tsaneku"
Mancy ta share hawayenta, nikuma ina tsaye kamar gunki, Dalo kuwa na zaune dirshen a k'asa.
Mancy ta matsa kusa da Dalo ta tallafota gabaki daya.
Yanayin da ban taba ganin Mancy a ciki ba, ta bude murya tace "Zaid, Sadiya, zamana ya k'are a gidan nan, rabonku ne dama ya kawoni gidan nan, ku sani Nan Gidan Ubanku ne, ba ku da inda ya fi nan, ko ma mai zai faru, i mean no matter what will happen, this is Your Father's house, kar ku taba mantawa, kar ku manta da kalar Soyayyar da ke tsakaninku, kar ku bari kowa ya shiga tsakaninku"
Hannayenta ta daga Sama "Ya Allah, ga Bayinka nan, Allah ga Zaid, Allah ga Sadiya, Allah kaine gatansu,Allah ka sakama duk wanda aka zalunta"
Shafa'atu ta fashe da Ihu "Ni Alhaji sai dai ka Sakeni, Matarka so take ta kafurtani".
Aiko ya yunkuro zai bige Mancy nayi saurin tareshi ina girgiza kai don ban ma da k'arfin magana.
Ki tafi da yaranki" Baba ya sake jaddada mata, tace "ba inda zani dasu, nan ne gidansu, gidan ubansu, Ba inda zani dasu, kamar Zaid? Yana Masters? Ina zani dashi? Dalo da ba nono take sha ba ina zani da ita? Ai suna gidan ubansu, su ba Mata bane balle a sake su, 'Ya'yane su".
Nan suka fara hayaniya, da karfi, ban taba sanin Mancy ta iya fada, don ko an kure hakurinta ne.
Kinsan mai hakuri in an taboshi.
Shafa'atu tace "kinga Maryama rufin Asirinki ki tafi dasu, kika san me zan musu in suka zauna? Ba kya tsorona ne? Ki tafi dasu, wannan Gidan daga ni sai yaran da zan haifa ma Alhajina Magada Babansu".
"Huh tsoro? Bana Shafa'atu, bana tsoron makircinki, ko da ba tsoronki nake ba, kawai na fi so a zauna lafia, kuma yarane gasu nan, ki sa kansu gabas ki yanke, suna Gidan Ubansu, haihuwa kuma Allah ya kawo miki 100, duk dai yaran da zaki haifa ba zaki taba haihuwan Yayan Zaid ba, koma Sadiya, dole sai Kannensu zaki haifa".
Sosai kalaman Maryama suka bata haushi, me zata mata ta bak'anta mata rai? Alhaji wai tsayawa zakayi tana gaya min magana? Wallahi sai dai ka sakeni".
Yana jin haka ya rufe Mancy da duka a karo na biyu, na shiga tsakani ya hada dani, Dalo ma ta shiga tsakani aka hada da ita, ya dinga dukanmu ko ta ina yana halbemu, mu ko muna rungume da junanmu, Dalo sai kuka mai sauti take.
:::::
Zaune yake da 'yar Matarshi, da jaririnsu, wani abu yake ji daga Makwaftanshi kamar hayaniya, kasa kunne yayi sosai,
Gabanshi ya yanke ya fadi, Gidan da ya sani a matsayin Gida da suka kansu a kan Soyayya, Aminci da juna, abunda be taba ji ba, hayaniya, ya ji kamar ana maganar Saki, ya ji kamar maganar Barin Gida ake, wacece Matar nan da ta shigo tsakanin Gidan nan da basu son komai ba sai SO?.
Matarshi ya kalla yace "Aseena, akwai matsala". A tsorace tace "Wai Sakin Mancy aka yi? Inallilahi" kafin ya bata amsa sukaji kamar kuka, da suka kasa kunnensu sai sukaji ashe dukansu yakeyi, da sauri suka tashi a sittin sukayi Gidan Alh Ali Zaki.
Kamar an tara Mutane don wurin cike yake, kowa mamakin Alh Ali yake, yau shine yake dukan Farincikinshi? Da girman Zaid yake dukanshi, yake dukan Sadiya diyar da yake gani itace Yar Gwal, ga matar da yake so kamar ranshi, yau itace yake duka da hannu duk ya galabaitar da ita, rigarta har ya yage har kana iya hango abunda ke ciki, da Zaid ya tashi taimaka mata sai ya sa security su rik'eshi.
Manyan Unguwan sai magana suke mishi suna rokonshi da ya barsu haka, amma be tanka kowa ba.
Muhammad ya shigo da Matarshi Asee, kutsawa sukayi tayi, gidan kamar ana shooting film, kutsawa yayi ya shiga, matarshi ta bi bayanshi, daidai nan Alhaji Zaki ya daga wani katako zai kwala ma Mancy kenan ya karasa da gudu.
"Haba Alhaji, Haba, menene haka? Meya sameka Alhaji? Wallahi ba Girmanka bane? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun"
Hajiya Shafa'atu ta dago ta kalli Muhammad da tsana, shi ko Alhaji samun kanshi yayi da maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" waigawa yayi yana kallon su yashe a k'asa, abun alfaharinshi, dukkansu yashe a k'asa.
Hajia Shafa'atu tace "nifa su tafi, ina son na huta" kamar an ingiza shi yace "duk ku fitar min daga Gida, yan iska shegu, duk na tsaneku".
"Alhaji ina kake so suje? Basu fa da inda ya wuce nan" ni wallahi sai sun fitar min a Gida, Muhammadu, ba na k'aunar ganinsu"
DanMakaho ya kalli Labiba sosai yace "Kinsan Unguwar nan kaf, ba wanda nake ganin mutuncinshi irin Yayanki?" Labiba ta murmusa tace "Yayana na da kwarjini" yace "ya min abunda ba zan taba mantawa ba, zuwa yayi ya dago ni ya rungumeni, ya lallasheni ya rada min a kunne, ka zama k'arfin Mahaifiyarka da kanwarka, tashi ka rik'o Dalo, muje gidana muyi magana".
Umurninshi na bi, na tashi na mik'ar da Dalo da ke kwance magashiyan a k'asa. Yayanki ya matsa kusa da Matarshi, ya karbi jaririn hannunta yace ki taimaka ma Mancy, bin umurninshi tayi, ta daga ta ta riko hannunta, ta ja ta, ba gardama Mancy ta bi bayanta.
Sosai mutane suka tausaya mana, ina jiyo muryar wani yana cewa "Me ya samu Gidan nan? Me ya samu jin dadi da walwalar Gidan nan" wani yace "ko nayi rantsuwa ba kaffara, wanchan ce, itace Ummul Abais" Wallahi DanMakaho Allah ya saka muku, Allah ya bi muku hakkinku".
Ba mu ce komai ba muka fita zuwa Gidan Yayanki, kan tabarman da suke zaune na kwantar da Dalo, na yi hanyar fita Mancy tace ma Yayanki donAllah kamo min shi, a wahalce take magana.
Mallam Muhammad yace ina zaka?" Zuwa zanyi ya gaya min dalili? Me muka mishi ya tsane mu, Mallam Muhammad Babanmu ya wulakanta mu gaban mutane, Babanmu ya daga hannu ya dake mu gaban mutane, me muka mishi? Me ya chanzashi".
"Zaid"
Mancy tayi kirana.
Na dan choge na tsaya tace "kazo ka zauna, donAllah, kana da Uwa, and i promise you, ba za ku bar Gidan Ubanku ba"
"Mancy, zaman me zamuyi ba kya ciki? Ta ya zamu fara rayuwa a Gidan nan ba da ke ba, Mancy kafarki kafarmu Allah".
Mancy ta girgiza kai, ta kawar da maganar "Maman Amira DonAllah kina da Panadol a ba Sadiya?".
Eh barin dauko mata, ta shiga Ciki, baban Amira ya bi bayan Matarshi.
Mancy ta matso kusa dani ta rik'oni tace "Stay Strong, kaine Gatan Dalo in bana nan".
"Mancy".
Ta katseni "Zaid, kayi min Alakawari, no matter what happens, ba zaka taba barin Gida ba, aure kawai zai rabaka da Gida, zaka kula da Sadiya, zaka kula min da kanku"
"Mancy"
"Zaid, DonAllah".
"Mancy, ba ki ga kallon da Baba ke mana ba? Ya tsanemu fa"
"Still Zaiduna, you wont leave home".
Kai na gyada mata nace "I wont leave home".
Dalo ta sha panadol, amma masassara ta rufeta, kinga yanda muka damu, lokacin Maghrib Yayanki ya sani Alwala don zuwa masallaci, na bar Mancy da Dalo tare da Antynki.
A waje sai kallona ake tayi, wai kinsan me nagani kofar Gidanmu? Labiba ta girgiza kai yace "Katuwar Mota nagani, tana kwashe kayayyaki wanda kallo daya na musu na san kayan dakin Mancy ne da nawa" nufansu nayi, amma yayanki ya rikoni tare da girgiza min kai, yace mu tafi Masallaci kaji?" Jikina rawa yake, idona ya ciko da hawaye, lallai baba yana son Wulakanta mu.
A gidan Yayanki muka kwana, daki daya ya bamu, Mancy tayi ta mishi godia, yace "haba Mancy, ai kowa ya san ke Uwa ce a Anguwar nan, duk me zamu miki ba zamu taba biyanki Alheranki ba".
Washegari Mancy tace "Zaid, Sadiya, yau zan koma Kano gidan Yaya"
Nace Mancy Dalo bata da karfin jikinta Masassara takeyi, ina zaki tafi ki barta? Ni ya zanyi? Mancy karki tafi? Kar ki juya mana baya donAllah, kar ki barmu, atleast not now, kina ganin korar da ya mana, na gya miki an fitar da kayayyakinmu tas".
Mancy tace "Zaid ya zanyi? Wa ke gareni duk dunia in ba Yayana ba? Ina zanje? Sakina yayi fa, saki 3, ina na nufa? Nan gidan zan ta zama? Ai ba zaiyiwu ba, kuna da Mahaifi, da ranshi, yanzu ba anjima ba zan raku Gida, nikuma na wuce, ina so kuyi hakuri da duk yanda rayuwa ta zo muku, donAllah kuyi hakuri, ina sonku sosai, fiye da rayuwa da kanta".
"Mancy"
Ta katseni tace "Zaid mun riga da mun gama maganar nan, dole ku koma Gidan ubanku, whatever happens he is still your Father, ku tashi mu tafi, so nake kafin karfe 11 in isa Kano".
Labiba banson ma Mancy gardama don wallahi a daren ranan bata runtsa ba, a kan idona tayi ta kuka, zuciyata ta karye amma sai nayi kamar bacci nake, banson ta sha wahalata shiyasa kawai na share, na rike dalo sosai ta ma Yayanki Godia, muka fita muka nufa Gida, dukkanmu gabanmu na faduwa.
Karfe 8 saura muka shiga Gida.
Da sallama Mancy ce me k'arfin halin Rafka Sallama.
Wata Yarinya da bata wuce saar Dalo ba ta fito daga kitchen tana mana kallon wulakanci, sai ga wani shikuma ya fito daga daki wanda nawa ne.
Hannayenmu Mancy ta ja, har cikin parlo, ta zaunar damu, Nasiha ta cigaba da yi mana.
Sallama aka sake yi muka amsa Yan Gidansu Babanmu ne, su Aunty Asabe da Baba Sani, Maza da Matansu, sun kai su 15. Wurin mu suka nufa, Mancy ta tashi ta taryesu da faraa, suko kallon tausayi suke mata.
Ina kwananku muka gaishesu, suka amsa Baba Sani yace "Maryama ashe abunda ya faru kenan? Wallahi sai yau da asuba wani