Showing 63001 words to 66000 words out of 133269 words
Chapter 22 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt
shine Zaid din da fara So ba, wannan ba Dan Makahonta ban, wannan wani ne daban, wannan shine MANKAS.
Da sauri ta juya ta shige cikin Gidan gudun ta tsaya gardama su ma Abu Sideeq wani abu, ba za ta iya dauka ba in har wani abu ya samu Abu Sideeq ba, bata san mai zatayi ba.
Abu Sideeq ido ya raina fata, jikinshi sai rawa yake, Zaid ya kalleshi cike da tasha yace "yan shaye-shaye ko? Uwar meke faruwa in ba a kula su ba? Kace me?" Shi dai Abu Sideeq ba bakin magana.
Zaid ya matso kusa dashi ya sausauta murya.
"Beebs Yarinyata ce, Beebs Tawa ce, kar ka sake zuwa inda take, wallahi ka sake zuwa Unguwar nan, hmmm, zan gwada maka Tudun Matawalle na Mankass ne".
Wuce su yayi tare da ma Master inkiya da su rabu dashi, Gidansu ya wuce ba tare da damuwan mutanen da ke kallonsu ba, afin kace wani abu Haruna ya finciko Abu Sideeq ya bashi mari kala Uku, ya gwada shi da hannunshi "kar ka sake taka k'afarka cikin Unguwar nan kanaji?" Abu Sideeq ya gyada kai da sauri.
Hannu Haruna ya sa cikin Aljihun Abu Sideeq ya zaro ya ciro kudin da ke cikin Aljihun dubu-dubu guda 7, Haruna da jajjayen hak'oranshi yace "mu raba? In dau 3 in baka 4?" Kafin Abu Sideeq yayi magana Master yace "dan uwarka mu fa?" Haruna yace "to kai Ware" da sauri Abu Sideeq ya hau Abun hawanshi ya burka ya bar unguwar a sittin.
Terror ya kalli Unguwar, cike tap kamar kallonsu suke kamar ana shooting film, yace "duk ku ware, ko in sareku magulmata" da sauri kowa ya dare suka bar wurin. Su ko suka wuce bencin Eskaley da murnan sun samu kudin siyan World.
Hannunta rawa yake tayi, safa da marwa take tayi, Aunty Aseey na toilet, hankalinta ya gaza kwanciya sai da ta lek'a ta k'ofa ta ga ba kowa wurin sai tsiraran mutane, ba su Mankas, gabanta ya tsananta bugu.
Chan sai gashi ta hango shigowarshi BQ, wurin ta tsura ma ido hawaye na neman kufce mata, shima tsayawa yayi yana kallonta idonshi cike da wasu abubuwa, wani abu yake ji game da ita da yake fizgarshi, dagaske yakeyi da yace "ita tashi ce, bai san ta yaya zata zama tashi ba, amma tabbas ita tashi ce shi kadai, dama kwanaki kadan ya rage mishi a duniya, zai kasance tare da ita kafin ranar rabuwarsu tazo, kafin tazo, in dai yana lumfashi, babu mamijin da ya isa ya zo kusa da Labs, ko tana so ko ba ta so, zai iya saran duk wani namijin da zai rab'i Beebs dinshi.
Wayarshi ya zaro ya tura mata text, tana kallonshi, yana kallonta ta bude message din.
"Saurayinki is fine, ya tafi Unharmed, ki gaya mishi, kar ya sake zuwa Inda kike, ke TAWA ce Beebs, You Are Mine alone, kin fahimta?".
Ba ta san wani sanyi na ratsata ba, sai da taji wani yanayi na neman rufeta, ba za ta so ya ga reaction dinta ba, kallonshi tayi ta galla mishi harara tare da buga wani tsaki ta shige daki.
Tana shiga ta fara latsar wayar Abu Sideeq amma wayar a kashe, duk ta damu, amma hankalinta ya dan kwanta da Mankas yace mata ya koma Gida ba tare da sun mishi komai ba.
Tsaye yayi ya bi bayanta da kallo tare da murzan idonshi ya wuce Cikin Gida.
"Kai Dan Makaho, mai nake ji ne a cikin Unguwa? Fada kayi da wani a kan Mace?" Mankas ya kalli Babanshi da ya shigo yana huci, be kula shi ba ya shiga kitchen don dafa indomie, sai kuma ya fasa, ya bude k'ofar dakin Dalo, ya ganta zaune jigum, murmushi ya mata tare da kashe mata ido daya, murmushi ta mishi, ya rufe mata k'ofa.
Baba da Aunty Shafa’atu na tsaye inda ya barsu, yazo zai wuce “Baba yace Don uwarka ba magana nake maka ba? Wallahi Zaid in ka nemo magana kar a sake a tunkareni a matsayina na Ubanka, duk wanda ya kawo min kararka zance kai ba dana bane a tafi da kai chan Police Station, shege har ka san yanda ake fada kan Mace”.
Wucewa yayi yaji Shafa’atu na cewa “ni tsorona Alhaji kar yayi ma Diyar Mutane Ciki, ka san halinshi” daga waje inda yake ya bude murya don ya tabbatar zata ji yace “Uwarki Zan Ma Ciki”.
Ihu Shafa ta sake, Alhaji ya bi bayan Zaid wai zai bigeshi yana tsinanshi amma ko a jikin Zaid ya buda daki ya shige ya rufe k’ofar a fuskar Alhaji Zaki.
Nan kamar an kunna shi ya hau bambamin Fada “Allah ya tsine maka Zaid, Allah ya k’untata maka yanda kake k’untata min da matata”.
A sukwane Labiba da Aunty Asee suka fito daga Daki, tsinuwar da yake mishi ba dadin ji, Aunty Aseey bata ankara ba, sai ganin Labiba tayi harta k’etara Gidansu Zaid”.
Da k’arfi Aunty Aseey tace “Uhm uhm Labiba”. Amma Labiba tuni tana gaban Baban Zaid da tunda ya ga Aunty Aseey ya ji wani irin mugun Kunya.
“Ina Wuni?” Alhaji Ali ya amsa mata da “lafiya lau” tace “Baba, sunana Labiba, ba ka san Bakin Iyaye halaka ne ga yaransu ba? Ka san tsinuwan Mahaifi ga yaro ba zai taba sa yaro ya dace a rayuwa ba? Shin baka san mugun alkaba’i na janyo halaka ga mutum balle dan da ka haifa? Shin baka son Yara amanar Allah ne a wurin Uwayensu ba? kuma tabbas Allah zai tambaye ka yaya ka yi kiwonsu, in rai ya baci hankali ke nemoshi. Magana mai dadi sadaka ce, in yau Zaid ya maka ba daidai ba, ka zaunar dashi kace “Zaidu Eh, ka min ka za kamin kaza ban so, don Allah ka bari” wallahi zai bari, in ka janyo shi a jiki a hankali zai shiryu, kai ka sa Dan Makaho ya kangare, tsinuwan da kake mishi ya bar damunshi, ya giga, wallahi duk mai zaka mishi yanzu ba zai dameshi ba, daga ranar da ka fara La’antarshi, daga ranar rayuwarshi ta chanza, ka samu gurbi Babba wurin durkushewar Rayuwarshi, kana da kwamasho Babba, Wallahi Baba Allah sai ya tambayeka”.
Juyawa tayi ta barshi tsaye a nan. Wannan Aljannace? Daga ina ta fito? Matar Muhammadu kadai ya iya ganewa, be son wacece ba. Maganganunta, sosai sukayi tasiri a ranshi.
Kanshi yayi nauyi yana barazanar rabewa biyu, wani irin yanayi yake tsintar kanshi a ciki, sosai maganganunta suka shigeta, tambaya daya kawai zuciyarshi ke wurgo mishi, MEYASA? Meyasa mene? Shine bai sani ba.
Na dan lokaci guda ya dawo daidai sai da ya ji muryar Shafa na cewa “taho Alhajina rabu dashi”.
Kamar robot da ake controlling da remote ya juya yace “ai da kin bari na lallasa shi, tsinanne”.
Zaid na ciki bai san wainar da ake toyawa ba.
Anty Asy tace “me kikace mishi Labeeba?” “Waazi na mishi Aunty, bai kamaya yana tsine ma dan cikinshi ba”
“Labiba ba yin kanshi bane”
“Yana iya yak’ar Asiri”
“Nidai Labiba da bakije ba, yanzu in yayanki ya ji fa?”
Labina ta yi gaba tace “shi yasa ba zaki gaya mishi ba”.
Aunty Aseey ta bita da ido.
Ran Labiba k’al ta shiga daki, wayarta ta shiga lalubar numbern Abu Sideeq, kamar dazu wayar kashe, zama tayi ta shiga rubuta message na ban hakuri a kan abunda ya faru ta tura mishi.
Shiko Mankas Wanka yayi ya zumbula Jallabiyarshi ya fita daga Gidan.
Alhaji Ali Zaki duk yayi wani sukuku, kamar mara Lafiya, wani iri yake jin kanshi, Hajia Shafa na lura dashi, ba ta san meke samunshi ba, amma zata sa mai ido ta ga iya gudun ruwanshi.
Bayan Maghrib Zaid ya shiga duba Dalo, ya ga Alhaji Ali zaune shi kadai a Parlo, har zai wuceshi yaji muryanshi na kiran ZAID. Chak ya tsaya saboda rabon da ya ji Babanshi ya kira shi da Zaid har mantuwa ta mance, ya dau seconds kafin ya juyo ga inda Baban ke zaune, daga inda yake ya hango wani abu mai wuyan fassaruwa a idon mahaifinshi.
K’afarshi ta mai nauyi, ya k’arasa jiki a mace.
“Zaid”
Ya k’ara fada wannan karon muryanshi cike da fargaba.
Hawaye ya cika idon Zaid, Hamdala ya farayi a zuciyarshi Mahaifinshi ya dawo daidai, duk da ya san Tashi ta k’are, atleast kafin ya bar duniya zai samu soyayyar Mahaifi.
Muryar Hajia Shafa ta chanza Mood din Baba nan da nan ya rikide kamar wanda aka jona ma Charge “Uban me kake so ka tasani gaba kana kallo?”
Runtse Idon da zaid yayi yayi daidai ta fitar hawaye daga idanunshi, for a moment, yayi zaton babanshi ya dawo hayyacinshi, har ya fara celebrating da zuciyarshi, ashe bai chanza ba, ba zai taba chanzawa ba in har matar nan na kusa dashi.
Kafin ta k’araso yayi saurin share hawayenshi, da yardan Allah Anamimmiyar matar chan ta bar ganin hawayenshi.
Dakewa yayi yace “Dama Maganar Dalo ne, ta gama makaranta, zaman gida kawai takeyi, so kafin ta samu admission, ya kamata ta fara wani abu, ko ta dinga zuwa koyon Dinki, ko cakes, ko wani abu dai haka, zaman Gida is depressing her”.
Baba yayi shuru yana kallon Hajia Shafaa, ya na jiram Go ahead dinta, aiko ta girgiza kai, yace “banda kudin enrolling dinta a ko ina”
Zaid yace “ni ina da kudin, kawai permission dinka nake so saboda fita zata dinga yi, kuma ka hanata fita”.
Hajia Shafa na son magana amma sosai take tsoron tashan Zaid sai ta rada ma Baba abu a kunne.
Baba yace “ Uban wa ya baka kudi? To eh din na hanata fita din, salon ta zubar min da mutunci ta ja min abun kunya, ka gama maidata karuwa ta je ta janyo min magana a waje”.
Zaid ya cije bakinshi tare da kallon Shafa’atu yayi k’wafa yace “In ba zaka bari ta fara training ba, ka bari taje hutu wurin Mancy”.
Shafaatu tace “a kan mene? Ba inda zata”
Zaid ya juya gareta yace “zan zubar miki da hak’ora Wallahi”
Baba yace “zo ka fara zubar min da nawa, DanMakaho wallahi ka fita idona”.
Tashi yayi ya bar musu wurin ranshi na soyuwa, ya san Dalo ta gama jin komai, be son ganin kukanta kawai ya fasa shiga wurinta ya fita daga Gidan Baki daya.
A B U J A
Mimi ke kwance Ruf da ciki tana buga game a wayar Mancy, a shekarunta ta iya bude wayar Mancy ta kunna game.
Wayar Mancyn ne ya fara ringing, ba tare da ta san waye ba tayi swiping ta amsa cikin muryarta da “Hello”
Kamar jira take ta fashe da kuka, “Mimi ina Mancy? Ki bata wayar” muryan addanta Dalo taji, Mimi ta fara kuka tace “Adda Dalo are you crying? Stop crying, barin kaima Mancy wayar” da kuka ta fita daga dakin tayi hanyar dakin Abbansu.
A babban Parlo Jawad ya ci karo da Mimi, kuka takeyi sosai wayar Mancy a hannunta, da sauri ya rage tsahonshi ya rungumota jikinshi ya na tamabayarta Lafia? Cikin kuka da muryarta na yara tace “Adda Dalo Is Crying” yace “Who is crying?” Maimakon ta amsashi sai ta mik’a mishi wayar, ganin DALO yayi a rubuce, kara wayar yayi a kunnenshi yace “Hello?” Dalo batayi magana ba sai sheshek’ar da takeyi, bata san waye ba, kawai sai ta kashe wayar.
Haka kurum ya samu kanshi da swiping wayar ya bude ya sake bin number da kira.
Ta dauka da Sallama, yace “Meyasa kike kuka?” Maimakon ta amsa sai cewa tayi “Ina wuni?” Daidai fitowar Mancy da Abba daga Daki, kamar mara gaskia Jawad ya tashi, kafin Mancy ta ankara wayarta ke hannun Jawad Mimi ta fara zubo zance.
“Mancy, Adda Dalo is crying out loud” Abba yace “a ina?” Jawad yayi saurin Mik’a ma Mancy wayar ta amsa, ta ga wayar is still on call, da sauri ta kashe tana murmushin yak’e tace “Dalo na da reason din kuka ne? Ai komai sai ta mai kuka” jawad dai ya yi gaba yana sak’a wani abu a ranshi.
Abba yace “Mancynsu, ko zaa ma Alhaji Ali magana ne? Ko hutu Dalo ta zo mana?” Mancy tayi jim tace “bari dai mu gani Abbansu,sai mutane biyu sun Amince” yace Dawa dawa? “Da Alhaji Alin, da kuma Hajia(Ummansu Jawad)” Alh yace “saboda gidanta ne?” Mancy ta girgiza kai tace “saboda tana da hakki” yace “shikenan zamuyi maganar” tace “to shikenan ina zuwa barin sa Mimi bacci” ta saba mimi a kafadarta tana babanta byebye, shi kuma ya zauna don kallon Channels.
Mancy na shiga daki tayi dialing numbern Dalo jikinta na rawa, Dalo na dauka ta fashe da kuka, Mancy hankalinta ya tashi, da kyar ta lallashi Dalo ta samu ta gaya mata abunda ke faruwa, ran Mancy ya baci, tace “kiyi hakuri Dalo, sharri kayan kwalba, Alhaji ya buk’aci zuwanki Hutu Abuja, all we need to do is convince your Father, inshaAllah zaki zo wurina, kuskurena daya da na k’i tafiya da ko kece, amma inshaAllah, komai zai wuce, zan samu Alhaji ya kira Babanku ya nemi alfarma gunshi, inshaAllah ba zai hana ba”.
Tayi ta lallashin Dalo, har sai da ta sa ta Daria.
“Mancy dazun waye ya karbi wayar daga Hannun Mimi?”
Mancy tace “Oh Autan Hajia ne, Jawad”
Dalo tace “Oh Okay”.
A haka suka cigaba da firan Uwa da diya har sai da Dalo ta sake, Mancy tace “Barinje gurin Alhaji” sukayi Bankwana.
K A T S I N A
10:45 pm duk sun kwanta, Aunty Asee ma dakin yau zata kwana saboda Baban Amira baya nan, Labiba ce ke chatting, tana ganin wayarshi ta yi ringing ta katse ta kara shigowa bata tabawa.
A karo na kusan Goma ya kira Wayarta a kashe, duk kiran da ya mata bata dauka ba sai ya zuk’i sigari, da ya ga abun na neman zautar dashi, ya fito waje kan Dakalin da suke waya.
Yafi karfin Awa daya zaune wurin, sauro duk sun cijeshi, amma ko a jikinshi.
Haka Ya cigaba da kiran Wayarta, Message ya tura mata.
“Ban taba Shan Giya ba, ban taba siyan Giya da hannuna ba amma yau na siya, Beebs, Ki na da Zabi uku, ko ki zo dakina yanzu, ko ni nazo dakinki yanzu, ko kuma na sha Giyar nan, kuma in na shata Alhaki a kanki, kina da ikon hanawa, in baki hanani ba, ko me ya faru, its on you, have your self to be blamed”.
Tirkashi, ta karanta message din ya fi so nawa, gabanta na faduwa, kar fa yazo dakin nan don yau harda Aunty Aseeyah, ya zata yi in ya zo?”
Message ya sake shigowa yana mai tambayarta “In zo ne? Ko zaki zo ne? Ko in sha giyar? Which is Which?”.
A ranta tace “to ya sha giyan mana ina ruwana? To kuma kar Allah ya kamata tunda tana da ikon hanashi ta ki hanashi kar ace tana da kwamasho, ko be sha giyan ba be da hankali yana iya zuwa dakin nan, kuma kar Aunty Asee ta farka ta samu wrong impression. Bata da wani zabin da ya wuce ta je ta iskeshi, cikin sando ta mik’e a hankali ta bude k’ofar ta fita a hankali.
Nanauyar ajiyar zuciya ya sake a lokacin da ya sanyata a idonshi, da taimakon hasken Farin wata ya ga fuskarta daure yake tamau wai ita fushi take, wani murmushi ya subuce mai daga baki.
Gyara tsayuwarshi yayi, a hankali take takowa gareshi, har ta iso gareshi ta tsaya a gabanshi.
Chan k’asar mak’oshi yace “Bibbbssss, KE TAWA CE”.
#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode
Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉
Babi na Sha Bakwai 1⃣7⃣
(K'AMSHI☺)
Cikin wata iriyar murya yace "K'AMSHI" Dariya tayi tace "Zaid dina ni kadai" hakan da ta fada ya sa shi tunawa da Labiba, da sauri ya waiga ya ga bata wurin da ya barta dazun, ya sake juyowa ga Yesmin yace "yaushe kika dawo?".
A tak'aice tace "jiya"
"Ba ki gaya min zaki zo ba?"y
"Ba zai zama zuwan bazata ba in na gaya maka"
Dan guntun murmushi yayi yace "K'amshi".
Itama murmushin tayi tace "Zaidun k'amshi".
Daga gefe ya ga travelling bag dinta yace "oh baki ma shiga cikin gidan ba?" tace "eh zuwana fa kenan" yace "okay kije, zan zo cikin Gidan, barin yi Sallah"
Gaba tayi tace "alright sai ka shigo" tafiya tayi ta bar wurin da k'amshinta kamar ko da yaushe, ciki ya shige shi kuma don yin sallah.
Daga Window Labiba ke lek'ensu, jikinta rawa yakeyi sosai, ranta ya sosu, kallon fuskokinsu ya tabbatar mata da cewa akwai tsantsar soyayya a tare dasu, "uhmm wannan itace Mai Aji? Gashi nan suna ta zabga k'walisa, dama ya na da kamar wannan mai zai yi da ita Mara Aji? Uhm su masu Aji".
Da k'yar ta bar wurin ta kabbara sallahr La'asar, zuciyarta na mata zogi.
Da sallama ta shiga Parlon duk suka hau shewa , Annah ta rugo ta rungumota "oyoyo Aunty Yesmin" itama ta rungumeta tayi "oyoyo Annahn Aunty Shafa" sukayi daria baki daya, "Dr Yasmin" Hudu ya fada cike da k'auna da Bege.
Murmushi tayi tace "Uncle Hudu muna lafia?" Ba ta jira amsar sa ba ta zauna kusa da Aunt Shafa tace "Aunty Ina wuni?" Shafa ta amsa ta na tambayarta mutanen Gidan.
Sunyi Minti 10 suna magana kafin Zaid ya shigo da Akwatin Yesmin.
Cewa yayi "K'amshi, ga Box dinki" da sauri ta tashi yan parlon suka bita da muguwar harara, tace "har kayi Sallahn?" yace "Yup" tace "sai ina?" yace "zan shiga na ga Dalo sai na dan fita".
Gaba tayi don zuwa dakin Dalo tana fadin "wai har yanzu Dalo baki bar zaman daki ba? Haba sai kace wata Mata mai Takaba?" Zaid ya rufa mata baya yana daria, a tare suka shiga dakin, aikam Dalo taji dadin ganin Aunty Yesmin dinta, Zaid yace "nidai ma fita, sai bayan Maghrib kuma" byebye k'amshi tace, dalo ta gyada mai Kai.
"Wai ke ba nace ki dinga fita parlo ki na zama ba? taso muje" da sauri Dalo tace "donAllah ki barni a wurin zamana, please" Yesmin tace "Waye yace daki shine wurin Zamanki? My friend taso muje Parlo inda mutane suke".
"Dalo tace banyi sallah ba" Yesmin tayi hanyar k'ofa tace "kiyi sallah ina jiranki kizo, in baki zo ba, ni zan zo". Dalo tace "Yes Ma".
Tunda ta fito daga dakin Dalo "Aunty Shafa take tarbanta da harara har sai da Yesmin ta zauna kusa da ita taja zabga murmushi.
Aunty Shafa'atu tace "Kinga Abunda ke hada ni dake kenan ko Yesmin? Na gaya miki ba ruwanki da yan iskan chan,