Showing 18001 words to 21000 words out of 133269 words

Chapter 7 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt

28 Dec 2024

13054

zo Gida, sai mu sake tautaunawa".
Hannunshi ya rike yace "Wallahi zanzo, kawai ka bani full address dinka." Alhaji Usman yace "ba damuwa".


Paper ya fallo a cikin Motarshi ya rubuta mishi Adireshin Gidanshi a Kano, shi ko Alhaji Ali hannu ya sa a Aljihu ya ma yara Alheri suna ta Godia, a nan ne kowanensu ya shiga Mota suka ma juna Oda kafin suka wuce.


Tunda ya zauna yake lumshe ido yana sake hasaso ma kanshi Maryama, haka Driver ya ta shatata gudu Alhaji Ali na ta begen Marayama a zuciyarshi.


Ya iso Katsina lafiya, sai da ya fara zuwa Gidansu ya gaida Mahaifiyarshi, kafin ya sauke mata tsarabar da yayi mata, ya ma Matasan Gidan Alheri kafin ya wuce Gidansi.
Shafa'atu ta tarbeshi kamar yanda ta saba, cikin shiga ta alfarma, suka rungume juna don sunyi kewan juna, sai da ta kaishi yayi wanka, kafin ta zubo mishi Abinci suka ci tare.


WasheGari, ya dauki hanyar Kano.


Alhaji Usman Aminin Alhaji Ali ne tun suna Makaranta, Maryama k'anwarshi ce, kasancewar Mahaifansu sun Rasu, Alhaji Usman ne ke rik'on Maryama tun bayan Rasuwar Mahaifiyarsu, yana kula da ita sosai don har makarantar Unguwanzomanci ya sakata(Midwifery).


Da Azahar suka karbi bak'uncin Alhaji Ali, Alhaji Usman yayi mamakin ganinshi, don beyi zaton zai zo nan kusa ba, lallai ya nuna mai dagaske yake. Abinci Matar A. Usman ta gabatar mai da shi, ya ci sannan ya gabatar mai da buk'atarshi,
Alhaji Usman yace "ba damuwa, shi dai ya bashi ita, kuma ya san yarinya ba zata bashi kunya ba, don Matsayin Uba yake a gunta" ya mik'e tare da cewa "bari ya turo mishi ita".


A daki ya isketa tana zaune kan wata kujera tana duba wani littafi, zama yayi a dan nesa da ita, tana ganinshi ta gyara zamanta tare da kulle littafin da ke hannunta.
"Maryama, ina so ki Saurareni, a Parlo, akwai abokina Alhaji Ali, wanda muka hadu jiya a Zariya a Masallaci! Na san kin ganeshi, to shine ya zo neman aurenki gurina, ni kuma na bashi ke, saboda na san kyawawan halaiyanshi, na san ba zaki watsa min k'asa a ido ba".


Shiru tayi batayi magana ba, yace "Maryama, ba dai bijiremin zakiyi ba ko?" da sauri ta girgiza kai tace "Yaya, kai ne Uwana kai ne Ubana duniya banda sama da kai, na san ba zaka zaba min abinda zai cutar dani ba, Nagode da zabinka gareni, Allah ya shige mana gaba". Da fara'a ya amsa da "Ameen, ni na san ba zaki bani kunya ba, ina Alfahari da ke Maryama, maza tashi, ki sanya Mayafi kije gareshi yana jiranki". Kanta a k'asa ta ciro Zaninta ta yafa ta fita waje.


Da Sallama ta shiga Parlorn kanta a k'asa, zama tayi a kan kujera daga farko, kafin ta dan rusuna ta gaisheshi, shi ko da kallon So da Kauna ya bita, ya amsa gaisuwarta cikin shaukin soyayya, a hankali a hankali ya ke tambayarta tana bashi amsa, sun dau lokaci suna zantawa, daga bisani yace "ta shiga ciki ta turo Yayanta".


Alh Ali ya gaya ma Alh Usman shifa ya samu Mata, ba bata lokaci yace "suje ya gabatar dashi wurin Kawun su".
Alhaji Ali be bar Kano ba sai da ya tabbatar an bashi Maryama.


Da farinciki ya koma Katsina, ya je ya sanar da Mahaifiyarshi yana neman Aure, ta sa mishi Albarka, Danginshi ko sunfi kowa Murna don su na son su ga gudan jininshi, k'ila Auren Rabo ne ke zuwa, nan fa aka fara shirin Biki.


Ba wanda ya sanar da Shafa'atu game da Auren.
Kudade ya biya masu dimbin yawa aka fara gina Mishi Katafaren Gida a wani Anguwa da kusan shi kadai ya fara Gini a wurin wato Tudun Matawalle,


Shafa'atu kuwa tausayinta yake sosai, yana shakkar gaya mata maganar Aurenshi, be so taji kamar zai kara aure ne saboda haihuwa, baya so ta ga kamar ya gaji da ita ne, baya son bata mata sam, karshe dai ya biya mata kudin Umra ta tafi Makka, kuma ya siya mata 190, a lokacin da wuya kaga Mace na tuk'a mota, amma ita ya mallaka mata Motar kanta, Bayan tafiyarta Makka ya samu ya fara shirin bikinshi a tsanake.


Ana saura Sati 3 Biki
Shafa'atu taje Gidan Surikanta da Akushi dauke da Tuwo Miyan Kubewa busassa dominos uwar Mijinta, tunda ta shiga ta ji gabanta ya fadi, da Sallama ta shiga k'urya, zaune k'annen Alhaji Ali suke su 9 suna diba kaya, da alamu lefe ne, akwati 2 manya, da fara'arta ta gaishesu, da Hajiyarsu, Hajiya ta amsa tana dan jin nauyinta, basu san zata zo ba.


Shafa'atu ta kallesu tace "to, lefe ne ake kallo? Karime wa aka kawo wa lefe bamu sani ba?" Karime ta dan kawar da kai gefe tana yak'e ta rasa me zata ce mata, Shafa'atu ta sa hannu tana daga kayayyakin tana gani tana yabawa "wai Kayan waye? Wa aka kawo mawa?" Ladidi tace "wa dai zaa kai ma wa ko?"


Karime ta zungurota da hannu, da yake Ladidi ta fi ki jinin Shafa'atu tace "har sai yaushe zaa boye mata? Ke Shafa'atu lefen Yayanmu ne, za'a kai Kano Gobe in Allah ya kaimu" Shafa'atu da dan yak'e a fuskarta tace "Ahh, Yaya Shehu Aure zai sake? Waiyo Allah shi kaimu, ashe muna da biki".


Ladidi tace "Iyeeee, wato Shehu kadai ne yayanmu? To babban Yayanmu nake nufi" Hajia tace "Ladidi kiyi shiru" Shafa'atu da bata fahimci komai ba tace "bangane ba, Babban yayanku? Wanne kenan?" Ladidi tace "baki gane ba? To Yaya Ali nake nufi" tsalle Shafa'atu tayi ta dire tace "Ba ku da hankali, kun ga dai bana san irin wasan nan" Asabe tace "wake miki wasa? Tunda kin kasa haihuwa, zaa auro me haihuwa".


Karamin bori Shafa'atu ta hau, ta hau facali da kayan cikin Akwatunan, kafin ta wawuri Akushin Miya ta bude Miyan ta juye a jikin kayayakin, nan suka yo kanta, ta dire ta yi kan Hajiyarsu. "munafuka, ke kikace yayi aure ko?" aiko su Ladidi sukayo kanta, suka hau dukanta wai ta zagar musu mahaifya da k'yar Hajia ta hanasu dukanta, har tace "zata tsine musu in suka sake bugunta"


Ina bakin shafa bai mutu ba, ta dinga surfa musu Zagi, tana laantarsu, tana cewa itace Ajalinsu, shegu k'azamai, talakawan banza, duk kyautata muku da nakeyi? Ni zakuyi wa butulci, biye nake da ku kamar na muku sujadda shine zaku saka min da wannan? Aiko zaku sha mamaki, ayi auren mu gani, ta fita fuuu, ko zaninta bata dauka ba, ta ci karo da Ali a hanya ko kallonshi bata yi ba ta fada motarta ta danna a guje, Ali ya ji gabanshi ya fadi. Ya shiga Gidan da sauri


Hajia ce tace "ta ga kayan lefen ne, ka bita ka lallasheta" kallon kayan yayi yace "meye wannan kamar miya?" Ladidi ta chafe tace "Wai baka ga ruwan wulakanci da tayi a gidan nan ba, har ta na zagin Hajia, kanta farau kishiya?" ran Ali ya baci yace "Ta zageki Hajia?" Hajia ta girgiza kai tace "aa ba fa ta zageni ba ladidi" tana wurgar Ladidin da harara, kai dai ka je ka san me za ka ce mata kasan mata ba sa son Kishiya.


Tashi yayi jiki a sabule ya nufi Gida, ya jima a bakin gate kafin ya shiga, zaune ya ganta har ta bashi tsoro don ta ci kuka har ta gaji, k'arasawa yayi a tsorace, be san ta inda zai fara ba, yana karasowa ta ci kwalarshi, tana jijigashi tana dukanshi ko ta ina, ni zaka yaudara Ali don kayi kudi, ni da nake zaune da kai tun baka da komai, ni zaka ci amanata Ali? Kasa magana yayi, ya kasa motsi, ta cigaba da dukanshi kafin ta fashe da wani irin kuka, rungumeta yayi tsam tun tana motsi har tayi lamo a jikinshi tana mayar da ajiyar zuciya, sai da ta daina motsi kafin ya soma magana.


"Shafa'atu na san ban kyauta miki ba da na boye miki maganar Auren nan, amma ki san cewa ina sonki fiye da zatonki, duk wata Macen da zan aura a bayanki take, kar ki manta irin Son da nake maki, ki dauka wannan Auren k'addara ce, ki bani goyon baya nayi auren nan, wallahi ba zan taba wulakantaki ba, wallahi Shafata kin fi karfin wulakanci a wurina, Shafa'atu ba ayi macen da take karshena da zata wulakantaki ba, in naga ba zata girmamin ke ba, wallahi ina iya rabuwa da ita, ki taimaka min" abun mamaki hawaye ta gani kwance a idanuwanshi tana son Mijinta sosai, kalamanshi sun darsu a zuciyarta, bata da wani zabi illa ta danne zuciyarta.


Bayan ta gama kumburinta ta sauko, hakan ya bashi kwarin guiwa ya cigaba da sabgarshi, amma walwalarta sam bata dawo ba, da tsanar danginshi da ya darsu a ranta, danne zuciyarta kawai take.
***.
Ba wai don tsoronta yake ba kawai don a zauna lafiya ya sakar mata ragamar bikin gaba ki daya, sai yadda tace ake yi, harta dakin da Amarya zata zauna ita ta za bar mata, ya so ta ba Amarya daki biyu, amma tace nata ne kawara daya ne na amarya, be damu ba don ya san da ya gama gininshi zasu koma sabon Gida kowa da Dakinshi da Parlornshi, shiyasa be ce mata komai ba.


A ka zo jere, da katifa da kujera da kayan kitchen duk aka jera a daki daya kasancewar dakin k'ato ne.


Tun daga jere dangin Maryama suka gano matsala daga gun Abokiyar zaman Maryama, amma basu ce komai ba gudun sa mata tsoro da fargaban kishiya, kuma sun lura Dangin Ali na son Abun.


"Kinsan Shafa'atu, ki bi a sannu, kinsan Mijinki yana daidai gwargwado gurin kyautata miki, to in kika faye zak'ewa kika kureshi, zai bar bi takanki, ke dai kawai ki bi ta bayan fage ki kori amaryar nan, ki mata zagon k'asa, kishin mimik'e zakiyi, kar ki yarda a gane ba kya sonta kin gane?" ta jinjina kai tana kwasan karatu gurin Aminiyarta Hajiya Er Rabi,


Nan ta kwantar da kai ta bi har Gidansu Hajiar Ali ta basu hakuri, kan haukan da tayi sharrin shaidan ne, Hajia tace ba komai ya wuce dama an san mata da kishi, balle ita da aka boye mawa.


Jumu'ah na zuwa aka daura Auren Alhaji Ali Zaki da Maryama Adamu a garin Kano ta dabo, an kawo Amarya dakinta.
Uwar Dakinta Matar Yayanta ta dade tana jadadda mata nasihan da yayanta ya mata, kafin suka bar Katsina, Maryama ta sha kuka kamar idanuwanta zasu fadi.


Murmushi ya mata yace "nagode Allah ya miki Albarka Maryama"
Shafa'atu kamar ta fashe amma sai ta hau yak'e tace "bari ta dauko musu Abinci".


Da sauri ta mik'e ta fice hanyar kitchen, Ali ya dinga bin Maryama da kallo ita ko kunya ma yake bata.
Tare sukaci abinci kafin suka gama, Shafa'atu tace bari ta shiga ciki ta musu sai da safe.


Shiga daki tayi ta dinga gwala kanta a bango, tana kukan bakinciki, anya hanyar nan mai bullewa ce? Anya zata cigaba da nuna komai lafiya lau ne alhalin ba haka bane? Gaskia da sake.
Su ko maaurata tuni suka shige dakinsu.


A GURGUJE


Bayan wasu 'yan Satittika


Zaman lafiya suke kadaran kadahan, Maryama dama sanyi gareta, biye take da Shafaatu, sun raba kwana bibbiyu, ko wacce burinta ta zama tauraruwa wurin Mijinta, sosai Shafa'atu ta danne zuciyarta don su zauna lafiya da Maryam, barin ma da ta ga bata da matsala.
****
Ta gane tana da ciki, saboda sauyin da ta ji jikinta nayi, bata ce ma kowa komai ba ta cigaba da harkokinta.
Sosai Mijinta ke nuna mata k'auna, a gaban Shafa'atu ya kan nuna kawaici, amma in suka kebe kamar ya hadiyeta.


Sannu a tashi alamun Ciki ya fara bayyana a jikin Maryam, tara miyau a baki, da amai in taji tashin zuciya, daga Shafa'atun har Alin ba su dago cikin bane don ba sani sukayi ba.
Ita dai Maryam ta san ciki ne da ita, in ta fara kwarara Amai kamar ta amayo hanjin cikinta.


Wata Rana Hajia Er Rabi, k'awar Hajia Shafa'atu tazo gidan, Maryam ta fito don gaisheta, kallo daya ta mata ta san cewa tana da shigar ciki, da ta shiga ciki, tace "kawata, ashe mutuniyar har ta dau ciki" Shafa'atu ta mata kallon rashin fahimta. Er Rabi tace "kar ki ce baki san tana da ciki ba?" ta dan zamo daga kujera tace "kar ki ce man ciki gareta, wallahi ban sani ba, shima Alin bai sani ba" Er Rabi tace "lallai kam, ban yi mamaki ba don ko bari baki ta ba yi ba, ba ki san yanda ake gane ciki ba, to Kishiyarki Ciki ne da ita".


Dam gabanta ya fadi "yanzu Maryam ciki ne da ita? Bata gaya mani ba?" Er Rabi tace "ke ya ma fi haka, kinga yanzu da kika sani, sai mu 6arar da cikin ba tare da kowa ya sani ba, balle mu shiga zargi" ido ta zaro tace "a barar da shi fa kika ce?" ta girgiza kai da sauri, tana da kishi sosai amma rashin imaninta bai kai nan ba, ta san Mijinta ya dade yana neman haihuwa, kuma amfanin Maryaman kenan ta haihu, bata ji dadin cewa ba ita zata haifa ma Ali 'ya'ya masu kama dashi ba, amma ba za ta taba halaka dan Cikin Maryama ba.


Ta kalli k'awarta tace "ba wannan maganar, duk da bana so ta haihu, ba abunda zan mata gaskia, Cikin Mijina ne, farincikinshi nake so, don gaskia be rageni da komai ba" baki sake take kallon Shafa'atu tace "lallai Shafa'atu, kina tafka wauta, wayace miki Dan Miji Da ne? Kinga zaki tafka kuskure, a duk ranar da Maryama ta haihu musamman Namiji ti kashin ki ya bushe, ba mai kara kallonki da daraja, ke ce Uwargida, amma gida zai koma nata. Dangin Mijinki kuwa dama sun tsaneki da ta haihu sunanki abar tausayi".


Hajiya Shafa'atu tace "nidai gaskia a bar maganar zubda cikin" Er Rabi tace "an bari, amma zakiyi kuka da kanki, ni kinga tafiyata" ta mik'e ranta a bace "haba kawata ina zaki?" tace "yo zaman me zanyi? Ana gwada maki annabi kina runtse ido".


Hajiya Er Rabi ta fita, Shafa'atu ta bi bayanta tana magiyar ta tsaya amma tak'i.


Da daddare wurin cin Abinci, suna zaune su uku kamar yanda suka saba, Shafa'atu tace "Alhaji, Albishir ne dani me zan samu" ya tsaya da cin tuwo ya kalleta yace "Shafata duk abunda kike so zan baki, gaya min" Maryama ta zuba mata ido, tana tunanin abunda Shafa'atu ke tafe dashi, murmushi tayi tace "Maryama Ciki gareta, akwai danka a Mahaifarta" mamakin ya sa Maryama kallonta, shi ko Gogan wani Yammm yaji a kunnenshi, ba zai iya fasalta abunda yakeji a tattare da shi ba a cikin wannan lokacin, duk suka zuba ido don ganin halin da zai shiga.


Mamaki ya basu duka, da k'yar yayi murmushi yace "Allah Sarki, to Allah ya raba lafiya" ya mik'e tare da cewa bari ya wanko hannunshi, Shafa'atu ta bishi da ido, a matsayinshi na wanda baa taba mishi irin wannan Albishir din ba, tayi mamakin yanda ya karbi zancen, to ko baya son Haihuwan ne shiyasa bai taba mata k'orafi kan rashin Haihuwar ta ba, tunaninka da yawa suka darsu a zuciyarta.


Ita ko Maryam ba ta ji dadin yanda Mijinta ya karbi Zancan ba, ko da ace ya saba haihuwa aka ce tana da ciki ya kamata a nuna farincikinshi, ita da take da burin haihuwa duk shekara don ta cika mishi Gida da 'ya'ya, amma ba komai, ta tashi ta kwashi kwanonin ta kai kitchen ta dauraye kafin ta koma daki.


Alh Ali Zaki na shiga dakinshi ya fada kan Kujera tare da fashewa da wani irin kuka, kuka ne mai dauke da ma'anoni da dama, shi ne Zai haihu? Shi Allah ya azurta matarshi da ciki? Shekara fiye da bakwai da aure? Yau shi matarshi ke da ciki? Farincikinshi ba mai fassaruwa bane. Alwala yayi ya jera nafilfili don nuna farinciki ga Allah SWT.


Watanni sun shude


Tun Safe ta ke jin nak'uda, amma sai ta daure, ganin ciwon na k'aruwa yana sake yawa ya sa ta fitowa ta kwankwasa dakin Shafa'atu tana cije baki.


"Yaya Cikina kamar zai balle, mutuwa zanyi" da sauri Shafa'atu ta kamota tace "gashi Alhajin be nan, ko zaki sake daurewa har ya dawo?". Maryam ta riko hannunta tace "ki taimakeni, wallahi mutuwa zanyi, nidai ki kira Unguwanzoma".


Kamar daga sama sukaji Sallamarsu Ladidi da Asabe, Shafa'atu ta manta rashin jituwarsu ta karasa gunsu tace "yauwa ina jin Maryama nak'uda takeyi" Ladidi tace "to da me zaki mata? Ke zaki karbi haihuwar ki danna kan yaro ya koma?" ran Shafaatu ya baci "ai da banson a haihun da tun lokacin da take da ciki na barar da shi" Ladidi tace "ai ko ba ki fada ba na san bakincikin cikin nan kikeyi, to ta Allah ba taki ba, sai an haifeshi munci moriyar Magajin Yaya Ali da yardan Allah". Asabe tace "kinga muje mu taimaka mata, tana cikin mawuyacin hali".


A daddafe suka kaita dakinta, haihuwar ce dama, bayan yan mintuna ta santalo danta jazur dashi, bayan Ladidi ta gyara Da da Uwan ta aiki Asabe zuwa chan GidanGandunsu taje ta fadi haihuwar.


Shafa'atu na nan tsaye gefe tana jin kukan jariri tsoro ya mamayeta, kasa shiga dakin tayi sai ta wuce dakinta ta fashe da wani kukan da bata san ko na meye ba, fargaba ne fal ranta.


Kamar daga Sama sai ga Alhaji Ali da Kanenshi, yana Gidansu Asabe ta je ta fado haihuwar, Shafa'atu na jin muryan Mijinta ta fito waje,
"Alhaji sannu da dawowa" be ko kalleta ba ya wuce ya barta tsaye, gabanta ya fadi, me kenan? Ta tambayi zuciyarta, bayanshi ta bi da ido, kafin ta rufa mai baya.


Yana shiga ya amsa Jaririn daga hannun Ladidi ya rungumeshi tsam a k'irjinshi, tsigar jikinshi suka mimike, wani yanayin da be taba shiga irinshi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login