Showing 51001 words to 54000 words out of 133269 words

Chapter 18 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt

28 Dec 2024

13069

Ta yaya ta iya fada mishi haka? Wani irin guts ne da ita? Karfe sha biyun dare? Ta yaya ta iya kallonshi har cikin kwayar ido tace mishi tana sonshi? Wace irin Macece? A ina aka taba haka? Haka sukeyi a Kudu? Tambayoyi ya ta ma kanshi.


Daga bisani kuma Ranshi kuma ya soma baci, don me za tace mishi tana Sonshi? Don me zatace dagaske take sonshi? Ko zolayarshi takeyi? Was she mocking him?" Hannu ya sa a cikin tulin sumanshi ya zube kan Gado don yin bacci, sai dai me? Tunanin Labiba da kalamanta ba su bar zuciyarshi ba.
Asuba ta gari
ZaiLab
*****


Alhaji Abu Shamsu na Tuk'i cikin kwarewa da iyawa, a lokaci guda yana taya Mamanshi da kawarta fira, a wani bangaren kuma yana daga kai ya kalli madubi daidai saitin Maryama da ke ta kuka a hankali.
K'awar mamarshi ta juyo tace "Ki bar kuka Maryama, ki gode Allah wallahi da bata nakasa ki ba, kishiya ai bala'i ce, nima haka na sha wahalarsu, aure na 4 duka banji dadi kishiya ba, amma da nayi hakuri, wallahi gashi na ci ribar hakuri".


Hajiya tace "kiyi hakuri, na san tunanin yaranki ke damunki, inshaAllah ba wata damuwa, kin ba Allah ajiyarsu shi zai kula miki dasu, ki kwantar da hankalinki kije kiyi Iddah ki samu miji kiyi aure.


Mancy dai murmushi tayi ba tace musu komai ba, suka dinga tafia har suka isa Kano, Unguwar Yayanta ta fada, da kwatance suka isa har Gidan Yayan, an ci saa ya na nan ta shiga Gidan, suna ganinta duk suka tashi, Matarshi ta rik'ota.
Maryama Lafia? Mun ga motar kaya akace daga Gidan Alhaji Zaki, shin Lafiya?" Wani kuka ta fashe da shi wanda ya tada hankalin Yayanta Umar da Matarshi.


"Yaya Baban Zaid ya Sakeni, Saki uku ya min Yaya" a tare suka rafka salati "Maryama me kika mishi?" A gurguje ta basu labari, sosai suka jinjina ma lamarin, ran Yayanta ya baci, har yana ikirarin sai yaje Katsina ya ma abokinshi rashin mutunci.


Hakuri ta hau bashi tana gaya mishi ba yin kanshi bane, sannan ta tuna mutanen da ta bari a waje, da sauri ta mike tace ba ita kadai bane, Yayan ya fita ya isa gurinsu Alhaji Abu Shamsu, Maryama ta shigo da Hajia da kawarta, ta basu ruwa a buta suka kama ruwa sukayi Sallar Laasar.


Alhaji Abu Shamsu ya ba Yaya Umar baki, ya mishi nasiha, Yaya Umar ya ji dadin dattakon Alhaji Abu ya mishi Godia sosai, ya tambayeshi in shi dan Kano ne, Alhaji Abu yace "Abuja yake da Iyalinshi, sun zo bin Jirgine zuwa Abuja don Mamarshi ba zata iya zaman Mota ba daga Katsina har Abuja, sai kuma kawar mamarshi da zasu aje a Rijiyar Zaki, Yaya Umar ya jinjina kafin suka dan yi fira, sukayi musayar number kafin suka musu Sallama.


Bayan tafiansu ne tayi wanka ta yi sallah, ta kulle kanta a Daki ta cizga kukanta son ranta, Yaranta sune damuwanta, wani hali suke ciki? Bata ma son sani, ta fi so ta yarda da cewa suna nan lafiya lau, bata son ta karaya har ta kirasu su ma ta karya masu da zucia don tana da htabbacin in har dai ta kira daya daga cikin Dalo ko Zaid to shakka babu sai sun sa kuka, har ta biye musu ba za a samu mai lallashin wani ba daga cikinsu, nan ne ta dau alkawarin kashe wayarta har sai ta samu natsuwa a cikin ranta.


Bayan Wata 5


Har ta gama Iddah bata nemesu ba, duk da Yayanta yayi ta rokonta kan ta rok'esu amma ta k'i, ko Zaid ya kira ta wayan Yayan yace a ba Mancy kin k'arba takeyi.
Haka ta kasance a Gidan Yaya Umar, ta na k'okarin ganin cewa ba ta zauna cikin damuwa ba, yaran Yayanta na debe mata kewa, har tau bata kunna wayarta ba, yanzu so take ta fara ko da neman aiki ne dama da kwalinta na nursing, dama shi Alhaji Zakin ne yace be yarda da aiki ba shiyasa batayi ba, yanzu ko dole ta nemi aiki don ba za ta zauna haka ba.


Gabaki daya suke zaune a Parlon cikin Gida, wayar Yaya Umar yayi Ringing, cirowa yayi daga Aljihunshi ya ga mai kiran.
Alhaji Abu Shamsu ne.


Bayan sun gaisa ne yake sanar mishi da cewa ai yana kofar Gidanshi.
Zumbur Ya Umar yayi "Ah aha, ka ja zance da yawa, ga ni nan fitowa". Ya kallesu yace "Bak'o mukayi, Alhaji Abu Shamsu ne".
Mancy da Matar Yayanta suka kalli juna suna neman karin bayani, amma yayi gaba don shigo dashi.


Parlornshi ya kaishi, suka gaisa sosai sukayi firan bayan rabuwa. Yaya Umar ya tambayeshi yaya Mahaifiyarshi? Ya sanar dashi cewa ai har ta gama hutun a Abuja tana Katsina, yanzu ma daga Katsinan yake yaje gunta.
Yaya Umar yace "Allah sarki, Allah ya ja kwana". Alhaji Abu ya amsa da Ameen.


Shiru suka danyi kafin Alhaji Abu yace "Alhaji Umar ina Maryama?" Da murmushi yace "aff kaga na shafa'a ban kirasu kun gaisa ba".
Yace "bakomai, dakata dai kaji Alhaji Umar, tun tuni na so zuwa Gidan nan amma na dakata saboda Maryama na cikin Iddarta, na yanke hukuncin zuwa bayan Iddarta shiyasa na zo yau, hak'ikanin gaskia tun randa muka dawo da Maryama take cikin tunanina, na tausaya mata, kuma ina son Aurenta in har zata amince dani".


Yaya Umar da murna yace "me zai hana in har Maryama ta amince da kai, barin turo maka ita dai ku tautauna in har ta amince sai ayi wallahi" Alhaji Abu Shansu yaji dadin hakan ya gyara zamanshi shi kuma ya shiga ciki.


Maryama dauki ruwa kikai parlo, akwai bak'o na nan na jiranki. Da mamaki ta kalli Yayanta tace "Yaya Bak'o kuma? Daga Ina?". Murmushi yayi yace "Yi Maza kije Maryama, ya na jiranki".
Mik'ewa tayi ta shiga kitchen don hado tray dama akwai Hijab cikinta straight parlon Yayanta tayi, tun daga k'ofar Parlon take jin wani daddan kamshi, nan gabanta ya shiga dukan uku-uku, kafanta yayi sanyi amma haka ta shiga da sallama, ganin mutumin da ke zaune ne ya sata karasawa cike da mamaki, amma sai ta dake ta fara mai murmushi.


Gaishe da shi tayi sosai da faraa a fuskarta, ya amsa shima cike da jin dadi, tambayar Hajiarsu tayi ya gaya mata tana Katsina lafia, shima tambayan mutanen gidan yayi ta amsa da Lafiyar kowa lau.
Shiru suka danyi kafin yace "Mancy"
Da sauri ta dago kai ta kalleshi cike da Mamaki, murmushi yayi yace "haka naji Zaid ya ce miki rannan a Gidan Sarki".
Sadda kanta tayi tana wani murmushi sakamakon irin kallon da Babban mutum kamar Alhaji Abu yake mata.


"Nasan zuciyarki na cike da tambayoyi kan me ya kawo ni ko? Ba tare da bata lokaci ba Mancy, so nake na shiga cikin jerin Zaurawanki don neman Aurenki, hak'ika bayan rabuwan mu na kamu da sonki duk da a farko tausayinki nakeyi amma daga baya na lura So ne, shiyasa ko da na ba Mamata labari ta karfafa min guiwa kan na nemeki".


Mancy tayi shiru ta cigaba da wasa da yatsunta.
"Uhmm?"
Ta dan dago tace "ni yanzu har wani aure zanyi? Ina da kamar Zaid? Sai dai in jira aurenshi".
Yayi yar daria yace "Shekararki nawa?"
Dan turo baki tayi tace "43" murmushi yayi yace "duka nawa kike? Ni ina da 65 shekarun babban Dana 32, amma bance na tsufa ba sai ke? Kuma ni fa ban ma yarda kin kai ko 25 ba".


Dariya ya sata sosai tace "Shekarun Zaid fa kenan".
Ji yayi ta sake burgeshi, har ranshi yake jinta cikin sanyin murya yace "Maryama, mu ba yara bane, bakiyi tsufa ba, koma kin tsufan nikam gani nakeyi kamar yar shekara 18 kike, ina so naji ta bakinki, in baki amince dani ba ba zan miki dole ba".


Shiru tayi ba tace komai ba
Ganin Shirun na neman yawa ne ya sashi cewa "ina iya baki Lokaci, kiyi shawara kiyi tunani, har zuwa jibi da nake shirin komawa Abuja".
Tace "to shikenan nagode".


Ba jimawa ya mata bankwana sukayi sallama ta shiga ciki ta ma Yayanta magana ya koma wurinshi ya rakashi har Gate ya sake jinjina mai dagaske yake sonta yake da Aure.


Da daddare ne Yaya Umar Ya kirata suka yi maganar Alhaji Abu Shamsu, Shawara ya bata a matsayinshi na Yayanta, yace "kar ta dakusar da kuruciyarta, kar ta manta Alhaji Ali saki Uku ya mata in ma tana tunanin koma mishi ne, tace "haba Yaya, tana sonshi amma wallahi ya fitar mata a rai, ba ta tunani ko aure ta sake ta fito zata iya sake aurenshi, ta hakura dashi" yace "to Ina ganin ya kamata kiyi tunani kan Alhaji Shamsu, ba zan miki dole ba, amma kar ki bari Alhaji Abu Shamsu ya subuce mata".
Godia tayi ta tashi ta koma dakinta.


Ta san ba zaiyiwu tayi ta zama a gidan Yayanta ba, duk da Uwa daya Uba days, yau da gobe sai Allah, Alhaji Abu baida wani aibu a zahiri, Zuciyarta tayi ta karanto mata shawarwari, har tayi naam da Alhaji Shamsu.
A ranar da zai tafi ya dawo, nan ta mishi Albishir da ta amshi bukatarshi, sosai ya nuna murnan shi, yace "zai basu Wata Biyu su Fahimci Juna, kuma ya na fatan suyi Bincikenshi kafin nan don da Wata biyu ya cika zasuyi Aure. Ita gani take kamar anyi gaggauwa amma shi cewa yake bata lokacin me zaayi.


Haka Alhaji Abu Shamsu yake zuwa Kano duk bayan Sati bibbiyu, har Mancy ta sake jiki suka shak'u sosai, suna fahimtar juna a lokaci daya kuma Yaya Umar na binciken Alhaji Abu Shamsu.


Wata rana suna tsakar Gida suna Zance kan Carpet, Alhaji Abu yake ce ma Mancy, in sunyi aure ta karbo su Zaid, Mancy tayi murmushi tace aa su yi zamansu a chan abunsu, yace "wai saboda me? Tace haba ina zani da manyan yara kamarsu? Dan shekara 25 da 'yar shekara 16?" Yace " to menene? Zan dauki nauyinsu, zan kula dasu a matsayin nawa" tace "aa Alhaji, ka barsu wallahi nagode sosai". Yace "to a dauko Macen" tace "aa ba wanda zaa dauko cikinsu, zasu dinga zuwa mana hutu". Ya juya kai cikin rashin jin dadi yace "to shikenan".


Ba su san shigowan mutum ba, sai dai suka ganshi tsaye kansu, hawaye ne ke kwaranyowa daga idanuwanshi, duk yayi bak'i ya rame ya jeme.


Da sauri Mancy ta mik'e zata rik'oshi yayi saurin yin baya kamar wanda wuta zai taba.
Alhaji yace "lafiya wanene ne wannan?"
Baki na rawa Mancy tace "ZAID".


Alhaji da faraa yace "Mallam Zaid muna lafia?".
Ba tare da yace ma kowa komai ba ya juya zai fita daga Gidan.
Mancy ta bi bayanshi tana kwala mai kira amma yak'i tsayawa.
Murya a kausashe tace
Zaid Aliyu Zaki kar ka sake ka fita daga gidan nan.


Chak ya tsaya. Ta taka har gabanshi ta tsaya tana kare mai kallo, idanuwanta suka ciko da hawaye amma sai ta dake, hannu ya sa zai murza idonshi ta rike hannunv.
"Baka ganni da bako bane Zaid?".
Juyawa yayi ya karasa inda Alhaji Abu ke tsaye yace "Ina Wuni?".


Alhaji Abu Shamsu ya amsa da Fara'arsa. Zaid ya juya ya kalli Mancy kafin ya dawo da dubanshi wurin Alhaji Abu yace "Daddy, ka aureta ka tafi damu Gidanka DonAllah".
ZAID mancy ta fada a kausashe.


Alhaji Abu yace "zan so hakan Zaid, zan so na hadaku da nawa 'yayan, kuma 'yayane, InshaAllah zan ga hakan ya faru".
Mancy tace "to lallai ka manta da maganar Aurenmu, na fasa ba zanyi ba kuma".


Alhaji Abu ya rikide yace "haba Maryama mai yayi zafi? Kiyi hakuri, dama ai sai da amincewarki zan daukesu, kiyi hakuri, ni niyyata masu kyau ne". Da sauri tace "Allah ya baka ladan Niyya, amma zasu tsaya Gidan ubansu" "Faqat".


Wani murmushin takaici Zaid yayi yace "Mancy, kina son mu kuwa? Mancy? Wace irin Uwa ce zata dafkar da Yaranta kamar wasu kayan wanki, ta tsallakesu ta yi tafiyarta, ta k'i waiwayonsu, ta ki nemansu? Ko sun nemeta ta guje musu? Mai muka miki? Ko mai na miki? Mai dalo ta miki? Eh Mancy?"


"ZAID mu shiga ciki mu gaisa ya kake?" Ta na mai nuni da Alhaji Abu da ke tsaye da Ido.


Bai damu da ba su kadai bane ba, yace "Mancy,kika tafi kika barmu, bai isheki ba, kika kashe wayarki baki neme mu ba, Mancy Mu kira Baba Umar, ko su Walid da Ummi, su baki wayar ki kashe ki ce zaki neme mu, baki taba neman mu ba? And now zaki ce min Ya nake? Really Mancy? Ya nake? Do i look alright to you? Bakiga nayi bak'i na rame ba? Bakiga na k'azance ba? To na ma fi kyan gani kan Dalo, ita in kika ganta so daya ba zaki so sake daga ido ki kalleta ba, saboda rama".


"Mancy Gidan Ubanmun da kike ta ik'irari bamu da wani gata ko galihu, Idi yafi mu matsayi a Gidan, Mancy ba wahalar rayuwar da ba ma gani, ba kallar Sharri da kazafin da baa mana, Mancy me muke ci a Gidan Uban da ba zaki bari a dauke mu ba, nan Kano zanzo sai da naci bashin Naira dubu daya wurin Eskaley, Mancy kamar ni yau ni ke ci bashi? Huh. DonAllah ki firda mu daga wannan k'angin, ki tafi damu duk inda zaki, Babanmu ba sonmu yake ba ba zai damu da duk inda zamuje ba, bai k'i mu shiga dunia ba, think of our Future wanda nawa ya fara rugujewa, da kanshi wanda kike son Aura ya miki tayin daukar mu amma kin hana, wai saboda me? Anjima sai kice kina Sonmu, kalar soyayyar taki kenan?".


Ganin yana magana ba tare da ya tuna wa yake ma magana ba ya sa ta daga hannu ta mareshi.
Dakata wa yayi tare da matse kuncinshi.
"Har Gobe, har abada ni Mahaifiyarka ce, ka san yanda zakayi man Magana". Kai ya sadda k'asa yace "kiyi Hakuri Mancy, ki yafe min, amma DonAllah ki tafi damu".


Alhaji Abu yayi tunanin tafia ya barsu don yana ganin kamar zasu zo su kebe, yayi hanyar Fita da sauri Mancy ta dakatar dashi ta hanyar cewa "dakata Alhaji, donAllah ka dawo, akwai abunda nikeso dukanku ku fahimta, mu zauna".
Alhaji ya dawo ya zauna
Shima Zaid din Zama yayi a bakin Carpet.


Mancy ta fara "Alhaji Nagode kwarai da kala Soyayyar da kake nuna min, na san Son da kake min ne ya shafi Yarana, nagode kwarai amma donAllah indai bani nace maka ina so ka taimaka ma Yarana ba kar kayi komai". Alhaji yayi mamakin Mancy Sosai, shakka babu bata da kwadayin abun dunia.


Ta kalli Zaid tace "Zaidun Babanshi, Mancy bata kyauta ba da bata nemeku ba, Mancy tayi laifi ku yafe mata kaji?" Kauda kai yayi yana son murza idonshi ta rik'o hannun tace "Haba DanMakaho na" murmushi ya subuce mishi don Mancy ba ta kiranshi da sunan sam sai in tana son sa shi daria.


Tace "to ka fahimceni, wallahi duk runtsi duk wuya baku da Gidan da ya wuce na Mahaifinku, kun fiso na tafi da ku Agolanci? Kama san meye hakan? Kana da Shekara 25 kake so ka bar Gidan Ubanka ka koma Gidan Mijin Mamarka? Haba Zaid kayi tunani mana, ban yi hakan ba don bana sonku, na yi hakan ne don na kwatar muku yancinku, ku zauna Gidanku, ku ma Mahaifinku Biyayya, ku maido da sonku zuciyarshi, ku samu albarkarshi".


Murmushi Zaid yayi yace "Ya riga da ya Tsine min, ta sa ya tsine min Mancy". Ba ta san lokacin da ta fashe da Kuka ba. Ganin haka Alhaji Abu yayi saurin Mik'ewa ya zaro kudi a Aljihu wanda zasu kai dubu 20 ya damk'a ma Zaid a hannu yace "barin tafi Zaid, kangaida Dalo, ku cigaba da Addua, Allah baya bacci". Yayi Gaba Zaid ya mik'e ya bishi a baya, Mancy kam bata yi yumkurin mikewa ba.


Sosai Zaid ya ma Alhaji Abu Godia, ya rakashi har Mota kafin ya dawo Gun Mancy dake durkushe a gurin, Zaid ya cigaba da bata labarin tun bayan rabuwar su zuwa yau da ya yanke hukuncin biyo Mancy. Sosai take Kuka kafin ta share hawayenta, Zaid ya yi zaton ta janye qudurinta amma da yaji tace "Allah ba ya bacci, ku cigaba da hakuri, gaskia zatayi halinta, kuma in dai ba saba mishi kayi ko addininka ba, to bakinshi ba zai bika ba, ba zai kamaka ba" ya gane cewa tana kan bakanta.


"Mancy ya maida tsine min fa kamar wak'a ko karatu, wata rana ko zai kamani". Mancy tace "Allah yana tare da ku Zaidu" sanin Mancy yar magana daya ce ya sashi mik'ewa don shiga ciki, ya san Magiyarshi da duk abunda zaiyi ba zai chanza mata raayinta ba, Mancy kaifi daya ce, ajiye mata kudin da Alhaji Shamsu ya bashi yayi, riko hannunshi tayi ta bashi kudin, tace na kune, ni banda kudin da zan baku da na k'ara maku, muje ka ci Abinci ka koma Katsina".


Murmushin takaici Zaid yayi yace "ba ma zan kwana ba?" Ta gyada kai tace "eh ba zaka kwana ba".


Mai makon yaji haushinta sai cewa yayi "Ya Rabb" zuwa yayi ya rungumeta sosai yace "nayi Kewanki da Yawa Mancy, ki kunna wayarki ki kira Dalo donAllah". Kai ta gyada mishi ya shiga ciki gurin Danginshi, sun ko ji dadin ganinshi sukayi ta rungumeshi suna fira, Ya gaida Kawunshi da Matarshi, Walid ya jashi zuwa Dakinsu, Ummi ta zubo mai Abinci, yayi Sallah Asahar da Laasar kafin ya mike don haraman tafiya, Walid ne ya fito don saukeshi a tasha, yaso sake kebewa da Mancy amma tak'i yarda. Haka ya musu Sallama Walid ya daukeshi zuwa Tasha.


Sai Gab da Isha'i Zaid ya isa Katsina, tun a hanya yace yau shagali zaiyi shi da kanwarshi, daga tasha ya wuce Chimex don siya musu Shawarma, ya tsaya a Mansho Suya ya siya Gassashen Kaza, ya siya musu Lemu da ruwa, kafin ya tsaya a Wani Shago ya siya ma Dalo Chocholates kafin ya hau Machine ya wuce Gida, sai da ya tsaya ya biya Eskaley dubu dayanshi kafin ya karbi World na dubu biyu, ya dan zuk'a kafin ya wuce Gida.


Yana Shiga Gida ya hau kwala ma Dalo Kira, babban parlo ya shiga ya gansu gabaki daya banda Dalo, hanyar Dakinta yayi yana kiranta da k'arfi, fitowa tayi da murna ta rungumeshi cike da jin Dadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login