Showing 69001 words to 72000 words out of 133269 words
Chapter 24 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt
baya.
Mur ya sha tare da hade girar sama da k'asa. Yace "me kika musu?" Kamar jira take ta fashe da kuka.
"Wai saidai na ba Annah Rigar da Mancy ta siya min" karbar rigar yayi kafin ya kallesu ya har sai da ya ba Yesmin tsoro yace "Saboda uwar babbansu ta siya? Sai su kwata in suna da k'arfi".
Ki tafi daki ki rufe, zan shigo ba da dadewa ba, da dan gudu ta wuce cikin gida, shi kuma ba tare da ya sake kallonsu da ke tsaye ba ya shige dakinshi dafe da k'irjinshi da ke mai zafi.
Shafa ta kalli Yesmin tace "kinga yanda dan mijina ya raina ni ko?" Yesmin tace "ke da kike da maganinshi a hannu".
Tace "ke dai bari, ai sai dai wasu ba su ba, chance nike nema, da ma samu zasu zama tarihi a mance su a rayuwa".
Yesmin ta jinjina kai. A tare suka koma ciki, yesmin ta dau jakkarta ta musu sallama ta fito. Mai makon ta yi hanyan parking lot sai tayi BQ.
Samun shi tayi kwance ringingine, idonshi na fitar da kwalla, wuri ta samu ta zauna a hankali ta kira sunanshi.
"Zaid"
Sai da ya dan bata lokaci kafin ya dan kallota "me kike so?"
K'amshi tace "Zaid, can we talk?".
A fusace yace "talk about what? How My step mother is your Aunty?".
Dan bude murya tayi tace "Zaid ya kamata ka san cewa ba zan taba yin wani abun da zai cutar da kai ba ta kowani fanni, wallahi in wani abu zai cutar da kai ko wani naka sai inda karfina ya k'are, right now i need you to trust me".
Dan jim yayi kafin ya tashi zaune yana kallonta, bakinshi na rawa da k'yar ya iya cewa "Meye alak'arki da Hajia Shafa'atu?".
A takaice tace "Aminiyar Mamata ce".
Zaid zaiyi magana tayi saurin katseshi ta hanyar cewa "Eh Zaid, kawarta ce kuma Halinsu yazo daya shiyasa suke abota, ba zan iya fada maka exactly what is happening ba, saboda wasu abubuwa zasu fi kyau in ba a fadesu ba, suna k'ulla wani abu game da kai da kanwarka amma ba zan bari su cutar da ku ba na maka alkawari".
Zaid ya kalleta kaifn yace "ta ya zan yarda da ke?".
Tashi tayi tsaye tace"Zaid i just told on my Mother, na ci amanarta ne fa, na yaudari yardanta, zaid kana ganin zan yaudari uwata ne in ba akwai kwakwaran dalili ba, dole akwai dalili?".
Shima tsayen yayi yace "nikam kinsan banda komai, i lost everything, banda abunda zan biyaki dashi".
Daria tayi tace "lallai kam ka manta k'amshi, ka manta k'amshi ba matsiyaciya bace ba ko? Ka manta ko a school k'amshi ke treating kanta bata yarda a siya mata ko da cup daya ne na coffee, so Zaid bana bukatar kudi ko wani abun duniya,abu daya nake bukata shine "in ka ganni, ko ka ji sunana, kayi murmushi a bayyane ko a boye kace "Na Santa".
Da mamaki yace "Yesmin ban gane ba"
tace "ba zaka gane ba, hakan kawai nake buk'ata, yanzu ba wannan ba, gaya min meyasa baka dawo School ba Last year, me ya faru da Zaid mai Zabga K'walisa? Mai ya faru da kai, why are you a complete mess now?".
Ya dan kalleta ya na so ya karanceta tace "Zaid ina son na taimakeka but ina buk'atar ka yarda dani, how can i help you when i dont know what happened to you exactly, please Zaid, Yesmin is not your Enemy, trust me".
A hankali ya soma karanto mata duk wani abu da ya gifta tsakaninshi da Hajia Shafa'atu tun yana dan Shekara bakwai, da Silar komai, har i zuwa yau, babu abunda ya boye mata.
Sosai take kuka kamar zata shide, ya zaayi Mutum yayi haka? Ya zaayi Mace ta yi irin wannan rashin imanin? Ina zata kai Hak'okin bayin Allah? Ta san Uwarta na da babbar sa hannu a cikin lamarin nan, ba abun mamaki bane in ma Uwarta ta sata bin boka, don ta san Uwarta Shedaniya ce.
Ganin kukan na neman yawa ya sa Zaiid cewa "K'amsshhiii, to yane? Ya school? Saura Months ko ki gama?" Itama ta na son mantawa da abun for a while ta share hawayenta tace "eh saura 7months" yace "inye Dr K''amshi Allah sanya Alheri" murmushi tayi kanta na wani irin sarawa.
Mik'ewa tayi tace "barinje Gida, I wont let them hurt you or your sister again, zan kuma bincika naga if theres anything i can do, da zai dawo da babanku cikin hayacinshi".
Murmushi Zaid yayi yace "nagode".
Tun daga ranar Yesmin ta maida Gidan Hajia Shafa'atu wurin zuwanta, duk wani Makirci da bak'ar aniyya da suke kullawa Yesmin sai ta kwance ta bata musu aiki, in ta zo Gidan, attimes sai dai ta wuce BoysQuaters wurin shi or in ta karyo Motarta a Unguwar ta ganshi bakin Bencin Eskaley, oda take mishi sai ya taso ya shigo motar su sha labarinsu ba tare da ta k'yamaci kaurin da yakeyi ba.
Tsakaninta da Dalo sai k'auna da janta a Jiki.
Har sai da wata rana Hajia Shafa'atu tace "wai ke Yesmin, na ga wani haba-haba kike da wanchan figigiyar yarinyar, baki san itace nake so na raba da gidan nan ba abun ya cutura, har gobe mamarki ta kasa hada min magani me k'ark'o? Ni ban so kina zuwa kusa da ita balle ki jata a jiki".
Dariya Yesmin keyi bata cewa komai.
Ba da dadewa ba Yesmin ta fara shirin komawa makaranta.
Bata koma Makaranta ba sai da ta tabbatar Shafa'atu ta hak'ura da batar da Zaid da Kanwarshi.
Don da bakinta take cewa "Aunty Shafa, kinga wai Mummy ta kasa biya miki Buk'ata, inada shawara, ki bar kashe kudinki wallahi, tunda ke ke da gida, babansu kuma sai abunda kikace mai zai dameki?".
Hajiya Shafa'atu tace" wallahi na kashe fiye da Miliyan Biyar kan wannan maganar, magana ta kici ta ki cinyewa, ba wannan ba Yass, ni tsagerancin yaron nan ne ya ke isata, har hannu yake sawa yana dukana" tace "abu mai sauk'i da ya tabaki ki fanshe a wurin Ubanshi?".
Tare suka fashe da daria harda kashe hanaye kamar wasu kawaye.
Yesmin tace "ba da dadewa ba zan gama Makaranta, zanje India yawon Bude Ido, akwai wani hatsabibin Boka, wallahi daga India zai dauko su ya batar dasu, ba tare da kinyi shakka ba, kinsan Bokan India ya miki aiki, sai godia kawai".
Cike da jin dadi da gamsuwa tace "shegia Yas, kin ko tsotso nonon Er Rabi, wallahi zaki fi Er Rabi tsula tsiya don a idonki naga ba Wasa".
Da wannan Yesmin ta koma London don kammala karatunta.
*BAYAN WASU 'YAN WATANNIN DA BASU KAI SHEKARA BA*
Yesmin ta shigo Gidan Alhaji Zaki da Sallama.
Hudu ya zo taryanta, guntun murmushi ta mishi ta wuce shi tsaye, Annah ta rungumeta tana Oyoyo Aunty Yesmin.
"Annah ya kike ya school? tace "lafiya lau gobe zanyi Jamb ma" "inye Allah ya bada saa"
Aunty Shafa tazo da murnarta tace "Oyoyo Mutanen Ingila, sannunku da zuwa"
Gaisawa sukayi sosai bayan duk suka mata murnan kamalla karatun Likitanci da tayi, ta kuma yi Qualification Exams ta ci, yanzu saura HouseManship sai ta tafi Service.
Hudu yace "Aure fa?" Yesmin tace "Lokaci ne" Hudu da mummunan murmushinshi yace "In fito?" tace "daga Mota?" Annah Ta fashe da daria, ya kalleta rai bace yace "Zanci Uwarki" Shafa ta hade rai tace "Ni kenan".
Zaid ne ya shigo ko Sallama babu, ba tare da ya kalli inda suke ba ya wuce kai tsaye dakin Dalo.
Yesmin ta bishi da kallo ganin ya chanza kama, ba da dadewa ba ya fita ya wuce ko kallonsu beyi ba, Hudu da Hajia Shafa suka bi bayanshi da ashar da zagi.
Haka kurum taji gabanta ya fadi, da sauri ta tashi tace "barinje gida" a tare sukace "tun yanzu?" Bakinta ya fara rawa wai "eh wallahi dama zuwa nayi na gaisheku" kafin su sake cewa ta figi jakkarta ta fita tana "sai anjima" Shafa tace "ki gaida Mamarku" ba ta amsa ba.
Hudu yace "kai aunty ban yarda da Yesmin ba, muje mu gani".
Bayan Zaid ta bi ta na kiranshi
Chak ya tsaya ya juyo da murmushi yace "tun a Parlor naji k'amshinki".
Tace "shine baka juyo ba?" Yace "kina tare da wanda bana k'aunar hada ido dasu, wurin dalo naje".
"Lahh dalo na ciki ba ta zo mun gaisa ba?" "Eh aikam tana ciki, ba zata fito ba? Ke dai barta da zaman daki" "kamar mai takaba?" Dariya sukayi baki daya.
Kallonshi takeyi sosai tace "Me ya sameka?" Murmushi mai kama da yak'e yayi yace "mefa?" tace "Zaidd, me ya sameka? Are you sick? You look pale" yace "maybe I am just tired" tace "ba wani gajia, you are sick, ka zo in dubaka" dariya yayi yace "Dr Yesmin, you dont have a License" tace "yet, amma a hankali zan samu, kazo in dubaka donAllah, in baka yarda dani ba Akwai friends dinka ai a General Hospital muje su duba ka".
Yace "su waye?" Da mamaki tace "kar ka ce min baka da whereabouts din kowa?".
Kai ya girgiza alamun aa tace"har Aliyu A Aliyu?" Ya gyada kai alamun "eh" ta bude baki tace "your bestfriend Zaid, you dont have contact with him...this is serious".
Kafin yace wani abu sai ji sukayi cikin fushi ance "Yesmin, me kikeyi a nan?".
Ta waiga taga Aunty Shafa, Hudu da Annah, dama Zaid na kallonsu, Yesmin ta maida kallonta kan Zaid tace "zan dawo dubaka, ko ka gaya min matsalarka or i force you to a hospital".
Ta juya ga su Aunty Shafa tace "dama yanzun zan tafi". Ta wuce ta barsu cike da mamaki. Zaid ya hade gabas da yamma ya hade rai ya shige daki.
Hudu bakinciki kamar ya kasheshi ya ga Zaid da Yesmin dinshi tare
Yace "Aunty ko sun san juna ne?".
Cike da fushi tace "a gidan ubanwa suka san juna? K'ila ganinta yayi ya tareta kasan dan akuya ne".
"Shege" cewar Hudu.
Washegari ta dawo, ko cikin Gida bata yi ba ta wuce BQ, ta na shiga taga Zaid na wani irin Tari mai hade da Jini.
Wani tsalle ta daka kan gadonshi inda yake zaune
"Zaid Jiniii?"
Ganinta ya sashi fara kauda kanshi.
"You are coughing out blood"
"Yesmin it's nothing please"
"Kana tarin jini kuma kace min its Nothing, ka tashi we are going to the hospital ?"
"Yesmin calm down, you are over reacting".
"Oh haba dai? To yi hakuri i am over reacting, you are coughing out blood and you are so stupid to realise what that means".
"Yesmin na kusa shekara ina tarin Jini".
Mutuwar tsaye tayi, duk wani lakka na jikinta ya mutu, ta dade a k'ame kafin ta samu da kyar ta bude jakkarta ta ciro Tissue pape bata damu da Kazantar da ke bakinshi ba ta sa tissue ta dinga goge mai baki.
Hawaye na zuba daga idanunta ta ki yarda ta hada ido dashi, har sai da ta gama ta kwashe dattin ta je waje ta zubar ta dawo.
Fuska daure tace "ka tashi mu tafi Asibiti, bana son gardama Zaid, ka tashi kawai mu tafi".
Murya chan kasa yace "Yesmin..."
Ta katseshi ta hanyar cewa "Zaid, zamuje Asibiti yanzu da kai, gardama ko jayyaya bana so".
Jim ya dan yi kafin ya Tashi, jallabiyan da ke kan Gado kawai ya zura, ta fita ya bita a baya.
A parking lot suka tsaya.
Hudu ya fara ganinsu tare kafin ya tabo Hajia Shafa, da mamaki Shafaatu tace "Yesmin?? Yaushe kika zo?"
Hankali tashe tace "Aunty Ina Zuwa, barin kai Zaid Asibiti".
Hajia Shafa ta figo Yesmin ta ja ta gefe tace "yesmin me kike shirin yi?" A rude tace "tarin jini yakeyi, ya kamata na kaishi Asibiti".
Shafa tace "ya mutu ma, ina ruwanki dashi?".
Wani kallo ta mata tace "ba zai mutu ba, asibiti zan kaishi, kuma zasuyi treating dinshi, da yardan Allah zai warke".
Kafin tace waniabu ta fincike hannunta ta iske Zaid tare da bude mai gaban Mota ya shiga ta mayar ta rufe kafin ta zagaya wurin kujeran driver ta shiga ta kunna mota tareda barin Gidan a sittin, barin su Hajia da tsananin Mamaki". Cikin Gida suka koma rai a bace Kasuwar da basu je ba kenan.
A hanya ta finciki Motarta ta zaro waya ta kira Dr Aliyu.
"Hello Dr Ali kana ina donAllah?".
"Hello K'amshi, ina Doctors Quaters".
"DonAllah yi maza ka fito Asibiti, gani kan hanya"
Ba ta tsaya jin me zaice ba ta kashe waya.
Zaid yace "Yesmin duk wannan is not necessary, ki tsaida motar muyi magana" banza tayi dashi ta k'yaleshi, ta cigaba da Jan Motar.
"Atleast kiyi tuk'ia hankali".
Bata kulashi ba har sai da suka zo Asibiti, ta sake kiran Dr Ali taji ana ina.
Nan ya ce mata yana consultation Room na Opd. Chan suka nufa.
Dr Ali ya gansu ya k'araso don su hade yana cewa"
"Yesmin Emergency ne? Ya Illahi wani kamar My Guy Zaid Ni"
Murmushi Zaid yayi yace "Sunana Zaid Kai, babana ya kake".
A tsorace ya kalli Zaid kafin ya waiga ya kalli K'amshi wanda tayi saurin kawar da kai".
Tuni Dr Ali ya rungume abokinshi yana kiran "abokina meya sameka, rana daya kawai ka bace bat no contact nothing, what happened to you man?".
K'amshi tace "nikam kar ma ku fara hiran bayan rabuwa dinnan. Dr Ali donAllah mu shiga kayi checking dinshi".
Shigewa tayi cikin CR din ta bar su tsaye, ko wannensu da abunda yake sakawa a rai suka bi bayanta.
Dr Aliyu ya zauna Zaid ya zauna shima.
Dr Aliyu yace "Zaid, ina so na san meke maka ciwo, i need you to tell me the truth akan duk wani tambayan da zan maka".
Zaid ya jinjina kai duk da ya san ba wani reason da zai sa ya kasance a nan tunda ya riga da ya san matsalarshi, kawai nan zaa yi ta jan magana ne ana maida shi wani big deal.
"Zaid me ya sa kuka zo Asibiti"
"Tari nakeyi"
"Akwai Mura?"
"Aa"
"Wani kalar tari ne?"
"Green ne attimes yellow"
"Akwai Jini?"
"Eh"
Dr Aliyu yayi dan jim kafin yace;
"In kana tari k'irjinka na ciwo"?
"Eh".
Sosai Dr Ali ke kallon Zaid ido cikin Ido, ya san Zaid for long, Zaid jajirtace ne, duk da Course dinsu ba daya ba don Shi Zaid Civil Engineering ya karanta shi kuma Ali ya karanta Medicine amma wurin kwnanan su daya, banda wauta na dan fari bai san Zaid da wani shashanci ba ko halin banza amma bari ya tambayeshi yaji.
"Zaid kana shan Giya?"
"Aa bana sha"
"Sigari fa?"
"Eh ina sha"
"Sosai ko kadan"
"Sosai"
"Ka na shan kara biyu a kwana 1?"
"Ina shan Kwali daya ko fi a rana daya".
A tsorace Dr Ali yake rubutu yace "Inalillahi, Zaid Akwai investigations din da zaayi yanzun nan, zaa ja jininka, zaka bada sample din kakinka, zaa dau hoton Kirjinka da na Huhunka"
Wata nurse ya kira yace Zaid ya bita.
Yesmin ta shigo ciki tace "Yadai Alee?" Report sheet din ya bata ta karanta hannunta chushe cikin kitson attachment dinta.
"Zaid is getting himself in real trouble, Ya Allah".
Dr Ali yace "K'amshi, donAllah me ya faru da Zaid? He is no longer Zaidun da na sani".
A tak'aice tace "He is no longer that kam".
Zaune sukayi jugum jugum suna jira Zaid su dawo har 1hr ta shure, fargaba fal kirjin k'amshi amma son ta samu sauk'i tace "Dr Ali baka da patients ne, ba ka zuwa rounds?" Shima jiki a sanyaye yace "ba nike call ba yau".
Zaid ya shigo da Sallama yace "yadai kamar masu zaman makoki?"
Yesmin tace "an gama investigations din?
"Yeah wai sai gobe zaa karbi duka results din
Muje ki maidani Gida."
Dr Ali yace "HELLO Ina son sanin abunda ke faruwa, donAllah muje Dr's quarters".
Zaid yace "muje to"
Tare suka fita, Yesmin na gaba suna binta a baya, jikinsu duk yayi sanyi, suka nufi Doctor's Qtrs, fira suka sha Sosai har bayan laasar suna Gidan Dr Ali, nan dai suka taru suka bashi shawara, suna bashi bakin wannan shaye-shayen ba me bullewa bane, ya bari, yace "to zai bari InshaAllah".
Yesmin ta dawo da shi Gida, ta shiga wurin Aunty Shafa, ta cika tayi pam.
"Wai Uban meye hadinki da Zaid? Ko ba ki san duk dunia banda abun k'i kamarshi ba?".
Yesmin tace "Nikam banda abun So kamar shi".
Aiko ta daga hannu ta mare Yesmin, Yesmin tace "ni kika mara? To ki tabbatar kamar kin daga hannu ne kin mari Mommyna".
Ta fice da sauri Hajia Shafa'atu ta biyo bayanta tana kwala mata kira amma tayi banza da ita, sai Shafa'atu ta fara nadamar marinta, motarta ta fada ta figa sai gida, tana isa gida ta tasa mamarta tama mata kuka wiwi, hankalin Er Rabi yayi mugun tashi, tace "uban wa ya mareki na batar da mutum".
Tace "mommy kawarkice Hajia Shafa'atu" cikin daga murya tace "Shafar ce ta mareki? Aiko zata ga tashin hankali".
Er Rabi ta iske Hajia Shafa har Gida, abunda Shafa ke tsoro kenan, ta manta Er Rabi bata da mutunci in aka taba yayanta, bata hada yranta da kowa da komai ba.
Kika dauki hannunki ki ka mari diyata? Ni Shafa? Bayan duk abubuwan da na miki? Kinsan sirrinki babu wanda babu a hannuna ko?wallahi kiyi a hankali duk randa kika sake gigin taba min yarinya wallahi daidai yake da tonuwar Asirinki". Ta juya ta barta tsaye jikina na rawa.
Bayan Maghrib ta kwashi jiki ita da Hudu da Annah ta nufi gidan Er Rabi don basu hakuri.
Er Rabi tace "me kuka zo yi min a gida?"
Kwantar da kai Hajia Shafaatu tayi tace "haba Kawata, ina diyata Yesmin? Zuwa nayi na bata hakuri, Er Rabi ki fahimceni, wai Yesmin DANMAKAHO take so, wai nace ta rabu dashi wai ba zata rabu dashi ba, shine zuciya ta ci ni na mareta, amma kinsan wallahi ba da san raina bane, ina Yesmin din take na bata hakuri".
Er Rabi tace "ai lallabata zaayi har ta rabu dashi, ba wai ki sa mata karfi ba, nidai kar a sake taba min yarinya, sai a zauna lafia".
Tace "na yarda".
Er Rabi ta kira Yesmin ta fito a yangace "Er Rabi tace baby meye hadinki da Dan Makaho?"
A wulakance take kallonsu tare da yatsina fuska tace waye haka?"
Tace "yaron gidan Anty Shafa'atu"
"Oh wai Zaid?"
Suka kalli juna gami da tabe baki tace "eh shi".
"Okay Zaid Ali Zaki Friend dina ne tun yana London, yana Cambridge ina Oxford so we know eachother for long, and relationship that i have with you ba zai hanani cigaba da abotana da shi ba, so incase kin ganni a gidanki to wurinshi na zo ba wurinki ba".
Duk da ran Hajia