Showing 3001 words to 6000 words out of 133269 words
Chapter 2 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt
shi, kafin ta saukar da kai ta fara magana cikin sanyinta ta ce "So na kake yi, kana jin nauyi na, kana tsoron yadda za ka gaya mini, kana gudun kar hakan ya zaman silar bacewar kyakyawar Alak'ar da ke tsakaninmu?" da sauri ya kalleta.
Kai ya fara gyadawa kamar k'adangare. "Haka ne, wallahi haka ne Labiba, tun farkon haduwarmu a office din HOD, lokacin da Yayanki ya rakoki Registeration na kamu da sonki" Labiba ta danyi murmushi ta ce; "Ban yi mamaki ba, its obvious ai".
K'arfin guiwa ya samu, ya ce "Ina fatan zaki amince mini?" murmushi tayi ta ce "wallahi ban sani ba, bansan me nake ji a kanka ba, bansan me zanji nan gaba a kanka ba, amma nasan cewa ina matuk'ar ganin girmanka, sosai kake burgeni Captain, bansan ko nan gaba wata alak'a da ta wuce wannan zata shiga tsakaninmu ba, amma ko me ke nan, Allah ya zaba mana abin da yafi Alheri a rayuwarmu".
Kallonta kawai ya tsaya yi, sosai ta burgeshi, sonta na k'ara ruruwa a zuciyarshi, bai taba ganin irinta ba, bai taba sanin Matan Katsina na iya kallon Namiji haka su gaya masa gaskaya ba tare da wani 6oye-6oye ba, ba ta rufe mishi komai ba, ta gaya mishi iyakar gaskiyarta, hakan da tayi ta matukar burge shi, yana da tabbacin da wata ce, yaudarar shi za ta yi, ko ta ce mishi eh itama tana sonshi ko don wani abu, ko kuma ta bata mishi lokaci, ko kuma ta ja mishi aji, haka yake so Mata su kasance Straightforward, in ana haka, da ba a samu Yaudara da cin amana a cikin Soyayya ba.
Mik'ewa yayi yace "tashi muje na nema muka abun hawa" murmushi tayi tare da sa6ar jakkarta, ta bi bayanshi, a bakin kofa suka ga Aisha, tace "muje ko?" Labiba ta gyada kai, a haka har suka fita bakin makaranta ya tsaida musu keke Napep, fadin inda zasu sukayi, mai Keke Napep yace "ke ta tudun Matawalle ciki zaa shiga?" Labiba tace "eh ciki ne ta wurin Makarantar Hope" yace "150 ne kudinki, ke kuma ta k'ofar k'aura layout ki bada 250" da yake hakan suke badawa ba su tsaya ciniki ba.
Aisha ta fara shiga kafin Labiba, Labiba na ganin AbuSideeq ya sa hannu cikin Aljihu tace ma Adaidaita sahu, mu tafi kaji" ba tare da bata lokaci ba ya ja Kekenshi, ta dan juyo ta daga ma Captain hannu, shi ko yatsarshi ya nuna mata alamun "ke ko" kafin suka sakar ma juna murmushi.
Aisha tace "Bawan Allah, be gajia" Labiba ta gyara zamanta tace "kullum cikin Hidima yake".
**
Abu Sadeeq Abu, dan Department of Engineering HUK Poly, wani irin Yaro ne me matuk'ar k'okari, HND2 yake, a nan ya gama ND ya jona HND dinsa, a Dept din kowa na sonshi sabida kyakyawar Alak'ar da yake dashi da Malamai da Dalibai, k'okarinshi be daura mai Girman kai ba.
So da yawa in ana darasi, kace ma Mallami ba ka gane darasin yau ba, zai ce "ka sa min AbuSideeq a HND2 ya ma bayani zaka fi ganewa" hakan ne ya faru da Labiba a ranar da suka samu Mallama Amina bayan darasi, tace "ta sake mata bayanin wani fannin da bata fahimta ba" mallamar tace "Wallahi sauri nake, amma kije HND, ki samu a AbuSadeeq a HND2, kice ni na aiko ki, ya miki bayanin topic din". Labiba ta mata godia ta ja Aisha suka tafi inda Mallama ta mata kwatance.
Ko da sukaje sukayi tambaya, nuna musu shi akayi, yana tsakiyar maza biyu da mata 3 daga gani 'yan ND2, yan gaba da ajinsu Labiba, yana ta faman musu bayani. Aisha tace "mu jira ya gama, ko muje mu dawo" Labiba ta girgiza kai ta musu Sallama" suka amsa tace "ina wuninku? DonAllah Abu Sadeeq muke nema" kallonta yake yi sosai, yarinyar nan ce da Yayanta ya kawota office din HOD ranar da yake ciki, murmushi ya mata yace "Ga wani Abu Sadeeq nan"
Murmushi tayi sosai, ta ganeshi, shine HOD yace mata in tana da matsalar karatu ta zo gurinshi zai mata bayani".
"Sannu da Aiki, Mallama Amina ce tace na sameka, wani abu ne ya shige min duhu a course dinta, shine nakeso in kana da lokaci ka dan min bayani" Agogo ya kalla, kafin yace "Alright ba damuwa, amma ga yayyinki nan muna karatu, saidai in mun gama" tace "lahh dama ai sai kun gama" yace "to nam da 30mins InshaAllahu" murmushi ta sakar masu duka, sosai ta burge duk na wurin, tace "bari mu dawo" ta ja hannun Aisha da ba tace ma kowa komai ba.
Ya musu bayani yanda ya kamata, Labiba da Aisha sun fahimta, suka mishi godia sosai, yace musu daga yau duk bayan ko wane lectures suzo ya sake musu bayani, hakan zaisa su fi fahimta. Godia suka sake mishi, tare da exchanging numbers.
Tun zuwansu Poly Aisha ke tare da ita, tana son Labeeba sosai, duk da a Ajin Maza sunfi Mata yawa, matan basu wuce sha biyar (15) amma Aisha bata da k'awar da ta wuce Labiba, ko wata daya basu rufe a Makarantar ba, amma Aisha na jin Labiba har ranta.
Labeeba za ta iya rantsuwa Aisha na sonta matuk'a, kodayake ita dai haka take, indai ta zauna a wuri, to tana da farin jinin mutane, kowa na sonta, ba za a ce don Kyau ba, don ba fara ba ce, a'a, don kyauwun zuciyarta ake sonta, ta iya zama da jama'a, kowa nata ne, bata da zabin mutane da take mu'amala dasu.
Wannan kenan.
Labari suke da Aisha kafin a shiga layin Unguwarsu Labiba, Aisha ke hada ta da Allah tazo gidansu don Mamarta na son ganinta, har k'arya ta mata cewa Mamar ta ce in ita Labiban bata je ba to ita za ta zo gidansu Labiban da kanta, duk dai don taje Aishar ta ce mata haka.
Dariya Labiba ta yi tace "Insha Allahu zanzo wannan Satin, ki ce Mama tayi hakuri.
"Allah ya sa kana da chanjin dubu daya" cewar Labiba, mai Adaidaita ya buga tsako yace "Hajia sai kiyi magana tun wuri ni banda chanji" Aisha tace "nima wallahi dubun ne" mai A daidaita ya fara mita da ya san Chanji ne da be dauko su ba, gashi har ya kusa shiga Tudun Matawalle, Labiba tace "Afuwan, akwai shago a ta wurin zasu samu Chanji" mai Napep yace "ga unguwanku ba dadin shiga, balle jiya anyi ruwa" Labiba dai hakuri ta sake bashi, Aisha dai tsaki tayi tace "ya cika mita".
Daidai Shagon Eskaley ya ci burki, Aisha ta mik'a mishi dubu daya tace "gashi ka samo chanji ka cire duka" ko waigowa beyi ba yace "Yo Anguwarmu ne? ko sani na sukayi da zasu bani chanji?" Labiba ta lura Mai Keke Napep dinnan dan tijara ne, ta sauka tace "bari na samo" Aisha ta bude baki tace "ya za'ayi kije gurin 'yan Shaye-shayen chan? Haba Labiba ba mutuncinki bane a ga kinje chan shagon, ki bari ya samo" Labeeba ba ta tsaya ba, illa ta karasa bencin Eskaley da Sallama.
*
Zaune yake kan plastic chair, cikin wata longsleeve shirt da 3 quartern Sojoji, face cap dinshi wanda ya rufe kanshi har wurin idonshi ruf ma irin wandon ne, kayanshi kenan duk dunia, ya dora k'afa d'aya kan d'aya, Idonshi lumshe. Yana shak'ar k'amshi, yana jin dadin yanayin da World ke sashi,
World shine sunan da 'yan bencin Eskaley ke kiran Tabar Wiwi, a cewarsu, Ita Wiwin Duniya ce, ma'ana komai, in suka zuk'eta, jin kansu suke daidai da Saraki, Sarauta Wiwin ke sasu. In ka zuk'i World, kafi kowa, wannan ma ya sa Zaid zama shi kadai tare da ba su Master baya, wanda suke fama buga Whot ko na Sigari basu dashi.
Duk k'ullin Worlda naira dari biyu Eskaley ke saidawa, yana bada bashin Sigari, amma be yarda ya bada bashin World ba.
Tunda suka ga ta nufosu suka k'ura mata ido, Eskaley ya amsa yana washe hak'oranshi jajjaye, da murmushi ta kallesu tace "Ina wuninku, DonAllah chanji naira dubu nake son ka taimaka min dashi" ta maida hankalinta gun na cikin shagon, Eskaley yace "Ahhh, chanjin dubu da sauk'i, basu kai ba wallahi" Labiba tace "akwai Credit? Mtn?" "Aa wallahi ya k'are" dubu dayan ta mik'a mishi tace "to DonAllah ka dan ara min #350 na ba me keke Napep" Eskaley yayi daria yace "Hajia yau wallahi da sauk'i, yau ba ciniki"
"Oh Allah!" ta fada a gajiye, ta musu Godia ta juya.
"Ga 350" taji an fada murya a dakushe, ta juyo ta ga wa ke magana, bata samu kallon fuskarshi ba sai gani tayi wani ya fincike kudin da aka mik'a mata.
"Shege Mankas, kana da kudi a aljihunka kasa Eskaley ya hana ni World, kai mik'o min World dinnan" ran mankas 6ace yace "donuwarka bata kudin" master ya kalleshi yace "mankas ni zaka ma wulakanci don nace ka siya min World, don ni ba mace ba ce, banda kayan dadi ko? to ranta min uku da hamsin dinnan, zan baka" daidai nan mai Napep ya sake buga horn, Labiba dai ikonAllah take kallo.
K'yallararen idonshi ya dago ya kalli Master bece komai ba, Master ya buga tsaki ya matsa kusa da Labiba yana cewa "Danmakaho ya ga Chikala" da sauri Labiba ta kalli mazauna gurin don ganin dan Makaho, amma bata samu nasarar ganinshi ba don ya juya mata baya, dubu dayan ta mik'a ma Master, tace "ka bashi, na biyo shi chanji, zan zo na amsa" master ya yashe jajayen hak'oranshi yace "Yayata, donAllah ki bar min chanjin mana" tace "aa gaskia ni ba zan baka kudina ka k'ona su ba" da sauri Master yace "wallahi ba Sigari zan sha ba, abinci zanci Yunwa nakeji". Labiba tace "ban yarda ba, nidai ka ba DanMakaho chanjina".
"Haba Babbar yaya kin fi k'arfin dari bakwai da hamsin, nidai Godia nake" Horn mai Napep ya sake buga mata har yana mata masifa, da k'arfi master yace "dallah ware Mallam, zaka ishemu da Oda, ka bita a hankali ko na ci uwarka, Yayarmu Allah ya kiyayeki" Mai Adaidaita tuni ya shiga taitayinshi, kar ya sha duka a banza, Labiba na shiga ya ja Napep dinshi suka shiga cikin Unguwa.
"Master, bani" cewar DanMakaho, "me zan baka?" master yayi kamar be san me yake nufi ba, Haruna yayi wuf yace "kai Master, muna gani fa ta baka 1k, kuma muna ji tace ka ba DanMakaho chnajinta, kawai kawo kowa a bashi world daidaiya" DanMakaho ya dago k'yallararen idonshi yace "ku bani nan" Master yace "haba Mankas, yawa kakeyi wallahi, kai ma fa World dinnan ka taba, kuma ka hanani, ka bari mana Eskaley ya bamu daidaya".
"DonAllah Mankas ka bar mana kudin nan, haba mana yawa kake" mik'ewa yayi ya fizge kudin, tare da cewa "In tazo k'arbar chanji ta uwar me kuke so na ce mata?" Master yayi wuf yace "ta fa bani" DanMakaho ya zira kudin Aljihun gaba inda Kwalin Sigari ke ciki, tare da fadin, "in na bata ta baku".
Barin gurin yayi, ya shiga cikin unguwa, su Master suka bishi da Ashar kala-kala ransu bace.
**
5:20pm
Baccin Awa 2:30 yayi, yana farkawa World ta sakeshi, ko da yake be shak'eta duka ba, Kewaye ya shiga ya dauro alwala, yazo ya hada Azahar da La'asar, rigarshi ya shinshina yaji tana warin zufa da rana ga kuma k'aurin hayak'i, guntun tsaki yayi, be yarda ya zauna da dauda ko k'azanta ba, duk da wadan nan sune suturunsa, sai wata bak'ar jallabiya da yake sawa a duk lokacin da zai wanke riga da wandonshi yana iya k'okarinshi wurin tsaftace su, be son shiga cikin Gida amma dole ya shiga ya dauko sabulu, ya ga dan Shegiar da zai hanashi.
Straight ciki ya shiga, da Hudu ya ci karo ya fito kamar mara gaskia, yana zare ido, da sauri ya wuce boysquaters, da dan mamaki DanMakaho ya kallesh yana mamakin saurin da yakeyi kamar wanda yayi k'arya, amma da yake ba damuwarshi bane sai yayi gaba ya shige Store ya dauko Klin.
Ya na fitowa daga Store yaji Aunty Shafa na cewa "Uban wa ya dauke min Naira Dubun da na aje kan Center Table" Annah ta fito daga daki tace "nidai Wallahi Aunty bani bace, tun dazun ina daki" Fati tace "ni kuma wallahi ban ma san kin aje kudi ba" "duk dauke dauken da ake min bana magana, yau abun ya isheni, daga in aje kudi in shiga in fito sai na nema kudi na rasa? ina Sadiya?" Fati tace "tana cikin dakinta ko?" Aunty shafa tace "na san itace, ya zaayi dama ku dauka, aiko ko ta bani kudina ko na mata mugun bugu, kuma Ubanta yazo ya biyani kudina"
Mankas be gama jin sauran zancen ba ya banko labulen Parlo ya shigo, ya na bude idonshi ganin ina Sadiya, ganin bata cikinsu ya kutsa cikin dakin ya ganta chan gefen gado me kama da na 'yan boarding durk'ushe tana karkarwa, ga dukkan alamu ta ji zantuttukan su Aunty Shafa, kuma ta tsorata, be tsaya kwantar mata da hankali ba ya finciko hannunta ya ja ta har Parlo gaban Aunty Shafa ya tsaya.
"Uwar da ta fasa taba ta, ta raina Uwar da ta haifeta" duk suka yi cirko-cirko ba me motsi, ya juya ga Annah da Fati, yace "duk randa kuka sake daga mata hannu, sai na sassareku" Aunty Shafa tace "Dubu daya ta ta dauka, kuma sai an biyani, DanMakaho ka fita idona, ni ba sa'arka bace, Uwarka ma bata fara yi dani ba, wallahi ku firdo min Kudina kafin Daddynku ya dawo, kaga duk inda yake yana daf da Gida, ku bani kudina, ba zai ji komai ba".
Baki na rawa Sadiya tace "Wallahi Aunty bamu dauka ba" Mankas ya daka mata tsawa yace "dallah kyaleta, munje mun dauka, ba za kuma a bayar ba, in ya dawo me zaiyi? Tsine min? Wani irin tsinuwa ne zai min wanda be min ba? Mtswww" ya buga tsoki kafin ya ja hannun kanwarshi suka fita daga Parlorn.
Daidai nan Hudu ya shigo yana zare ido, "Wai meye ke fariwa nake jin Hayaniya Hajia?" Kwafa Aunty Shafaa tayi tace "dani Dan Makaho yake cikin Gidan nan, wallahi zaman Gidan nan sai ya gagareshi fiye da yanzu, bari Alhaji ya dawo".
*
Zaunar da Sadiya yayi gaban k'ofar dakinshi ya dan bata baki, tare da kwantar mata da hankali ta hanyar gaya mata zai rok'i Babansu kan ya barta taje Gidan Mamansu hutu, sai da ya ga ta saki ranta kafin ya koma daki ya dauko Bak'ar jallabiyarshi ya zura, ya kwaso Riga da Wandon da zai wanke tare da bucket a toilet, cire abubuwan gaban Aljihunshi yayi, da Mukulli, da kwalin Sigari, da Naira dubu daya ya ajiye k'asa, Klin ya Jik'a ya fara tsoma rigar ya fara cudawa.
Be gama wanke Rigar nan ba yaji muryan Daddynshi yana fadin "Ina Dan Makahon yake?" dago idonshi yayi ya kalli Daddynshi da ya nufosu kamar Zakin da ya kwana 7 be ci abinci ba, duk 'yan Gidan sun rufa mai baya, kafin ya ankara Daddynshi ya sakar mai nushi kala biyu a gefen baki, ko motsawa beyi ba, Sadiya ta fashe da kuka.
" Sata? A gidana DanMakaho? Dama duk sace-sacen da akeyi kai ne? Yau dubun ka ya cika, yau wallahi sai ka kwana bayan Kanta" wayarshi ya dauko ya latso DPO, Sadiya ta zube gabanshi tare da rikon kafarshi, tace "Daddy Wallahi ba shi ya daukar mata Dubu dayanta ba, wallahi bashi bane, Daddy, Klin kawai ya shigo ya dauka, Daddy ka yarda damu" Haurinta yayi dai da ta matsa gefe, da sauri Mankas ya karasa gunta ya durkusa tare da dagota yana watsa ma 'yan Gidan mugun kallo, ya tsaida kallonshi ga Mahaifinshi ido cikin ido yake kallonshi.
"Zaid Mahaifinka ne, Zaid kar ka manta Soyayyar da ya wanzu tsakaninku, Zaid kar ka sake ka yi ma Mahaifinka ba daidai ba, duk yanda zuciya ke tunzuraka kan ka mishi wani abu, Zaid ba zan yafe ma ba, kar ka ga tsinuwan Mahaifinka kamar baya tasiri a kanka, Zaid a ranar da zan juya ma baya, Zaid ka rasa Lahirarka wanwar, Zaid Mahaifinka ne, ba komai tsakaninku sai k'auna da kyautatawa" muryar Mahaifiyarshi yaji na mai kuwa kamar a lokacin take magana.
Runtse ido yayi sosai, muryar Hudu ta katseshi inda yake cewa "Lahhh, ga Dubu daya chan" da sauri ya bude idonshi, ya ga Hudu har ya durkusa ya dauka, da azama ya karasa shima ya rik'o kudin, idonshi duk biyun ya bude su yace "Sake min kudi".
Aunty Shafaa ta karade da