Showing 111001 words to 114000 words out of 133269 words

Chapter 38 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt

28 Dec 2024

13064

surgery din ba zan rayu ba, kuma donor din will be at risk, kar kiyi, ba zan yarda ba, i am dying”.


Murmushi take mishi mai tarin ma’anoni daidai ta digar hawayenta tace “ZAN RAYU DA KAI, ZAN MUTU DA KAI”.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode




Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉


BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS 2⃣8⃣
(MAKOKI).


Hankalinta kasa kwanciya yayi kwata kwata, kiran number takeyi yafi so nawa amma kwata kwata wayar bata shiga, me zatayi? Me ya samu diyarta? Ko ta aika Aljanni ya dubo mata Yasmin? Gani tayi process din zai bata mata lokaci ya sa ta kira Driver Mallam Haladu don tafiya Kankia.


Mutanen Kankia an rasa abunyi, babu abunda ya tsira bayan Plate number na Mota.
Muhawara aka tafka na tafia da gawar Asibiti ko police station, 'yan kauyen suka sa baki aka tafi da gawar Asibiti don kaiwa Mortuary, tuni aka gane mai Rasuwar ta hanyar Plate Number din.
Kafin kace kobo Mutuwar Dr Yasmin K'amshi ya zagaye garin Katsina da kewaye ta hanyar Social Media, wane ya gani ga wane haka mutuwar Dr Yasmin K'amshi ya zagaye Nigeria baki daya.


Mutuwarta Abin tausayi ne, in ka duba Statuses din mutane Hoton Dr Yasmin ne, da yawa masu sakata ma basu santa ba.


Shigowar Hajia Er Rabi Asibitin Kenan ta ga tayi wata irin cikowa, a hanyarsu ta zuwa taga wata Mota tayi accident a bakin titi ta wurin Gidan Mutum daya, ta fi zaton ko wanda sukayi Accident din ne aka kawo Asibiti.


Reception ta tsaya tana tambayar Dr's Quarters.
Receptionist cikin rashin walwala tace "wa kike nema? Duk suna common room".
Da murmushinta tace "Diyata Dr Yasmin".
Receptionist ta rasa mai zatace mata, ta kalleta da kallon tausayi, ba huruminta bane fadan mutuwa, tace "zo muje".
Er Rabi ta murmusa tace "yauwa nagode".
Receptionist tayi gaba Er Rabi ta bita a baya, ba su tsaya ko ina ba sai common room, nuni ta mata da ta shiga ciki.
Er Rabi bata tsaya wani tunani ba ta shiga cikin Dakin.


Doctors ne a ciki Maza da Mata wasu zaune wasu tsaye, Matan kuka suke wi wi, Mazan kuma akwai masu hawaye wasu dai idonsu yayi ja.
Er Rabi batace ma kowa komai ba ta bisu da ido, da ta gama rarraba idanuwanta tana neman diyarta bata gani ba ya sata magana.


Doctorn da ya fi kusa da ita ta kalla tace "Dr, danAllah ina Dr Yasmin?".
Hankalin kowa dake common room ya dawo kan Hajia Er Rabi.
Tambayar ta sake yi, wani yace "wacece ke?".
Da faraarta tace "Nice Mummy, Mummyn Dr Yasmin".
Jin sautin kukan wasu matan ya k'aru.
Tace "wai ya? Meke faruwa ne?".
Wani Dr yayi ta maza yace "Mummy saidai muyu hakuri, Dr Yasmin ta rasu bayan Accident din da tayi 1hr ago".
Er Rabi tace "kutumar Uba ne, meye rasuwa? Kai dallah baka santa ba".
Taje kusa da wata ta mace da ke kuka tace "ke kawar Yasmin ce? Ta na ina? Muna cikin waya wayarta ta mutu, muje ki nuna min ita please".
Dr ta fashe da kuka mai sauti.
Wani Dr yace "Mummy zo muje ki gani".
Ba gardama ta bi bayanshi
Tace "Haladu, fito zo" driver ya bi bayansu da Mota, a tunaninta Wurin Yasmin zaa kaita taji yana cewa "Mummy, kinga ruwan saman nan bai dade da tsayawa ba ko?" Ta gyada kai yace "ba mu dade daga fitowa daga OR ba ni da Yasmin, wallahi Mummy sai gawar Yasmin nagani da idona".
Mummy ta buge mai bakitace "kai bakinka ya sari danyab kashi, Yasmin nawa gareku? Ba dai tawa ba, ni fa yanzu yanzu muka gama waya da tawa Yasmin din".
Yace "kiyi hakuri, yanzu yanzu sai Allah, in ta Gidan Mutum daya kika biyo zaki ga wata Motar da ta kone bakin Titi, wallahi motar kamshi ce"


Wani irin razanannen Ihu tayi wanda duk wanda yaji ya san ba na lafia bane, zubewa tayi k'asa Sumamma.
Tuni Drs sukayi kanta aka basu Gado.
Haladu Driver ya kira Mijin Er Rabi ya sanar gasu a Asubiti Hajia ta suma Yasmin ta mutu.
An dade a kan Hajia Er Rabi amma bata san wake kanta ba, ba ta farfado ba.
Baban Yasmin yazo da wani kanenshi, hankalinshi ya tashi, dalili daya da ya sa yake zaune da Er Rabi saboda Yasmin ne, Yasmin na sonshi, in Mamarta ta guma mishi bakinciki ita ke lallashi tana bashi hakuri, yayi kuka kamar zai shide da ya ga gawar Yasmin.
Karban gawar sukayi suka wuce Katsina ba tare da ya damu da duba halin da Er Rabi take ciki ba.
Duk Doctors sun biyo don suma a samu Taaziya dasu.
Ya gama waya da Yanuwa da abokan Azziki da ya isa zaayi janaiza, gata daya zai ma Yasmin, da an isa Katsina a mata sallah a kaita makwancinta kafin Er Rabi ta farfado ta musu jahilci, don yasan ba zata taba bari a rufe Yasmin ba.


Messages dinta ya gani na ban hakuri sai na karshe na tafiyarta Edo gida amma zata dawo ba da dadewa ba, Zuciyarshi ta gama karyewa da jin ta tafi, kila ba zata dawo ba, amma layin karshen message dinne ya bashi tabbaci inda take cewa "Na maka Alkawari zan dawo, kasan kuma Labiba Kaifi daya ce, nace Zan dawo, zan kuwa dawo ma". Da tunanin Beebbs dinshi ya shiga cikin Gida don girka abinda zai jefa a bakin shan Sigari.


Hudu da Shafa'atu na zaune a parlo, bakinta har kunne tana jira ta ji haukacewar Zaid ko mutuwarshi kamar yarda Er Rabi ta shaida mata.
Wuce su kawai yayi ya shige kitchen.


Hajia Laraba ta fado Gidan ko Sallama babu.
Hajia Shafa'atu ta rikota tace "ke lafia? Me ya sameki?".
Cikin tashin hankali tace "Daga Gidan Er Rabi nake, kinga mutane sunfi 1000, wai Yas ta rasu, tayi accident ta kone".
Hajia shafaatu ta kar kade kunnenta tace "mene mene mene?".
Tace "wallahi wai Yasmin din Er Rabi ta mutu".
Zaid ya ji wani jiri na dibanshi, parlorn ya fito ya kalli Matar yace "me kikace?".
Shafa'atu tace "ke yanzu yanzu fa daga gidan Er Rabi nake? Ina kikaji wannan karyar? Kun iya baza rumors wallahi".
Hajia Laraba ta goge zufan da keto mata tace "Wallahi ba rumors bane, naje anso sakona a Gidan Er Rabi, naga mutane cike, na tambaya akace diyar Gidan tayi accident ta rasu a hanyar Kankia, yanzu haka babanta yaje daukota zaa rufeta, ko Er Rabi na da wata diyar ne bayan Yasmin?".


Ihu Shafa'atu tayi ta daura hannu a kai, babu abunda takeyi sai Ihu, Hudu ya rada abunyi sai ji yayi zawo yazo mai, da gudu ya shige toilet ya bar Shafa'atu na chanyara Ihu tana neman Layin Er Rabi..


Zaid Fa? Zaid? Zaid na nan zube zaune a k'asa, hannunshi rike da kanshi wanda ke barazanar ballewa, Daga bisani kwakwalwarshi ta soma kai mishi cewa Yasmin ta mutu, nan kuma duk wata na'urar jikinshi suka soma tsayawa, fuskarshi tayi Ja, Yasmin ta mutu? Ya zaayi Yasmin ta mutu? Anya kuwa Yasmin ce ta mutu? Ya kamata ya tabbatar fa, amma in karya ne sai ya shake matar nan.


Zuciyarshi tace "To wanene ba zai mutu ba a duniyar nan? Kullu nafsin za ikatul maut, shima dai ba abun mamaki bane ya ji shi a kabari ya mutu, inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Ya Illahi. Ya Salamu. Ya Rabb.
Tashi yayi yana tafia kamar mai koyon tatata, wani Okada ya sauke wata mata, tsaidawa yayi kawai ya haye, a kan machine din yace "Goruba Road". Tafiya sukeyi duk iskan Machine dinnan bai zuwa mishi.


Ana Kwanowa Unguwar su Yasmin zuciyarshi ta dinga mishi zugin zafi, daidai zuciyarshi ya dafe, so yake yayi kuka, ya kasa, bai san ta ina zai fara ba, mutanen da ya gani ya tabbata dai Yasmin ta mutu.
Bai da kudin ba mai Machine, don daga shi sai shi ya fito, ganin bai cikin hayyacinshi mai Machine yayi tafiyarshi.


Ko Minti daya Zaid baiyi ba da zuwa gurin Motar Baban Yasmin ya tsaya.
A nan waje, ba a shiga ciki da ita ba, aka nadeta a cikin Likafani don ta riga ta dunkule ta kone ba batun wanka, a nan waje aka mata Sallah, aka tafi makabarta don kaita Makwancinta.


A yayin da ake haka k'abarinta, Mallam ya fara tunatarwa.
Mallam yace "Ya ku Al'ummar Musulmi muji tsoron Allah, Mutum ba komai bane, farat daya zaka wayi gari kajika a k'abari, ba ciwo, in ajali yayi kira ba makawa sai mun tafi, mu kasance masu tsoron Allah a duk inda muke, mu kuma roka Allah yasa mu samu kyakyawan k'arshe".
Zaid yace "wallahi wallahi mutum ba komai bane ba".
Mallam ya cigaba da tunasar wa da jan hankali, har aka rufe Yasmin, Zaid na daga gefe yana kallon komai kamar Film.


Gida suka koma don karban gaisuwa kamar yanda akeyi, Yasmin tayi mutane kam ta ko ina zuwa ake gaisuwa.
Mallam yace "DonAllah wani abu nagani yanzu a wayan wani bawan Allah, naga abun shi ake yayi yanzu, kamar jira ake mutum ya mutu, a yi ta yada hotunan mamaci, wasu ma har daukar gawa suke hoto su daura a kafafan sada zumunci ta yanar gizo, wallahi mu daina, hakan baida wani amfani, mu guji sanya hoton mamaci, ku bar mamaci ya huta, addua kadai mamaci ke bukata, sunfi bukatar ta fiye da komai yada hotunansu karin nauyi ne, donAllah mu gyara mu daina, na lura abunda ke faruwa kenan, in akwai wadanda suka saka hoton wannan mamaciar a daure a cire, a mata addua, kuna iya posting wance ta rasu a sata addua donAllah banda hoto".
Kamar jira ake, da yawa suka ciri wayarsu suka cire hotunanta da suka saka a Status.


Zaid dai na takure wuri daya, yana bin kowa da ido.
Duk masu shiga yana kallonsu, masu fita ma haka.


Katsina aka dawo da Er Rabi duk da bata san wake kanta ba, Asibiti Baban Yasmin ya umurta akaita don baison ta farfado da tashin hankali ta tada ma yan zaman makoki hankali.


Aiko ta na farfadowa ta fasa Ihu, ta sake suman, su Hajia Shafa da mutanensu duk sun garzayo Asibiti wurin Bokanyarsu nan suke zaman makokinsu, duk da tana kwance kamar matatta, haka suke zuwa ganinta, ba wani dangi nata sai abokan shedanarta, tana cikin semi coma, Shafaatu ke karbar mata gaisuwar.


Har bayan Isha'i Zaid na Gidansu K'amshi, da k'yar Dr Ali ya lallabashi ya maidashi Gida. Ya kaishi har dakinshi ya zaunar dashi ya bashi baki tare da shawartarshi da duk lokacin da ya tuna Kamshi ya mata addua.


A B U J A.


Wani Whatsapp group mai suna NationWide a ka turo BC.
Idan Dalo ya kai ga
*Dr Yasmin Hamza died @27*
She was a Beautiful Doctor from General Hospital Kankia Katsina State....
Bata iya karasa karatun ba ta furta "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun".
Mancy tace "Dalo mai ya faru?"
Hawaye takeyi jikinta ko ina ba inda baya bari, tace "Mancy Aunty Yasmin ta rasu".
Sanin wacece Yasmin tace "Meye? Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, ciwo tayi?". Dalo ka amsawa tayi.
Da sauri ta rungumo tana lallashinta tare da shafa bayanta tace "ki ta Inallilahi wa ina ilaihir rajiun, ki mata addua Sadiya".
Dalo cikin kuka tace "Mancy.. Yaya. Yaya Zaid".


K A T S I N A


Ita fa ta tadashi dazun da safe wurin 9, tace "daga jin muryarka bakayi sallah ba, Allah ya shirya ka Zaid, nikam na tafi OR, zamuyi ma wani Yaro aiki zamu cire mai appendix, zamuyi CS ma ka min addua, in bangaji ba zan taho yau, in kuma nagaji sai gobe in Allah ya kaimu, ka kula da kanka, Be Happy".
Ko tak bata bari yace ba fa ta kashe wayar, bai sake kira ba, bata sake kira ba.


Tun daga ranar da ya fara ganinta a UK zuwa yau da yaji muryarta ya soma tunowa, yanda take Sonshi bai bace mai ba, yanda take daria bai bace mai a fuska ba, yanda take kiranshi bai manta ba, ya rasata wallahi rashi na har abada.
Yanzu Yasmin ta rasu? Ta tafi? Ta barshi? Yasmin ta tafi kwatakwata, Ya Allah, mai son shi ta tafi? Wallahi da sonshi ta Rasu, bai taba furta mata so ba, bata taba fushi ba, ba ta taba gajia ba, bata taba kosawa ba, burinta daya, burinta ya ji dadi, burinta ya kasance cikin jin dadi, ta zabi farincikinshi a kan nata, shikenan ya rasa Masoyiya ta hakika, zai iya rantsewa ba zai taba samun mai mishi irin son Yasmin ba.


Wayarshi ta yi vibrating, ya dauka jiki a mace.
Dalo ce.
Jiki a mace ya dauka " Dalo".
Cikin Kuka tace "Yaya, Aunty Yasmin ta rasu dagaske?".
Zaid ya hadiye bakin miyau mai daci da kyar yace "a gabana aka rufeta".
Dalo ta fashe da kuka tace "Kayi Kuka?".
Murmushi mai ciwo yayi yace "banyi ba Sadiya, na kasa".
Cikin kuka tace "Kayi Kuka Yaya, cry it all out".
Ta kashe wayar sakamakon wani kuka da ya ci karfinta.


Shima Zaid din kamar jira yake a bashi umurninya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya.
"Yasmin, Yasmin, Allah ka yafe miki, halinki na gari ya biki, Allah ka yafe mata Allah ka yafe min nima". Abunda yake ta cewa kenan yana kuka, ji yayi kamar shima zai mutu sakamakon zafin da zuciyarsa ke mishi, bai san awanni nawa ya dauka yana kuka ba, bai son kukan da yake harda Majina ba, ba sauti, hawaye ne kawai, mai zaiyi? World zai sha? Allah shi kyauta ya sha World ranar da Yasmin ta rasu, Yasmin bata son yana sa ma cikinshi wuta kamar yanda take cewa, wallahi ya bari ma gabaki daya, ba zai kara ba, bai iya bari tana da rai ba, amma yanzu ya bari.


*Mamaci baya son Kuka, kukan da kukeyi kuna k'ara ma mamaci nauyi ne*
Maganar Mallam ta dazu da dawo mishi.
Zumbur ya tashi ya fada toilet.
Abunda bai taba yi ba yayi in yana cikin damuwa. Alwala. Alwala yayi ya na mai jin kunya ya fuskanci Alkibla don yin Sallah.
Saboda bai iya tuna ranar da yayi raka'a biyu kacal ba farilla ba.
Salloli yayi da baisan yawan su ba, shi dai ya san duk sujjada yana ma Yasmin Addua.


E D O


"Ga Labee Ga Labee" abunda manyansu da yaransu suke fada kenan. Gida mai dadi, wani farinciki da jin dadi ya mamaye zuciyanta, oyoyo ake ta mata, ta duba fuskokinsu don ganin damuwa, babu sai tsantsar farinciki dake fuskokinsu.


Rungume Maminta tayi tana tambaya ko lafiyarta lau, Mami ta harareta tace na miki kama da mara lafia ne? Kai ta girgiza tace "Allah baki hakuri Mami" ta sake rungume Mahaifiyarta.
To ko Abbanta ne? Da sauri ta nufi dakinshi, ganinshi zaune yana jiran isowarta ya sata nufarshi da gudunta, suna hada ido ta durkusa a gabanshi tana zuba mishi gaisuwa tare da adduoi, ya shafa kanta yace "Labiba wannan zuwan bazata haka? Ina Muhammadun?".
Tayi daria tace "Lafia lau, gashi nan shigowa, suna waje da Su Yaya Ali".


"Abbanmu kana lafia?" "Abbanku na lafia Labee, ya Mamarsu Amira da su Amira? Lafiya lau Abbanmu".
Abba yace "ai banyi zaton yanzu Yayanku zai maido ki ba, na fi zaton sai kunyi hutu, ashe shima jira yake a bayar dake ya cireki".
Labiba ta kalleshi da sauri tace "ya cireni a ina?".
Abba yace "a makaranta mana, bikinku ai wata mai kamawa ne".


Sallamar Baban Amira ya sa ta kallon Kofar ta inda zai shigo, sai yanzu abun ya zo mata, sai yanzu ta gane, kowa lafia, babu abunda ya faru a Edo, wayau Baban Amira ya mata, dawo da ita Gida Yayi, ya rabata daga Katsina".


Be kalleta ba ya durk'usa a gaban Abbansu "Abbanmu barka da dare".
Gaisawa sukayi sosai kafin yace "ashe kuna tafe".
Labiba kallonshi kawai takeyi har sai da Baban yace "yaya dai Labee?".
Baban Amira yace "tagaji ta sha hanya, tun asuba fa muka fito".
Abbansu Yace "ai sai ki tashi kije kici abinci kiyi bacci ki huta".


Idonta ya kawo ruwa ta tashi, ta fita, tana fita kuma ta watsake ganin danginta nata haba haba da ita.
Samira ta janyota suka shiga dakinsu don a buga cikinta.
Ga yayyin Samira da Mamarsu ana ta mata gyatsine, amma ita ko a jikinta, tsakaninta da Allah take son su.


"Wai ke ina kika samo wannan?"
Labiba tace "wa?"
Tace "wanda suka zo rannan, wanda Abba ya ba su ke".
Labiba ta dan zaro ido, har ta manta dashi".
"Gayamana ina kuka hadu, naga masu kudi ne"
Labiba ta harareta tace "ke kika sani".
Tace "ko dai hadaku akayi?".
Labee tace "ba wanda ya hadamu, shi ya ganni".
Ta mike tsaye zata fita taji mamarsu Samira na cewa "ba a gaya mana inda aka samo shi, ko ba a so mu sani?".


Chak Labiba ta tsaya tace "yo ai ba wani abu bane, Mama, Yaya kawata da muke karatu tare ne".
"Wani aiki babanshi yakeyi?".
Labiba tace "ban taba tambayarshi ba, ga numbernshi ko zaku nemeshi? Barin in je dakin Mami".
Ta tashi ta fita.
Ba su manta ba, ba su manta rashin kunyar Labiba ba, Samira da mamarta suka hada ido, suna mamakin rashin chanzawar Labiba.


Haushi duk ya kama Labiba, ganin Yayanta ya yaudareta, aikam ita ba zata iya tsiya ba, komawa dakin Abbansu tayi ba kowata durkusa gabanshi.
Yace "yadai baki kwanta ba?".
Tace "Abba naji Labarin su Jawad da Babanshi sunzo, har ka sa bikin rana daya dana Samira".
Abba ya murmusa yace "Eh Labee, raba bikin duk wahala ce".
Tace "nifa Abba ba na son Jawad, hasali ma ban san sunzo ba".


Daidai da shigowar Maminta Parlon.
Abba ya muskuta yana kallonta.
Labibarshi ce wacce bata barin abu a ranta, ko meye damuwarta zata fito dashi fili, bata nuk'u nuk'u".
Maminta tace "tashi ki fita".
Abba yace "taje ina? Magana muke, ina jinki Labee".
Ko shakka babu tace "Abba, Zuwan Jawad biyu Katsina Yaya ya turo shi nan, nifa gaisawa mukeyi".
Abba ya kalleta sosai yace "kira min Kowa".


Fita tayi kanta tsaye, bata damu ba, gwara ta warware komai once and for all.
Haka Abbansu yake, in yana da magana, baya ware 'yan daki ya musu magana,Iyalenshi ne, insani abu ya faru, zaunar da kowa yakeyi ya zartar da hukunci.
Haka Labee ta dinga Kiransu har sai da aka cika Parlon.
Baban Amira na shigowa gabanshi ya fadi, yasan wannan zaman Labiba ne.


Kowa ya zauna Abba yace “Labiba, yi magana”.
Numfashi ta ja tace “Abbanmu, Jawad Danuwan Aisha ne, mun hadu sanadiyar Aisha, yana kirana muna gaisawa har wata rana yace yana son zuwa Gida, na barshi yazo, a zuwa na biyu ne suka hadu da Yaya, shine fa ya turo su nan”.


Abba ya saurareta da kyau yace “to naji haduwarku Labee, to sai me?”. Tace “Abbanmu Aure fa, ni gaskia son da nake mishi bana aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login