Showing 102001 words to 105000 words out of 133269 words
Chapter 35 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt
nemeki?".
Tace "eh fa, ba zai ganni ba".
Suna dan fira sai ga Yasmin ta kira.
Sai da ya kalli Labiba ya ga ta tsura mishi ido kafin ya Amsa tare da sa Speaker.
Muryarta ya cika dakin "Zaidun Bibbs".
Labiba ta sake wani murmushi jin furuncin Yasmin.
Zaid yace "K'amshi, k'amshi yana tashi".
Tayi 'yar daria tace "kana lafia?".
Yace "Lafia lau, Dama yanzu nake shirin kiranki".
Tace "ta samu ne?".
Yace "Albishirinki"
Tace "Goro"
Yace "Mancy came for us, tazo har ta tafi da Dalo".
Yana jin sautin dariayarta mai dauke da murna sahihhiya.
Tace "Alhamdulilah, naji dadi, Dalo na jikin Mancy right now am so sure about it".
Yayi daria tace "i need details daga farko".
Yace "i will fill you in, ga wata ku gaisa".
Labiba ta girgiza mai kai, ya gyada mata kai alamun tayi magana.
Labiba tace "Assalam Alaikum"
Wani shewa taji Yasmin tayi tana daria tace "waalaikum salam Beeeebsss dinmu oh my God kece?".
Tace "Eh Aunty Yas nice ina kwana ya aiki?".
Yasmin tace "Lafia lau, ya School? Ya kike ya su Yaya Muhammadu?".
Tace "kowa lafia lau, yaushe zaki zo?".
Tace "Yau nike call, gobe ma haka inshaAllahu Jibi Tuesday kenan, zan zo na ganki, yauwa akwai wata colleague dita da ta kawo wasu Malaysian Shoes, size nawa kike sawa? In dauko miki random colors".
Kunya ya cika Labiba tace "ki barsu".
Yasmin tace "'yar kauye, come on tell me size dinki".
Labiba cike da kunya tace "37-38".
Yasmin tace "Oh oh, na tuna fa our biebbs is a small person hahaha, to inshaAllah zan dawo miki dasu jibi kinji?".
Labiba tace "Nagode Aunty Yasmin".
Yasmin tace "abunda zakiyi kawai ki kula min da Zaid sosai, love him endlessly, take good care of him, and kiyi fushi in ya sha Sigari ko world".
Labiba da Zaid suka kalli Juna, idon Zaid ya cika sosai da ruwa, ya kawar da kanshi, har yanzu yana jin Yasmin a ranshi sosai, soyayyar da take mishi mai tsafta ce, ita burinta kawai Zaid ya samu Farinciki".
Sukaji muryarta tana cewa "Ohh, bibbs, kina gabanshi ko? Kar ya ji sirrin mu, ki karbi numebrna donAllah ki min flashing zan kiraki zuwa anjima"
Labiba tace "Tou Aunty Yas, zan karba".
Zaid yace "Me ake ce mata?".
Yasmin tace "ina ruwanka ba sai ka ji ba".
Yayi daria yace "kun fi kusa".
Labiba ta mishi alama da zata tafi.
Ya daga mata hannu tare da muting Yasmin na two seconds yace "I love you".
Labiba ta amsa mishi ta fita ta fada gidansu da sauri.
Zaid suka cigaba da waya da Yasmin.
Har ya bata labarin Hudu da duk abunda ya faru
Jikinta rawa yake tayi tana Tsine ma Hudu, wallahi da kun kaishi Police station"
Yace "Mancy tace a kyaleshi, tunda Allah be bashi nasara a kanta ba".
Yasmin tayi ta fada, kafin tace "kai wallahi all needs to stop, bari dai na zo Katsina Jibi InshaAllah"
Murmushi yayi yace "Allah ya kawo ki K'amshi k'amshi".
Sunyi fira fiye da 1 hr kafin sukayi hanging.
Cikin Gida ya shiga don hado breakfast.
Yana kallon Shafa'atu na ta sintiri.
Tace "Dan Makaho baku tafi ba? Amma na ji dadi ina Dalo?".
Mugun Harara ya zabga mata ya shige kitchen.
*
Bari ta shiga ta gaida Yayanta da Aunty Asey.
Ta shiga da Sallama, ba wanda ya iya amsa mata, ganinsu tayi a kafe kamar an kafasu, ba mai iya motsi sai dai kallo daya zaka musu ka san cewa ransu a bace yake.
Labiba tace "Yaya lafia? Aunty Aseey meya faru?".
Babu wanda ya amsa mata sai chn yace "Labiba, Zauna".
Jin muryarshi tayi ba wasa ta zauna kan kujerar da ke kallon Gadon da suke.
Yace "Yanzu Labiba, tsakaninki da Allah, mai ya kaiki dakin Dan Makaho?".
Ta dan tsorata amma sai tace "Yaya, wallahi tun jiya nake ta kiranshi wayarshi a kashe, kuma banji duriyarshi ba, shine na je duba shi naji ko lafia ashe mamarshi ce tazo jiyan".
Ba wannan yake son ji ba.
Yace "dama chan kina zuwa dakinshi?"
Kai ta saddar k'asa tace "Eh Yaya".
Yace "Wallahi Labiba kin bani mamaki, kin ban mamaki matuk'a banji dadi ba, Labiba da na ga kin fito dakin dan makaho wallahi sai da zuciyata ta tsaya, wai kanwata da na fi so a rayuwa ta fito daga dakin Namijin da ba muharamminta ba, Labiba me kike so ki zama ne wai? Me kike maida kanki? Ba kya tsoron ya miki wani mugun abun?".
Da sauri ta giirgiza kai tace "aa yaya ba abinda zai min, na yarda dashi, ba zai min komai ba ba haka yake ba".
Baban Amira a kausashe yace "Labibaa, kar na sake ganinki kin shiga dakinshi, Labiba kar na kuma jin an ganki da DanMakaho, Labiba ki fita idona, na gaya miki sadakinki na gurin Abbanki, shekarunki 18 ke ba yarinya bace, Labiba kar ki yarda in sa miki ido a gidan nan".
Labiba ta sauka kan guiwowinta tace "Yaya kayi hakuri donAllah, ka yafe min, amma ni wallahi ina son dan Makaho Yaya, shi nake son aure, ka san labarinshi, danMakaho abun tausayi ne".
Ya sausauta murya yace "kinsan me kike cewa? So fa kika ce? Aure? Tab, Tausayinshi kike na tabbata, ki rufa ma kanki Asiri, banso mu bata dake Labiba".
Labiba tace "kayi hakuri Yayana Babana, inshaAllah ba za ka sake ganina a dakinshi ba, kayi min hakuri, ba zan kara ba, Aunty ki ba Yaya hakuri, ba zan sake ba". Ta tashi ta fita daga dakin.
Suka bita da kallon tausayi, kamar ba a hayyacinta take ba, lokaci daya ta zama wata zararrara.
"Ta na Sonshi" inji Aunty Aseey.
"Wani irin so"
Aunty Aseey tayi murmushi tace "Baban Amira So gaskia ne".
Yayi shiru yace "ya zanyi? Kar Labiba ta bamu kunya".
Aunty Aseey tace "donAllah kayi kokari dai ka rufe Wurin chan".
Yace "Aseey Bulo tsada , wurin chan zai ci Bulo 50 zuwa 60".
Tace "ko zaka ma Alhaji Zaki magana, tunda ba bayan yake zuwa ba na tabbata ya manta da tuni ya gyara".
Yace "gaskia ba zan mishi magana ba, kwanaki bakiji me yace ba".
Yanzu dai barinyi buga buga na ga zan iya siyo Langa Langan nan a rufe kafin na samu kudin Blocks, ya fita ta mishi fatan dawowa Lafia.
Aunty Aseey ta shiga gun Labiba ta ganta zaune ta na kuka.
Aunty aseey ta dafata tace "Labiba".
Labiba ta dago kanta ta kalleta.
Aunty Aseey tace "Me zakiyi da dan shaye-shaye?".
Da sauri ta share hawayenta tace "ni na san me zanyi dashi, Sonshi nike, Sonshi nake domin Allah Aunty Asiyah, Allah ka sa ya aureni, Allah ka sa in zama matar ZAID ALI ZAKI".
Da tsananin Mamaki take kallon Labiba, tafi zaton wani abu ya tabeta a k'wak'walwa.
**
Ta na zaune ta ga Message din Zaid, numbern Yasmin ya turo mata, kiranta tayi.
Yasmin na jinta ta kashe ta sake kiranta, sun dade suna waya. Kafin ta kashe ta kwanta don yin bacci kafin Azahar.
*
"Hello, gani k'ofar gida"
Hargowanta yaji "toufa, ba kuje Habujan ba? Sai yaushe?".
Zaid yace "donAllah nidai ina waje".
Baa yi minti 3 ba sai gata ta fito ko mayafi babu.
"Danubanka baka daina kirana kace kana waje, budurwarka ce ni? Zance kazo guna?".
Zaid ya harareta "wallahi zan danneki na dura miki World".
Harararshi tayi tare da kawo hannu kusa dashi, da ba dan ya gota ba da ta mareshi "Ubanka zaka dura min ba wall ba".
"Gaya man, kun fasa zuwa Habujan ne?".
Yace "sun tafi fa, suna hanya".
Tace "toufa, kai ya bakaje ba".
Yace "ni Nene? Ina zani? Babba dani, ni ina nan Gidan Babana"
Ta harareshi "ka zauna nan matar uba ta cigaba da gasa ma aya a hannu".
Yace "yo ai Nene ko da chan bata gasa min Aya a Hannu ba".
Tace "Ina dan shegiyan nan, kanenta, ai da Alhaji ya barni sai na gilleshi, na gunduleshi".
Sai yanzu abun ya fado mishi yace "wai da an barki sai ki yankeshi?".
Tace "Chab, takwaran Zaidu Bawan Allah har yau baka sanni ba, tsaf zan yankeshi billahilazi".
Zaid yace "Ni Yunwa nikeji Nene".
Tace "aiko yanzu na jefa Danwake, bakaji dadin da yayi ba".
Bata fuska yayi yace "Danwake kukayi?".
Tace "Kai wannan abun sukayi Macaroni, ban fa ci, shine fa na jefa danwaken".
Yace "Ni Macaroni zanci"
Ta bata fuska tace "Jibeka uban yan iyayi, wanda iyakan ka Nigeria, ko iyaport baka taba zuwa ba, ka tsaya feleke, to jikata Nasiba na chan Ingila tana bina na aika masu da Garin danwake".
Zaid ya girgiza kai yace "Zaki ban Abincin ko ba zaki bani ba".
Kallon Sama da kasa ta mishi tace "Zan baka, Ubana, Mamman, Macaroni ko? Jira na zubo ma, kar ka juyan baya na shiga duniya, naga sai wani kallo kake man kamar zaka zagar min Uwa".
Da hannu biyu ya dafe kai yana Nadamar duk abunda ya sashi zuwa Gidan Lema Gun Nene.
*
Ta tashi bacci, ta fito yin Alwalar Azahar ta ga Gidan duk Langa Langa, an rufesu, ta san aikin Ya Muhammad ne, girgiza kai kawai tayi ta shiga Toilet.
Zaid ma ya sha mamakin ganin an katange Gidan da langa langa, haka kurum sai ya ji ba dadi, amma ya zasuyi?.
Da Laasar suka hadu a Masallacin Bakin Titi.
Gaishe shi yayi ya amsa ba yabo na fallasa.
Yace “DanMakaho, meke tsakaninka da Labiba? Ka gaya min gaskia tsakaninka da Allah”.
Zaid ya dan murji Idonshi yace “Yaya Sonta nikeyi, kuma ina son Aurenta”.
Baban Amira yace “Ashe sonta kake? Dan Makaho kayi nauyin baki, akwai wani mai Sonta, sunje chan Gida Edo, an bashi Labiba, karshen magana ma, Sadakin Labiba na hannun Babanta”.
Gaban Zaid ya fadi, yace “Yaya, na san ba zaka so tarayyata da Labiba ba, amma dagaske nake sonta, kuma wallahi na bar shan komai, har sigari, donAllah kar ka raba ni da ita Yaya”.
Tausayi ya bashi yace “kayi hakuro Zaid, wallahi dagaske nake, an bayar da Labiba, wallahi sadaki naira dubu 50 na gun Baba, daurin Auren cikin kwana 40 da wani abu, wallahi kaji na rantse ma”.
Jiri ya ji yake dibanshi sosai, sai da Baban Amira ya tallafo shi, kwacewa yayi yayihanyan Gida, sauri sauri gudu gudu.
Hankalinshi in yayi dubu ya tashi.
Gadonshi ya fada, zuciyarshi wata irin zafi take.
Wayarshi yayi ringing, ‘yar halak ce, ya dauka.
“Hello Soulmate”.
Da kyar ya iya cewa “Bibbs, meyasa ba ki fada min you are engaged ba”.
Gabanta ya dan fadi tace “Inji wa?”.
Yace “ba Inji wa ba, gaya min dagaske ne?”
Tace “Eh dagaske ne amma..”
Bai tsaya jin mai zatace ba ya katseta yace “babu amma, abunda nake sonji kenan, ina miki fatan Alheri, Allah ya sa Alheri ya baki dauwammen Farinciki a rayuwa”.
K’it ya kashe wayar.
Hankalin Labiba in yayi dubu to ya tashi, ta kira wayar kashe, da sauri ta tashi ta fita, karo sukaci da Baban Amira, ta dan ja birki, me ta tuna me ta tuna ta koma cikin daki.
Shikam Zaid Zuciyarshi wani irin tafasa take.
Mai zaiyi? Ji yayi kamar zata tarwatse, abu daya ya zo mishi, ba tare da wani dogon tunani ba, ya janyota daga karkashin Gado, sai da ya hadata sosai kafin ya kyasta, shegiar ce World, abunka da an dade ba a hadu ba, ya zuketa kamar ba gobe, yama gamawa ya hada da sigari, nan inda yake yayi Mankasss sai bacci.
Baban Amira zaune yayi a kan kujera tsakar Gida Labibata fito, kamar ba abunda ya faru tace “Yaaya, Babansu Aisha yayi Accident, ina so naje na duboshi”. Yarinyan nan wayau take so ta mishi, kila wani wuri zata hadu da Zaid.
Yace “Muje na rakaki, nima sai na duboshi”.
Mamaki ya kamata, meye haka? Don dai kar ta fita ita kadai? Tace “to muje”.
Haka suka fita, ya tsaida musu Napep, suka shiga tare sukaje Gidansu Aisha, tace da Yayanta suke, aka mishi iso, ya shiga ya gaidasu ya musu Allah kyauta gaba, ya tusa keyar Labiba suka koma Gida. Ba abunda ke fitar dashi sai Sallah Maghrib da Ishai, har yanzu wayar Zaid kashe.
A B U J A
7:45pm
Masu Aiki sun musu setting Abinci a kan Table, kowa ya samu guri ya zauna, banda Dalo da tace ta k'oshi.
Alhaji Abu yace "Ina Sadiya?".
Mancy tace "wai bata jin yunwa".
Alhaji Abu yace "yo me taci? Tun lemun da kowa ya sha a Mota? Ban yarda ba".
Ya kalli Jawad da shine k'arshen shigowa yace “Jawad, je kira man Sadiya”.
Mik’ewa yayi ya tafi dakin Mancy.
Tana zaune ta tana Waya da Yasmin ya shigo da Sallama.
“Aunty Yas, ina zuwa”.
Ta kashe wayar ta amsa Sallamarshi.
Zama yayi kan kujera yana kallonta.
Yace “me kika ci da zakice bakiji Yunwa”.
Murmushi tayi tace “dagaske bana jin Yunwa”.
“Oya tashi muje dining table ke kadai muke jira”
Bambarak’wai taji abun, bata saba ba, ita yau ake jira a dining? Tafi sabawa da zaman Daki.
Muryarshi taji “Sadyyy”.
“Tashi mu tafi, stand up”
Kallonshi kawai tayi, ya tisa k’eyarta suka fita.
Gabaki daya ‘yan table din suka juyo suna kallonsu, sai da ta zauna Abba yace “to Bismillahnmu, Sadiya, kiyi serving dinmu”.
Ta tashi a tsanake ta shiga zuzzuba ma kowa abinci.
K A T S I N A
Abun ya tsaya mishi a rai shiyasa ya kasa bacci.
Karfe 11:30 ya ji ana bude kofar dayan dakin. Tashi yayi ya leka, yaga Labiba ta fito tana Sanda kamar me shirin shiga sata.
Mamaki abun ya bashi.
Ya bita da ido yaga ta nufa Hanyar Gidan Ali Zaki, wurin Langa Langan, ido ya zuba mata yaga gudun ruwanta, ta ina zata bi?.
Gani yayi ta fara girgiza langa langa tana daddako kusoshi da suka danneshi.
Baki Baban Amira ya bude.
Aunty Aseey ta tashi tace “lafia?”
Bai bata amsa ba, ta tashi tazo bakin Window, baki ta bude da mamaki.
“Labiba?”.
Baban Amira yace “Shhh, tsaya muga mai take shirin yi”.
A hankali suka bude kofa suka bi bayanta a hankali, ta langa langa suke kallonta tana gaban dakin Zaid tana magiyar ya bude mata.
“DonAllah Soulmate ka bude min, zuciyana zafi, hankalina ya kasa kwancia, donAllah ka taimaka ka bude min na maka bayani”.
Kusan minti 20 tana mai magiya, sauri duk sun bi kafafunta.
Dabara tazo mata ta leka wurin ramin jikin kofar ta hangoshi sheme kan gado yayi baje baje.
Ta dan yi daria tace “au ashe bacci yakeyi, zan dawo gobe i love you”.
Baban Amira ya kalli Asiya suka jinjina kai, a hankali suka koma daki, suna kallonta ta shigo, ta gyara langa langan, harda daukan dutse ta bubbuga wurin kusa, ko tsoro batayi, ta lallaba ta shige daki.
Ai mamaki kashe su yayi, Aunty Aseey dai ta kwanta ta barshi zaune.
Jikinshi sanyi Yayi, Labiba tayi nisa haka bata jin kira, ya santa, kafiya gareta, in ba rabata yayi da garin ba, ba zasu rabu da junansu ba, yanke hukunci maidata Gida zaiyi Gobe InshaAllah.
Da Asuba ya gaya ma matarshi shawarar da ya yanke, bata ji dadi ba amma wannan ce hanya mai bullewa
Baban Amira ya sameta kan dardumarta a dakinta, ta gaishe shi, yace “Labiba, tashi ki hada kaya, Edo zamu tafi”.
Tace “Yaya Lafiya? Wani abun ya faru?”.
Yace “Eh to ina jin wani abu ya faru, amma sun ki gaya min, kuma na san in na ce musu zamuzo Abba zai hana, gwara muje kawai mu gani”.
Gabanta ya fadi tace “Mami ce ko Yaya?”
Ya girgiza kai yace “aa ba ita bace”.
Wayarta ta wawuro, ya fizge ya jefata Aljihu yace “na gaya miki banso su san zamuzo, in ba zaki tafi ba in yi tafiya ta”.
Da sauri ta tashi tace “Yaya wallahi ba zan iya zama ba, hankalina yayi Gida kuma muje”.
Yace “kiyi sauri kiyi wanka”.
Tace “Aa Yaya, mu tafi kawai, ka siya min Bread a Tasha”.
Baya son ta chanza raayinta, yace hado kayanki, tace “Akwatin a shirye yake, jiya na shiryashi”.
Yace “to mu tafi”
Yara na Bacci, Aunty Aseey tana ta hawaye, hawayen rabuwa da Labiba, sosai take son Labiba, bata so rabuwa da ita ta wannan hanyar ba.
Ganin Aunty Aseey na kuka, ya sa jikin Labiba yin sanyi sosai, ta rungumeta itama tana hawayen tace “Aunty Aseey inshaAllah bakomai, ki bar kuka, Yaya mu tafi da ita”.
Yace “Labiba ga yara, ba kudi sosai hannuna, kudin dawowa ma sai Abba ya bamu”.
Ta share mata hawaye tace “Ba zamu dade ba kinji Aunty Aseey?”.
Har bakin Kofa ta rakasu, suna fita bakin Titi suka samu Express guda biya. Ya tsaida su ka tafi Tashar KTSA don hawa motar Suleja, kasancewar babau Motar Edo daga Katsina, daga Suleja zasu hau Motar Edo.
Allah ya tsare Hanya.
*
Wurin karfe 1 na rana ErRabi ta kira kawarta tace mata ta dawo da Asuba, ance mata tazo.
Tace “gata nan zuwa yanzu yanzu akwai matsala”.
Aiko suna gama wayar ta ciri gyale ta fita ko Annah bata gaya ma fitarta ba.
*
Garin Kankia yayi dadi sosai sakamakon yayyafin da ake ta yayyafawa mai dan k’arfi, a gajiye ta dawo Call Room ta zauna, ta cire wannan takalma irin ta likitoci tana matsa k’afarta da wuyanta, wani doctor da suke cema Chief ya na mata daria “You look tired doc?”.
Tayi daria tace “Chief i am so exhausted Allah, i want to go home today but i cant drive, but first thing in the morning tomorrow InshaAllah”.
Ba ta ji mai Chief yace ba saboda wayarta da ta shiga ruri.
Ta dauka taga Sam ne.
Sam mai aikinsu ne kuma amintaccen Mummynta ne don cikin gidan ba inda bay shiga, shi Er Rabi ke aika yana kaima mabiyanta magani.
Dan tsaki tayi, kiran me yake mata? Ta dauka da “Hello Sam, what is it?”.
Yace “Ehn small madam, na you talk say make i holla you anytime wey Aunty Shafa show ba?(Eh Hajia karama kece kika ce na gaya miki duk ranar da Aunty Shafaatu tazo ba?”.
Da sauri ta gyara zama tace “Ehen..”
“She don come house, and she dey vex, i greetam sef she no answer me(Ta zo gida, tana cikin bacin rai, har gaidata nayi ma bata amsa ba”.
Yasmin tace “Sam, where them they?(Sam suna ina?”)
Yace “them dey Madam’s room”.
Tace “Abeg Sam, hurry enter the room on that switch wey i give you the other day, puttam for their front, send your account number nownownow” (danAllah Sam ka shiga Dakin nan, wannan abunda na baka kwanaki ka kunna minshi, ka ajeshi gabansu, ka turo min Account number dinka yanzu yanzun nan”.
Daria yayi yace “no wahala madam”.
Sai da yayi Knocking ya shiga da tray din karfe a hannu ruwa ne da juice, a jikin tray din ya manna recorder din, kamar magnet take ‘yar karama, in baka san da ita ba ba za ka gane zamarta ba, ya aje a gaban Aunty Shafa’atu ya fita.
K’amshi ta ciro wani abu kamar Mp3 a jakka ta sa earpiece. Ta dauki Jakkarta ta rataya tana tafiya zata tafi dakinta a Doctors quaters tana sauraran maganganunsu wanda duk hargowa ce ta zuwan Mancy da