Showing 54001 words to 57000 words out of 133269 words

Chapter 19 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt

28 Dec 2024

13062

"Ya Zaid ashe gun Mancy kaje baka tafi dani ba? Ya Zaid nayi waya da Mancy na, Mancy na ta kirani" Zuba musu ido yan Parlorn Sukayi, Shafaatu bakinciki kamar ya kasheta, wannan farincikin da sukeyi ya fi daga mata hankali, bata so ta ga ko da hakori daya ne ya fito da sunan daria, ranta ya baci.


Kasa hakuri tayi tace "DanMakaho tafiya kayi? Wa ka gaya ma zakayi tafiya?" Kallonta DanMakaho yayi yace "Kar naje gun Uwata? Sai na nemi izini? Kin yi kadan na nemi izininki" ya kalli Dalo da ta ki bari ranta ya baci yace "muje daki Dalo, muje kiga abunda na siyo miki" tsalle ta daka tace "Allah Ya Zaid naji dadi ko ba ka siyo min komai ba, da Mancy na nayi waya, kuma tace za mu dinga waya kullum" daria yayi wanda ya kara bak'anta ran Shafa, yace "muje Daki kar su huce.


Binshi Dalo tayi sai ji sukayi tace "ina zaki da daren nan? Dakin Yayanki? Ke karuwa ce zaki bi namiji dakinshi?" Zaid ya mika mata ledojin yace jeki gani nan zuwa ta bi umurnin Yayanta. Zaid ya taka har Parlo inda suke tsaye yace "Uwarki Ce Karuwa"
Hudu ya taho Zaid yace "kar ka soma, Agolan banza, ka san kayi gigin wani Abu bugun burauba zan maka yanzu".
Ya kalli Annah, yace "kinyi Asarar Uwa, Agola".


Ya kalli Shafa da take tsaye kamar an disata yace "Ni da Dalo muna nan zama daram a Gidan Ubanmu, baki isa ki koramu ba, ba ki isa ba wallahi, ko me zakiyi kiyi, ko me zaki sa ya mana ki sashi, amma baki isa ki sa ya koremu ba don ba inda zamu wallahi, in kinga mun bar Gidan nan, to Aure mukayi".


Ya juya yayi tafiyarshi, sai huci rai bace tace "bari Ubanka ya dawo" daga bakin kofa ya dakata yace "sai dai shi da kika raina, kar ki fasa hada mu da Mahaifinmu nikuma ba zan fasa miki duka ba, kinga ba wani abu bane don DanMiji ya bigeki" ya sa kai ya fice.


Wani ihun Bakinciki Shafa ta sake, Hudu da Annah sukayi kanta, bangaje su tayi ta wuce daki ta rufe.


DanMakaho Ya iske dalo a daki har ta fara cin shawarmanta dadi kamar ya kasheta.
"Yaya nagode nagode this is the happiest day of ny life tun bayan tafiyar Mancy".
Daukan shawarman yayi shima ya zauna yace "Nasani Dalo, i know".


Alhaji Abu Shamsu ya isa Gidanshi da Dare, yau ne yayi shirin gaya ma Uwargidanshi Hajia Lubabatu da Iyalanshu batun Aurenshi wanda zaizo a sati 3 masu zuwa.
Da Sallama ya Shiga Parlon Inda suke jiranshi gabaki daya.
Hajia Luba da Yaranta biyu Abdulhafeez da AbdulMajeed suna sanye cikin shiga ta alfarma.
Sannu da zuwa suka mishi gabaki daya, ya amsa da fara'arshi.
Direct Dinning Area suka wuce don yin Dinner.


Suna ci suna sha suna fira cikin jin dadi da soyayyar junansu. Alhaji yace "nikam Abdulhafiz ina Ummita ne? Kazo kana cinye min abincin gida" daria sukayi gabaki daya yace "Abba ta tafi Biki Kaduna sai ranar Lahadi zata dawo" Hajia tace "Ai Gauro ne bai da mata" suka sake daria.


AbdulMajeed yace "Abba da kaje Katsina ka ga Aisha?" Abba ya kurba ruwa yace "na ganta wai har ta kai SS2, ikonAllah yara suna ta girma". Umma tace "amma ka dai san dalilin da yasa Majeed ya tambayeka ko ka ga Aisha ko?" Majeed ya fara shurin Umma da kafa kan tayi shiru ta fara Dariya tace "to ba zan fada ba" Abdulhafiz yace "ni zan gaya ma Abba in ke baki gaya mishi ba".


Abba yayi daria yace "na san Zancen, ai sai ta gama Secondary zamuje ayi magana". Shidai Abdulmajeed kunya ya kama shi. Suka cigaba da cin Abinci kafin suka gama, suna niyan tashi ne Abba ya dakatar da ita, ta zauna su kuma suka wuce parlo.


Ya kalli Ummar yace "Hajia Luba, akwai abunda nake so na gaya miki".
Ta tattaro nutsuwanta ta bashi, "Hajia Luba, kin tuna Maryama wacce na baki labari? Da muka zo Abuja da Hajia?" Kai ta gyada tace "eh naganeta wanda Mijinta ya saketa ko" Alhaji Abu ya gyada kai sannan yayi dan Jim, kafin yace "So nike na Aureta".
Dimmm taji kafin ta dafe kirjinta tace "Aure kuma Alhaji? Wani irin Aure?" Yace "afuwan, donAllah kar ki daga hankalinki".


Nifa bangane ba, a kan wani dalili zakayi aure? In tausayinta kakeji ka bata jari mana, ba sai ka aureta ba, baka sakr aure tun kuruciyarka ba sai yanzu? Haba Alhaji".
Lallashinta ya fara yi, amma bata tausu ba ta cigaba da bude murya har sai da Abdulhafiz da Abdulmajeed suka zo.


Abdulmajid yace "Abba meke faruwa?"
Kafin Alhaji Shamsu yayi magana Umma tayi karaf tace "Majeed ni Abbanku ke son tonawa asiri, wai aure zaiyi, yana da Yara kamarku wai zai sake aure, ko Autanshi Jawad na neman shekaru 25 shine yake son tona min asiri".


Duk da sun ji maganar wani iri amma ba su nuna ba AbdulMajeed ya karasa gunta ya dafa kafadarta yace "Umma donAllah kar ki tada hankalinki".


Cikin karaji tace "Aure fa zaiyi, mai na rageshi dashi?" Abdulhafiz yace "Haba Umma, menene haka kike shirin yi? Ba mu taba jin kanku ba, menene don Abba zai kara aure? Umma ba a kanki zai ajeta ba, Umma Abba ba zai ki yin adalci tsakaninku ba, in Abba yau ya kawo wacce zata raina ki, kinsan mu Yaranki ba zamu yarda ba, donAllah ki kwantar da hankalinki, kiyi fatan a kawo maki ta gari wacce zaku zauna ku sake kwantar ma mahaifinmu da hankali" Abdulhafiz ya kalli Abbansu yace "donAllah Abba in wacce kake son aura zatazo ta tarwatsa maka farincikin Gidanka ne DonAllah kayi watsi da lamarin, amma in har zata kwantar maka da hankali ta k'i tada hankalin Mahaifiyarmu to Allah ya kawota Lafiya".


Fuuu Hajia Luba ta wuce daki, Da sauri Alhaji Abu yace "wallahi Maryama ba ta daga cikin Mataye masu tarwatsa farinciki Gida, in kuka ji labarinta zaku tausaya mata kuma zaku so ta kasance Aunty a gareku".
Abdulmajeed yace "In har ba zata daga Ma Mahaifiyarmu hankali ba to kana da goyon bayanmu Abbanmu, zamu tayaka shawo kan Ummanmu".


Hadesu yayi ya rungume yana sanya musu Albarka, Madallah da yara masu hangen nesa.


Da ban baki da Nasiha suka shawo kan Hajia, aka dai samu ta sauko daa fushin da tayi da Abbansu.
Biki ya matso aka sake gyara Gidan aka ware mata dakuna Biyu a cikin Gidan.


Zaid da Dalo kullum sai sunyi waya da Mancy, sun san zatayi aure, Mancy tace "suyi zamansu ba sai sunzo ba.


Haka aka daura Auren Maryama da Alhaji Abu bisa sadaki naira dubu 30 a nan kano, kamar auren Fari haka abokan Alh Abu suka zo.
Danginsu sunzo, Abdulhafiz da AbdulMajeed suka dauko Matar Babansu tun daga Kano har Abuja, ba ruwansu da taya Mamansu kishin haukan nan wanda yawancin mata keyi in aka ma Mahaifansu kishiya.


Nan aka danyi Walima wanda da shawararsu Majeed Hajia Luba ta hadashi. Dangin Maryama suka damk'a ma Hajia Luba Maryama, ba yabo ba fallasa sun karbi dangin Mancy, aka musu adduar zama lafia.
Da dare Alhaji Abu ya hada iyalanshi ya musu Nasiha ya musu fada ya masu fatan Allah ya hada kawunan su.
Abdulhafiz ma ya musu Nasihan zama lafia don kwanciyan hankalin Mahaifinsu, ya gargadesu kan su toshe kunnuwansu da ga jin tsegumin mutane.
**


Zama sukeyi da juna tsakani da Allah, ko wacce burinta ta burge Mijinta, Kishi irin na Yan Bariki sukeyi, Hajia Luba ta lura Mancy bata zo da raini ba, bata da matsala ko kadan, shiyasa ta kwantar da Hankalinta suke zamansu, Mancy ko ta na biye da ita, abunda yake dan sosa ran Hajia Luba shine yanda Abdulhafiz da AbdulMajeed ke son Mancy, komai Mancy Mancy, harta Matar Abdulhafiz ko ta zo Gidan da sun gaisa da Hajia Luba sai ta wuce dakin Mancy ta shantake, in Abdulhafiz yazo daukarta da ya shiga gun Mancy to fitowarshi ba lokacin ba sai sun sake bata lokaci, ta rasa mai suke cewa. Duk da ta san Mancy da son labari da jan fira shiyasa ta saye zuciyan kowa.


A duk lokuttan da suka shude tun bayan Sabon auren Mancy, ta kan tura ma su Zaid kudi duk wata, shiyasa ba ya rasa kudin zuk'an World.
Akwai wani Rana da Mancy ta aiko musu da kaya Shadda laces da atamfa kai harda provisions cike da Ghana Mustgo, Zaid yaje Tasha ya karbo, yana zuwa Gida ya kira Dalo ya na nuna mata Sak'on Mancy, kamar daga sama sai ga Alhaji Ali da Hajia Shafa.


Hajia Shafa tace "wannan kayan fa?" Banza Zaid yayi da ita ya cigaba da firdo da kayan ya na nuna ma Dalo, daka mishi tsawa Alhaji Ali yayi yace "bakaji ana magana ba? Wadannan kayan daga Gidan Uban wa suke?" Shiru yayi bai da niyyar amsawa.
Dalo tace "Mancy ta aiko mana dashi".
Sai da gabanshi ya fadi ya bi kayan da Ido. Hajia Shafa tace "ina ta samu kudin siyan wadannan kayayyakin tana zawarci?".
Dalo ta zuro baki tace "ta fa yi Aure".


Gaban Alhaji Zaki ya fadi da sauri yace "Maryamaa Tayi Aure?" Hajia Shafa da tsoronta kar ace Mancy Auren Kisan wuta ta yi don ta dawo dakinta, da sauri tace "to sai me in Auren tayi?" Nan ya fara "Sai me in Aure tayi? Ina abunda ya damemu da aurenta, zancen banza zancen hofi?".


Zaid tsaki yayi ya fara maida kayan cikin Ghana, Aunty Shafa tace "wai yanzu kai Alhaji ce mata sukayi kai baka daukar nauyinsu ne? Baka basu ci ba ka basu sha da zata aiko musu da provisions? Har da kayan sakawa, harta lipton don tonan asiri? Duk k'okarin da kakeyi a kansu ba sa gode ma ba sa godeAllah? Sai sun ce baka musu?" Ran Alhaji yayi dubu ya baci, yace "Allah ya tsine muku marasa gode Allah, duk abunda nike maku ba kwa gani?" To wallahi ba ku isa ku tona min Asiri ba, kamana ace ana turo da irin kayyayaki nan kamar na Mabuk'ata a gidana, ina Samson, kuzo ku k'onemin Kayayyakin nan".


Da Gudu Samson yazo don cika Umurnin Alhaji, Zaid yayi yunkurin hanawa amma Alhaji tuni ya fara tsinanshi, Dalo ta runtse Ido ta riko hannun Zaid, ta jashi baya, suna hange aka cinna ma Kayan Wuta.


Fargaban Hajia Shafa ace Mancy auren kisan wuta zatayi, ta samu Sarari ta kira Er Rabi ta gaya mata fa Mancy tayi aure a yi bincike a ga wata aure. Nan ErRabi ta kira Hajia Shfa tace "ke Maryama ta fi karfinmu don tana Auren Wani k'usa" nan kuma sai bak'inciki ya kaure.
**
Ran Mankas ya baci Ainun, amma Dalo ta taushe shi, ba su gaya ma Mancy ba, itama bata daina turo musu Sak'o in ta samu dama ba.
Ba da dadewa ba Mancy taje Dubai ita da Alhaji da Hajia Luba, ta musu Tsaraba, ta aiko musu dashi bayan dawowan su.
wani Jallabiya Dalo ta saka cikin tsaraban Dubai, Annah na ganin kayan taji Kayan sun mata kyau, cewa tayi ta je ta cire ta bata, dalo ta kalleta da mamaki, kafin ta bata amsa sai dai ji tayi Hajia Shafa tace "ina kika samo rigarnan? kije ki ciro ki bata kafin ranki ya baci, don munafunci ba Babanku ya hanaku karban abubuwa daga gurin Mahaifiyarku ba? Kije ki cire ki kawo ma Hannah ko yau Babanki ya tsine miki a karo na ba adadi. Jiki na rawa ta shiga ta ciro ta ba Annah, Annah ko ta fuzga taje ta chanza.


Annah ta ci kwalliya wai zata Gidansu kawarta, ta fita tana karairaya wurin inda ake prking Mota, kamar daga Sama sai ga Zaid, a Hak'e yake don yanzu ya zuk'i world yace "Ke wannan ba rigar Dalo bace? Tace "Aa" hr yayi gaba ya dawo baya yace "danubanki ba rigarta bace? Uwar wa ya siyo miki? Zaki gaya min gaskia ko sai na yankaki?" Da sauri tace "A ra min tayi" damk'o wuyarta yayi yace "cire don ubanki" jiki na rawa tace "barin je daki zan bata abunta" daka tsawa ya mata yace "a nan zaki cire danubanki".


Ihu ta kwala "Mummy" Mari ya katse mata hanzari, ya ja rigar tun daga Sama har kasa ya dire, ya fincikota ya kwabe mata rigar tas, kuka ta fara sosai ga cin mutunci gashi ya farka rigar. Allah ya so ta da vest a jikinta amma sharara ne har ana ganin Bireziyarta.


Shafa ta fito hankali tashe tana tambayar Annah me ya faru? Be bi ta kansu ba ya barsu a gun bayan ya dauki farkaken rigar ya saka a Bolan kusa dashi yayi hanyar dakinshi yana cewa da kuci arzikinmu gwara kowa ya rasa.


Ranan Har Daki Baba ya bi Zaid ya na ta tsinanshi kamar zai ari baki, shi ko Zaid din ko a jikinshi.
***


Watan Mancy 9 ta haifi diyarta Mace mai kama da Babanta, sosai akayi murnar samun karuwa a cikin Dangi balle duk yaran Alhaji babu Mace, dangi daga Katsina da Kano sukayi ta zuwa barka.
Hajia Luba ma ba a barta a baya ba don ta nuna Son Jaririyar.
Ranar Suna diya taci sunan Hajiar Alhaji Abu wato Halima amma ana ce mata Mimi.
Mimi na da Wata Biyar Autan Hajia Luba ya dawo daga Makaranta da sakamonshi na Masters wanda ya hado a Malaysia.
Jawad Miskili ne, shine Autan Umma, yasan Babanshi yayi aure amma ba ruwanshi da Mancy, daga gaisuwa shikenan, be iya shiga wurinta ya zauna kamar yanda yayyinshi keyi, indai Sun hadu a Parlo yana mik'a hannu ya karbi Mimi don Mimi son kowa ce, baya ganan bai da matsala da Mancy.


Wannan Kenan.


Jaje suka sake yi ma Juna a Massalaci, Alhaji Ali ya sake tabbatar ma Mallam Muhammad kan cewa kar ya damu shi zai sake gyara Bangon Gidan.
Kamar jiya Aunty Aseeyah ta tafi Gidan Iyayenta ta bar Labiba da niyyar in 10 tayi zata wuce Makaranta.
Kamar Jiya haka ta sake sando ta shiga dakin Mankas, yana zaune yana cin Bread da k'wai.


Kallo daya ya mata ya dauke kai, ko sau daya tunaninta bai fita daga kwakwalwanshi ba.
Da murmushi ta ce "Ina kwana YaZaid".
Shareta yayi ya cigaba da Breakfast dinshi ta k'araci zamanta bai tankata ba, ta mik'e da murmushi a fuskarta tace "ni na tafi Makaranta sai na dawo". Tak bai ce mata ba, haka ta fita ta barshi zaune ya bi bayanta da ido,ta tsallaka blocks ta fice abunta.


Runtse ido yayi ya bude, zuciyarshi na mishi wani irin zugi, sigari ya dauko ya fara zuk'a cikin Zafin nama.


Washegari


Haka aka sake Wani Ruwan Saman Ginin ya sake Rushewa, sau 3 kenan kasancewar lokacin damina ne kusan kullum sai anyi Ruwan Sama.
Hajia Shafa tace da Alhaji "wai kai ke da kudin banza? Kar ka sake ka kara gyarawa, in banda son banza shi ba zai gyara ba? Kuma su ma ake rufa ma Asiri tunda tsakar Gidansu ake gani, in abun ya dameshi ya gyara, kai kar ka k'ara Gyarawa kaji ai?" Da sauri Alhaji yace "Ba zan kara gyarawa ba, ai Muhammadu akwai son banza, ai kudin ba a bishiya nake katso su ba, in bai gyara ba ruwanshi". Da murmushi tace "yauwa Alhajina".


"In har ba damuna ta tsaya ba, Ginin nan ba zai bar rushewa ba"
Cewar Yaya Muhammad cike da damuwa.


"To ya zaayi" inji Aunty Asiya.
Baban Amira yace "wallahi ni kunyan Alhaji Zaki ma nike, ace duk rushewan da bangon yakeyi ko so daya ban taba gyarawa ba?" Tace "Ai ya san baka dashi kar ma ka damu". Yace "bari InshaAllah zan gaya mishi a bar gyaran haka har sai ruwa ya tsaya, in ba haka ba Allah na tuba asara zaayi tayi, anayi yana rushewa" Aunty Asiya tace "eh gaskia, Allah dai ya rufa Asiri".


A zuciyar Labiba kuwa ba ma taso a gyara, ita bata k'i a zauna a haka ba, hakan ne zai sa ta ga Sanyin Idaniyarta, sosai take jin shi a ranta, yanzu ma Jira take Baban Amira ya fita ta faki Idon Aunty Asiyah ta shiga.


Aiko yana fita tayi sadap sadaf ta fada Gidan Alhaji Ali.
Ba tare da jira ba ta fada dakin Zaid wanda daidai yake da fitowanshi daga Toilet daure da Towel a k'ugunshi.


Da sauri ta runste Idonta shi ko cikin zafin rai ya fincikota ya wurgata kan Gado yace "yau sai kin ci Ubanki, Wallahi yau ba zan daga maki ba".


Gadangadan yayo kanta...


Ghen Ghen.
Whats about to happen? Anyone?


Vote and comment line by line please


#1love
#DM
#FWASonSo
#anatare
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


Babi na Sha Hudu1⃣4⃣
(FUSHI😒😏)


Jin tambayar tayi wani iri, shi kuma gani yayi kamar ba ta ji bane, ya sake maimaita mata, "kin bar So na ne? Me na miki to da zaki bar So na? Ki cigaba da So na, kar ki daina".


Baki ta hangame ta na sauraro zantuttukan bakinshi, takaici ya turniketa, bai zo don ya fada mata yana sonta ba, ko kuma don yayi kewanta sosai, ta zata ya zo nemanta ne kamar yanda ya gaya mata cewa in tayi Aji k'ila ya kawo kanshi gareta, shin ba ta yi Ajin ba? Ko yin Ajin ya wuce Kama kanta na kwana biyu? Cikin daren nan zuwa yayi kawai ya gaya mata ta cigaba da sonshi? Seriously? Ya ma mugun raina mata wayau cikin zafin nama ta k'arasa wurin k'ofa ta bude ta sosai tace "Fita".


Sosai yayi mamakinta amma abun mamaki shine yanda ta rikide ta chanza lokaci guda.


A kausashe tace "ka fitar min a daki, kar kuma ka sake shigo min daki, duk randa ka fado min daki haka kamar yanda kayi, wallahi zan maka Ihun Barawo, tun muna Shaida Juna yanzu, ka fitar min a daki".


Sosai yayi mamakinta, jiki a sanyaye ya daga kafaffunshi da kyar ya fita ta gabanta, yanayi yana waiwayonta, ya na sa k'afa ya fita daga dakin ta datse kofar da k'arfi tana numfashi samasama, hawaye ta fara, ta ba kanta wahala , ta wahalar da zuciyarta.
Tashi tayi maimakon ta kwanta, sai ta cigaba da Sallolinta har bacci ya kwasheta a gurin.
Zaid kam tunda ya bar dakin k’afafuwanshi suka mishi nauyi, da k’yar ya isa dakinshi, ya zube kan Gado.


Hannun damanshi ya sa ya murji idon hagunshi, a baiyane yace “Mai ke faruwa da Beebs? Ya Allah!”.


A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login