Showing 90001 words to 93000 words out of 133269 words

Chapter 31 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt

28 Dec 2024

13073

da "Waalaikum Salam"
"Sunana Abdulhafiz Abu Shamsu, nine Babban wa a guri Jawad mai neman k'anwarka Labiba".
Baban Amira yace "to to, muna lafia?"
Suka sake sabon gaisuwa.


Yaya Abdulhafiz yace "Mahaifina ya Umurceni da na tuntubeka da Maganan Jawad".
Baban Amira yace "MashaAllah, kamar yanda na gaya ma Jawad, nace mai Inda gaske yake da Aure yazo, ya turo Manyanshi ga Manyanta, sai su nema mishi izinin zuwa zance kafin ayi na neman Aure".
Yaya Abdulhafiz yace "dama haka ya kamata, to yaushe zamu iya zuwa?"
"Ko yaushe kuka Shirya".
Yaya Abdulhafiz yace "shikenan zan tuntubi magabatarmu da maganan, kaima ka tuntubi naku, tunda ga waya sai mu ji yanda zaayi, amma for now muna son sanin Asalinku, Abbanmu ke tambaya".


Baban Amira yace "Mahaifanmu na cikin Garin Edo,a unguwar Uromi, Bari zan maka Text"
Yaya Abdulhafiz yace to shikenan mungode kwarai dagaske, ba, mu yan Anguwan Alk'ali ne, da ka tambayi Gidan Shamsu Abdulrahman Alo, zaa gwada maka gidan kakaninmu, sunan Mahaifin Alhaji Abu Shamsu, nima haka zan maka text gudun mantuwa".


Baban Amira yace "Ba laifi mungode kwarai".
Yaya Abdulhafiz yace "Sai kun jimu".
Sukayi Sallama.
Jawad baki uwa gonar audugu don burinshi na kan cika.


E D O


"Muhammadu kace akwai yaro mai neman Labibata?"
Daga bangaren Baban Amira yace "Eh Abba, suna ma maganar zuwa gunku neman Izini".
Alhaji Ahmad Dakata yace "MashAllahu, ya maganar mu?"
Duk da ya san maganar yace "Wacce Abba?"
Yace "Muhammadu Alkawarin da ka min na cewa da Labiba ta samu Miji zaka cireta daga Makaranta ka maido man Ita Gida na mata aure".


Baban Amira yace "ban manta ba Abba".
Abban yace "yauwa, auren shine rufin asirin duk wata diya mace, wanda tayi Allah ya sa mai Albarka, in Mijinta na da raayin karatu sai ya sakata in baidashi kuwa sai tayi yar sanaa tunda haka sauran yayyinta sukayi, amma Labiban ta amince ko?".
Baban Amira yace "Eh Abba, ita ta bashi numberta ya ba yayanshi ya kirani ai, kuma da yazo Gidana na gaya mata zan turo muku su, kaga ko tanayi tunda ta barshi yazo Gidana".
Baban yace "MashaAllah, wallahi naji dadi sosai, sai kaima ka fara naka binciken yanda suma zasuyi, in babu wata matsala sai a hade da bikin Yaruwarta Samira kafin Azumi".
Baban Amira yace "to InshaAllah Abba, a gaida su Mami da mutanen Gidan".
Sukayi Sallama.


K A T S I N A


Strike Din Likitoci bai dade ba, a hanyar Yasmin ta komawa Gidan Alhaji Zaki ta samu wayar sun dawo Yajin Aiki, ta garzayo Kankia she's on call, kuma akwai patients da yawa suna jiranta.
Gani tayi zata bata lokaci in taje Gidan Alhaji Zaki kuma ta tafi Gidansu ta kwashe kayanta, ya sa ta kira Zaid kamar jira yakeyi ya dauka nan da nan.
"Yasmin, ina kikaje you got me worried".
Murmushi tayi tace "Kankia zani, ana jirana a Asibiti, in aiki yayi yawa sai Weekends, in kuma ba aiki sosai zan dawo within the week, ka kula da kanka, kayi duk wani abun da ka san zai saka farinciki da jin dadi".
Zaid yace "InshaAllah"
Suka katse wayar.
A nan ne ya tashi ya shiga Cikin Gida don ganin Dalo kuma yayi Breakfast.


3:07 ta shigo Anguwar cikin Keke Napep, da 'yan Bencin Eskaley ta ci karo, ce ma mai napep din tayi ka tsaya nan. Ba ta fito ba sai da ta k'are musu kallo, ko wannen su da karan Sigari banda Mankas, ko ya gama shan na shi ne oho.
Fitowa tayi daga Keke Napep din ta k'arasa gun su, kanshi a k'asa, hayaniyar da suke mata ne yasa shi dago kai a hankali ya sauke a kanta.
Itama shi din take kallo.
Da sauri ya kauda kai, shi yanzu Labiba tsoro take bashi, kar ta mishi wani magana mara dadi, kar ta mai wulakanci gaban mutanen shi.
K'in kallonta yayi amma tana kallo yana dan satar kallonta, bata ce ma kowa komai ba.


Eskaley ne yace "Mankas wurin ka aka zo fa".
Kallonta ya danyi yaga tabbas shi din take kallo, to me ya faru? Me take so? Sai da ya dan bata lokaci kafin ya mik'e tsaye ya tako har gabanta.
Ido cikin Ido suke kallon Juna, 'yan Bencin Eskaley suka zuba musu ido.


Chan Labiba tace "Kai kace Kana Sona?".
Ido ya k'ura mata sosai kafin yace "Ni na ce ina Sonki.
"Har yanzu kana So na?"
Hannu ya sa ya dafe Zuciyarshi yace "Har gaban Abada zan So ki".
Idanuwanta ta lumshe ta budesu kafin tace "ina Sonka Fisabilillahi".
Murmushi yayi sosai har hak’oranshi suka bayyana tace “kaga Sauro ya cijeka, kar ka ya k’ara cizon man kai, bana so”.
Shewa 'yan Bencin Eskaley suka hau suna tafi, murna suke yi.
Terror yace "to wallahi Yayata ke gonarmu ce, duk wanda muka gani yazo gunki sai na sare mishi k'afaffu".


Murmushi tayi, ganin fuskokinsu da farinciki, its genuine, farincikin da ba kudi ya basu ba, farincikine na Solidarity da ta musu na son Danuwansu.
Ta gwada musu cewa Suma fa ‘yan Shaye Shayen mutane ne, suna da damar So, suna kuma da damar a So Su, Labiba kam ta tabbatar musu da hakan.


Zaid ya kallesu kafin ya dawo da kallon gareta yace “mu tafi Gida” murmushi ta mishi tace “mu tafi”.
Ba magana sukeyi ba, kallon juna sukeyi sai su dauke ido, sai su sake kallon junan, sai su kuma kawar da kai, sai suyi murmushi, sai suyi dariya, shine jin dadi da farincikin da suke ciki, duk wanda ya kallesu sai ya k’ara, kallo daya zaa musu a san cewa masoya ne cike da Soyayya da shaukin juna a lokacin.,basu damu da kallon da yan anguwa ke musu ba, don bama sa ganin kowa, junansu kawai suke gani, sauran mutanen dont matter, in dai zasu kasance tare, ba su da damuwa.


A bakin Gidansu Labiba suka toge suka tsaya.
Sama da k’asa ta kalleshi tace “Ka san kayi kyau Jiya?”
Daria ya subuce mai, be yi kokarin hana dariyar fitowa ba, bata taba ganin expression dinnan a tattare dashi ba, kawai sai ta jita cikin farinciki da walwala ganin ya sake da ita.
DanMakaho ya ga dai har nuna su ake ya lumshe ido ya budesu yace “Shiga Gida”.
Ta gyada mai kai alamun Amincewa.
Sai da ya ga shigewarta kafin shima ya shige Gidansu.


In har wani abun Farinciki ko na Bakinciki ya sameshi, world yake sha, amma yau kawai sai ya fadi kan guiwowinshi yayi Sujadda raka’a biyu don kam yaji dadi fiye da zato.


Ko da Yayanta ya dawo Gida suna zaune bakin daki akan tabarma suna cin Ayaban da ya kawo, Idonta kan Gidan Alhani Zaki so take taga ta inda zai bullo.
Baban Amira yace “dazu su Jawad sun kirani”.
Ita ina ruwanta? Ba ta shi take ba, ta Zaid take, bata damu da tambayan mai ya kira yi ba sai cewa tayi “dazun ne ya kirani wai na tura mishi numbernka”. Don ma kar ya ja wani magana ya sa ta mikewa ta shiga Dakinta.


Aunty Aseey tace “ke kuma da an fara magana sai ki fita? Baban Amira ya kuka kare?”
Baban Amira yace “eh yayanshi ya kira, na dai basu Sunan baba da Adireshin Gida kuma sun bada nasu, yanzu haka a kasuwa na tambayi wani abokina dan Anguwan Alkali a kasuwa, yace ya san Family din, kuma Alhamdulah naji bayani mai kyau, amma duk da haka ba zan tsaya nan ba, zuwa gobe InshaAllah zan shiga Anguwar Alkalin na tsananta Bincike kan Mahaifin yaro da shi kanshi Yaron duk da ba tashin nan bane, ba zai gaggara ba, da ka san wani wani ya san wani haka komai zaizo da sauk’i”.


Aunty Aseey tace “hakane, Allah ya sa a daidaita a yi damu”.
Amsawa yayi da Amin.
“Amma ka kira su Baba?”
Yace “eh munyi magana, ya bar min komai yace in fara bincike saboda su san wa zai zo neman diyarsu, in ma an daidaita so yake a hada da na Samira, kuma ya tuna min Alkawarim da na daukar mishi na da ta samu Miji za ta bar karatu, to muna Addua Allah ya sa shine Mijin”.


Guda Aunty Aseey ta sake tace “Ameen Wallahi, Karatun wa? Haba dai ai aure shi ne kan Gaba, ai wallahi Allah dai ya tabbatar”.


8:50pm


Ko da Jawad ya kirata sai taji yau duk haushinshi ma takeji, ko mai ya fada sam baya burgeta, a k’agare take ta katse wayar, da ya dauko magana a dokance sai ta sace mishi guiwa.
Ko da ya ce mata dazu Yaya ya kira Baban Amira.
Da sauri tace “Eh ya gaya min”.
Ita burinta ta katse wayar, shima ya lura kamar yau bata cikin yanayin, so sai bai matsa ba yace bari ya barta ta huta, haka suka aje waya”.
***
Ta na jin fitar Aunty Aseey daga dakinsu ta koma nasu dakin, tana ji ta saka sakata ta tashi ta dauko wayarta ta ma Zaid text.
Yana cikin shan sigarin shi yaga shigowar message dinta
“Kayi bacci ne?”
Daria Yayi kamar tana gabanshi ya ja sigari ya fesar cikin jin dadi yace “haba dai ko 11 batayi ba fa”
“Me kakeyi?”
“Zaune, missing dinki”
Tace “buri daya”
Yace “In kasance tare da ke daga yau har har abada”.
Batayi reply ba sai yayo zaton ko katinta ya k’are ya yanke hukuncin kiranta.
Ya zuk’i Sigarin karshe ya hangota ta window da sauri ya yarda ya murje be kai ga fesar da hayak’in bakinshi ba ta shigo dakin da murmushi a fuskarta.
Kallo daya ta mai ta san cewa baida gaskia sai tace “Yadai nawan?”. Kai ya gyada mata, tace “ka zama kurma ne?” Ya sake girgiza mata kai tace “fito da hayak’in zai maka illa”.
Cike da kunya ya juya mata baya ya fitar da hayak’in ba tare da ya bari taga yanda hayakin ya bar bakinshi ba”.


Zama tayi tace “its obvious, na san shan sigari kake, tun daga Tsakar Gidanmu na jiyo hayakin, kunya yaji sosai ya shafa k’eyarshi yace “Sorry”.
Ba ta damu ba tace “Well, burinka na son kasancewa tare dani daga yau har abada nazo ka ganni na yau din kafin kayi bacci”.
Sosai yake kallonta yana nazarinta ganin kallon yayi yawa tace “Yadai?”.
Yace “Ina tsoro”
“Tsoron me?”
Yace “ni dake bamu dace ba”
Tace “ah haba dai?”.


Ganin tana son maida abin wasa yace “dagaske nake, i am serious, bamu dace ba, wallahi gani nake kamar ma na kwareki, kamar cin mutunci ne nace ki Soni, kamar na zubar miki da kima nace ke nake so, ina jin kunya harga Allah”.
Tace “DonAllah ya isheni, ashe a goshi ake rubutawa ace wance da wane sun dace, ashe a goshi ake rubuta wane da wance basu dace ba, ashe baka yarda da Son So daga Allah bane, ashe baka yarda domin Allah nike sonka ba”.
Ya girgiza kai yace “ba haka nake nufi ba donAllah, wallahi bakiji kunyarki da na ji ba da kika kamani redhanded ina shan sigari, naji kunya, kuma ina tsoron abunda zai faru nan gaba in mutane suka son cewa soyayya mukeyi”


Tace “huh, yaushe ka fara damuwa da abunda mutane ke cewa game da kai?da zaka damu da abunda mutane ke cewa da ba ka taba fara shan sigari ba, da baka taba zama a bencin Eskaley ba, da baka yi abota da mutanen da sukayi kaurin suna ba, to kar ma ka sake kaji kunyata wai don kayi shayeshaye, in har ba zaka ji kunyan Allah ba, waceni Labiban Dakata?”


Kai ya sadda k’asa ta hango nadama da da nasani a cikinta sasauta murya tayi tace “ba a film ko novel bane balle na ce zan chanza ka kafin na soka, banda ikon chanzaka, kai kadai ke da ikon chanzaka, kai kadai zaka iya chanza kanka, Sigari, addiction ne ko? Fine ka saba, ba zaka iya daina sha ba, okay, regulate in kana shanta so dari a sati, ka shata so sha biyu a sati, in so 10 kake shanta a rana, ka shata rabi a rana, in so daya kake shanta a kwanaki 3, ashe zaka ma iya bari kwata kwata, na san da wahala, i know its hard, i know amma regulate, ba umurni nake baka ba, shawara ce, ba don Labiba ba, don Lafiyarka, na san kana shayeshaye amma na furta maka kalmar so, which means ban damu ba”.


“Allah ne ya dora min sonka, to ya zanyi? Cizgeka zanyi a raina bayan Allah ne ya dasa min Sonka a raina? Ba fa zabina bane, in zabi na ne Makka zanje na So Sudaiz, so ina so ka san its Natural, Ina sonka saboda Allah, fissbilillahi wallahi, kafin na furta maka kalmar So, na san akwai k’alubale da yawa, da complications kala kala da zasuzo, akwai abubuwa da dama wanda na san Sonka zai ja min, i damned the consequences and chose to love you, so ka min adalci ka bar cewa bamu dace ba, ni da kai mun dace fa, ban cire rai zaka daina shan sigari ba, ka ceci unborn kids dinmu kar a dinga jefansu da maganganu marasa dadi saboda haka, so you need to change for good”.


“Labiba zaki iya aurena?”
“Toh zancen kake so, wai kai baka da android phone? Da kana dashi da video call zamuyi whenever you miss me, ba sai na sha wuyar zuwa ba kamar wata baraniya”.
Murmushi ya mata yace “tashi na raka ki Gida”.
Ba musu ta fito ya rakota tare da jaddada mai tana sonshi din, ya gasgata din,ya dawo zuciyarshi wasai tare da k’uddirtawa zai rage shan Sigari kuma ya bar shan world”.


Washegari Zaid ya tattara kudin Account dinshi Tas ya siyo Android phone ba don komai ba don ya dinga Chatting da Bibbs dinshi.
Aikam cikin kwana dayan nan sukayi wata irin Shak’uwa, son junansu suke sosai, har ya jirata ta dawo daga makaranta, ta tsaya Shagon Eskaley, suna faman yin selfie da wayarshi, ya na ganinta ya nufota yau ma shigar Yard akayi Ash wanda K’amshi ta dinka mishi
Labiba tace “wai hotuna akeyi da sabuwar waya? Inye, kayi kyau sosai wallahi naji dadi da na ganka haka”.
Yayi murmushi yace “naji dadi da kika ji dadi, nima zan dinga saka irin kayan nan don in miki kyau kiji dadi”
Tafi tayi cike da jin dadi
Yace “na san kin gaji ko? Muje Gida ki huta”.
Sallam sukayi da su Eskaley suka fara strolling, ba su damu da masu binsu da kallo ba, kawai son junansu suke ba su damu da kowa ba”.
***


Yana son kiranta amma bai da kudi, sabuwar waya na gun Tero da ya koma an so wayar ba ya nan, baya so kuma ya matsa mata kar ta ga kamar so yake tazo gunshi irin na jiya, shiga yayi cikin Gida ya bata lokaci wurin Dalo kafin ya dawo Daki. Yasmin ta kirashi wurin k’arfe 10:30 waya suka hau yi tana bashi labarin gajiar da tayi, sai wurin 11 suka aje wayan.
Mai ya kamata yayi? Baya jin bacci, fitowa yayi wajen daki, ya zauna kan dakalin gaban daki yana tunanin karon su da Labiba dazu kalar farinciki da ta sakashi, kai ya daga sama yana kallon kyawawan taurari.


“Fitsari ta fito? Ruwa ta fito Sha? Allahu Aalam, shidai kawai yaga Labiba ta tako har Gidansu ta zauna a kan Dakalin da yake zaune a kai tare da daga kai sama suna kallon sararin samaniya a tare.
“Suna da kyau” tace mishi cikin wani murya.
Yace “taurari? Suna da kyau sosai kam”
Wani irin dadi ke ratsasu yana shiga kowani sassa na jikinsu.
Idonshi ya murza ta girgiza kai tace “ka daina, ka daina murza idon nan” kallonta kawai yakeyi, kamar ya hadiyeta don So yace “Ina Sonki Bibbs”.


Cike da shagwaba tace “wannan Auntyn fa?” Zaid ya murmusa yace “ta koma Aiki”
Ta dan maido hankakinta gareshi ta “Son ka takeyi ko?”.
Dan jim yayi kafin yace “Yas ba matsala bace”.
Labiba ta turo baki tace “wace iri ce ita? Tana Sonka kuma take son ganin ta hadamu?”.
Murzan ido ya sakeyi yace “yin maganarta dake, ban mata adalci ba”.


Labiba ranta ya dan sosu ganin Antyn na da mahimmamci a rayuwanshi tace “Fine, ni son iyawanta ne bana so, tana acting kamar ta fi kowa Sonka a dunia, ga feleke da iyayi, shekaran jiyan nan da tace ta rakoka zance wurina kamar na mutu wallahi saboda da takiaci, kai ma ka fi ban takaici duk ka ban haushi da ka biyota wani zololo kai an rakoka zance, dont you have legs?”.


Ji yayi ta burgeshi Ainun yanda take magana cike da sanyi amma ita a ganinta ranta bace yake.
Zaid yace “Kishi kenan?”.
Baki ta turo tace “oho, nidai kar ta sake wani cewa ta rakoka Zance”.
Dariya yayi yace “Yes Ma”.


Kema wannan da yazo gunki rannan Sonki yakeyi, kuma har daria kike mishi, you look happy, harda murguda baki..
Daria tayi tace “Jayy dina kenan”
Hararta yayi yace “meye kuma Jay”.
Tayi daria tace “J for Jawad”.
Baki ya tabe “meye wani J? Aa H ne, you are so Unromantic”
Tayi daria tace “why are you like this?”.
Yace “point is i dont like him, kuma dagaske kar ya sake zuwa wurinki, kin dai ji ai mai su Terror suka ce miki jiya? Wallahi they will hurt him suka ganki dashi, and I cannot stop them, don ba ji zasuyi ba, so in ba so kike su karya mai k’afa ba, he should never come back again” ya fada yana dage kafada.


Harara ta zabga mai tace “kaga kai da mak’arabanka su fita daga hanyan mutane na? Poor Abu Sadeek tun ranar bai sake bari mun hadu ba, ina ta so mu hadu na bashi hakuri baya bari, kuma yayi blocking din chance din haduwar mu, bai ma zuwa School din sosai, ko yana zuwa wallahi nidai ban ganinshi”.
Dadi Zaid yaji ya tafa yace “weldone yaro yaji warning, so same thing will happen to that spoilt brat, dagaske kar ya sake zuwa”.


Dadi maganganun shi ke mata, ashe yana kishinta haka tace “nifa ka daina kora min samari”.
Ya hayyak’o yace “Labiba Ahmad i am dead serious, kar wanda ya sake zuwa wurinki, ke tawa ce nikadai”.
Kamar ta narke don jin dadi ta lumshe idanuwanta ta bude tace “I am dead serious Zaid Ali Zaki, ni taka ce, kai nake so har cikin raina”.
Cikin wani yanayi ya kalleta yace “har ranki?”..
Ta murmusa tace “Ehh, har chan cikin raina nike sonka”.
Yace “Ina Sonki Wallahi, ina Sonki nima”.
Tace “to dai Jawad kam ba matsala bane, abunda ya faru Cousin din Bestyta ce, kuma ni dama wallahi Girmanshi nake gani, and other days da muka samu sabanii, ji nayi zaman Katsina ya isheni, ni kawai i was desperate na yakiceka shiyasa nayi tunanin maybe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login