Showing 114001 words to 117000 words out of 133269 words

Chapter 39 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt

28 Dec 2024

13066

bane”.
Yace “Me kike nufi Labee?”.
Tace “Abba, a bar maganar Aurena da Jawad”.


Abba yace “Labee har Babanshi ya zo Cikin Parlo na, har ince na bashi ke? Har in karba Sadakinki yanzu kuma kice a bar maganar aurenku, ki sani karamar magana? ai ba zai yiwu ba Labee, ki maza ki fara mishi irin Son Auren, ba zanyi karamar Magana ba?”.


Labee tace “kayi hakuri Abbanmu, Auren dole kenan”.
Mamarta tace “Labibaaaa”.
Labiba tace “Abba aure ana so in anyi shi to zaayi zama na har abada, an fi so a aurar da Mace ga Zabinta”.
Abba yace “kina da wanda kike so ne?
Da sauri Baban Amira yace “Abba banso kowa yaji maganar nan ba, wani dan shayeshaye yake hure mata kunnuwa, wai shi take so”.
Tuni ‘yan Parlo sun fara tofa albarkacin bakinsu.


Abba yace “Labee, me nake ji? Dan shaye shaye kikeso?”.
Tace “Abba tsaya kaji, ba yin kanshi bane wallahi, k’addara ce ta maida shi haka, amma ya bari Baban Amira kai ka san waye Zaid a da, kai ka san ba halinshi bane, akwai dalilin da ya sa yake haka, ku tsaya kuji Labarinshi”.
Da alamu ta manta wa take ma magana.


Maminta ta jefeta da chazbin hannunta.
Shiru Labiba tayi.
Yaya Ali yace “Sigari kadai Abdulfatah ke sha, kika ce baki taba sonshi ko wani mai shan sigari, amma yanzu kice ga wanda kike so dan Shaye Shaye ne, baki isa ba to, bikin ki tare da Samira gwara ki shirya”.
Mamar Samira tace “Ku bar yarinya mana ta zabi wanda take so”.
Ita gwara Labiba kar ta auri mai kudi a barta da watsatse shiyasa ta fadin haka.


Ta k’i yarda ta hada ido da kowa ta ke cewa “Abba kai fa ka mana Alkawarin aura mana wanda muke so, kayi alkawarin ba za ka mana auren dole ba, haka ka ma yayyinmu da suka gabata”.


Abba ya gyaran murya yace “tabbas nayi ma diyana Alkawarin ba zan musu auren dole ba, wanda kika kawo shi zaa aura miki madamar baya da matsala, amma Labiba ke matsalar ta ki daban ne, da ba dan Shaye shaye bane, da na je har Gidansu Jawad na bawa Mahaifin shi hakuri na maida musu sadakinsu, na jaddada musu hakuri, amma auren dan Shaye shaye akwai illa sosai”.


Tace “Amma Abba..”
Ya katseta ta hanyar cewa “Ya Isa Labee, da dai wani ne ba wannan ba, in ba ki son Jawad din sai na samu mahaifinshi kafin ayi auren ki hanaku zaman lafia, na san halinki in har baki so abu ba, da kuma in kika sa kanki abu, to kar kisa mutuncina ya zube a idon jamaa, maganin kar a fara, kar ayi, amma ko kin ki auren Jawad dinnan, ba zaki taba samun wannan da kike so ba, don ni da hankalina ba zan aura ma Diyana dan shayeshaye ba, nagama magana, duk ku tashi ku ban wuri”.


Tuni hawaye sun wanke mata fuska, da gudu ta tashi ta fita daga parlon ta shige chan cikin dakin mamarta ta fada kan gado, kuka take sosai, zuciarta na mata zafi, haka daren ranan ta kwana kuka, Maminta na jinta tayi banza da ita don ta bata haushi sosai gaban mutane, ita ba a isa a gaya mata abu ta ji ba, sai abunda ta sa kanta tayi niyya.


Washegari haka ta kasance sukuku jikinta duk yayi laasar, ba ta jin dadin Maminta da Yaya Muhammadu, kyararta suke da tsangwamarta, duk ta fice musu a rai, to ba dole ba, tunda ba isa a saka ko a hanata ba.
Dakinsu Samira ta shiga nan ne take samun kwarin guiwan Samun Zaid don Mamar su Samira zugata takeyi kan ta nace ta dage sai Zaid, in ba ta auri wanda take so ba, zata dade tana nadama, ai ba zan yarda ba.


Haka ta yini a dakinsu Samira suna mata famfo, ta san da biyu suke bata shawaran nan, don dai kar ta auri mai kudi.
Zaid Fa?.


K A T S I N A


Jiya zaune ya kwana, bai kwanar Lafiya ba, baya da Lafia, jikinshi zafi sosai, massassara ce ta rufeshi, amma bai yarda ya kwanta ba, komai bai saka a cikinshi ba ya tafi Gidansu Yasmin , ji yake kamar zai ganta ta fito daga wani wuri, yanaso ace duk mafarki ne, wuri ya samu ya zauna, da yaji ance “ashe Yasmin lokaci yayi” sai ya fashe da kuka. Har wani abokin Baban yasmin ya nunashi yana tambayar shi waye wanchan? Ko danuwansu ne? Baban Yasmin ya kalli Zaid, ya yafito shi da hannu. Jiki a mace Zaid ya mike ya karaso su ya durkusa, daga inda ya durkusa suna iya jin hucin zafin jikinshi.
Baban Yas yace “kai wannan ma baka da lafia”.
Zaid ya murmusa yace “Ya k’arin Hakurin mu?”.
Baban yace “hakuri sai maaiki, kai zan tambaya haka, ina kula da kai jiya kowa ya tafi ya barka, yau kam tunda kazo kake kuka, Mamarta bata dangi nasan baka cikinsu, ba kuma ka cikin dangina, yaya kuke da Yasmin?”.
Gaban Zaid ya fadi, mai zai ce? Ya suke da ita? Zaice tana sonshi shikuma bai sonta? Wannan shine tsaka mai wuya”. Kasa amsashi yayi, abokin yace “kai ko Alhaji, ka san dai Mace ba a rabata da samari”.-
Alhajin yace “hakane, ko kaine Zaidu?”
Mai Zaid zaiyi? Ya fashe da kuka kawai, har babanta ya sanshi? Wani irinso take mishi?.
Allah sarki Zaid ashe dole kake kuka,haka kurum Yasmin na min maganarka, Allah ka gafarta ma Yasmin” abokin ya amsa daAmin.


Jiri Ke diban Zaid, da kyar yace “zan zauna”.
Alhajin yace “aa ka tafi Asibiti, baka da Lafia”.
Zaid yace “lafia na kalau”.
Alhajin yace “ka zauna”
Zaid ya koma chan wurin zamanshi a daddafe.
Yana zaune sai ga Doctors na General hospital katsina sunzo mazansu da matansu.
Gaban Baban suka gurfana.
Suka ma juna gaisuwa.


Dr Ali ya hango Zaid, ya karaso gunshi yana dafashi, da sauri ya janye hannunshi yace “Zaid you are sick”. Kallo daya Zaid ya mishi ya dauke ido.
Zama yayi kusa dashi, yace “Zaid wallahi baka jin dadi”.
Zaid cikin fada yace “Yasmin ce ta mutu, ta yaya zan ji dadi?”.
“Ba haka nake nufi ba, baka da lafia”
A takaice yace “Lafiata lau”.
Shiru yayi be sake ce mishi komai ba.
Drs sukayi mata Addua a bayyane suka tashi zasu tafi Baban Yas yace “DonAllah Drs ga dana chan ku duba min shi”
Wasu sukace “me ya sameshi?”.
Dr Ali yace “abokina ne, zan ganshi”.
Zaid tashi muje Asibiti, bai mai gardama ba ya mike, ya kalli Baban Yasmin yace “zan dawo anjima”.
Baban Yas yace “Yasmin ta yafe, ka dawo gobe”.
Zaid bai yi magana ba ya tafi luu kamar zai fadi, sai da Dr Ali ya tallafo shi.
Suka shiga Mota.
“Gida zaka saukeni”.
Ya fada cike da umurni.
Dr Ali yace “Zaid”
Yace “aa donAllah, banda karfin gardama kawai saukeni Gida”.
Dr Ali bai ce komai ba ya nufa Gidansu Zaid.


Tunda Zaid ya kwanta kan Gadonshi yake ji kamar ana sakko mishi da wani irin azaba, a hakarkarinshi da cikin cikimshi, wani irin tari yakeyi mai jini, ya na dafe kirjinshi, ga yunwar da ke cinshi, rabonshi da abinci, tun kafin yaji mutuwar Yas.
Bai ma da karfin fita, haka dare ya riskeshi, yayi Sallah, Sallahr Isha’i ciwon ya lafa ya samu bacci..


Ita kam yau ta kasa bacci, karfe daya saura ta gani, cikin kayanta ta ciro wayarta, rabon da ta kunnashi tun Jiya, ta kunna.
Ta shiga whatsapp.
Besty dinta online tana tambayarta me ya sa yau bata je School ba? Tace mata ta zo Edo amma weekends zasu dawo, besty tace ta gaida Gida
Labee ta tambayeta yaya jikin Baba? Ta amsa da ya ji sauki.
Status ta shiga, ta ga Post din Soulmate wanda yayi 18seconds ago, da sauri ta bude.
*Ya Allah ka gaffarta ma Yasmin, ka sa ta Huta, Allah ka yafe mata kurakuranta, I miss you Yas, alot*.


Gaban Labiba ya yanke ya fadi, wace Yasmin ta rasu? Wacce? Jikinta na rawa yana bari, ta dialling number Zaid kamar jira yake ringing daya ya dauka.


Ya na dauka tace “Wace Yasmin ta rasu, donAllah ba Aunty Yasmin ba”.
Zaid yace “Ta rasu Beebs, Yasmin ta rasu” ya fashe da wani irin kuka da ya sa Labiba Kuka.
Tace “na shiga Uku, inallilahi wa ina ilaihirrajiun, Ya Allah, ta rasu? Ya Rabb, me ya sameta?Shekaran jiya fa mintinmu Arbain muna waya”.
Yace “Accident fa, Motar ta ci da wuta, Wuta ya kasheta Beebs,”.
Tace “Alhamdulilah, tayi shahada, da wanda Gini ya fado mishi, da wanda aka kashe, da wanda wuta ta kashehi, da wanda” bai bari ta kai aya ba yace “nasani Beebs, na sani, Allah ka karbi shahadarta”.
Wani sabon Kuka ya sake, ta san yanda yake son Yasmin, ta san yana cikin tashin hankali, jibtake kamar tayi tsuntsuwa ta duro katsina, ta lalasheshi tace “How are you now?”.
Kusan da sauri kamar jira yake a tambayeshi yace “Beebbs i am not fine, i am Sick Wallahi, beebs ina ji cikin jikina i am dying”.


Hankalinta ya tashi, tace “in maka addua?”
Kamar yaro k’arami yace “ki min Addua”.
Hawaye take sharewa tace “ka dafe inda ke maka ciwo”
Da sauri ya dafe saitin zuciyarshi yace “na dafe”.
Tace “bismillahi Bismillahi Allahumma La Sahla illa ma ja’altahu sahla, wa anta taj alal hazana iza shi’ita sahala”. So bakwai ta maimaita mai.
Tace “kayi hakuri, zakaji sauki kaji?”.
Yace “ki kwanta”
Tace “To, in ka kasa bacci ka tashi kayi sallah ka rokar mata Yafiya gurin Allah, shi ta fi bukata kaji? Banda kuka, ka min Alkawarin ba zaka sake kuka ba”.
Yace “Beebs, ba na mata kuka mai sauti, ba zanyi magana ba kuma, amma Yasmin ce, yau kwananta biyu a k’abari”.
Labiba ta rufe baki sakamakon wani kuka da ya ci karfinta,tace “bye” ta kashe wayar.


Tana aje wayar ta fashe da wani irin Kuka mai tsuna zucia, Yasmin ta rasu, Allahu Akbar, Allah mai yanda yaso, Allah mai rayyukan mutane, duk lokacin da ya bukaceka sai kaje, shekaran jiya ta kirata fa, sun dade a waya har ta kosa Yasmin din ta kashe wayar don ta gaji da waya da ita maganganun da suka ba Labiba haushi a lokacin da take gaya mata su suka soma dawo mata *ki So Zaid da duk wani abun da kike dashi, da zuciyarki da jikinki, da ruhinki, ki soshi, ki kuma kula dashi*
Ta fada haka yafi so goma, ashe maganarsu ta karshe kenan? Ashe wasiyya ma ce kenan? Ya Allah, bata san Yasmin da dadewa ba, amma ta san tana da kirki sosai.
Tashi tayi ta dauro Alwala ta hau Sallah har karfe ukun dare, sosai ta ma Yasmin Addua.


Kasa bacci sukayi su duka,
Labiba tace bari muga ko yayi bacci, kiranshi tayi a waya, ya dauka, a lokacin wani tari yake mai karfi, ya dauka beebs, muryarshi taji tace “ka fara bacci ne?”.
A wahalce yace “aa beebs”
“Ya naji muryarka haka?.”
Yace “bani jin dadi, i naji kamar zan mutu, tarin Jinina ya karu”.
Da dan karfi tace “tarin jini? Wani irin tarin jini?”
A ranshi yace ashe bata sani ba, kafin yace wani abu wayarshi ta mutu Low battery.
Labiba ta kira ta kira kamar tayi ihu wayarshi kashe, nadamar duk wani abun da ya sa ta biyo Mallam Muhammadu Edo, da bata biyo shi ba da yanzu tana gefen Zaid, hankalinta kacokam yayi gun Zaid, jikinta duk ya mutu, me zatayi? Ta rasa abunyi.


Shi kuma ciwo yafi karfinshi ya sheme a daki yana jin ciwo ko ina a jikinsa.
Baccin da baizo idon Labiba ba kenan, zuciyrta ta gama yanke mata hukunci, katsina Zataje, katsina zata, ko biyar bata da shi.
Abunda bata taba yi ba tunda uwata ta haifeta yau tayi, Sata.
To sata ne mana tunda ba bata akayi ba, ma’ajiyar Maminta ta bude ta dauka naira dubu biyar.
Asubar Fari ta faki ido, ta fita, daga ita sai side bag, ko tsoro bata ji ba, ta tsaida Okada tace a kaita Tasha.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉


BABI NA TALATIN 3⃣0⃣
(FASA K'WAI 🥚)
(YAFIYA🤗)
(FARINCIKI😃)




Zaid ya runtse ido hawayenshi na fita, yace "Beebbs ina sonki da duk wani numfashin da nake ja ina saki, na san kina sona, ba sai kin sadaukar min da ranki ba, ba sai kin min haka ba, beebs donAllah ki bari, na rok'eki da Allah".
Labiba ta kyafta idanuwanta so biyu tace "Ina Sonka Sabida Allah, abin Alfahari na ne ace yau akwai ni a jikinka, in Allah ya sa an dace, zamu rayu tare, in ba haka ba, zamu mutu tare".
Yace "kinsan hakan na nufin kin kashe kanki da kanki, kinsan hukuncin wanda ya kashe kanshi?".
"Ni ba haka nake nufi ba, Allahn da rai na ke hannunsa ya san Zucia na, ya san niyyata, zaa dibi Hanta ta a dasa maka, end of discussion ".


Kyaleta yayi ya runtse ido tare da juya mata baya, gwalo ta mishi tare da maida hankalinta kan k'ofar da aka turo.
Dr Habib ne, Dr Ali yace "za a tura kudin Surgery account din Asibiti before a shiga da shi Operation Room".


Labiba ta dan kalleshi tace "Ohh, I thought Government Hospital ne, gwamnati ba ta biya ba?".
Dr Habib ya kalleta, yana son Confidence dinta yace "Gwamnati na dai tallafawa, amma ai ana biyan Aiki, ba kamar private hospital ba, sosai ba zaki hada kudin da na chan ba, akwai sauk'i rangwame sosai".
Tace "Okay nawa ne?".
Yace "ga takardan nan kije bursary department, ki basu zasu baki bank details da transaction slip ki biya sai ki kaima cashier ta baki receipt dai ki kawo mana".


Zaid na jinsu yayi lamo, hankalinshi ya dan kwanta, ya san bata da kudin da zata biya, ko da 20k ne balle ya san sai ya fi.
Direct chan ta nufa da taimakon sign boards.
Ta bada slip din, a computer akayi danne danne aka mata printing.
Expenses din naira dubu dari uku da saba'in.
Gaban Labiba yayi mugun sarawa.


Chabda, in ba a biya kudin nan ba zata iya rasa Zaid ko? Aikam ba zata iya jure rashinshi ba, ya kama ko meye zatayi don ta samo kudin nan, dakin Ta koma hankalinta a dan tashe.
"Kanaji ba?".
Banza yayi ya kyaleta.
Tace "Masoyin, na fa san ba bacci kake ba".
Ya juyo fuska daure yace "Meye?".
Tace "Wai kudin Aikin 370k".
Yace "Alhamdulilah, your Liver is safe".
Tashi tayi tace "kayi ka gama, zan je neman taimako".
Yace "Ina? Tace ko ma ina ne, ko bara ne i will do it, but ganin bamu da time zan rok'a su mana bashi zamu biyasu".
Zaid kallonta kawai yakeyi, sonta na tsaga hantarshi mai ciwo, komai nata na burgeshi, wautarta na kayatar dashi.
Cikin wasa yace "ke kika aje su da zasu miki aiki Kyauta? Ohh bashi kika ce ko? Tsoron ki sukeji Ko?".
Ganin yana son maida abun wasa tace "ka yi ka gama, banda lokacin wannan yanzu barin je in ga Dr Ali".


Har ta kai gaban k'ofa ta choge ta tsaya, mai ta tuna oho, maida kofar tayi ta rufe ta dawo cikin Dakin Zaid na kallonta.
Mai take shirin yi?
Wayarshi ta dauko ta kunna, har tayi 19%.
Har gabanshi ta tako ta dauki yatsarshi ta dangwala a wurin thumbprint wayar ta bude.
Hoto yaga ta daukeshi kusan guda uku, kafin ta dauki takardan hannunta hoto.
Kallon Mamaki yake binta dashi.
Matsawa tayi dan gefe amma yana kallonta taka danne danne a wayarshi.
Baayi minti 3 ba yaji wayar tayi ringing.
Amsawa yaga tayi ta sa wayar a Kunne.


Tana jin muryar ta san hankalimta a tashe yake "Hello? Zaid meya sameka? Me ya faru?".
Labiba ta amsa a ladabce "Assalam Alaikum Mancy, Sunana Labiba Ahmad Dakata".
Da sauri Zaid yayi yunkurin tashi amma ya kasa.
Mancy tace "wacece ke? Me ya samu Zaid? Ina yake?"
Labiba tace "Ya na bukatar Emergency Open Liver Transplant Surgery".
Kusan da karfi Mancy tace "Lahaula wa la kuwatta illa billah, Zaid din? Me ya sameshi haka?Liver Transplant fa kikace"


Labiba tace "Emergency ne,Hantarshi ya fara damage, suna so a cire infected area a saka wani, an samu donor, amma ba a samu kudin Aikin ba".
Da sauri Mancy tace "DonAllah zan kiraki, Ina zuwa".
Mancy ta kashe wayar ta fita,dalo ta bi bayanta.


Wai Beebs ke baa gaya miki magana kiji? Ba kya jin maganata ko? Ba a isa a hanaki abu ba ko?".
Kulle idonta ta tayi ta bude, murya ta sassauta tace "ya kake so ayi?".
Shima ya saukar da murya yace "kar ki wahalar da kanki, ki bar Hantarki, Hanta fa ba kamar k'oda bane, aka samu matsala, akwai yiwuwar daga ni har ke babu mai tsira".
Tace "to ai yafi nayi ta zaman jiran gawan shanu, yafi ace na zauna banyi komai ba, yafi ace na kasa taimaka ma wanda nikeso, donAllah mu bar maganar nan, Mancy tace zata kirani".


Zaid yace "Beebs ba kya jin magana".
Ta murmusa tare da mikewa don amsa kiran Mancy tace "nima ina sonka".
Harara ya galla mata ta fits tana daria.


Alhaji Abu Shamsu ya karbi wayar yana magana da Labiba, itama Office din da ta bar Dr Ali da Dr Habib ta nufa, ta ba Dr wayar, nan ya ma Alhaji Abu Shamsu bayani, da cewar an samu Donor wani bawan Allah, kamar yanda Labiba tacr musu su ce.
Alhaji Abu yayi ma Dr Ali Transfer din kudin, tare da basu go ahead din yin aikin.


Hankalin Mancy da Dalo ya kasa kwancia, sun kasa daurewa sai kuka suke, Alhaji Abu yace "Ku shirya ku bi jirgi gobe, sai Jawad ya rakaku".
Mancy ta dan ji sanyi, don gobe da sassafe zasu tafi, duk nadama ta mata katutu, bata ganin laifin kowa sai nata, itace sila, da bata barsu a Kt ba, da baiyi shaye shaye ba, da bai jama kanshi cuttutikan zamani ba, laifinta ne, in ta rasa Zaid yanzu bata san ya zatayi ba.
Alhaji Abu ya cigaba da kwantar mata da hankali yace "InshaAllah komai zai wuce, zai warke, Allah zai tada kafudunshi.


Bayan an gama komai ance su shirya kasancewar taci Abinci shima yaci suka kara 5hrs kafin su yi aikin, sai gab da Asuba zaayi aikin.
Zaid ya dan runtsa, ita kam ta fito waje.
Zama tayi kan kujera tana tunani.
Tsoro ya dan kamata, data ga dai dagasken aikin zaayi, ba zata fasa abunda tayi niyya ba, ba kuma tayi nadaman zuwa katsina ba, amma In bata rayu ba bayan aikin? Ya kenan? In ta mutu fa? Iyayenta fa, ya kamata ta nemi yafiyarsu, gwara su san halin da take ciki k'ila adduarsu ta bita.
Da sauri ta kunna wayarta ta ga messages da yawa bata bude ko daya ba, ta shiga create message ta hau typing, tana yi tana kuka, ta kusa daukan minti talatin tana yi kafin tayi marking ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login